Wednesday, December 28, 2011

GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!!

Bayan sallama irin wadda addinin Musulunci ya koya mana "Assalamu Alaikum" da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai, nake gayyatar 'yan uwana maza da mata, yara da manya, dattijai da tsofaffi kai har ma samari da 'yan mata, taron kungiyar TSANGAYAR ALHERI na kasa baki daya, karo na II mai taken "KANO AGAIN 2012"

Za'a gabatar da laccoci guda a wurin wannan taro, wadda ta farko mai taken "Mahangar Musulunci game da sada zumunta a shafukan Yanar Gizo" Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shugaban hukumar rundunar Hizbah na jihar Kano zai gabatar. Sai lacca ta biyu mai taken "Cigaba da kalubalen da Yanar Gizo ta kawowa matasan Nijeriya" wadda Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq) mashahurin masanin Fasahar zamani, marubuci a shafin Kimiyya da Fasaha na jaridar Aminiya kuma malamin makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa dake shafin Yanar Gizo, zai gabatar. Sai sharhin wadannan laccoci daga bakin Malama Sadiya Adamu, shugabar kungiyar mata Musulmi reshen jihar Kano da kuma babban marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino.

Bayan wadannan laccoci akwai lambobin yabo da kungiyar zata raba ga wasu mutane, saboda irin jajircewarsu a bisa aikin alheri ga al'umma da kasa baki daya, sannan za'a bada irin wadannan lambobin yabo ga mashawartan kungiyar da kuma wasu daga cikin 'yayan kungiyar da suka yiwa kungiyar hidima ba dare ba rana domin ganin ci gaban kungiyar ta kowane bangare.

Za'a gudanar nan da wannan gagarumin taro a ranar Lahadi daya ga watan sabuwar shekarar miladiya (1st January 2012) a babban dakin taro na Sheikh Bashir El-Rayyah dake makarantar koyon harshen larabci (School for Arabic Studies [SAS]) Dake kan titin zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr. Ado Bayero. Da misalin karfe 11:00 Na safe. Uban taro Mai Girma Galadiman Kano, Alh. Tijjani Hashim.

A washe garin taron kafin komawar bakin da suka zo Kanon Dabo daga wasu jihohin a sassan kasar nan, za'a kai ziyara babban gidan Yari (Prison) na Kano sannan kuma za'a kaiwa Mai Girma Dan Masanin Kano Alh. Dr. Yusuf Maitama Sule ziyara girmamawa. Daga nan kuma sai a sallami baki kowa ya koma garinsu sai kuma wata shekarar idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.

Bashir Ahmad
Sakataren Riko na Kasa baki daya.

Thursday, November 24, 2011

HALIN BABBAN YARO (ABBA MUHAMMAD SAVIOLA)

Abba Muhammad Saviola, abokina ne kuma aminina ne. Allah ya hore masa iya sarrafa zance gami da mai dashi yayi dadi, wannan tasa yake jan hankalin 'yan mata da zarar ya samu damar magana dasu, wannan dalili yasa yake yiwa kansa kirari/lakabi da cewa ABBAN MAI RABO, wato duk macen da ta same shi a matsayin mijinta to itace mai rabon.

Abba babban yaro ne, wadda kalmar babban yaro a yaren samari da 'yan mata na nufin wani dan saurari kyakkyawa da yake da fafa da ji da kansa, ta bangaren iya mu'amala da ta shafi zamantakewa a tsakanin samari da 'yan mata.

Wata rana Saviola ya tashi da sanyin safiya aljihunsa babu ko kobo gashi a matsayinsa na babban yaro shi kansa ya tabbatarwa kansa ba girmansa bane ya fito yana fadin bashi da kudi. Babban tunaninsa a lokacin yadda zai samu kudin da zaiyi transpot daga hostel zuwa school, domin kuwa wannan yafi damuwa dashi ba ciki ba.

Can yana cikin wannan hali sai yaji karar shigowar sakon text a wayarsa dake cikin aljihu, yana duba sakon sai yaga sako ne daga banki ana sanar dashi an aiko masa da kudi a account dinshi. Nan take yayi wani bushasshen murmushi tare da tashi tsaye, anan ya fara tunanin yadda za'ayi aje bankin don dauko kudin, domin kuwa babu kudin da za'aje bankin dasu. A karshe ya yanke shawarar tafiya a kafa.

Isar sa bankin ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa son kowa kin Bashir Ahmad, tunda kuwa ya rasa, ta fito daga bankin. Abba komai girman budurwa bata bashi tsoron yi mata magana, kuma da zarar ta bashi dama to kuwa ya gama da ita. Kamar yadda na fada a baya. Hakan tasa bai nuna tsoro ko shakka ba, ya tunkari wannan budurwa tare da yi mata tambaya "Gimbiya don Allah nan ne Zenith Bank?" tayi murmushi ta amsa masa "eh nan ne" saboda kuwa tasan ba wannan magana ce a zuciyarshi ba, kawai dai yayi tambayan nan don ya samu daman magana da ita.

Da bashi amsa bata tsaya karin bayani ba sai tayi gaba, shi kuwa Abba maimakon ya shiga bankin tunda ya samu amsar tambayarsa, sai shi ma kawai yabi bayanta, da ta fuskanci ya biyo bayanta sai ta tsaya tace "Malam ko akwai wata tambayan ne"

Na takaice muku bayani dai, tuni Abba ya sanar da ita abin dake zuciyarshi, har ma yana kokarin karban phone number ta, sai anan ya tuna saboda farin cikin turo masa kudi da akayi a lokacin da yake bukatansu, ya bar phone din nashi a hostel. Aka kuma nemi takardar da za'a rubuta number ba'a samu ba, kawai sai yarinyar ta bude jakarta (Hand Bag) ta dauko sabuwar N1000, ta rubuta masa number a gefe.

Karka manta da cewa Abba babban yaro ne, mai son nuna isa da fafa. Sannan kuma ka tuna tashin da yayi a ranan ba tare da ko sisi ba. Da karbar wannan sabuwar one thousand maimakon ya jefa ta a aljihu sai kawai ya yage gefen da aka rubuta number, sauran kuma ya rinka yayyagawa yana wasa da su lokacin da suke tafiya da yarinyar zai rakata wurin da tayi packing din motarta.

Lalle Abba ya cika babban yaro, wannan abu da Abban yayi ba karamin kara burge tsaleliyar budurwar yayi ba, gami da kara sace sauran zuciyarta gaba daya. Bayan ta shiga mota sukayi sallama da alkawarin zai kirata da zarar ya koma hostel.

To fa, a karshe da Saviola ya shiga banki don amsar kudin da aka turo masa sai jami'an bankin suka tabbatar masa da cewa ai an samu matsala ne ba account dinsa akayi niyyar turo kudin ba, saboda haka ma tuni wanda ya turo kudin ya debe abinsa. Da farko har Abba ya bata rai, sai kuma ya tuno irin barazanar da yayi wa kyakkyawar budurwan nan kawai sai yaji farin ciki ya mamaye shi, har ma ya samu damar komawa hostel cikin kwarin gwiwa.

Kaji kadan daga cikin halayen manyan yaro.

A karshe ina jinjina ga babban yaro, Abban mai rabo kuma madugu uban tafiyar shafin DAUSAYIN MASOYA a shafin sada zumunta na Facebook.

NB: It is not true life story, it is just for joke.


Bashir Ahmad
bashirahmad29@yahoo,com
08032493020, 08050600160

Wednesday, October 26, 2011

JAMILAH TANGAZA: Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram

JAMILAH TANGAZA: Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram: Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akai. Dalili kuwa shine suna ganin muddin suka yi magana watakila ‘yan Bo...

Sunday, October 23, 2011

Ka Zama Mai Yunwar Ilimi, Ka Zama Mai Budaddiyar Zuciya - Steve Job

"Babu mai son ya mutu. Hatta wadanda ke ganin sun yi aikin kwarai ba su cika son su mutu ba, sai dole. Amma kuma babu
makawa, mutuwa ce masaukin da za ta tattaro mu duka. Babu wanda ya taba guje wa mutuwa
a baya. (Kuma babu wanda zai guje mata a gaba) haka lamarin ya kamata ya zama. Domin mutuwa ce abin da har zuwa yau duniya ba ta taba samar da irinta ba. Ita ce abin da ke kawo canji a rayuwa. Ita ce ke share tsohuwar al’umma don kawo sabuwa. A halin yanzu da nake muku wannan jawabi, ku ne sabuwar al’umma, amma nan ba da dadewa ba, watarana za ku zama tsohuwar al’umma, an share ku don kawo wata sabuwar ta maye gurbinku. Ku yi mini afuwa idan wannan
zance nawa ya firgita ku, amma wannan ita ce hakikanin gaskiya.

Rayuwarku ‘yan kwanaki ne takaitattu, don haka kada ku shagala wajen kwaikwayon rayuwar wani. Kada ku zama
‘yan abi yarima a sha kida. Kada ku yarda surutan wasu su hana ku bin shawarar da za ta fisshe ku a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne, ku zama masu juriya wajen bin abin da zai zama maslaha a rayuwarku da fahimtarku. Domin su ne kadai suka fi kowa sanin abin da kuke son ku zama. Duk wani abin da ba wannan ba, to, ya zo a bayanshi".

Wannan wani gutsuren jawabi ne, daga cikin wani dogon jawabi da marigayi Steve Job, shugaban Kamfarin kera kayayyakin sadarwa na Apple Inc., ya gabatar a ranar bikin yaye dalibai na Jami'ar Stanford "STANFORD COMMENCEMENT ADDRESS" a watan June na shekarar 2005.

Inda a karshen jawabin nasa ya kara da cewa "Ka zama mai yunwar ilimi. Ka zama mai budaddiyar zuciya. Kuma a kullum nakan yi wa kaina wannan fata. Don haka na ga dacewar yi muku wannan fata ku ma, a daidai wannan lokaci da kuke kokarin fara wata sabuwar rayuwa bayan barin Jami'a, cewa: "Ku zama masu yunwar ilmi a kullum. Ku zama masu budaddiya zuciya wajen karbar fahimta" Nagode matuka!!!

Saturday, October 22, 2011

Tafiya Mabudin Ilimi (Bashir Ahmad a Sokoto Birnin Shehu)

Gaskiyar Hausawa da suka ce "Tafiya Mabudin Ilimi" duk da na yarda da hakan, amma ban gama tabbatarwa ba, ko nace ban taba jarrabawa ba, sai lokacin da nayi tafiya daga Kano zuwa Sokoto. Taron kungiyar Dandalin Siyasa e-Forum, karo na 3, Tafiyar da ban tabayin mai nisanta ba, a tarihin rayuwata, sai dai kuma nan gaba idan Mai duka ya barmu da rai da kuma lafiya.

Wannan tafiya tawa, mai kunshe da kalubale, alfahari, ilimi gami da abubuwan al'ajabi, nayi tane ranar 14 October zuwa 16 October 2011. Tabbas wannan tafiya ko shakka babu, ta shiga cikin tafiyoyin da bazan taba mantawa dasu ba (Unforgetable Journey).

Da farko a ranar tafiyar na tashi daga bacci tun da sanyi safiya na fara shirye shirye, kamar mai barin kasar kwata kwata. Na fito daga gida misalin 7:56am ba tare dana kammala 'yan shirye shirye na ba, saboda ina tsoron kar mota ta tashi ta barni, kamar yadda aka tabbatar min za'a hadu 7:30am a tashi zuwa birnin Shehu 8:00am.

Na isa kofar shiga tsohuwar Jami'ar Bayero, inda za'a hadu, amma saboda Nigerian Time da wani bawan Allah yayi bamu tafi ba sai 9:00am. Abinka da sabon shiga, fara tafiyar ke da wuya na dakko mujallar MURYAR AREWA na fara karantawa don kar ko gyangyadi ya dauki ni a shige wani wuri ba tare dana kashe kwarkwatar idona ba. Bayan na gaji da karatun jaridar sai na dauki wayata, na shiga shafin sada zumunta na Facebook na rinka sanarwa da yan uwa da abokanan arziki halin da tafiyar tamu ke ciki. Su kuma suna taya mu adduar fatan alheri gami da sauka lafiya.

Can da tafiya tayi tafiya sai wayar ma na hullata a aljihu, nayi zuru na zubawa sarautar Allah ido, wato dai na gaji kenan amma saboda tsegumi irin nawa, ko kadan ban nuna gajiyar ba, balle na kishin gida har bacci ya samu damar kwashe ni.

Nasan masu karatu ku kanku kunsan a wannan tafiya idanuwa na sun sha kallon abubuwan da ba sai na tsaya ina bata bakina wurin lissafa muku su ba, kai zahirin gaskiya ma dai idan nace zan lissafo zan iya yi muku ragi, don haka zan fadi wasu abubuwa guda biyu zuwa uku da suka fi daukar hankalina. Na farko naga shimfida shimfidan tituna amma ba motocin yawatawa akansu a jihar Katsina. Na biyu naga wani rusheshen dutse a jihar Zamfara, wanda idan mutum ya nemi kallo tsayinsa to tabbas hular zata fadi kasa ba tare da ya sani ba. Abu na uku shine karamcin da Sakkwawa sukayi mana, wanda bazan taba mantawa ba.

A takaice dai bamu isa cikin birnin Shehun ba, sai misalin 3:36pm, kai tsaye aka wuce damu, Sokoto Guest Inn, wanda shine masaukinmu. Kai mutane Sokoto akwai iya karbar baki sai kace wadanda suka zo Kano suka dauki darasi, domin kuwa da isarmu ba abinda suka tarye mu dashi sai wani daddadan kilishi hade da sassanyan lemo. Kasan Bakano bai da filako nan take muka tashi da wannan hidima.

Misalin 9:30pm na wannan rana, aka debe mu cikin zungureriyar mota, zuwa wurin wani shakatawa mai suna Daddy's Smart dake cikin birnin na Shehu, domin gabatar da Cultural Night wanda kungiyar ta Dandalin Siyasa ta shiryawa 'yayanta domin debe kewa. A wannan wurin na sha dariyar da tayi kusan sa cikina ciwo, domin kuwa tsohon dan wasan Hausan nan na barkwanci Golobo (Boloko) shine ya cashe tare da jama'arsa.

Washe gari ranar 15 October, ranar da aka ware don yin taron, mun tashi mun shirya, sannan muka nufi wurin da za'a gabatar da taron a dakin taro na makarantar koyon karatun Al Kur'ani da Kimiyya na Muhammad Maccido, amma kafin a fara gabatar da laccocin da za'a gabatar sai da aka kai ziyarar girmama fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III. Bayan an dawo daga fada sai aka koma wurin taron.

An gabatar da laccoci a wurin taro wadanda suka shafi halin da kasarmu Nigeria ke ciki a halin yanzu, kamar irinsu TABARBAREWAR TSARO, ILIMIN BOKO, sai kuma DEMOCRADIYA wanda Prof. S. A. Yakasai na jami'ar Shehu Usman Danfodio da kuma Dr. Usman Muhammad na jami'ar Birnin Tarayya Abuja suka gabatar.

An kammala taro misalin 3:30pm, daga nan bayan an gabatar da sallar La'asar sai kuma aka tafi kai wata ziyarar girmamar gidan Alhaji Abubakar Alhaji (Alhaji Alhaji) Sardaunan Sokoto na yanzu, dattijon arziki, namiji uban masu kudi da 'yan boko. An gabatar masa da kungiya, ya kuma yi farin ciki gami da karfafa gwiwa.

Sai kuma wajen 9:30pm aka tafi wurin dinner a Mr Bigs wanda aka kai har zuwa 11:30pm daga nan kowa ya tafi masaukinsa. Kuma wannan shine abu na karshe da aka shirya gabatarwa a taron.

Washe gari ranar 16 October rana ce da duk wanda yaje birnin na Shehu zai waiwayi inda ya fito, a ranar ne muma da misalin 9:30am muka kama hanyarmu ta dawo gida Kanon Dado mai mata mai mota mai Dala da Goron Dutse.

A karshe ina kara mika godiyata ga dukkan SAKKWATAWA wadanda suka dauki dawainiyarmu tunda muka je har muka dawo gida. Allah yasa da alheri, Allah ya kara hada fuskokinmu da alheri, ameen!

Wednesday, October 12, 2011

Ibada ko Siyasa? Sunan Kwankwasiyya a Gidan Alhazan jihar Kano a birnin Makkah

Hausawa suka ce wai "Sabon salo kidan ganga da lauje" kullum siyasar kasar nan sai zama take yi gara jiya da yau, misali idan yau wannan mai mulki wa'adinsa ya kare wani kuma ya karba, sai kaga talakawa na murnar an samu canji, amma da zarar wanda ya hau an fara ganin rikon ludayinsa sai kaji talakawan sun dawo suna fadin ai gara na jiya dana yau. Ko me ke kawo haka oho. Ko kuma mu duk haka muke Nigeria ba'a zuciyarmu take ba, bama son canji da ci gabanta, mun fiso mu zauna kurar baya kodayaushe, Allahu a'alamu.

Ba komai ne ya sanin fadin hakan ba, sai ganin yadda masu mulki ke wuju - wuju da shafawa talakawa jan baki, ba tare da suna sara suna duban bakin ga tarinsu ba. Anan zanyi misali da siyasarmu ta jihar Kano, wadda masu iya magana ke yiwa lakabi da "Siyasar Kano Sai dan Kano" A lokacin da tsohon gwamna, wadda ya mayarwa da sabon gwamna dake kan karagar mulkin jihar yanzu, bana mantawa duk lokacin daya gudanar da wani sabon abu musamman a bangaren addini, sai kaji ana kiran wai ai fakewa yake da addini yana wawashe kudaden talakawa.

To sai gashi yanzu bayan shudewar tsohuwar gwamnatin, masu shafa jan baki da jar hula suka cigaba da jan ragamar gwamnatin, sai suma suka shigo da sabon salo kala - kala. Wanda duk abin dake faruwa ba wanda ya bani mamaki kamar wannan. Abin mamaki shine kuwa yadda itama sabuwar gwamnatin ke neman aron mayafin tsohuwar gwamnatin ta yafa, wato itama ta fake da addinini ta wawashe kudaden talakawa. Domin kuwa hatta a bangaren aikin Hajjin bana ma sai da gwamnatin tasa siyasa a ciki. Saboda a gidan da alhazan jihar Kano ke yada zango a birnin Makkah sai da aka rubuta KWANKWASIYYA HOUSE da baro - baron rubutu yadda ko makaho ya shafa zai ji alama. Ba a iya nan sabuwar gwamnatin ta cuso harkokin siyasa ba, bangaren aikin Hisbah da kwamitin Shari'a ma duk haka abin yake.

A karshe ba ina kare wani bangare bane, ko goyan baya tsakani wadannan gwamnatotin biyu, kawai ina son na aika wani sakona ne zuwa ga wadanda abin ya shafa don susan tuni mun gane duk wani shiri da suke yi don wawashe dukiyar talakawa.
Fatanmu Allah ya bawa wannan sabuwar gwamnati ta masu jar hula karin gwiwar yi mana aiki da kawowa jiharmu ci gaba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Sunday, October 9, 2011

Muhimman Shafukan Gidajen Yanar Gizo domin karuwar Musulmai

Yanar gizo (Internet) a wannan zamani ta zama abokiyar rayuwa, wanda masu amfani da ita ba zasu iya koda kwana daya ba tare da sun kai ziyara ba, sai dai da wani kwakkwaran dalili, kamar rashin lafiya ko rashin service. A wani bincike da masana suka gabatar a wannan zamani jama'a sunfi cinye lokacinsu a wurin amfani da Yanar Gizo sama da komai. Wasu na cinye lokacin nasu a bincike bincike da kalle kalle marar amfani, wasu kuma basu da aiki sai neman abokan hira daga sassan duniya daban - daban, wasu kuma Allah ya taimake su, suna cinye lokacin nasu ne akan karin neman ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci.

Ga duk masu sha'awar amfanar lokacin a duniyar yanar gizo ga shafuka masu muhimmanci domin Musulunci da Musulmai:-

Islami City (http://www.islamicity.com) - shafi ne daya kunshi abubuwa masu yawan gaske kamarsu bayani game da Shika-shikan Musulunci, Lokutan sallah, litattafai da sauransu.

Qur'an Complex (http://www.qurancomplex.org) - shafi ne da tsohon sarkin kasar Saudi Arabia King Fahaq bin Abdallah ya samar dashi game da Al Qur'an Mai girma.

Fatwa Islam (http://www.fatwaislam.com) - shafi ne dake cike da fatawoyin manya manyan Malam na da dana yanzu. Sannan kuma mutum zai iya tura fatawarsa a dawo masa da amsa nan take.

Islam Online (http://www.islamonline.com) - wannan shafi ne daya danganci bangaren labarun abubuwan dake faruwa a duniyar Musulunci. Sai kuma hira ta keke da keke (Video Chat) tsakanin Musulmai dake sassan duniya daban - daban.

Islam Question & Answer (http://islamqa.com) - shafi ne dake kunshe da tambayoyi da amsoshinsu dangane da abubuwan da suka shigewa Musulmai duhu.

Ja'afa Mahmud Adam (http://www.jaafarmahmudadam.org) - wannan shafin na kunshe da wa'azin Marigayi Malam Ja'afar Mahmud Adam da kuma fatawoyinsa.

Haruna Yahya (http://www.harunyahya.com) - Shafin haziki kuma fasihi Harun Yahya wannan yake bayani game da kimiya da fahasa, a mahangar Musulunci.

Idan kuma mutum yana neman wani abu bai samu ba, a cikin wadannan shafuka dake sama zai iya ziyarta shafin bincike na Google don bincikowa. Allah ya kara taimakon addinin Musulunci da Musulmai baki daya.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Friday, October 7, 2011

Lokaci ne babban makiyinmu ba Mutuwa ba

Mutuwa ita ce karshen duk wani abu da Allah (SWA) Ya halitta, mutum, aljan, dabbobi da sauran halittu na ciki ruwa, na doron kasa har ma dana sararin samaniya. Mutuwa na dauke mutum ba dare da saninsa ba, ma'ana ko ya shirya ko bai shirya ba. Kuma bata son kai, wato ta dauki talaka tabar mai kudi, don tarun dukiyarsa, ko tadauki mai kudi tabar talaka don jin tausayinsa. Bata barin yaro bare babba, bata barin mace bare namiji. Ita ke raba 'yayan da iyayensu, ba tare da tayin la'akari da halin da zasu shi ba. Ita ke raba ango da amarya duk kuwa da irin soyayyar dake tsakaninsu. Saboda kuwa bata sabawa umarnin mahaliccinta kuma mahaliccinmu Allah daya.

Wasu mutanen na ganin mutuwa bata da tausayi ko kuma itace babbar makiya a gare mu, musamman a wurin mutanen da ta dauke musu iyaye tabarsu cikin watangaririya, halin kuncin rayuwa, da rashin kulawa ta musamman.

Gaskiya ni a tunanina, mutuwa bata da laifi ko kadan, idan ka hada ta da LOKACI, domin kuwa shi ke tura mutum koyaushe kusa da mutuwa har ta dauki shi. Da zarar an haifi mutum duk wani dakika (second) daya da yayi, to lokaci yana kara kusan tashi da mutuwa ne. Mutuwa bata zuwa ta dauki wani har sai lokaci ya dauke shi ya kaita wurinta, wato sai wa'adinsa (lokacinsa) yayi. Ga shi lokacin kullum kara gudu yake, Shekara ta zama kamar wata, wata ya zama kamar sati, sati kuma kamar kwana. Kuma babu yadda zamuyi mu tsayar da gudun lokacin ko murage shi. Lalle karshen duniya ya zo.

Ta hanya daya zamu ci ribar wannan lokaci tun kafin ya kaimu ga mutuwarmu, wannan hanya itace mutattara rayuwarmu gaba daya mu koma kan Al-Kur'ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Muyi kokarin ganin kar dakika daya ta wuce ba tare da munyi amfani da ita ta hanya mai kyau ba. Koyaushe ya zamana ace bamu da lokacin daya fi na bautar Allah ko neman ilimin yadda za'a bauta masa. Idan mukayi haka to munci ribar lokaci.

A karshe karmu manta duk dakika daya da tawuce bazata sake dawowa ba har abada. Mu daina cinye lokacinmu, wurin kalle kalle marar amfani. Yi amfani da lokacin da kake cinyewa a shafukan Internet ta hanya mai amfani. Yawaita ziyartar shafukai fatawoyin addinin Musulunci dan karu da abinda baka sani ba. Maimakon karanta tarihin manya manyan kafirai makiya Allah, makiyanmu mu Musulmai binciko tarihin manya manyan malamai da suka bada muhimman gudunmawa a addinin Musulunci.

Allah yayi mana jagora a dukkan al'amuranmu na yau da kullum. Ya bamu ikon yin amfani da lokacin daya bamu ta hanyar bauta masa bata hanyar saba masa ba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Tuesday, October 4, 2011

Labarin Sarki da Babban Amininsa mai taken "Yayi Kyau"

Abu-asid-az-zinayya, sarki ne dake mulkin daular Zinayya a can kudu maso gabashin sahara, wato bangaren tekun Nilu daga bangaren dama.

Abu-asid ya kasance sarki mai adalci ga al'ummar da yake mulka, ga tausayin talakawa da karrama baki, wannan dalili yasa koyaushe baki sai tururuwar zuwa wannan kasa suke yi, wasu na zuwa domin fatauci, wasu kuma na zuwa don yawon bude ido da shakatawa.

Sarki Abu-asid mutum ne mai sha'awar fita farauta tun yana karami, hakan tasa bayan ya hau kujerar sarauta mai bai daina fita wannan farauta ba. Yakan shirya fita yawon farauta lokaci - lokaci don debe kewa da nishadi, koyaushe idan zai tafi farauta suna tafiya ne da abokinsa mai suna Usudul-azman, wanda suka taso tare tun lokacin kuruciya. Saboda saukin kan sarki Abu-asid daya zama sarki ma bashi da abokin zuwa farauta da shawara kamar shi. Usudul-azman yana da wata dabi'a da ta zame masa jiki, wanda shi duk abinda ya faru a gare shi mai kyau ko akasin haka sai yace "YAYI KYAU"

Wata rana sarki da abokinsa sun fita farauta, sai suka ci karo da barewa, a kokarin harbin wannan barewa, sarki bai seta bundigar daidai ba, hakan ta jawo ya harbi hannunsa na hagu, nan take babban dan yatsan sarki ya fadi kasa cikin jini. Duk da irin wannan hali da sarki ya tsinci kansa, budar bakin Usudul-azman abokin sarki, sai yace "YAYI KYAU" Nan take sarki cikin fushi da kunan rai, yana gurnani kamar tsohon zakin da ya shekara baici nama ba yace karya ne baiyi kyau ba.

Saboda wannan magana da Usudul-azman ya fadawa sarki, bayan sun dawo daga farautar, sarki yayi umarnin a kaishi gidan kurkuku a daure shi, kowa yayi mamakin wannan hukunci na sarki, domin kuwa ba'a taba gani ya yiwa wani bawansa irin wannan hukunci ba tare da yin wani laifi ba, bare kuma Usudul-azman babban amininshi. Haka dai kowa ya gama fadin albarkacin bakinshi yayi shiru, domin ba mai iya zuwa yace sarki bakayi daidai ba.

Bayan kusan shekara daya da faruwar wannan al'amari, sarki yana cikin wani kungurmin daji mai nisan gaske yin farauta, wanda duk jarumtaka irin tashi amma hankalinshi bai kwanta da wannan daji ba. Kwatsam! Sai jin ihun arnan daji yayi ta gaba da bayansa, kafin yayi wani kokarin kubuta daga wurinsu tuni sun kamashi, suka daddaure shi hannu da kasa, suka nausa cikin daji dashi, sun ihun samun nasara. Da isarsu gida aka fara shirye - shiryen watanda, daman kuwa sun dade basu ci naman mutum ba sai dabbobi. A lokacin da sarkin wannan arnan daji yazo yanka sarki sai ya gane ashe babban dan yatsansa na hannun hagu ya gutsere. Nan take cikin bakin ciki yayi kururuwa yace ba cikakke bane, wato wani bangare daga jikinsa bai cika ba. Kuma daman a al'adarsu idan suka kama mutane da nakasa a jikinshi basa ci, nan take sarkin nasu ya bada umarni a sake shi ya kama gabansa.

Tun akan hanya sarki Abu-asid ya tabbatar lalle maganar da amininsa, Usudul-azman ya fada lokacin daya harbi hannunsa abune mai kyau, domin kuwa da badon hakan ba da tuni anyi wadanta da namansa yau. Saboda haka yana isa gida yayi umarnin a saki abokin nashi, kuma ace yana son yin magana dashi. Bayan Usudu ya fita sai yazo wurin sarkin don jin mai ya faru. Sarki ya fada masa duk abinda ya faru gare shi, kuma ya roki afuwar abokin nasa saboda sawa da yayi a daure shi.

Budar bakin Usudul-azman sai yace "YAYI KYAU" Nan sarki ya tambaye da mai yake nufi da hakan? Kai da kasha wahala a kurkuku amma kace yayi kyau? Sai Usudu yace "eh mana da badon ina cikin kurkuku ba da tuni ni anyi watandar nama na, saboda da tare da ni za'a kama mu, kuma ni cikakke ne. Nan sarki shima da kansa yace lallai "YAYI KYAU"

Wednesday, September 14, 2011

Lambar Mutuwa 09141 Karya ko Gaskiya?

Duk mutumin da yace kace bai ji labarin jita-jitar 'Lambar Mutuwa' ta 09141 a yau 14 September 2011 kai tsaye zance shi ba dan asalin Nigeria, ko kuma nace baya kasar a halin yanzu.

Wannan jita jita ta lambar mutuwa ta cika shafukan yanar gizo, inda ake cewa idan an kira mutum da lambar 09141 a wayar tafi da gidanka kuma ya amsa kiran nan take zai mutum, hakan tasa aka sawa lambar suna 'The killer number' wato lambar mutuwa.

A irin wadannan jita jita akwai wadda ake cewa wai mutane sama da 10 sun mutu sakamako amsa kiran da sukayi daga wannan lamba ta mutuwa a karamar hukumar Wukari dake Jihar Adamawa, duk da har yanzu babu tabbacin hakan daga majiya kwakkwara.

Duk da a matsayinmu na Musulmai mun tabbata babu mai kashewa da rayawa sai Allah don haka ko kadan ba zamuyi imani da cewa wannan lamba ce ke kisan ba, sai mu yarda idan itace sanadin mutuwar mutum to tabbas sai ya mutum koda idan an kira shi da ita bai amsa ba, saboda haka ya kamata muke lura da irin mu'amalar da zamu ke yi da mutane musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo. Kowa dai yana sane da irin yadda matsafa suka cika irin wadannan shafuka, kuma wannan lamba ko shakka babu tsafi ne.

Wasu kuma na ganin kawai wani ne ya zauna ya kirkiri jita jitarsa ya rinka yadawa, domin lambar da ake amfani da ita tayi daidai da kwanan wata da shekarar da muke ciki a yau. Misali 09 = September 14 = Kwanan watan 1= 2011. Ko ma dai menene fatanmu Allah ya kare Musulunci da Musulmai duk inda suke a fadin duniya.

Don Allah ka sanar da wanda bai sani ba! Save innocent life!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020

Manyan Matsalolin Dake Addabar Ilimi a Arewa

Ilimi ba karamin muhimmanci da dajara ke gare shi ga al'umma maza da mata, yara da manya ba, domin da ilimi ne zamu koyi yadda zamu bautawa Ubangiji mahaliccinmu. Ilimi shine kashin bayan duk wata kasa da ta cigaba ta bangaren tsaro ko tattalin arziki, da ilimi ne zamu koyi zaman duniya da mutane daban daban, ba tare da kowa na gaba da kowa ba, da ilimi ne ake banbance abu mai kyau da marar kyau, sannan ilimi ne ke bawa likitoti damar duba marar lafiya har su gane me ya dame shi, kuma su bashi magani ya samu lafiya da taimakon Allah.

Duk da irin wannan muhimmanci na ilimi, da irin rawar da yake takawa ga zamantakewar al'umma, amma abin mamaki da haushi gwamnati da sauran al'umma sun kasa maganin matsalolin dake addabar ilimin musamman a wannan yanki namu na Arewa, kadan daga cikin matsalolin sun hada da:-

Rashin kulawar da ta kamata daga gwamnati da sauran jama'ar gari, wannan rashin kulawa da ilimin baya samu ta wadannan bangarori, hakan ya kawo babban nakasu ga ilimin a Arewa.

Rashin tsayawa da iyaye basa yiwa 'yayansu wurin ci gaba da karatu na zamani a manyan makarantu, saboda lokacin da ilimin yazo yankin kakanmu na ganin za'a koyawa 'yayansu (Iyayenmu) addinin Kiristanci, wannan matsala har yanzu tana addabar ilimi a wannan yanki namu.

Wata babbar matsalar dake kara zama nakasu ga ilimin itace, shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma shan magunguna ba tare da ka'ida ba, irin wannan shaye shaye na lalata hanta, hunhu, koda da kwakwalwa, wanda a sakamakon haka matasa ke rasa hankalinsu. Abin haushin kuma wannan shaye shaye daga maza har mata ba'a bar kowa a baya ba. Sannan wannan matsala ita ce jijiyar duk wata fitina a wannan yanki, gami da munanan dabi'u da halaye irinsu, Fashi da makami, fadan kabilanci, gaba tsakanin matasa, da sauran abubuwa mararsa dadi.

Sai kuma matsalar satar jarrabawa, ita ma wannan matsala ce dake addabar ilimi, satar jarrabawa wani bangare ne na cin hanci, da mafiya yawan daliban da basu mai da hankalinsu akan karatu ba ke yi a wannan zamani. Hakan tasa matasa da dama basa samun aikin yi bayan gama karatu, daga nan kuma sai su shiga sahun masu shan miyagun kwayoyi.

A karshe mafita ga wadannan matsaloli sune: Gwamnati take bada gudunmawa mai tsoka ga bangaren ilimin, kamar yadda kasashen da suka cigaba ke ware kaso mafi tsoka ga bangaren ilimi daga cikin arzikin kasashen. Sannan ake tantance malamai wurin daukarsu domin koyarwa a makarantu.

Wayar da iyayenmu musamman na karkara da suke barin 'yayansu suna tafiya manyan makarantu don samun ilimi mai zurfi, a bangaren kimiya da fasaha, tattali, ilimin noma, na'ura mai kwakwalwa da sauransu.

Attajirai suke taimakawa yara masu basira, wadanda iyayensu basu da halin daukar nauyin karatunsu zuwa makarantun gaba da sakandare ko wurin siyen litattafan kimiya masu tsada.

Koyar da wani darasi koda daga makarantun firamare ne zuwa karamar sakandare game da kishin kasa, da bada labarun wasu jarumai da irin gwagwarmaya da wahalhalun da suka sha wurin nemawa kasashensu 'yanci da ci gaba.

Bude wasu santoti domin koyawa masu rubuta jarrabawar karshe ta NECO da WAEC yadda tsarukan jarrabawar yake da yadda ake amsa tambayoyi, hakan zai kawo raguwar faduwa jarrabawar da ake yi a wannan yanki namu na Arewa.

Allah ya kara daukaka wannan yanki, ya kawo masa zaman lafiya a lungun da sakon yanki dama kasarmu Nigeria baki daya.

Bashir Ahmad
Sakataren Kungiyar Tsangayar Alheri
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Tuesday, September 6, 2011

Tsangayar Alheri ta kai ziyara da bada taimako ga Gidan Marayu

Kungiyar Tsangayar Alheri ta shafin sada zumunta na Facebook a duniyar yanar gizo, ta kai ziyara Gidan Marayu (Children's House) dake Nassarawa a birnin Kano, ranar 3/9/2011. Bayan makamanciyar ziyarar da kungiyar ta kai Asibitin Kananan Yara na Asiya Bayero a watan daya gabata.

Abdulkadir Sardauna, shugaban kungiyar ta Tsangayar Alheri ya bayyana makasudin shirya wannan ziyara da kungiyar tayi, da cewa ziyara ce domin ganin halin da 'yan uwanmu kuma 'yayanmu ke ciki, da kuma ganin yadda suke kudanar da rayuwarsu ba tare da kulawar iyayensu ba, duk da suna lokacin da suka fi bukatar kulawar iyayen fiye da komai.
Shugaban ya kara ma cewa Tsangayar Alheri ta dauki alwashin bayyanawa duniya halin da wadannan yara marayu ke ciki da kuma irin taimako da suke bukata, ta shafukan kungiyar take Facebook da Yahoo Groups.

Wannan ziyara ta samu rakiyar wasu kungiyoyi masu akida irinta Tsangayar Alheri, kamar kungiyar Gizago Club, karkashin jagorancin Nura Adamu Ahmad. Sai kungiyar Youth Mobilazation via Media karkashin jagorancin Salisu D. Toll. Da kuma Woman Enlightment and Enpowerment Organization, karkashin jagorancin Fatima A. Dala. Kuma wadannan kungiyoyi suma ba'a barsu a baya ba wurin bada taimako ga wadannan Marayu.

A jawabinsa, Shugaban gudanarwar gidan Yaran, ya bayyana cewa a halin yanzu suna da yara tamanin da takwas (88) maza da mata, ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga wurin gwamnati, kamar wurin kula da karatun yaran. A karshe ya mika godiyarsa ga al'ummar da suka kawo wannan ziyara, sannan ya kara mika godiyarsa ga Asibitin Nassarawa da yake bawa duk wani yaro marar lafiya magani kyauta.

Daga karshe shugaba Abdulkadir Sardauna ya mika taimakon da wannan kungiyar ta bayar ga wadannan yara Marayu. Sannan kuma aka hadu aka dauki hotuna kafin kowa ya kama gabansa.

A karshe ina kira da al'umma da su irinka kai irin wadannan ziyara ko ba zasu bada komai ba, hakan zai sa yaran farin ciki, domin ganin ana sane dasu, sannan irin wannan ziyara zata karawa masu imani karfin imani a zuciyoyinmu, da kara godiya ga Allah da ya barmu tare da iyayenmu badon dabararmu ko don mun fi su ba.

Bashir Ahmad
Sakataren kungiyar
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Tuesday, August 30, 2011

Barka Da Sallah Daga Bashir Ahmad

A yau ne (30 August 2011) daukakin al'ummar Musulman Nigeria suka bi sahun takwarorinsu Musulmai dake sassan duniya daban - daban wurin gabatar da bikin Sallar Idi karama, bayan sauke azumin watan Ramadan.

Allah mai iko! Kamar ko yaushe an samu wasu 'yan tsirarun mutane da su kayi Sallar Idin su tun jiya, saboda sabanin ra'ayi. Abin mamaki wasu mutanen kuma sai gobe 31 August 2011 zasu gabatar da Sallar Idin tasu. Wannan ba shine farko ba, kusan kowane lokacin daukar Azumi da sauke shi hakan tana faruwa, saboda banbancin akida ko kuma rashin ganin wata bai dayawa, ko kuma wasu idan basu ga watan da idonsu ba basa yarda su dauki Azumin ko sauke shi. Fatanmu dai Allah ya kawo mana hadin kai a addininmu na Musulunci, wadda zai kawo samuwar magana da murya daya. Amin!

A karshe zanyi amfani da wannan dama na mika sakon taya murna da barka da shan ruwa ga ilahirin 'yayan kungiyoyin Tsanyarar Alheri, Muryar Talaka, Zauren Shawara Facebook, Gizago Club, Dandalin Siyaya, Nigerian Youth Forum, da sauran kungiyoyin matasa da suka sadaukar da kawunansu wurin fafutukar ganin cigaban kasarmu abar alfarinmu Nigeria.

Duk da tuni na mika wannan gaisuwa tunda da sanyin safiya amma zankara mika wannan gaisuwa a yanzu saboda muhimmancinta ga dukkan abokanaina da nake zaune tare dasu, a gida da makaranta, sannan ga daukakin abokaina dake shafukan sada zumunta na yanar gizo musamman na shafukan Facebook, Twitter, 2go. Bazan taba mantawa daku ba masu ziyartar matattarar tunani wato DANDALIN BASHIR AHMAD. Nagode! Allah ya saka muku da alheri abokaina, ko yaushe addu'ata a gare ku itace Allah ya biya muku bukatunku na Alheri.

Allah ya karbi ibadunmu na watan Ramadan, Allah yasa muna cikin bayin da aka 'yanta akayi musu gafara. Allah ya maimaita mana. BARKA DA SALLAH!

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
+2348032493020

Tuesday, August 23, 2011

Abin mamaki ko abin dariya? Sa'insa tsakanin Obasanjo da Babangida

Chief Olusegun Obasanjo, da General Ibrahim Badamasi Babangida tsofaffin shugabannin kasar nan ne, kuma suna daga cikin dattawan kasar nan da ake ganin girmansu saboda irin mukaman da suka rike da kuma gwagwarmayar da suka sha game da yakunkunan basasar kasar nan, da kuma kokarinsu na ganin kasar ta zauna a matsayin tarayya guda mai cikakken iko.

Abin mamaki ko nace abin dariya duk da dattijantaka irin ta wannan bayin Allah wadanda duk sun haura shekaru 60 a duniya, amma bai hana barkewar zazzafar sa'insa a tsakaninsu ba, ko sun manta da cewa 'yayansu dasu zasuyi koyi oho.

Obasanjo ya bayyana Babangida a matsayin wawa a shekaru 70, kuma bai amfanarwa kasar nan komai ba a shekaru 8 da yayi na mulkin soja. Dalilinsa kuwa, yace yayi amfani da izu na 26 aya ta 4 da ta 5 na cikin littafin Karin Magana (Proverbs).

Shi ma Babangida ya bayyana mulkin da Obasanjo yayi tsakanin 1999 zuwa 2007 ba za'a kira da komai ba sai bata lokaci domin kuwa bai tsinanawa kasar nan komai ba sai ci baya. Ya kuma bayyana Obasanjon a matsayin mai karancin tunani da hangen nesa.

Nan shi ma Obasanjon ya cigaba da cewa IBB yana da damar gina tashoshin wutar lantarki, lokacin da yake kan mulki, saboda irin kudin da kasar ke dasu a lokacin, kamar yadda shi ya gina Jebba dam, da Shiroro dam kuma ya fara shirin gina Egbin wanda Shehu Shagari ya gina a lokacin mulkinsa.

Obasanjo yace "Na gina dam guda biyu saboda muhimmancinsa, kowa yasan wutar lantarki ita ce kashin bayan ci gaban duk wata kasa mai tasowa. Tun lokacin da aka gina tashar Egbin har na dawo mulki a 1999 babu wata tasha wutar lantarkin da aka sake ginawa, kusan shekaru 20 kuma Babangida yayi shekaru 8 a lokacin yana mulki, wannan ba karamin rashin cigaba bane.

Bayyana mulkina na 1999 da 2009 da IBB yayi a matsayin bata lokaci da koma baya, ya kamata ya nemi afuwar fadin hakan. Na karanta inda yake cewa a lokacin mulkinsa ya bada ribar demokradiya, duk da ya nuna nadamarsa, to amma masu iya magana na cewa wawa a shekaru 40, wawa ne har abada. Ni kuma nace nadama a shekaru 70, makararriyar nadama ce, kuma nadama ce ta kabari".

A martanin da Babangida yayi ta bakin mai magana da yawunsa, Prince Kassim Afegbua yace "wannan ba dabi'ar Babangida bace ya shiga irin wannan sa'insa marar ma'ana. Tarihin Obasanjo a bude yake, lokacin da ya roki IBB ya bashi damar kara wa'adin mulkinsa, IBB ba wawa bane sannan. Lokacin da aka sake shi daga kurkuku, aka yi masa wanka aka bashi kayan alfarma ya saka a karshe ya zama shugaban kasa, IBB ba wawa bane sannan, sai yanzu da yakai kololuwar tunaninsa, zai cirewa IBB zani a kasuwa, ya kira shi da wawa"

Anan dai ya kamata talakawan Nigeria wadanda suka ga mulkin wannan dattijai guda biyu suyi alkalancin wanene wawa, Babangida ko shi kansa Obasanjon?

A matsayina na wanda naga mulkin Obasanjo na 1999 zuwa 2007, idan nine alkali zan kira Obasanjo ne wawan ba IBB ba, idan nayi duba da irin mulkin kama karyar da ya shinfida a kasar nan. Yayi ikirarin ya gina tashoshin bada wutar lantarki guda biyu a mulkinsa na soja, amma kuma ya zo ya lalata wutar kasar nan a mulkinsa na farar hula, shin wannan ba wawanci bane? Ya zo ya samu man fetur a kasa da naira 30 lita daya, ya maida shi sama da naira 60, shin wannan ba wawanci bane? Ya zo ya samu kasar nan da tsaron da kasashen waje ma na tsoronsa, amma ya kori manyan sojoji, ya lalata tsaron, idan su al'ummar kasar ma ke masa barazana, wannan ba wawanci bane?

Amma kuma kai tsaye ba zance Obasanjo wawa ba, saboda ko kadan bansan yadda shi IBB ya gudanar da nasa kalar mulkin ba ko nace nasa kalar wawancin. A wannan sa'insa aikinmu kadai kallo, inda akayi abin dariya, muyi dariya. Inda akayi abin mamaki, muyi mamaki. Inda akayi abin haushi muyi Allah wadai.

A karshe, fatanmu Allah ya kawowa kasarmu dauki. Ya fatattaki duk wasu azzalumai, Ya canja mana adalai a madadinsu.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Sunday, August 21, 2011

Rebel entered Tripoli and Gaddafi's son has been captured by forces

Rebel fighters streamed into
Tripoli as Muammar Gaddafi's
forces collapsed and crowds
took to the streets to celebrate,
tearing down posters of the
Libyan leader.

A convoy of rebels entered a
western neighborhood of the
city, firing their weapons into
the air. Rebels said the whole of
the city was under their control
except Gaddafi's Bab Al-Aziziya-
Jazeera stronghold, according to
al-Jazeera Television.

Gaddafi made two audio
addresses over state television
calling on Libyans to fight off the
rebels.

"I am afraid if we don't act, they
will burn Tripoli," he said. "There
will be no more water, food,
electricity or freedom."

Gaddafi, a colorful and often
brutal autocrat who has ruled
Libya for over 40 years, said he
was breaking out weapons
stores to arm the population. His
spokesman, Moussa Ibrahim,
predicted a violent reckoning by
the rebels.

"A massacre will be committed
inside Tripoli if one side wins
now, because the rebels have
come with such hatred, such
vendetta...Even if the leader
leaves or steps down now, there
will be a massacre."

NATO, which has backed the
rebels with a bombing campaign,
said the transition of power in
Libya must be peaceful.
After a six-month civil war, the
fall of Tripoli came quickly, with
a carefully orchestrated uprising
launched on Saturday night to
coincide with the advance of
rebel troops on three fronts.

Fighting broke out after the call
to prayer from the minarets of
the mosques.

Rebel National Transitional
Council Coordinator Adel
Dabbechi confirmed that
Gaddafi's younger son Saif Al-
Islam had been captured. His
eldest son Mohammed Al-Gaddafi
had surrendered to rebel forces,
he told Reuters.

Only five months ago Gaddafi's
forces were set to crush the
rebel stronghold of Benghazi, the
leader warning in a television
address that there would be "no
mercy, no pity" for his
opponents. His forces, he said,
would hunt them down "district
to district, street to street, house
to house, room to room."

The United Nations then acted
quickly, clearing the way for
creation of a no-fly zone that
NATO, with a campaign of
bombing, used ultimately to help
drive back Gaddafi's forces.
"It's over. Gaddafi's finished,"
said Saad Djebbar, former legal
adviser to Libyan government.
Al Jazeera television aired images
of people celebrating in central
Tripoli and tearing down posters
of Gaddafi, which had
dominated Libyan cities for
decades.

In Benghazi in the east,
thousands gathered in a city-
center square waving red, black
and green opposition flag as
news filtered through of rebel
advances into Tripoli.

"It's over!" shouted one man as
he dashed out of a building, a
mobile telephone clutched to his
ear. Celebratory gunfire and
explosions rang out over the city
and cars blaring their horns
crowded onto the streets.
Overhead, red tracer bullets
darted into a black sky.

"It does look like it is coming to
an end," said Anthony Skinner,
Middle East analyst, Maplecroft.
"But there are still plenty of
questions. The most important is
exactly what Gaddafi does now.

Does he flee or can he fight?"
"In the slightly longer term, what
happens next? We know there
have been some serious
divisions between the rebel
movement and we don't know
yet if they will be able to form a
cohesive front to run the
country."

Gaddafi, in his second audio
broadcast in 24 hours, dismissed
the rebels as rats.
"I am giving the order to open
the weapons stockpiles," Gaddafi
said. "I call on all Libyans to join
this fight. Those who are afraid,
give your weapons to your
mothers or sisters.

"Go out, I am with you until the
end. I am in Tripoli. We will ...
win."

A Libyan government official
told Reuters that 376 people on
both sides of the conflict were
killed in fighting overnight on
Saturday in Tripoli, with about
1,000 others wounded.

A diplomatic source in Paris,
where the government has
closely backed the rebels, said
underground rebel cells in the
capital had been following
detailed plans drawn up months
ago and had been waiting for a
signal to act.

That signal was "iftar" -- the
moment when Muslims
observing the holy months of
Ramadan break their daily fast.

Via ABC News.

Monday, August 15, 2011

Tsangayar Alheri ta kai ziyara asibitin Kananan Yara

Kungiyar Tsangayar Alheri ta kai ziyara a karon farko tun bayan yiwa kungiyar kwaskwarima daga Sansanin Samari da 'yanmata, kuma shine karon farko data fitar da irin wannan alheri zuwa ga sauran jama'a, ba kamar da da alherin kungiyar ke tsayawa a tsakanin 'yayan kungiyar kadai ba.

Tsangayar Alherin ta kai ziyarar ne zuwa asibitin kananan yara na Hasiya Bayero dake Kofar Kudu a birnin Kanon Dabo. A yayin wannan ziyara kungiyar ta rarraba sabulan wanka da omon wanki ga masu zaman jinya a asibitin.

A jawabin shugaban kungiyar na kasa Abdulqadir Sardauna ya bayyana makasudin kawo wannan ziyara, sannan ya jawo hankalin iyaye da su rinka amfani da hanyoyin rigakafin kariya daga kamuwa da cututtuka musamman gidan sauro mai magani. Shugaban ya kuma bayyana aniyar kungiyar na kara kai wasu ziyarorin zuwa gidan Marayu da gidan Yari (prison) nan bada dadewa ba.

A martanin da wakiliyar ma'aikatan asibitin tayi Dakta Ummu Badaru, ta nuna farin cikinta da kuma godiya ga wannan kungiya, sannan ta bayyana samuwar irin wadannan kungiyoyi a wannan al'umma ba karamin ci gaba bane. Sannan ta kara da cewa suma a matsayinsu na likitoci Musulmai suna da makamanciyar irin wannan kungiya mai suna Islamic Medical Association (ISMA) wadda take taimakawa marassa lafiya masu karamin karfin wadanda basu da yadda zasu yi wurin siyan magunguna. A karshe tayi fatan Tsangayar Alheri zata tafi kafada da kafada da kungiyar tasu ta ISMA.

Bayan kammala ziyarar duba marassa lafiya ne, kai tsaye tawagar Tsangayar Alheri ta nufi wurin da aka tanada dan buda baki (shan ruwa) wanda kungiyar ta shiryawa 'yayanta a karo na biyu bayan wanda akayi a baya ranan 5 Ramadan / 5 August, kuma daya daga cikin 'yayan kungiyar Usman Aminu Alqadiri ya dauki nauyi kamar yadda na bayan ma 'yar kungiyar Shamsiyya Habib ta dauki nauyi. Kuma a ranan 25 Ramadan kungiyar zata gabatar da shan ruwan da ta shirya karo na karshe, wadda shi ma daya daga 'yayan kungiyar Abubakar Abdullahi Kofar Na'isa yayi alkwarin daukar nauyi, fatanmu Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya.

A wurin shan ruwan, an ci an sha anyi hani'an, an kuma yi wasanni da dariya, sannan shugabannin kungiyar na kasa dana reshen jihar Kano suka gabatar da jawabansu, kuma aka bawa wasu daga cikin 'yayan kungiyar suka tofa albarkacin bakinsu. Su ma Malaman kungiyar ba'a barsu a baya ba, sun gabatar da addu'o'i ga kungiya da 'yayanta baki daya. Daga nan aka gabatar da sababbin 'yayan kungiya. A karshe bayan gabatar da Sallan Isha'i kowa ya kama gabansa.

Bashir Ahmad
Acting National Secretary
08032493020, 08050600160.

Saturday, August 13, 2011

Jama'a Ga Mujallar Muryar Arewa

Ina farin cikin gabatar muku da sabuwar mujallar MURYAR AREWA!

Muryar Arewa sabuwar mujalla ce da kamfanin Northern Media Link LTD ke tsarawa da wallafawa wata - wata (monthly) domin samun cikakken labarun da suke faruwa game da yankinmu na Arewa dama kasa baki daya. Babbar manufar Muryar Arewa shine gano matsalolin dake addabar yankin Arewa da kuma kokarin samo hanyoyin magance su, ta hanyar labarai da rahotonni gami da bayar damar fadar ra'ayi, hirarraki da fitattun shugabanni, talakawa, ma'aikata, yan siyasa, malamai, mata da matasa baki daya, duk don samowa Arewa mafita da ci gaba.

Muryar Arewa ta dauki alwashin ganin dukkan jinsunan da ke wannan yanki na Arewa sun hada kansu ba tare da nuna banbanci addini, darika, yare, kabila, sashe ko nuna wani bangaranci ba a tsakaninsu, Muryar Arewa na da burin ganin duk dan Arewa daga kowane bangare ya zauna da kowa lafiya a matsayin uwa daya uba daya.

Ana wallafa Muryar Arewa da harshen Hausa, harshen da kullum yake kara habaka da bunkasa yake a sassan duniya kamar wutar daji.

Kabir Assada shine daraktan gudanarwa kuma babban edita na wannan mujalla, sai kuma kwararrun abokanan aikinsa irinsu: M. K. Muhammad, Ibrahim Basit Ahmad, Sheriff Sidi. Ga kuma wakilai a kusa dukkan jihohin Arewa, sannan kuma ga hazikan marubuta na musamman kamar su Ado Ahmad Gidan Dabino, Yusuf Dingyadi, Binta Spikin, Bashir Ahmad, Nasir Abubakar da sauransu.

Muryar Arewa na da tsari na daban da zai zama abin burgewa da sha'awa ga kowa, inda komai aka tsarashi daki - daki yadda zai kayatar da fahimtar da masu karatu, misali zaka samu rukuni - rukuni a mujallar kamar haka: Labarai, Rahotonni, sharhi, tattaunawa, ra'ayi, taskar al'adu, hirar musamman, tsokaci, kimiya da fasaha, rigar yanci, tsumagiya, nasiha, duniyar finafinan Hausa, adabi, duniyar mata, da sauran shafuka masu ilmintarwa, fadakarwa gami nishadantarwa. Kai abin dai sai wanda ya gani. Sannan kuma akwai shafukan da aka tanada dan talla, don tallar hajar masu karatu.

Kash! Saura kadan na manta da shafin da yafi kowane kayatarwa wato shafin tsakiya, shafin da ya kunshi..... Bari dai na hakura haka, kar na cikaku da surutu, kuma masu iya magana na cewa gani ya kori ji, don haka kayi kokarin mallakar taka don kaima ka samu damar bada labari.

Wannan mujalla an samar da ita don mu Hausawa yan Arewa, saboda haka ya kamata mu bada gudunmawar da zamu iya bayarwa wajen ganin wannan jan aiki da mawallafanta suka dauko an samu gagarumar nasara.

A karshe sako guda daya ko biyu da nake son aikawa ga wannan mujalla shine, ya kamata a samar da filin da masu karatu zasu ke aikowa da gajerun ra'ayoyinsu ta wayar hannu, sannan kuma a samu wani shafi da za'a ke tattaunawa da kungiyoyi don jin manufofinsu da irin ayyukan da suka aiwatar. Hakan zai kara kusanta wannan Mujalla da jama'a na sassa daban - daban. Sannan idan wannan sako nawa ya samu isa cikin nasara, ina fatan wannan mujalla zata bawa kungiyarmu ta TSANGAYAR ALHERI damar bayyana manufofinta ga al'ummar duniya baki daya.

Kafin na ajiye abin rubutun nawa za'a iya samun Muryar Arewa a dukkan wani wurin sai da jaridu da mujallu a kudanci da arewancin kasar nan baki daya, akan kudi kalilan.

Ya Allah ga Mujallar Muryar Arewa don ci gaban Arewa da al'ummar Arewa da ma kasar Nigeria baki daya!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Saturday, August 6, 2011

TSANGAYAR ALHERI TA SHIRYAWA YAYANTA SHAN RUWAN AZUMI

Kungiyar Tsangayar Alheri reshen jihar Kano ta shiryawa 'yayanta Shan Ruwan Buda baki ranar 5 Ramadan 1432 wanda daya daga cikin 'yayan kungiyar Shamsiyya Habib ta dauki nauyin shiryawa.

Taron ya samu halartar 'yayan kungiyar da dama ciki har da sabbin yan kungiya, duk da ruwan sama da ya hana wasu zuwa. Wadanda suka halarta sun hada da:
Ali Adamu Jauro
Usman Aminu Alqadiri
Alhaji Nafiu Sharifai
Abubakar A. Kofar Naisa
Auwal M. Danlarabawa
Haruna Adam
Abubakar Suleiman Dan Auta
Muhd Ahmad Idris
Bashir Abdullahi El Bash
Shamsu Ibrahim
Al Jamil Ahmad
Bala Garba Kumbotso
Abdussalam Saidu
Musa Abdullahi DZ
Shamsiyya Habib
Bashir Ahmad
Jummai Shu'aibu
Kamal Muhammad
Balarabe Yusuf Babale Gajida

Aminu Abdu Bakanoma

An tashi daga taron cikin farin ciki da annashiwa, kowa na yiwa kowa fatan alheri.

A karshe Allah ya baiwa wannan baiwar Allah da ta shirya wannan aikin lada, ladan ciyarwa cikin watan azumin Ramadan.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Wednesday, August 3, 2011

Hamza Al-Mustapha ya fasa kwai a bainar Jama'a

Dogarin tsohon Shugaban kasar Nijeriya Marigayi General Sani Abacha, Major Hamza Al-Mustapha ya fasa kwai game da yadda shugabannin yankin Kudu maso yammacin kasar nan wato yankin Yarabawa, suka karbi cin hancin makudan kudi bayan kashe tsohon babban dan kasuwa kuma dan siyasa M.K.O Abiola.

Al-Mustapha ya baiyana hakan ne a babbar kotun jihar Lagos, yayin da ya baiyana don kare kansa game da zargin kisan Hajiya Kudirat Abiola matar tsohon marigayin, tun a shekarar 1998 ba tare da an yanke masa hukunci ba. Ya kuma kara baiyana cewar tsohon Shugaban kasa General Abdulsalam Abubakar ya sa an tsare shine domin tsoron kar ya baiyana irin badakalar da aka tafka a kisan na Abiola.

Al-Mustapha yace ai baiwa shugabannin Yarabawan sama da dalar Amurka miliyan 200 inda ya shaida cewar ya dade yana son baiyana wannan ta'asa amma saboda tsoron tashin hankali ya hakura sai yanzu da yaga ba mafita sai yayi hakan. A karshe ya shaidawa kotun a zama na gaba zai baiyana fefan bidiyo domin ya zama sheda.

Fatanmu Allah ya taimaki dukkan mai gaskiya akan azzalumai.

Bashir Ahmad
Bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Monday, August 1, 2011

Jadawalin Alfijir dana Shan Ruwa (Ramadan 2011)

Wannan lokutan ya shafi jihar Kano ne sai wasu bangarori na Jihohin Jigawa, Katsina da Kaduna kawai, za'a iya samu kari ko ragi a wasu jihohin dake nesa da Kano, kamar Nasarawa +5 Lagos +20 Kebbi +18 Zamfara +17 Yobe -14 Bauchi -4 Taraba -10 Jos -4 Maiduguri -19 da sauransu.

Ga lokutan kamar haka:-

Alfijir === Shan Ruwa
1. 4:58am = 6:52pm
2. 4:58am = 6:51pm
3. 4:58am = 6:51pm
4. 4:58am = 6:51pm
5. 4:59am = 6:50pm
6. 4:59am = 6:50pm
7. 4:59am = 6:50pm
8. 5:00am = 6:49pm
9. 5:00am = 6:49pm
10. 5:00am = 6:48pm
11. 5:00am = 6:48pm
12. 5:01am = 6:47pm
13. 5:01am = 6:47pm
14. 5:01am = 6:47pm
15. 5:01am = 6:46pm
16. 5:02am = 6:46pm
17. 5:02am = 6:45pm
18. 5:02am = 6:45pm
19. 5:02am = 6:44pm
20. 5:02am = 6:43pm
21. 5:03am = 6:43pm
22. 5:03am = 6:42pm
23. 5:03am = 6:42pm
24. 5:03am = 6:41pm
25. 5:03am = 6:41pm
26. 5:03am = 6:40pm
27. 5:04am = 6:39pm
28. 5:04am = 6:39pm
29. 5:04am = 6:38pm

Allah ya karbi Ibadunmu, kuma karmu manta da yiwa juna addu'a ta gari, gami da kasarmu Nigeria baki daya.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Friday, July 29, 2011

TSARABAR WATAN AZUMI

Azumi a addinin Musulunci na nufin kauracewa cin abinci, shan ruwa, fadin munanan maganganu, shan taba, saduwa tsakanin ma'aurata da kuma dukkan wani aiki da ya sabawa koyarwa addinin Musulunci tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana da nufi bautawa Allah madaukakin sarki.

Azumi na daya daga cikin shika-shigan Musulunci guda biyar, haka tasa ya zama wajibi ga dukkan Musulmin da ya balaga, a duk watan tara (Ramadan) na shekarar Musulunci kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Al Kur'ani mai girma inda yake cewa "Ya ku wadanda suka yi imani, mun wajabta azumi a gare ku kamar yadda muka wajabtawa wadanda suka gabace ku, domin ku kara tunawa da Allah" Q2:V183

A watan Ramadan Allah ya saukar da Al Kur'ani mai tsarki ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Watan azumi wata ne na rahma, alfarma, gafara da karbar addu'a. Wata ne da dukkan wani Musulmi ke kara zage dantse wurin ibada da kyautatawa yan uwa Musulmai don samun rahmar Allah.

Amma abin mamaki wasu daga cikin Musulmai na yin amfani da wannan wata mai albarka wajen kara tsauwalawa yan uwa Musulmai, misali wasu daga cikin yan kasuwa da zarar watan azumin ya kusanto sai su fara tashin farashin kayan masarufi kamar shinkafa, nama, lemo, kayan miya da sauran kayan masarufi saboda ganin ya zama wajibi ayi amfani dasu, saboda duk wanda ya sha ruwa zaiso yadan karya da abinci mai dan dadi.

Haba bayin Allah, shin mai zai sa ba zamu rinka rage farashi ba idan watan azumin yazo sai akasinsa, shin bama ganin yadda yan kasuwa mabiya addinin Kirista ke yi ne idan lokacin Kirismeti yazo zasu rinka rage farashin kayayyaki, bai kamata a ce su suke wannan aikin kyautatawa ba mu ba.

Wasu ma daga cikin yan kasuwan namu suna siyan kayan ne suna boyewa kafin watan azumin don idan watan yazo su sami riba mai yawa. Haba yan uwa, mu tuna fa komai yawan wannan riba da zamu samu Allah bazai taba sa mata albarka ba. Shin ina ta shekarar da ta gabata? Shin wane amfani tayi mana nasan wadannan tambayoyi zasuyi wahalar amsawa.

Sai dai ko yaushe na Allah basa karewa, wasu bayin Allah daga cikin yan kasuwan su kuma suna yin iya kokarinsu kanin sun kyautata a wannan wata mai albarka, suna rage farashin kayansu ko da kuwa zasu tashi babu ribar komai, amma sai kaga saboda Allah yasa albarka sunfi yan uwan nasu walwala da jin dadi, ga kuma lada mai tarun yawa da yake can yake jiransu ranar alkiyama.

A karshe a matsayinka na dan kasuwa yi kokari ka rage farashin kayanka koda kuwa kana ganin ba zaka samu riba da yawa ba, idan Allah ya sawa abinda zaka samu komai kankantarsa albarka yafi wanda zaka samu komai yawansa marar albarka. Sannan ya kamata mu yi kokarin ciyar da junanmu koda da kwayar dabino guda daya ne.

Allah ya karbi ibadunmu a wannan wata mai albarka, Allah yasa muna cikin wadanda za'a yanta a yi musu gafara, Allah ya taimaki yankinmu na AREWA ya kara daukaka shi tare da kasarmu Nigeria baki daya.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Saturday, July 23, 2011

Kamfanin Google yayi wa shafin Facebook kishiya

Kamfanin Google ya gabatar da sabon shafin sada zumunta mai suna Google Plus (Google+) wannan shafi zai bawa masu amfani dashi damar karba da aika sakonni, zuwa ko ina a fadin duniya, wato shafin yayi kamanceceniya da shafukan Facebook da Twitter da kuma mySpace, duk da shugaban kamfanin na Google Larry Page ya musanta cewar shafin an kwaikwaiyi wani shafi ne na daban.

Bayan fitowar wannan shafi mutane da dama a fadin duniya sun tofa albarkacin bakinsu game da shafin, inda wasu ke ganin shafin ya fi dukkan shafukan da muke amfani dasu a halin yanzu a duniyar yanar gizo, inda wasu kuma ke ganin ina ai shafin Google yayi nisan da ba wani shafin sadarwa da zaizo ya kamo shi nan da kusa, inda shafin ke da masu amfani dashi sama da 720 miliyan.

A halin yanzu shafin na amfani akan kumfutoti da kuma manyan wayoyi irin su iPad, Apple da sauransu. Ga mai sha'awar yin rijista a wannan shafi zai ziyarci (plus.google.com) don ganin wainar da ake toyawa.

Shafin Google Plus cikin dan lokaci kalilan har tara masu amfani dashi sama da 20 miliyan, ciki har da mai kamfanin Facebook Mark Zuckberg. A nazarin da jaridar New York Daily ta kasar Amurka da gabatar tabbatar da cewa babu wani shafin sadarwa da ya samu irin wannan daukaka cikin dan kankanin lokaci, hakan tasa ake ganin lalle shafin zai zamewa shafin Facebook babban kalubale, duk da wasu masana harkar sadarwa sun nuna cewa wannan tagomashi da shafin ya samu ya same shine da taimakon shafin Facebook da Twitter, domin tun lokacin da kamfanin na Google ya sanar da aniyarsa ta yin Google+ din, masu amfani da shafukan suka rinka sanarwa abokanansu na sassan daban daban na duniya. Tabbas nima zan iya yadda da hakan domin nima na samu labarin wannan shafi ne daga wuri wani abokina dan kasar India.

To koma dai menene dai, fatanmu Allah ya bawa jama'armu basirar yin amfani da wannan shafuka da hanyar da baza sabawa addininmu na Musulunci ba, Allah ya bamu ikon yin amfani da wannan shafuka na sadarwa wajen yada addinin Musulunci.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Friday, July 15, 2011

TSARIN BANKIN MUSULUNCI BA A NIGERIA AKA FARA BA

Bankin Musulunci, wato bankin da ba'a bada kudin ruwa (Riba), ko kuma ba da rancen kudaden jama'a ga wuraren daya sabawa addinin Musulunci, kamar kamfanonin giya. Bakin Musuluncin ya samu karbuwa a kasashen daban daban na duniya.

Daga cikin kasashen dake amfani da irin wannan tsari na bankin Musulunci sun hada har da kasashen Kiristoci kamar su United States, United Kingdom, Germany da France.

Sai kasashen yankin Asia dayawa su ma na amfani da wannan tsari kamar Indonesia, India, Pakistan, Bangladash, Malaysia da Afganistan.

Dukkan daukakin kasashen larabawa na amfani da irin wannan tsari kamar Saudi Arabia, Yemen, Qatar, Dubai, Iraq, Kuwait, Iran duk na amfani da irin wannan tsari.

Hatta kasashen Afrika irinsu South Africa, Egypt, Senegal, Gambia, Niger, Kenya, Tanzania, Algeria, Libya, Tunisia, Morocco da kuma jamhuriyar Benin duk sun rungumi wannan tsari hannu bibiyu.

Shin idan wannan kasashe zasu rungumi wannan tsari mai zai sa Nigeria ba zasu rungume shi ba. Nigeria fa na daya daga cikin kasashen duniya da suka fi yawan Musulmai.

Bankin Musulunci, banki ne daya samar da tsari kala kala ga Musulmi da wanda ma ba Musulmin ba, wannan tsari bai sabawa kudin tsarin mulkin Nigeria.

Shin mai zai sa wasu daga cikin jama'ar kasar nan basa goyan bayan wannan tsari? Shin mai zai haifar musu idan anyi shi? Nasan duk abinda bai haifarwa kasar America matsala ba, to ba zai taba haifarwa Nigeria ba. Shin wannan tsarin da muke kai yanzu, tsarin wane addini ne, Musulunci ko Kiristanci? Kowa na sane da cewa tsarin Kiristanci ne, tunda muka hakura muka bi wannan tsari shekara da shekara mai zai sa zasu ki goya mana baya muma muyi namu. Bafa cewa akayi za'a daina kowane tsari ko a koma na Musulunci ba, a'a kowa zaiyi nashi ne. Kuyi naku muyi namu.

Mutane da dama na zargin Sanusi Lamido Sanusi da cewa shi ya dage sai an kawo wannan tsari, Sanusi shi ma zuwa yayi ya tarar kuma yake so dorawa. Wannan tsari tun lokacin Joseph Oladele Sanusi yana matsayin gwamnan babban banki ya aika takardar neman amincewa zuwa ga JAIZ International PLC Sannan kuma a lokacin Charles C. Soludo JAIZ ya tambatar da amincewar.

Don haka shi kuma Sanusi ke son bankin ya fara aiki a lokacinsa.

A karshe muna yi wa Sanusi Lamido Sanusi fatan nasara a wannan aikin na alkhairi. Allah ya taimake shi.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Wednesday, July 13, 2011

Takaitaccen Tarihin Dr. Abubakar Imam

An haifi Alhaji Dr. Abubakar
Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.)
N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin
garin kagara sa’an nan tana cikin
lardin Kwantagora, yanzu kuwa
Jihar Neja. Ya Yi makaranta a
Katsina Training College kuma ya
kama aikin malanta a Makarantar
Midil to Katsina a shekarar 1932.

Yana da shekara 22 ya rubuta
`Ruwan Bagaja’. Ganin kwazonsa
wajen Raga labari mai ma’ana ya
sa Dr. R.M. East shugaban
Offishin Talifi na Zariya ya roki a
ba da shi aro daga Katsina ya yi
aikin rubuce rubuce a Zariya.
Bayan ya koma Katsina aka bi shi
da rokon ya kara rubuta wasu,
littattafan. A can ya rubuta
‘Karamin Sani kukumi’ cikin 1937.

A cikin shekara 1938 sai
Gwamnan Kaduna ya roka a
dawo da Imam Zariya a koya
mashi aikin edita ya zama editan
jaridar farko to Arewa. Shi ne ma
ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi
Kwabo’ aka fara bugawa a
watan Janairu na shekara 1939.
Ya yi shekara 12 yana wannan
aiki na edita har ma ya rubuta
wani littafi a lokacin `Yakin
Duniya Na Biyu’ watau `Yakin
Hitila’ da ya ba suna `Tafiya
Mabudin Ilmi’. Wannan littafi ya
ba da Iabarin tafiyarsa tare da
wasu editoci na jaridun Africa to
Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa
a shekara 1943.

Wani mashahurin littafi kuma da
ya rubuta shi ne ‘Tarihin Annabi
da na Halifofi’ wanda aka fara
buga shi a shekara 1957 lokacin
nan yang shugaban Hukumar
Daukar Ma’aikata to Nijeriya to
Arewa.
Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka
fara nadawa Kwamishinan Jin
Kararakin Jama’a a shekara 1974
a Jihar Kaduna, lokacin ana
kiranta Arewa to Tsakiya. Ya rasu
yana da shekara 70 a duniya
ranar Juma’a 19 ga watan Yuni,
1981.

Alhaji Abubakar Imam ya rike
cewa wannan aiki da ya yi, na
talifin ‘Magana Jari e’ ya yi masa
amfani ainun. Ya kan ce wannan
aiki shi ne ya ba shi damar zama
tare da mashahurin Baturen nan
na talifin Hausa, Dr. R.M. East,
O.B.E. Ya ce daga gare shi ne ya
koyi duk dan abin da ya koya na
game da talifi.

Abin mamaki, shi kuma wannan
Bature, Dr. East O.B.E., a wajen
`Mukaddamar’ da ya yi da
Turanci tun farkon buga ‘Magana
Jarice, ga. abin da ya ce : ‘Muna
godiya ga En’e ta Katsina, saboda
da taimakonsu, da hangen nesa da
suka yi, har suka yarda,suka bamu Malam Abubakar Imam.
Suka yarda, ya bar aikinsa, na
koyar da Turanci a Midil to
Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi
wata shida domin ya taimake
mu, mu sami wadannan
littattafai a cikin harshensa.

`Iyakar abin da mu ma`aikatan
wannan ofis muka yi, na game
da talifin wadannan littattafai,
shi ne aiki irin na ofis, na shirya
al’amuran, yadda suka kai har
aka buga su. Ban da wannan sai
su kuma taimakonsa da muka yi
na tattara masa littattafai iri iri,
don ko zai kwaikwayi wani
samfur. Sai fa kuma wajen
shiryawa bayan da ya rubuta.
‘Kai, in dai har muna da wani
abin da za mu yi kirari mun yi,
game da talifin wadannan
littattafai, to, babban abin
kirarimmu kawai, shi ne yadda
muka yi har muka binciko
wannan malamin talifi’.

Monday, July 11, 2011

KANO TA DABO TUMBIN GWIWA

KANO na daya daga cikin manya manyan jihohin Nigeria dama yammacin Afrika baki daya. Kano tsohon gari ne daya haura sama da shekaru 1000+ da kafuwa.

Kano babban gari ne mai dauke da jama'a masu tarun yawa, sama da miliyan tara 9,000,000 kamar yadda hukumar kidaya ta kasa ta tabbatar a kidayar da ta gabata a shekarar 2006. Kuma itace jihar da tafi kowace yawa jama'a a Nigeria da yankin yammacin Afrika.

Wannan yawan jama'a da Kano ke dashi ya samo asali ne sakamakon shahara da garin yayi ta fannoni da dama kamar: Ilmi, tattalin arziki, Kasuwanci, karbar baki, zaman lafiya da sauran dalilai da dama. Tun kafin zuwan turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya Kano tayi kaurin suna wajen wadannan fanni, inda al'umma daga sassan duniya daban daban ke kwararowa don neman ilmi ko kasuwanci.

Kano gari ne daya tara manyan Malam addini, manyan attijirai, manyan sarakai, manyan masu ilmin zamani, manyan komai da komai ciki har da manyan barayi da yan iska. Hakan tasa akewa Kano kirari da "Koda mai kazo an fika" wasu sukewa garin kirari da cewa "Kano ta dabo tumbin giwa, mai mata mai mota, mai Dala da Goron Dutse" ko kuma ace "Jalla babbar Hausa" da sauran kirari dai kala kala na girmamawa.

Mafi yawan mutanen Kano yan kasuwa ne musamman wadanda suke zaune cikin gari, sai kuma manoma da suke zaune a garuruwa kamar Kura, Rogo, Gaya, Dambatta da sauran garuruwa da dama.

Duk wannan martaba da muhimmanci da garin ke dashi amma yanzu a wannan zamanin na siyasa kullum Kano koma baya take samu ba ci gaba ba, garin babu wutar lantarki, babu isasshen ruwan sha, babu kyawawan magudanen ruwa, babu tsari wurin gine gine kullum sai cunkushewa ake yi wuri daya. Babu sana'ar yi a wurin mafi yawan matasa, wanda kuma matasan suka dogara da ita, ko yaushe sai tabarbarewa take yi, amma har yanzu an kasa daukar mataki.

Misalin an bawa yan China dama suna shigo da hajarsu daga kasarsu suna talla, da kuwa mutanen Kano ke zuwa kasashen nasu suna siyowa, suna kuma tafiya musu abinda suke bukata daga nan suna siyarwa a can. Wannan shigowa da yan kasashen waje ke yi da hajarsu zuwa Kano ba karamin nakasu bane ga kasuwancin mutaten Kano, amma har yanzu masu ruwa da tsaki akan abin sunki daukar matakin komai akan wata manufa tasu daban. Haka tasa ake samun karuwar masu zaman kashe wando kullum a Kano.

A shekarun baya kafin wadannan matsalolin su addabi Kano garin yana da kayatarwa, burin duk wanda bai taba zuwa Kano ba yazo ya sha kallo, amma yanzu abin ba haka yake ba. A wancan lokacin ne garuruwa ke daukar salo kala kala a wurinmu, gwamnonin sauran jihohi da sarakuna ke kawo ziyara Kano akai akai ba don komai ba, sai don idan sun zo su ga wani sabon abinda basu san dashi ba, wasu ma daga cikinsu har filaye suka siya suke gina gidaje.

Fatana masu fada aji zasu yi duba irin na basira, su samowa Kano da mutanen ta mafita, Kano ta koma Kanon da aka sani tun tuntuni. Don kuwa Kanon yanzun ba Kano bace kawai suna ne.

A karshe Ya Allah ka daukaka wannan gari na masoya Fiyayyen Halitta bawanKa wanda bai taba saba ma ba, Annabi Muhammad (SAW). Ya Allah ka karawa wannan gari Albarka, zaman lafiya gami da yalwar arziki.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Sunday, July 3, 2011

KAMUN DA HUKUMAR SSS TA YI WA SU EL-RUFA'I BAYA NUFIN KOMAI SAI ADAWAR SIYASA

A safiyar ranar 2nd July, 2011 ne hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS ta kama tsohon Ministan birnin tarayya Abuja Mallam Nasir el-Rufa'i tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar CPC a filin jirgin saman kasa da kasa na Nmandi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja. Jim kadan da saukarsu daga birnin London, inda suka raka dan takarar shugaban kasa a zaben 2011 Janar Muhammad Buhari a wata mukala da aka shirya game da zaben da ya gabata a watan April.

Mutane da dama na ganin wannan kamu da aka yi wa su el-Rufa'i an yi shine ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, kawai dai an kama su ne saboda adawa irin ta siyasa da gwamnati me ci a yanzu ke yi da Janar Muhammad Buhari, domin kuwa a lokacin da el-Rufa'i ya dawo Nigeria daga England a shekarar da tagaba bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Alhaji Umar Musa Yar'adua, bai samu matsin lamba ba ko kadan, amma tun daga lokacin da ya nuna bangaren da yake goyan baya a siyasa nan suka fara takun saka da gwamnati. Tun daga lokacin ake ta kakalen laifin da za'a lika masa a kama shi amma ba'a samu ba.

Da manema labarai suka nemi jin dalilin kama tsohon ministan, mai magana da yawun hukumar Uwargida Marilyn Ogar tace ''An kama tsohon Ministan ne saboda wasu tambayoyi da zasu yi masa game da wasu kage da yayi wa gwamnatin tarayya, wanda aka wallafa a jaridar National Daily ta ranan Juma'a da ta gabata. wanda kuma a cewarta maganganun da ya fada ba gaskiya ba ne''

Uwargida Ogar ta bayyana cewa kagen da Mallam el-Rufa'i yayi wa gwamnatin Nigeria ya sabawa "Freedom of Information" (FOI) amma kuma bata yin gamsasshen bayani akan kagen ba.

Janar Muhammad Buhari ya bayyana cewa a gaggauta sakin el-Rufa'i da sauran mutane da ake tsare da su, sannan kuma yace ko kadan hakan bai kamata ba, don kuwa maganganunsa basu sabawa kundin tsarin mulki ba.

A mukalar el-Rufa'i ta ranan 1st July, 2011 ya bayyana irin magudan kudin da Nigeria tayi kasafin wannan shekara, kuma ya tabo kasafin kudin shekarar da ta gabata idan kuma ya tabbatar da cewa ko kadan wadannan makudan kudade da aka batar basu amfanar da dan Nigeria da ita kanta Nigerian komai ba. Ya bayyana kudaden da kasar ta samu dalla-dalla. Wanda hakan gwamnati dake ganin ya sabawa dokar bayyana yancin fadin bayyanai (FOI).

A gaskiyance maganganun Mallam el-Rufa'i basu sabawa doka ba, ko kudin tsarin mulki, ko wata hukuma ta daban. A matsayin shi na dan kasa kuma mai bibiyar al'amuran mulkin kasar yana da yancin fadawa talakawa irin bada kalar da watandar da ake yi da kudaden su, tun da kuwa kasar na tafiya ne akan turbar demokradiyya.

To a karshe abin tambayar anan shi ne su sauran manyan jam'iyyar CPC da aka kama su tare menene makomarsu? Wane dalili yasa aka kama su? Ko su ma rubutun suka yi wanda ya sabawa (FOI)? Ko daman suna da wani laifi na daban? Tabbas ni kam a tunani na wannan kamun an yi shi ne da wata manufa ta daban, ba wai akan rubutun da Mallam Nasir el-Rufa'i yayi ba.

Allah yana bayan mai gaskiya!!!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Wednesday, June 8, 2011

KUNGIYAR TSANGAYAR ALHERI

TSANGAYAR ALHERI kungiya ce mai zaman kanta wato ba ta gwamnati ce ko ta siyasa ba, wasu mutane ne hazikai masu kaifin basira da hangen nesa, Allah ya basu ikon kirkirarta domin fahimtar da al'umma game da abubuwan da suka shafi al'amuranmu na yau da kullum da kuma irin matsalolin dake fuskantarmu a wannan zamani, mai cike da rikita-rikita, da karancin jin tsoron Allah a zuciyoyin jama'a, inda babba ke danne karami, mai kudi ke danne talaka wato zaman kashin dankali kenan.

Manyan Manufofin wannan kungiya sune: Ilmintar da al'umma game da halin wannan rayuwa, sada zumunta, taimakawa masu karamin karfi, ziyartar asibitoci, gidan marayu da kuma gidan yari (prison) don ganin irin halin da suke ciki. hakan tasa kungiyar taci sunan TSANGAYAR ALHERI sannan kaso 75% na aikin wannan kungiya na lafiya ne a shafukan Yanar Gizo kamar Yahoo Groups, Facebook da sauran shafukan sada zumunta, ta wannan hanyar ne kungiyar ke samun damar aika sakon da take son aikawa ga al'umma.

TSANGAYAR ALHERI kungiya ce ta kowa da kowa (wato Maza da Mata, Matasa, har ma da Dattijai) musamman yan arewacin Najeriya (Nigeria). Sakamakon mafiya yawan yan wannan kungiya Hausawa ne, hakan tasa kungiyar ke gabatar da harkokinta da harshen Hausa gami da koyarwar addinin Musulunci. Amma haka ba yana nuna cewa kawai Musulmi dan arewa ke da damar shiga kungiyar ba. Indai mutum dan asalin Nigeria ne da ya haura shekaru 18+ yana da damar shiga kungiyar kai tsaye tare da yardar shugabannin kungiyar.

Kungiyar na zama meeting dan tattaunawa sau biyu a duk sati. Ranar Talata da Ranar Juma'a, ranar Talata shugabannin wannan kungiya na zama don tattauna abin da ya dace a gabatar ranar Juma'a (Agenda) wato zasu duba ne a cikin satin da ya gabata wane abu ne ya faru da ya dace a tattauna akansa don samun mafita. Idan ba abin da ya faru cikin satin shugabannin cikin irin basirar da Allah ya hore musu zasu kawo wani abu da yake damun jama'a don tattaunawa.

Ranan Juma'a ranan ne za'a hadu da dukkan dan kungiya daga jihohi daban-daban a fadin kasar nan, anan za'a tattauna abin da shugabannin suka yanke ranar Talata. Daga karshe kuma a bawa kowa dama da yayi tambaya akan abubuwan da aka tattauna ko wani abu da ya shige masa dahu a cikin wannan kungiya. Sannan bayan tambaya sai a bawa masu kawo shawara dan cigaban kungiya dama da su fadi shawarwarinsu.

Na san za ayi mamakin jin cewa ana haduwa meeting da mutanen jihohi daban-daban, to wannan meeting dai ana zamansa ne cikin iska, wato ta wayar hannu (Handset) da misalin karfe 12:30 na dare (Free Call / Conference Call) sannan kuma wasu johohin masu members da yawa suna yin meeting cikin sati biyu biyu, amma wannan ba ta waya ake yin shi. A zahiri yan kungiya ke haduwa don tattauna abubuwa da dama game da kungiyar.

Ga duk mai sha'awar zama daya daga cikin dan wannan kungiya to kofa a bude take kuma cikin sassaukar hanya, misali idan mutum na amfani da shafin sadarwa na Facebook ko Yahoo Groups zai iya binciko kungiyar ta hanyar rubuta sunanta (TSANGAYAR ALHERI) anan zaiyi rijista/joining sannan ka/ki aje numbarka/ki ta MTN wadda za'a kiraka/ki yayin meeting na kungiya. Kuma idan mutum baya amfani da shafin Facebook ko Yahoo Groups zai iya zama dan wannan kungiya ta hanyar tuntubar wadannan bayin Allah:-

Jibrin Muhammad Yusi - Bajoga - 08034760327

Abdulqadir Sardauna - 08039644376

Ali Adamu Jauro - 08032950453

A cikin wadannan mutane duk wanda mutum ya tuntuba zasu yi masa cikakken bayani game da wannan kungiya daidai yadda mutum zai gamsu. Anan bazan wuce ba sai nayi amfani da wannan damar amadadin kai na nake godiya da addu'ar Allah ya karawa wadannan jajirtaccun mutane hikima da basira ya kuma daukaka su a dukkan al'amuransu, sannan ya cika musu wannan buri nasu na fahimtar da al'umma, kamar yadda suke yi ba dare ba rana. Allah ya saka da alheri.

Fatana Allah ya daukaka wannan kungiya da dukkan yayanta baki daya. Allah ya yalwata alheri a cikinta. Allah ya kara hada kanmu, Ya cika mana burinmu game da wannan kungiya ta TSANGAYAR ALHERI amin.

A karshe ina kira da jama'a masu irin wannan akida da son ci gaban al'umma da su shigo wannan tafiya, su ma su bada tasu gudunmawar ga al'umma. Da irin Ilmin da Ubangiji ya hore musu. Don shi aikin alheri baida kadan, kuma mutum bai san wane aiki Ubangiji zai duba daga cikin ayyukansa yayi masa Rahma da Gafasa ba. Don duk abin da kayi shi don Allah ba don wani ya gani ya fadi ba to tabbas Allah zai baka mafificin lada. Allah ya shige mana gaba a dukkan al'amuranmu na yau da kullum, amin!

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Wednesday, May 4, 2011

INA MAFITA MATASAN AREWA?

Matasan Arewa gaisuwa gareku, ya
zabukan da suka gabata? Matasan
Arewa, mafi yawancinmu Hausawa ne
kuma mabiya addini daya wato
Musulunci sannan masu akida daya
wato akidar son ganin Nigeria ta
cigaba, ana gogayya da ita cikin
manya manyan kasashen duniya
masu tattalin arziki, kamarsu America,
England, Germany da sauransu.
Shin yaushe wannan buri namu da
muke ta mafarki da muradi zai cika?
Shin kuma wace irin gudunmawa
zamu bayar wajen ganin wannan buri
ya cika? A tunani bamu da wata
gudunmawa illa ta zaben shugabanni
nagari, tabbas munyi hakan har karo
uku amma Allah bai cika mana
wannan buri ba (wato shugaban da
muke ganin shine nagari Allah bai
bashi nasara ba karo ukun) kuma
gashi ahalin yanzu ya sanar da ajiye
muradinsa nason zama shugaban
namu ba don ya karaya ba sai don
yawan shekaru.
To yanzu wane mataki kuma ya dace
mu dauka nan gaba, kowa yana sane
da yadda wannan kabila tamu ke
zama koma baya a ko yaushe a kasar
nan, alhali mune mafiya rinjaye,
Hausawa ya kamata mu farka baccin
ya isa haka kafin lokacin da za'a zo a
tashe mu ace mu ba yan kasar bane,
Eh mana tabbas idan zamu tafi a haka
to nan gaba za'a ce Hausawa ba yan
Nigeria bane.
A tunani na mafita itace mu shiga
wayar da kan yan uwanmu matasan
Arewa, game da halin da wannan
kabila ke ciki, kowa yana sane da
cewa ba wata kabila a kasan nan da
bata da iyaye sai kabilarmu ta Hausa,
wadanda suke ikirarin sune iyayen to
dasu akewa kabilar zagon kasa, kuma
kowa yasan haka. A duk cikin
Hausawa babu wani mutum guda
daya da yake kare wannan kabila da
kuma kwato mata hakkinta.
Hakan tasa mu matasa ya zame mana
dole mu tashi mu karbi jagorancin
wannan kabila mu kwace ta daga
hannun makiyanta, idan kuwa ba
haka ba, wata ran za'a wayi gari
zaman Nigeria yayiwa Bahaushe
wuya. Mu tashi muyi gwagwarmaya
dan kwato hakkinmu a wurin masu
siyar mana dashi.
"Mu tashi mu farka yan Arewa mu bar
bacci aikin kawai ne" Mamma Shata.
Allah ubangiji ya bawa Arewa
jagorori nagari, masu kishinmu,
al'adarmu da addininmu. Amin.

SHIN OSAMA BIN LADEN YA RASU KO YANA RAYE?

Osama Bin Laden shine mutumin da
kasar America tafi kishirwar ganin ta
kama shi ko da rai ko babu, saboda
zargin shi yakai harin 11 September
2011 kan cibiyar kasuwancin duniya
dake America. Kuma suna ikirarin
shine shugaban 'yan ta'adda na
duniya.
A yau ne (2nd May 2011) da sanyin safiya shugaban
Kasar America Barack Obama ya bada
sanarwar cewa sojojinsa na
musamman sun kashe shugaban
kungiyar al-Qa'ida Osama Bin Laden a
wani gida dake Birnin Islamabad dake
kasar Pakistan.
Wannan sanarwa ta dauki hankalin
dukkan wani mutum dake bibiyar
siyasar duniya, wasu sunyi jimamin
abin da Allah-wadai akan wannan
munmunan aiki, wasu kuma sunyi ta
murna da jinjinawa America, akan
wannan namijin kokari da tayi, domin
suna ganin shine ya hanasu jin dadin
rayuwarsu taduniya.
Amma kuma wasu basu ma yarda da
cewar an kashe Osaman ba, saboda
rashin nuna gawarsa da ba'ayi ba.
Amma sojojin kasar American sunce
bayan sun kashe shi sunyi masa
jana'iza kamar yadda addinin
Musulunci ya koyar sannan suka
bunne shi a cikin teku.
Tabbas idan kayi nazari akan abin
zaka gane akwai wani abu a kasa,
abin mamaki ne ace a yadda America
ke neman Osama ruwa a jallo ko a
mace ko a raye, amma su samu
nasarar kashe shi basu nuna kawarsa
ba. Dukkan mai hankali yasan ba'a
binne mutum cikin ruwa kamar yadda
suka sanar.
A karshe wani abin haushi wai duk
kasashen Musulmi na duniya da
kungiyoyin Musulmi ba wata da ta fito
tayi suka akan wannan abu, su kuwa
shugabannin kasashen duniya sai
turawa da sakon goyan baya suke ga
kasar America, wai yanzu duniya zata
zauna lafiya tunda an kashe shugaban
yan ta'adda.
Allah ya taimaki Musulunci da
Musulmai a ko ina a fadin duniya.
Allah ya karawa kasashen kafirai
tsoron Musulmai. Ameen.

Tuesday, March 29, 2011

ZUWAN BUHARI KANO YA BATAWA WASU RAI AMMA BANDA NI

A yau ne General Muhammad Buhari dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam'iyar CPC ya kawo ziyarar yakin neman zabensa a jihar Kano (Cibiyar Masoyansa) tabbas taro ya kai taro, har kuwa ya fice kiyastawa, idan kuwa za'a kiyasta to za'a iya cewa a kalla mutanen da suka halarci taron zasu kai kimanin Mutum million daya da rabi ko million biyu (1.5 million or 2 million). Mata da maza, yara da manya, tsofaffi da dattijai duk sun halarci wannan gangami. A zahiri tunda nake a rayuwata ban taba halartar taro mai yawan jama'a kamar na yau ba, saboda kuwa ban taba zuwa Aikin Hajj ba, duk da kuwa a jiya da daddare aka sanar da taron a gidajen radio amma mutane sun fita taryar limamin Canji.
Baba Buharin Kanawa.

Da misalin karfe 3:30 na yamma jirgin Gen. Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda mutane sama da miliyan daya suke jiran zuwansa tunda sanyin safiya, bayan da ya sauka kai tsaye aka nufi gidan Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero don gaisuwar ban girma. Saboda cunkoson mutane da gosulon motoci ba'a samu damar zuwa gidan sarki ba, sai waje 5:30 na yamma. Daga gidan sarki kuma tawagar limamin canjin ta nufi filin sukuwa ne (Polo) inda aka tanada don yin taron, nan ma saboda yawan mutane da motoci, babura da kekuna ba'a halarci wurin taron ba sai wajen 7:00 na yammaci.

To anan abin ya batawa jama'a da dama rai, wasu kuma saboda soyayya basu nuna ransu ya baci ba, amma dai sun damu sosai, dalili kuwa jama'a masoya General Buhari tun shekarar 2003 wasu basu kara ganinshi ba, domin baizo yakin neman zaben 2007. Wasu kuwa daman ma basu taba ganinshi ba, hakan tasa jama'a suka yi cincirindo don ganin Baba, wasu sun bar suna'o'insu, wasu sun bar karatunsu, sunzo tun safe don ganin wanda suke so kuma shima yake sonsu. Akwai wadanda naji suna cewa sunzo filin nan tunda 9:00 na safe. To ko ni ma dai naje wurin ne tun wajen 10:30 na rana, baci ba sha, Sallan Azhar dai na samu nayi amma La'asar, Magrib da Isha'i duk sai bayan na dawo gida nayi su, ba don komai ba kuwa sai rashin haryan fita saboda jama'ar da suka zo don ganin Buhari. A zahiri nasha wahalar da ban taba shan irin ta ba, na sha taku wurin jama'a an mammatse ni, an bubbuge ni, an tutture ni. Amma saboda nazo ne domin Babu Buhari ko kadan ban damu ba, kuma ban nuna gajiyawa ko kosawa ba.

Duk da irin wannan wahalhalu da nasha ni da sauran jama'a abin haushi bamu samu damar biyan bukatarmu ba, domin kuwa abinda muka je don gani yayi mana nisa, a takaice General Muhammad Buhari bai samu halartar zuwa wurin taron ba, saboda wasu dalilai, wasu sunce yazo wurin taro a mota amma bai fito ba, wasu kuma sunce daga gidan Sarki ya nufi wani wurin, mu dai da muke cikin wurin taro sai labari cewa yazo muka ji amma ko rigarsa bamu gani ba.

Babban abin haushin ma aka rasa wanda zai sanar da mutane da dalilin rashin zuwansa, kuma a baiwa jama'a hakurin jiran gawon shannu da suka yi. Wannan tasa jama'a da dama suka bar wurin taro suna yan surutai marassa dadi. Wai suna cewa don kar ya daga hannun Muhammad Sani Abacha dan takarar gwamnan a jihar Kano shi yasa yaki zuwa, wasu kuma sun ce jami'an tsaro suka hanashi fitowa, saboda gari ya fara duhu.

A gaskiya dai idan akan karya daga hannun Abacha yasa yaki zuwa wurin taron to tabbas wanda ya bashi shawarar yayi hakan ya zalunci mutane, domin nasan General Buhari ko yaushe mai son ganin bai batawa jama'a ba yake, sai gashi yau ko waye ya bada shawarar yasa jama'a da dama ransa ya baci saboda Buhari abinda mukam masoya bamu so ba.

Ni dai kam tabbas nima banji dadi ba, amma dai ranna bai baci ba, saboda son da nake masa yafi karfin ya bata min rai, sai ma hakuri da na rinka bawa jama'a ina nuna musu ba laifin Buhari ba ne. Wasu sun fahimci hakan wasu kuma sunki tsaiwa ma su saurare ni akan ko suna ganin ni yaro ne ko kuma ransu ne ya baci sosai oho.

A karshe ina kira da masoya Baba Buhari da mu sake juriya da jajircewa domin wannan abu muna yin sane badan kanmu ba, sai don cigaban Nijeriya da yan Nijeriyar baki daya. Allah ya amsa adu'o'inmu ya wannan lokaci ya albarkance mu da shugabanni nagari dun daga sama har kasa a kasarmu NIGERIA ameeen.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Thursday, March 17, 2011

101 REASON WHY GENERAL MUHAMMAD BUHARI IS THE ANSWER 2011

1. Our dear country Nigeria is in dire
need of qualitative and substantive
change from retrogression of the past
twelve years under PDP to a future of
progress, beginning from May 29 2011.
This is what GMB represents and offers.
2. We are tired of broken promises
and broken down infrastructure. The
railways are gone, the shipping lines
have disappeared, roads are dilapidated
and the power situation is still epileptic
after twelve years of wasted Billions of
Dollars. GMB promises 15,000MW of
electricity by 2015 and 50,000 by 2019.
3. We want somebody that will come
and fix our roads and basic
infrastructure. GMB plans to construct
3,000km of Superhighway including
service trunks and build up to 4,800km
of modern railway lines – one third to
be completed by 2015.
4. We are tired of being ruled by the
Party of Do or Die politics and
politicians. GMB plays politics of
persuasion and policy articulation.
5. We want to be free from the ‘nest of
killers’ who can do anything for power.
We need a peaceful polity as envisaged
by GMB
6. We are tired of non-functional
refineries. GMB is set to optimise their
productions once again and initiate new
ones with the private sector. He has
done it before.
7. GMB will put a stop to the
importation of 70% of our petroleum
products when we can produce same.
8. We are tired of shameful and
disgraceful importation of petroleum
products. Prices will come down when
GMB takes over on 29th May.
9. We need solution to our secondary
school education decay where 70%
failures are recorded and the PDP is
audacious enough to seek our votes.
10. We are tired of the celebration of
corruption by the PDP. They organised a
party to welcome Bode George back
from prison where he had been for the
past two years for stealing.
11. We are tired of the PDP president
spending 100 million Naira public funds
daily for only presidential jets ’ fuelling
during campaigns while many Nigerians
are hungry, jobless, homeless and
hopeless.
12. We are tired of the negative image
of a corrupt nation stamped on us by
the PDP government ’s twelve years of
waste.
13. We are tired of a baby president
who is completely clueless about the
solutions to our problems. It is time to
separate the boys from the men. It is
time for GMB
14. We are tired of being ruled by
stooges with godfathers pushing them
like a barrow and telling them what to
do at all times. We want a real self
confident President.
15. We are tired of attempts at
introducing third term through the back
door.
16. We do not want a man who
supported, funded and campaigned for
third term.
17. We are tired of the chop I chop
government of PDP. The public till is for
all members of the Nigerian society and
this is what GMB will ensure.
18. We are tired a president that is
playing politics with University
education. He announced new
Universities to win votes, while the
existing ones are barely effective.
19. We are tired of a government that
cannot secure our lives and property. So
many lives have been lost in Jos, Port
Harcourt, Maiduguri, Bauchi,
Okerenkoko, Ayakoroma, etc
20. We are tired of an illiterate
government without an ideology,
without social and political principles
and without an understanding of
society and governance.
21. We are tired of election riggers
and government of thugs and ritualists.
22. We are tired of a government of
cult men and Ogboni members.
23. We are tired of a president that
says one thing and does exactly the
opposite.
24. We are tired of a president that will
brazenly rig his own party primaries
with impunity and still go and beg for
help from the same people.
25. We are tired of a president that
blackmailed and arm-twisted fellow
convoluted governors to win his party’s
nomination.
26. We are tired of a president who
inaugurated a presidential advisory
committee (PAC) to advice him but later
turns round to snub their patriotic
advice.
27. We are tired of a president whose
only qualification for the presidency is
goodluck.
28. We are tired of an economy in
comatose while the PDP government is
in denial.
29. We are tired of a government that
has borrowed more than $32bn in four
years for no tangible course and is set
to borrow more.
30. We are tired of a government that
spends more than 30% of its 2011
budget to pay foreign debt. A
government that makes foreigners rich
and Nigerians poor.
31. We are tired of a PDP government
that does not care about the welfare
and wellbeing of the Nigerian people
but is only pre-occupied with being in
power for 100 years. WE NEED CHANGE.
32. GENERAL MOHAMADU BUHARI (GMB)
is the answer and the change agent
because he supervised and delivered
our existing refineries as petroleum
minister and Head of state.
33. He is set to entrench true
federalism and fiscal federalism in the
body politics of the Nigerian state.
34. He is predisposed to the
restructuring of the Nigerian federation
to achieve the above.
35. He is determined to achieve a
proper devolution of power between
the three tiers of government.
36. He strongly supports the removal
of the immunity clause on criminal
matters under which governors steal
and kill.
37. He will make local councils more
accountable to the people, by making
them publish minutes of their meetings,
service performance data and items of
spending that exceed 10 million Naira.
38. He plans to reform and strengthen
the judicial system for efficient
administration of justice in the country.
He remembers that the judiciary is the
last hope of the common man.
39. He plans to create special courts
for accelerated hearing of corruption,
drug trafficking, terrorism etc., cases.
40. He will fight corruption in public
office through strict enforcement of
anti corruption laws. He did before, he
will do it again.
41. He plans to create serious crime
squads to combat kidnapping, armed
robbery, militancy, and ethno-religious/
communal clashes nationwide.
42. GMB supports the vociferous calls
for state and community police and
would work to establish the principle.
43. He plans to make Nigeria a liberal
society by removing issues such as
state of origin, tribe, ethnic and religious
affiliations and replace them with only
the principle of state of residence.
44. He plans to immediately embark on
vocational training, entrepreneurial and
skill acquisition scheme for graduates to
tackle youth and graduate
unemployment.
45. GMB will create two million new
jobs by 2015 when he ends his tenure.
46. He will create two million new
home owners by 2015 through a
nationwide mortgage system.
47. He plans to put in place a N300bn
regional growth fund for the
development of the regions of the
federation.
48. GMB has pledged to do only the
bidding of the masses and honest
Nigerians and not serve a small click of
business men as they are doing in PDP.
49. He is set to restore faith in the
Nigerian project so that no ‘Andrew’ will
check out again.
50. He will strengthen INEC and
reduce/eliminate electoral malpractices.
51. He will institute a process of full
disclosure of government business to
the public.
52. He will build the capacity of law
enforcement officers to do their work
effectively.
53. He will work to end acute poverty,
inequality and insecurity in the country.
54. He is completely detribalised and
has the reputation of being a bridge
builder.
55. He is willing and able from day one
and does not have to learn on the job
like Lucky.
56. He is well loved by the people of
Nigeria across the North, South, East and
West.
57. He will fight for the welfare and
well being of the people.
58. He has a wife that is quite and
knows her place in the society unlike
others who cannot draw a line.
59. GMB commands the respect of all
political and traditional leaders in the
country.
60. He will lead in accordance to the
constitution and would not twist the
constitution to favour his party or a
narrow interest like they do in PDP.
61. He is set to restore hope and
respect in politics so that more honest
and decent people like you can go into
it.
62. His driving philosophy in politics
and governance is ‘knowledge is
Power’.
63. Only GMB has the structure,
personality, temperament and character
to stop the drift in government and
bring direction back to public
administration.
64. What he did in road construction
while in the PTF has not been matched
by 12 wasted years of PDP who have
squandered billions of naira building
nothing.
65. As Head of state, taking over from
the Pre-PDP government of Shagari, GMB
reduced inflation from 23% to 4% in
twenty months only.
66. In his regime, there was no single
religious crisis unlike what we have
today with PDP.
67. He put a final stop to the Maitasine
sect in Kano. Today we have Mend, OPC,
Boko Haram etc and the PDP is watching
in amazement with.
68. As Head of state, he stamped out
corruption in public office by making
politicians to be held accountable for
their actions while in office.
69. Hospitals and Universities in the
country have not received more
benefits from PDP than they did from
PTF under GMB.
70. As former petroleum minister and
former Head of state, GMB owns no oil
block, no petrol station unlike the PDP
presidents.
71. GMB is the answer because he has
followership across the country which
money cannot buy. Do you know that
PDP pays people to attend their rallies?
72. He is the Leader of the Masses and
the Talakawas. Mr. Integrity and Mai
Gaskiya.
73. The oppressors and political
gladiators fear him and love to stop him
but the Masses love him and would do
all in their might to steer him to victory.
74. He is very liberal in his religious
beliefs and that was why he appointed
a Pentecostal and Charismatic Pastor as
his vice.
75. GMB is the only former Nigerian
leader who does not own a house or
Land in Abuja. Amazing!
76. He is the first Head of state to
promote affirmative action for women
in Nigeria by directing that all state
cabinets must have female
commissioners.
77. His achievements in twenty
months as Head of state dwarf those of
all who came after him especially the
now ending inept and corrupt 12 years
of PDP.
78. He is the most capable, competent
and creative candidate in this years ’
presidential election. He has been
military governor, petroleum minister,
Head of state and chairman Petroleum
Trust Fund (PTF).
79. Many people do not know that it
was while working with PTF that Dora
Akunyili was discovered and it was
because of her antecedents working
with GMB that Obasanjo appointed her
into NAFDAC. See what PDP has done to
her reputation.
80. GMB from the outset has identified
with the poor masses in all his
endeavours. That ’s why he is called the
People’s general. Now he will be called
the ‘People President’.
81. His main opponent identifies with
the rich. His close friends include, Femi
Otedola, Aliko Dagote, Jim Ovia, Jimoh
Ibrahim, the Anyiam Osigwes, James
Ibori, DSP Alamieyeseigha, Peter Odili,
Ebitimi Banigo, Olusegun Obasanjo,
Anthony Anenih, etc who all have one
thing in common.
82. While GMB is being backed by the
masses, others are being sponsored by
the enemies of the masses.
83. No single money bag is bank
rolling his campaign unlike the PDP.
84. GMB is the answer because as
Head of state, he introduced the War
Against Indiscipline (WAI) which gave
birth to discipline, patriotism, the queue
culture and the monthly sanitation
exercise in Nigeria among other things.
85. GMB has never had a case with
EFCC while some at the helms now will
continue their case in EFCC when they
leave office on May 29th 2011.
86. GMB will permanently solve the
problem of violence in the Niger Delta
originated by Lucky and his friends.
Many people do not know the level of
involvement of the PDP government in
the Niger Delta crisis.
87. GMB represents change, hope,
progress and honesty in Nigeria.
88. He is incorruptible.
89. He is honest, credible, hardworking
and patriotic.
90. He loves Nigeria more than
himself. This is evidenced in his dogged
determination to fight for the masses
the third time at the presidency.
91. He is a master strategist and
organiser cum mobilize. He built with
the masses a political movement into
the fastest growing national political
party in the world in less than two
years.
92. He is from a humble background
and worked his way to national
recognition. He is set to do the same to
millions of Nigerian youths who need
Mentoring.
93. GMB represents the last set of the
Murtala legacy and is set to ignite the
sparks of that regime with actions and
actions on all aspects of the polity with
his team.
94. GMB was the only Head of state
that devoted and committed more that
26% of the nation ’s budget to
education.
95. He is not anybody’s stooge. The
third campaigners cannot claim same.
Can they?
96. GMB is well respected and
recognised by the international
community as a committed anti-
corruption crusader.
97. GMB discouraged drug trafficking
when he was Head of state. The menace
increased when he left office but will be
banished again.
98. He is ready and willing to bring
back confidence to Nigeria ’s economy
by tackling headlong the problems of
insecurity and lack of infrastructure.
99. GMB is the answer to our problems
now because he understands them and
knows how to tackle them. The PDP is
completely bereft of any idea on how to
move our nation forward.
100. GMB He is the epitome of sincerity,
honour, and integrity and will keep his
promise to Nigerians, unlike those who
cannot even keep a gentleman ’s
agreement in their party.
101. GMB IS THE ANSWER BECAUSE ONCE
AGAIN NIGERIANS NEED HELP.
Signed,
OBORO ANDAOLOTU
POSITIVE ACTION FOR SOCIAL JUSTICE
(PASOJ)

Saturday, March 12, 2011

WHO IS AFRAID OF BUHARI?

I write this because of millions of Nigerians
who are below 30 and who constitute a
significant chunk of our voting population.
This is the ICT generation that is largely
ignorant about the events of the Buhari era
(1983-85) and so can be misinformed and
misled by needless propaganda. I have sat
with many in the under-30 bracket and
those slightly above who only have faint
recollections of the Buhari era and the level
of ignorance about that era is amazing.
Before being MILITARY Head of State, Buhari
had been Governor of one of the Northern
States (under Obasanjo’s Military
government) as well as Minister for
Petroleum. He later served as Chairman of
PTF under Abacha.
Please consider the following unassailable
facts:
* he birthed and supervised the
establishment of our existing refineries.
* there was no religious crisis while he was
Head of State. It started under his successor
IBB!
* in his time as Head of State he reduced
inflation from 23% to 4%, by fiscal
discipline and a homegrown economic team
(not achieved under any other era, even
military).
* JJ Rawlings of Ghana took over 2yrs
before him, and killed all the corrupt leaders,
while Buhari only sentenced the corrupt
leaders here to prison
* Under his watch as PTF Chairman, what he
did in road construction in that short period
hasn’t been matched by 12yrs of the PDP
* hospitals and universities around the
country never witnessed as much benefits
as they got from the PTF from any
government after or before his time.
* despite serving in senior capacity in the
oil sector, first as Minister for Petroleum and
then Petroleum Trust Fund, Buhari has no
petrol station, much less a rig, refinery or an
oil block like so many of our leaders.
* He could have retired into nauseating
opulence like an IBB or Danjuma or even
OBJ but didn’t
* Instead of hobnobbing with the high and
mighty, he has cast his lot with the ordinary
man most of who follow him out of hope
and belief in his values. People who know
him have said of him… “All I need from
Buhari is his word, I can take it to the bank”.
* he is the only politician in the North today
who fills rallies without renting a crowd.
The Kaduna rally of 2nd March is eloquent
proof!
* He refused to collect an allowance while
serving as Chairman of the PTF because he
said since he was already drawing a
pension from government, his conscience
would not allow him to draw another salary
from the purse of the same government
* He is the only former head of state that
does not own property or land in Abuja.
* Every attempt to rubbish him through
probes in time past eneded up vindicating
him! The man who was asked by OBJ to
take over the running of PTF before it was
scrapped with the aim of probing and
indicting Buhari, was the one who ended up
being prosecuted for misappropriating
$100m of PTF funds! Buhari again, was
vindicated
* He has OPENLY challenged those who
accuse him of religious fundamentalism to
come out and show proof. No one has till
today, taken up the challenge. His personal
driver of many years is a Christian from
Plateau State!
* Nigeria was only invited to OIC in
observer status. IBB took us into full
membership. This is a quote from a 2001
write-up by Prof Omoruyi, one of
Babangida’s hatchet men. “The period of
General Babangida (1985-1993)
represented the beginning of unmitigated
Islamization of Nigeria. General Babangida
was one of the loyal followers of General
Murtala. This was why General Babangida
took the fateful decision in 1986 to face the
Nigerian Christians in particular and
Nigerians in general with the plan of
Muslims. He without the approval of the
governing organs of the Federal Military
Government organized a mission led by a
non-member of the Government, the Sultan
of Sokoto to formally admit Nigeria into the
Organization of Islamic Conference (OIC).
When the Chief of General Staff, Commodore
Ebitu Ukiwe complained that he knew
nothing about it and definitely said that he
could not remember the matter coming to
the Armed Forces Ruling Council (AFRC), he
was shown his way out.
* His government initiated the War Against
Indiscipline that has made environmental
cleanliness, queuing up, not urinating by the
roadside etc features of our national life
even till today
Does it then surprise you why corrupt
people would be spreading such heinous
rumours about Buhari? He is a threat to
them and they know what he is capable of
doing to corruption and corrupt people
when he comes into office! So shine your
eyes and make the right decision.
If honesty and probity are the things you
want for Nigeria, now is the time to choose
right. When you cast your vote for the
BUHARI/BAKARE ticket, you would have cast
one vote for two honest men.
Now that you know better, will you please
educate another person BY FORWARDING
THIS TO AS MANY AS YOU CAN

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
+2348032493020