Wednesday, September 14, 2011

Lambar Mutuwa 09141 Karya ko Gaskiya?

Duk mutumin da yace kace bai ji labarin jita-jitar 'Lambar Mutuwa' ta 09141 a yau 14 September 2011 kai tsaye zance shi ba dan asalin Nigeria, ko kuma nace baya kasar a halin yanzu.

Wannan jita jita ta lambar mutuwa ta cika shafukan yanar gizo, inda ake cewa idan an kira mutum da lambar 09141 a wayar tafi da gidanka kuma ya amsa kiran nan take zai mutum, hakan tasa aka sawa lambar suna 'The killer number' wato lambar mutuwa.

A irin wadannan jita jita akwai wadda ake cewa wai mutane sama da 10 sun mutu sakamako amsa kiran da sukayi daga wannan lamba ta mutuwa a karamar hukumar Wukari dake Jihar Adamawa, duk da har yanzu babu tabbacin hakan daga majiya kwakkwara.

Duk da a matsayinmu na Musulmai mun tabbata babu mai kashewa da rayawa sai Allah don haka ko kadan ba zamuyi imani da cewa wannan lamba ce ke kisan ba, sai mu yarda idan itace sanadin mutuwar mutum to tabbas sai ya mutum koda idan an kira shi da ita bai amsa ba, saboda haka ya kamata muke lura da irin mu'amalar da zamu ke yi da mutane musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo. Kowa dai yana sane da irin yadda matsafa suka cika irin wadannan shafuka, kuma wannan lamba ko shakka babu tsafi ne.

Wasu kuma na ganin kawai wani ne ya zauna ya kirkiri jita jitarsa ya rinka yadawa, domin lambar da ake amfani da ita tayi daidai da kwanan wata da shekarar da muke ciki a yau. Misali 09 = September 14 = Kwanan watan 1= 2011. Ko ma dai menene fatanmu Allah ya kare Musulunci da Musulmai duk inda suke a fadin duniya.

Don Allah ka sanar da wanda bai sani ba! Save innocent life!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020

Manyan Matsalolin Dake Addabar Ilimi a Arewa

Ilimi ba karamin muhimmanci da dajara ke gare shi ga al'umma maza da mata, yara da manya ba, domin da ilimi ne zamu koyi yadda zamu bautawa Ubangiji mahaliccinmu. Ilimi shine kashin bayan duk wata kasa da ta cigaba ta bangaren tsaro ko tattalin arziki, da ilimi ne zamu koyi zaman duniya da mutane daban daban, ba tare da kowa na gaba da kowa ba, da ilimi ne ake banbance abu mai kyau da marar kyau, sannan ilimi ne ke bawa likitoti damar duba marar lafiya har su gane me ya dame shi, kuma su bashi magani ya samu lafiya da taimakon Allah.

Duk da irin wannan muhimmanci na ilimi, da irin rawar da yake takawa ga zamantakewar al'umma, amma abin mamaki da haushi gwamnati da sauran al'umma sun kasa maganin matsalolin dake addabar ilimin musamman a wannan yanki namu na Arewa, kadan daga cikin matsalolin sun hada da:-

Rashin kulawar da ta kamata daga gwamnati da sauran jama'ar gari, wannan rashin kulawa da ilimin baya samu ta wadannan bangarori, hakan ya kawo babban nakasu ga ilimin a Arewa.

Rashin tsayawa da iyaye basa yiwa 'yayansu wurin ci gaba da karatu na zamani a manyan makarantu, saboda lokacin da ilimin yazo yankin kakanmu na ganin za'a koyawa 'yayansu (Iyayenmu) addinin Kiristanci, wannan matsala har yanzu tana addabar ilimi a wannan yanki namu.

Wata babbar matsalar dake kara zama nakasu ga ilimin itace, shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma shan magunguna ba tare da ka'ida ba, irin wannan shaye shaye na lalata hanta, hunhu, koda da kwakwalwa, wanda a sakamakon haka matasa ke rasa hankalinsu. Abin haushin kuma wannan shaye shaye daga maza har mata ba'a bar kowa a baya ba. Sannan wannan matsala ita ce jijiyar duk wata fitina a wannan yanki, gami da munanan dabi'u da halaye irinsu, Fashi da makami, fadan kabilanci, gaba tsakanin matasa, da sauran abubuwa mararsa dadi.

Sai kuma matsalar satar jarrabawa, ita ma wannan matsala ce dake addabar ilimi, satar jarrabawa wani bangare ne na cin hanci, da mafiya yawan daliban da basu mai da hankalinsu akan karatu ba ke yi a wannan zamani. Hakan tasa matasa da dama basa samun aikin yi bayan gama karatu, daga nan kuma sai su shiga sahun masu shan miyagun kwayoyi.

A karshe mafita ga wadannan matsaloli sune: Gwamnati take bada gudunmawa mai tsoka ga bangaren ilimin, kamar yadda kasashen da suka cigaba ke ware kaso mafi tsoka ga bangaren ilimi daga cikin arzikin kasashen. Sannan ake tantance malamai wurin daukarsu domin koyarwa a makarantu.

Wayar da iyayenmu musamman na karkara da suke barin 'yayansu suna tafiya manyan makarantu don samun ilimi mai zurfi, a bangaren kimiya da fasaha, tattali, ilimin noma, na'ura mai kwakwalwa da sauransu.

Attajirai suke taimakawa yara masu basira, wadanda iyayensu basu da halin daukar nauyin karatunsu zuwa makarantun gaba da sakandare ko wurin siyen litattafan kimiya masu tsada.

Koyar da wani darasi koda daga makarantun firamare ne zuwa karamar sakandare game da kishin kasa, da bada labarun wasu jarumai da irin gwagwarmaya da wahalhalun da suka sha wurin nemawa kasashensu 'yanci da ci gaba.

Bude wasu santoti domin koyawa masu rubuta jarrabawar karshe ta NECO da WAEC yadda tsarukan jarrabawar yake da yadda ake amsa tambayoyi, hakan zai kawo raguwar faduwa jarrabawar da ake yi a wannan yanki namu na Arewa.

Allah ya kara daukaka wannan yanki, ya kawo masa zaman lafiya a lungun da sakon yanki dama kasarmu Nigeria baki daya.

Bashir Ahmad
Sakataren Kungiyar Tsangayar Alheri
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Tuesday, September 6, 2011

Tsangayar Alheri ta kai ziyara da bada taimako ga Gidan Marayu

Kungiyar Tsangayar Alheri ta shafin sada zumunta na Facebook a duniyar yanar gizo, ta kai ziyara Gidan Marayu (Children's House) dake Nassarawa a birnin Kano, ranar 3/9/2011. Bayan makamanciyar ziyarar da kungiyar ta kai Asibitin Kananan Yara na Asiya Bayero a watan daya gabata.

Abdulkadir Sardauna, shugaban kungiyar ta Tsangayar Alheri ya bayyana makasudin shirya wannan ziyara da kungiyar tayi, da cewa ziyara ce domin ganin halin da 'yan uwanmu kuma 'yayanmu ke ciki, da kuma ganin yadda suke kudanar da rayuwarsu ba tare da kulawar iyayensu ba, duk da suna lokacin da suka fi bukatar kulawar iyayen fiye da komai.
Shugaban ya kara ma cewa Tsangayar Alheri ta dauki alwashin bayyanawa duniya halin da wadannan yara marayu ke ciki da kuma irin taimako da suke bukata, ta shafukan kungiyar take Facebook da Yahoo Groups.

Wannan ziyara ta samu rakiyar wasu kungiyoyi masu akida irinta Tsangayar Alheri, kamar kungiyar Gizago Club, karkashin jagorancin Nura Adamu Ahmad. Sai kungiyar Youth Mobilazation via Media karkashin jagorancin Salisu D. Toll. Da kuma Woman Enlightment and Enpowerment Organization, karkashin jagorancin Fatima A. Dala. Kuma wadannan kungiyoyi suma ba'a barsu a baya ba wurin bada taimako ga wadannan Marayu.

A jawabinsa, Shugaban gudanarwar gidan Yaran, ya bayyana cewa a halin yanzu suna da yara tamanin da takwas (88) maza da mata, ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga wurin gwamnati, kamar wurin kula da karatun yaran. A karshe ya mika godiyarsa ga al'ummar da suka kawo wannan ziyara, sannan ya kara mika godiyarsa ga Asibitin Nassarawa da yake bawa duk wani yaro marar lafiya magani kyauta.

Daga karshe shugaba Abdulkadir Sardauna ya mika taimakon da wannan kungiyar ta bayar ga wadannan yara Marayu. Sannan kuma aka hadu aka dauki hotuna kafin kowa ya kama gabansa.

A karshe ina kira da al'umma da su irinka kai irin wadannan ziyara ko ba zasu bada komai ba, hakan zai sa yaran farin ciki, domin ganin ana sane dasu, sannan irin wannan ziyara zata karawa masu imani karfin imani a zuciyoyinmu, da kara godiya ga Allah da ya barmu tare da iyayenmu badon dabararmu ko don mun fi su ba.

Bashir Ahmad
Sakataren kungiyar
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160