Wednesday, October 12, 2011

Ibada ko Siyasa? Sunan Kwankwasiyya a Gidan Alhazan jihar Kano a birnin Makkah

Hausawa suka ce wai "Sabon salo kidan ganga da lauje" kullum siyasar kasar nan sai zama take yi gara jiya da yau, misali idan yau wannan mai mulki wa'adinsa ya kare wani kuma ya karba, sai kaga talakawa na murnar an samu canji, amma da zarar wanda ya hau an fara ganin rikon ludayinsa sai kaji talakawan sun dawo suna fadin ai gara na jiya dana yau. Ko me ke kawo haka oho. Ko kuma mu duk haka muke Nigeria ba'a zuciyarmu take ba, bama son canji da ci gabanta, mun fiso mu zauna kurar baya kodayaushe, Allahu a'alamu.

Ba komai ne ya sanin fadin hakan ba, sai ganin yadda masu mulki ke wuju - wuju da shafawa talakawa jan baki, ba tare da suna sara suna duban bakin ga tarinsu ba. Anan zanyi misali da siyasarmu ta jihar Kano, wadda masu iya magana ke yiwa lakabi da "Siyasar Kano Sai dan Kano" A lokacin da tsohon gwamna, wadda ya mayarwa da sabon gwamna dake kan karagar mulkin jihar yanzu, bana mantawa duk lokacin daya gudanar da wani sabon abu musamman a bangaren addini, sai kaji ana kiran wai ai fakewa yake da addini yana wawashe kudaden talakawa.

To sai gashi yanzu bayan shudewar tsohuwar gwamnatin, masu shafa jan baki da jar hula suka cigaba da jan ragamar gwamnatin, sai suma suka shigo da sabon salo kala - kala. Wanda duk abin dake faruwa ba wanda ya bani mamaki kamar wannan. Abin mamaki shine kuwa yadda itama sabuwar gwamnatin ke neman aron mayafin tsohuwar gwamnatin ta yafa, wato itama ta fake da addinini ta wawashe kudaden talakawa. Domin kuwa hatta a bangaren aikin Hajjin bana ma sai da gwamnatin tasa siyasa a ciki. Saboda a gidan da alhazan jihar Kano ke yada zango a birnin Makkah sai da aka rubuta KWANKWASIYYA HOUSE da baro - baron rubutu yadda ko makaho ya shafa zai ji alama. Ba a iya nan sabuwar gwamnatin ta cuso harkokin siyasa ba, bangaren aikin Hisbah da kwamitin Shari'a ma duk haka abin yake.

A karshe ba ina kare wani bangare bane, ko goyan baya tsakani wadannan gwamnatotin biyu, kawai ina son na aika wani sakona ne zuwa ga wadanda abin ya shafa don susan tuni mun gane duk wani shiri da suke yi don wawashe dukiyar talakawa.
Fatanmu Allah ya bawa wannan sabuwar gwamnati ta masu jar hula karin gwiwar yi mana aiki da kawowa jiharmu ci gaba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

3 comments:

  1. naji dadin karanta wannan zance matuqa.

    ReplyDelete
  2. Ni ina ganin sun fara campaign din takarar shugaban maha....2011

    ReplyDelete
  3. Malam bashir kaji tsoron Allah, ko wanda ba dan kano bane ya san waye kwankwasiyya da kuma dalilin rubuta kwankwasiyya a jikin gine gine, wannan ai hassada ce ka kasa boye wa a zuciyar ka, kuma yanzu in Allah ya tashe ka a gaban sa ya ce maka meye shaidar ka na cewa kwankwaso yana wawashe kudin talakawa, me zaka ce? A karshe ina roko da ku daina hassada, kyashi da bakin ciki, kasan dai a duk family din ku ba wanda ya kai kamar kwankwaso, ni dan kano ne, ban san ku ba, ban san asalin ku ba da dai sauransu.
    DA KA CI MUTUNCIN KWANKWASO, GARA KA RUNGUMI TRANSFORMER MATUKAR MUNANAN!!! sai a kiyaye

    ReplyDelete