Friday, July 29, 2011

TSARABAR WATAN AZUMI

Azumi a addinin Musulunci na nufin kauracewa cin abinci, shan ruwa, fadin munanan maganganu, shan taba, saduwa tsakanin ma'aurata da kuma dukkan wani aiki da ya sabawa koyarwa addinin Musulunci tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana da nufi bautawa Allah madaukakin sarki.

Azumi na daya daga cikin shika-shigan Musulunci guda biyar, haka tasa ya zama wajibi ga dukkan Musulmin da ya balaga, a duk watan tara (Ramadan) na shekarar Musulunci kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Al Kur'ani mai girma inda yake cewa "Ya ku wadanda suka yi imani, mun wajabta azumi a gare ku kamar yadda muka wajabtawa wadanda suka gabace ku, domin ku kara tunawa da Allah" Q2:V183

A watan Ramadan Allah ya saukar da Al Kur'ani mai tsarki ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Watan azumi wata ne na rahma, alfarma, gafara da karbar addu'a. Wata ne da dukkan wani Musulmi ke kara zage dantse wurin ibada da kyautatawa yan uwa Musulmai don samun rahmar Allah.

Amma abin mamaki wasu daga cikin Musulmai na yin amfani da wannan wata mai albarka wajen kara tsauwalawa yan uwa Musulmai, misali wasu daga cikin yan kasuwa da zarar watan azumin ya kusanto sai su fara tashin farashin kayan masarufi kamar shinkafa, nama, lemo, kayan miya da sauran kayan masarufi saboda ganin ya zama wajibi ayi amfani dasu, saboda duk wanda ya sha ruwa zaiso yadan karya da abinci mai dan dadi.

Haba bayin Allah, shin mai zai sa ba zamu rinka rage farashi ba idan watan azumin yazo sai akasinsa, shin bama ganin yadda yan kasuwa mabiya addinin Kirista ke yi ne idan lokacin Kirismeti yazo zasu rinka rage farashin kayayyaki, bai kamata a ce su suke wannan aikin kyautatawa ba mu ba.

Wasu ma daga cikin yan kasuwan namu suna siyan kayan ne suna boyewa kafin watan azumin don idan watan yazo su sami riba mai yawa. Haba yan uwa, mu tuna fa komai yawan wannan riba da zamu samu Allah bazai taba sa mata albarka ba. Shin ina ta shekarar da ta gabata? Shin wane amfani tayi mana nasan wadannan tambayoyi zasuyi wahalar amsawa.

Sai dai ko yaushe na Allah basa karewa, wasu bayin Allah daga cikin yan kasuwan su kuma suna yin iya kokarinsu kanin sun kyautata a wannan wata mai albarka, suna rage farashin kayansu ko da kuwa zasu tashi babu ribar komai, amma sai kaga saboda Allah yasa albarka sunfi yan uwan nasu walwala da jin dadi, ga kuma lada mai tarun yawa da yake can yake jiransu ranar alkiyama.

A karshe a matsayinka na dan kasuwa yi kokari ka rage farashin kayanka koda kuwa kana ganin ba zaka samu riba da yawa ba, idan Allah ya sawa abinda zaka samu komai kankantarsa albarka yafi wanda zaka samu komai yawansa marar albarka. Sannan ya kamata mu yi kokarin ciyar da junanmu koda da kwayar dabino guda daya ne.

Allah ya karbi ibadunmu a wannan wata mai albarka, Allah yasa muna cikin wadanda za'a yanta a yi musu gafara, Allah ya taimaki yankinmu na AREWA ya kara daukaka shi tare da kasarmu Nigeria baki daya.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Saturday, July 23, 2011

Kamfanin Google yayi wa shafin Facebook kishiya

Kamfanin Google ya gabatar da sabon shafin sada zumunta mai suna Google Plus (Google+) wannan shafi zai bawa masu amfani dashi damar karba da aika sakonni, zuwa ko ina a fadin duniya, wato shafin yayi kamanceceniya da shafukan Facebook da Twitter da kuma mySpace, duk da shugaban kamfanin na Google Larry Page ya musanta cewar shafin an kwaikwaiyi wani shafi ne na daban.

Bayan fitowar wannan shafi mutane da dama a fadin duniya sun tofa albarkacin bakinsu game da shafin, inda wasu ke ganin shafin ya fi dukkan shafukan da muke amfani dasu a halin yanzu a duniyar yanar gizo, inda wasu kuma ke ganin ina ai shafin Google yayi nisan da ba wani shafin sadarwa da zaizo ya kamo shi nan da kusa, inda shafin ke da masu amfani dashi sama da 720 miliyan.

A halin yanzu shafin na amfani akan kumfutoti da kuma manyan wayoyi irin su iPad, Apple da sauransu. Ga mai sha'awar yin rijista a wannan shafi zai ziyarci (plus.google.com) don ganin wainar da ake toyawa.

Shafin Google Plus cikin dan lokaci kalilan har tara masu amfani dashi sama da 20 miliyan, ciki har da mai kamfanin Facebook Mark Zuckberg. A nazarin da jaridar New York Daily ta kasar Amurka da gabatar tabbatar da cewa babu wani shafin sadarwa da ya samu irin wannan daukaka cikin dan kankanin lokaci, hakan tasa ake ganin lalle shafin zai zamewa shafin Facebook babban kalubale, duk da wasu masana harkar sadarwa sun nuna cewa wannan tagomashi da shafin ya samu ya same shine da taimakon shafin Facebook da Twitter, domin tun lokacin da kamfanin na Google ya sanar da aniyarsa ta yin Google+ din, masu amfani da shafukan suka rinka sanarwa abokanansu na sassan daban daban na duniya. Tabbas nima zan iya yadda da hakan domin nima na samu labarin wannan shafi ne daga wuri wani abokina dan kasar India.

To koma dai menene dai, fatanmu Allah ya bawa jama'armu basirar yin amfani da wannan shafuka da hanyar da baza sabawa addininmu na Musulunci ba, Allah ya bamu ikon yin amfani da wannan shafuka na sadarwa wajen yada addinin Musulunci.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Friday, July 15, 2011

TSARIN BANKIN MUSULUNCI BA A NIGERIA AKA FARA BA

Bankin Musulunci, wato bankin da ba'a bada kudin ruwa (Riba), ko kuma ba da rancen kudaden jama'a ga wuraren daya sabawa addinin Musulunci, kamar kamfanonin giya. Bakin Musuluncin ya samu karbuwa a kasashen daban daban na duniya.

Daga cikin kasashen dake amfani da irin wannan tsari na bankin Musulunci sun hada har da kasashen Kiristoci kamar su United States, United Kingdom, Germany da France.

Sai kasashen yankin Asia dayawa su ma na amfani da wannan tsari kamar Indonesia, India, Pakistan, Bangladash, Malaysia da Afganistan.

Dukkan daukakin kasashen larabawa na amfani da irin wannan tsari kamar Saudi Arabia, Yemen, Qatar, Dubai, Iraq, Kuwait, Iran duk na amfani da irin wannan tsari.

Hatta kasashen Afrika irinsu South Africa, Egypt, Senegal, Gambia, Niger, Kenya, Tanzania, Algeria, Libya, Tunisia, Morocco da kuma jamhuriyar Benin duk sun rungumi wannan tsari hannu bibiyu.

Shin idan wannan kasashe zasu rungumi wannan tsari mai zai sa Nigeria ba zasu rungume shi ba. Nigeria fa na daya daga cikin kasashen duniya da suka fi yawan Musulmai.

Bankin Musulunci, banki ne daya samar da tsari kala kala ga Musulmi da wanda ma ba Musulmin ba, wannan tsari bai sabawa kudin tsarin mulkin Nigeria.

Shin mai zai sa wasu daga cikin jama'ar kasar nan basa goyan bayan wannan tsari? Shin mai zai haifar musu idan anyi shi? Nasan duk abinda bai haifarwa kasar America matsala ba, to ba zai taba haifarwa Nigeria ba. Shin wannan tsarin da muke kai yanzu, tsarin wane addini ne, Musulunci ko Kiristanci? Kowa na sane da cewa tsarin Kiristanci ne, tunda muka hakura muka bi wannan tsari shekara da shekara mai zai sa zasu ki goya mana baya muma muyi namu. Bafa cewa akayi za'a daina kowane tsari ko a koma na Musulunci ba, a'a kowa zaiyi nashi ne. Kuyi naku muyi namu.

Mutane da dama na zargin Sanusi Lamido Sanusi da cewa shi ya dage sai an kawo wannan tsari, Sanusi shi ma zuwa yayi ya tarar kuma yake so dorawa. Wannan tsari tun lokacin Joseph Oladele Sanusi yana matsayin gwamnan babban banki ya aika takardar neman amincewa zuwa ga JAIZ International PLC Sannan kuma a lokacin Charles C. Soludo JAIZ ya tambatar da amincewar.

Don haka shi kuma Sanusi ke son bankin ya fara aiki a lokacinsa.

A karshe muna yi wa Sanusi Lamido Sanusi fatan nasara a wannan aikin na alkhairi. Allah ya taimake shi.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Wednesday, July 13, 2011

Takaitaccen Tarihin Dr. Abubakar Imam

An haifi Alhaji Dr. Abubakar
Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.)
N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin
garin kagara sa’an nan tana cikin
lardin Kwantagora, yanzu kuwa
Jihar Neja. Ya Yi makaranta a
Katsina Training College kuma ya
kama aikin malanta a Makarantar
Midil to Katsina a shekarar 1932.

Yana da shekara 22 ya rubuta
`Ruwan Bagaja’. Ganin kwazonsa
wajen Raga labari mai ma’ana ya
sa Dr. R.M. East shugaban
Offishin Talifi na Zariya ya roki a
ba da shi aro daga Katsina ya yi
aikin rubuce rubuce a Zariya.
Bayan ya koma Katsina aka bi shi
da rokon ya kara rubuta wasu,
littattafan. A can ya rubuta
‘Karamin Sani kukumi’ cikin 1937.

A cikin shekara 1938 sai
Gwamnan Kaduna ya roka a
dawo da Imam Zariya a koya
mashi aikin edita ya zama editan
jaridar farko to Arewa. Shi ne ma
ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi
Kwabo’ aka fara bugawa a
watan Janairu na shekara 1939.
Ya yi shekara 12 yana wannan
aiki na edita har ma ya rubuta
wani littafi a lokacin `Yakin
Duniya Na Biyu’ watau `Yakin
Hitila’ da ya ba suna `Tafiya
Mabudin Ilmi’. Wannan littafi ya
ba da Iabarin tafiyarsa tare da
wasu editoci na jaridun Africa to
Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa
a shekara 1943.

Wani mashahurin littafi kuma da
ya rubuta shi ne ‘Tarihin Annabi
da na Halifofi’ wanda aka fara
buga shi a shekara 1957 lokacin
nan yang shugaban Hukumar
Daukar Ma’aikata to Nijeriya to
Arewa.
Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka
fara nadawa Kwamishinan Jin
Kararakin Jama’a a shekara 1974
a Jihar Kaduna, lokacin ana
kiranta Arewa to Tsakiya. Ya rasu
yana da shekara 70 a duniya
ranar Juma’a 19 ga watan Yuni,
1981.

Alhaji Abubakar Imam ya rike
cewa wannan aiki da ya yi, na
talifin ‘Magana Jari e’ ya yi masa
amfani ainun. Ya kan ce wannan
aiki shi ne ya ba shi damar zama
tare da mashahurin Baturen nan
na talifin Hausa, Dr. R.M. East,
O.B.E. Ya ce daga gare shi ne ya
koyi duk dan abin da ya koya na
game da talifi.

Abin mamaki, shi kuma wannan
Bature, Dr. East O.B.E., a wajen
`Mukaddamar’ da ya yi da
Turanci tun farkon buga ‘Magana
Jarice, ga. abin da ya ce : ‘Muna
godiya ga En’e ta Katsina, saboda
da taimakonsu, da hangen nesa da
suka yi, har suka yarda,suka bamu Malam Abubakar Imam.
Suka yarda, ya bar aikinsa, na
koyar da Turanci a Midil to
Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi
wata shida domin ya taimake
mu, mu sami wadannan
littattafai a cikin harshensa.

`Iyakar abin da mu ma`aikatan
wannan ofis muka yi, na game
da talifin wadannan littattafai,
shi ne aiki irin na ofis, na shirya
al’amuran, yadda suka kai har
aka buga su. Ban da wannan sai
su kuma taimakonsa da muka yi
na tattara masa littattafai iri iri,
don ko zai kwaikwayi wani
samfur. Sai fa kuma wajen
shiryawa bayan da ya rubuta.
‘Kai, in dai har muna da wani
abin da za mu yi kirari mun yi,
game da talifin wadannan
littattafai, to, babban abin
kirarimmu kawai, shi ne yadda
muka yi har muka binciko
wannan malamin talifi’.

Monday, July 11, 2011

KANO TA DABO TUMBIN GWIWA

KANO na daya daga cikin manya manyan jihohin Nigeria dama yammacin Afrika baki daya. Kano tsohon gari ne daya haura sama da shekaru 1000+ da kafuwa.

Kano babban gari ne mai dauke da jama'a masu tarun yawa, sama da miliyan tara 9,000,000 kamar yadda hukumar kidaya ta kasa ta tabbatar a kidayar da ta gabata a shekarar 2006. Kuma itace jihar da tafi kowace yawa jama'a a Nigeria da yankin yammacin Afrika.

Wannan yawan jama'a da Kano ke dashi ya samo asali ne sakamakon shahara da garin yayi ta fannoni da dama kamar: Ilmi, tattalin arziki, Kasuwanci, karbar baki, zaman lafiya da sauran dalilai da dama. Tun kafin zuwan turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya Kano tayi kaurin suna wajen wadannan fanni, inda al'umma daga sassan duniya daban daban ke kwararowa don neman ilmi ko kasuwanci.

Kano gari ne daya tara manyan Malam addini, manyan attijirai, manyan sarakai, manyan masu ilmin zamani, manyan komai da komai ciki har da manyan barayi da yan iska. Hakan tasa akewa Kano kirari da "Koda mai kazo an fika" wasu sukewa garin kirari da cewa "Kano ta dabo tumbin giwa, mai mata mai mota, mai Dala da Goron Dutse" ko kuma ace "Jalla babbar Hausa" da sauran kirari dai kala kala na girmamawa.

Mafi yawan mutanen Kano yan kasuwa ne musamman wadanda suke zaune cikin gari, sai kuma manoma da suke zaune a garuruwa kamar Kura, Rogo, Gaya, Dambatta da sauran garuruwa da dama.

Duk wannan martaba da muhimmanci da garin ke dashi amma yanzu a wannan zamanin na siyasa kullum Kano koma baya take samu ba ci gaba ba, garin babu wutar lantarki, babu isasshen ruwan sha, babu kyawawan magudanen ruwa, babu tsari wurin gine gine kullum sai cunkushewa ake yi wuri daya. Babu sana'ar yi a wurin mafi yawan matasa, wanda kuma matasan suka dogara da ita, ko yaushe sai tabarbarewa take yi, amma har yanzu an kasa daukar mataki.

Misalin an bawa yan China dama suna shigo da hajarsu daga kasarsu suna talla, da kuwa mutanen Kano ke zuwa kasashen nasu suna siyowa, suna kuma tafiya musu abinda suke bukata daga nan suna siyarwa a can. Wannan shigowa da yan kasashen waje ke yi da hajarsu zuwa Kano ba karamin nakasu bane ga kasuwancin mutaten Kano, amma har yanzu masu ruwa da tsaki akan abin sunki daukar matakin komai akan wata manufa tasu daban. Haka tasa ake samun karuwar masu zaman kashe wando kullum a Kano.

A shekarun baya kafin wadannan matsalolin su addabi Kano garin yana da kayatarwa, burin duk wanda bai taba zuwa Kano ba yazo ya sha kallo, amma yanzu abin ba haka yake ba. A wancan lokacin ne garuruwa ke daukar salo kala kala a wurinmu, gwamnonin sauran jihohi da sarakuna ke kawo ziyara Kano akai akai ba don komai ba, sai don idan sun zo su ga wani sabon abinda basu san dashi ba, wasu ma daga cikinsu har filaye suka siya suke gina gidaje.

Fatana masu fada aji zasu yi duba irin na basira, su samowa Kano da mutanen ta mafita, Kano ta koma Kanon da aka sani tun tuntuni. Don kuwa Kanon yanzun ba Kano bace kawai suna ne.

A karshe Ya Allah ka daukaka wannan gari na masoya Fiyayyen Halitta bawanKa wanda bai taba saba ma ba, Annabi Muhammad (SAW). Ya Allah ka karawa wannan gari Albarka, zaman lafiya gami da yalwar arziki.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

Sunday, July 3, 2011

KAMUN DA HUKUMAR SSS TA YI WA SU EL-RUFA'I BAYA NUFIN KOMAI SAI ADAWAR SIYASA

A safiyar ranar 2nd July, 2011 ne hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS ta kama tsohon Ministan birnin tarayya Abuja Mallam Nasir el-Rufa'i tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar CPC a filin jirgin saman kasa da kasa na Nmandi Azikiwe dake birnin tarayya Abuja. Jim kadan da saukarsu daga birnin London, inda suka raka dan takarar shugaban kasa a zaben 2011 Janar Muhammad Buhari a wata mukala da aka shirya game da zaben da ya gabata a watan April.

Mutane da dama na ganin wannan kamu da aka yi wa su el-Rufa'i an yi shine ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, kawai dai an kama su ne saboda adawa irin ta siyasa da gwamnati me ci a yanzu ke yi da Janar Muhammad Buhari, domin kuwa a lokacin da el-Rufa'i ya dawo Nigeria daga England a shekarar da tagaba bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Alhaji Umar Musa Yar'adua, bai samu matsin lamba ba ko kadan, amma tun daga lokacin da ya nuna bangaren da yake goyan baya a siyasa nan suka fara takun saka da gwamnati. Tun daga lokacin ake ta kakalen laifin da za'a lika masa a kama shi amma ba'a samu ba.

Da manema labarai suka nemi jin dalilin kama tsohon ministan, mai magana da yawun hukumar Uwargida Marilyn Ogar tace ''An kama tsohon Ministan ne saboda wasu tambayoyi da zasu yi masa game da wasu kage da yayi wa gwamnatin tarayya, wanda aka wallafa a jaridar National Daily ta ranan Juma'a da ta gabata. wanda kuma a cewarta maganganun da ya fada ba gaskiya ba ne''

Uwargida Ogar ta bayyana cewa kagen da Mallam el-Rufa'i yayi wa gwamnatin Nigeria ya sabawa "Freedom of Information" (FOI) amma kuma bata yin gamsasshen bayani akan kagen ba.

Janar Muhammad Buhari ya bayyana cewa a gaggauta sakin el-Rufa'i da sauran mutane da ake tsare da su, sannan kuma yace ko kadan hakan bai kamata ba, don kuwa maganganunsa basu sabawa kundin tsarin mulki ba.

A mukalar el-Rufa'i ta ranan 1st July, 2011 ya bayyana irin magudan kudin da Nigeria tayi kasafin wannan shekara, kuma ya tabo kasafin kudin shekarar da ta gabata idan kuma ya tabbatar da cewa ko kadan wadannan makudan kudade da aka batar basu amfanar da dan Nigeria da ita kanta Nigerian komai ba. Ya bayyana kudaden da kasar ta samu dalla-dalla. Wanda hakan gwamnati dake ganin ya sabawa dokar bayyana yancin fadin bayyanai (FOI).

A gaskiyance maganganun Mallam el-Rufa'i basu sabawa doka ba, ko kudin tsarin mulki, ko wata hukuma ta daban. A matsayin shi na dan kasa kuma mai bibiyar al'amuran mulkin kasar yana da yancin fadawa talakawa irin bada kalar da watandar da ake yi da kudaden su, tun da kuwa kasar na tafiya ne akan turbar demokradiyya.

To a karshe abin tambayar anan shi ne su sauran manyan jam'iyyar CPC da aka kama su tare menene makomarsu? Wane dalili yasa aka kama su? Ko su ma rubutun suka yi wanda ya sabawa (FOI)? Ko daman suna da wani laifi na daban? Tabbas ni kam a tunani na wannan kamun an yi shi ne da wata manufa ta daban, ba wai akan rubutun da Mallam Nasir el-Rufa'i yayi ba.

Allah yana bayan mai gaskiya!!!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020