Ilimi ba karamin muhimmanci da dajara ke gare shi ga al'umma maza da mata, yara da manya ba, domin da ilimi ne zamu koyi yadda zamu bautawa Ubangiji mahaliccinmu. Ilimi shine kashin bayan duk wata kasa da ta cigaba ta bangaren tsaro ko tattalin arziki, da ilimi ne zamu koyi zaman duniya da mutane daban daban, ba tare da kowa na gaba da kowa ba, da ilimi ne ake banbance abu mai kyau da marar kyau, sannan ilimi ne ke bawa likitoti damar duba marar lafiya har su gane me ya dame shi, kuma su bashi magani ya samu lafiya da taimakon Allah.
Duk da irin wannan muhimmanci na ilimi, da irin rawar da yake takawa ga zamantakewar al'umma, amma abin mamaki da haushi gwamnati da sauran al'umma sun kasa maganin matsalolin dake addabar ilimin musamman a wannan yanki namu na Arewa, kadan daga cikin matsalolin sun hada da:-
Rashin kulawar da ta kamata daga gwamnati da sauran jama'ar gari, wannan rashin kulawa da ilimin baya samu ta wadannan bangarori, hakan ya kawo babban nakasu ga ilimin a Arewa.
Rashin tsayawa da iyaye basa yiwa 'yayansu wurin ci gaba da karatu na zamani a manyan makarantu, saboda lokacin da ilimin yazo yankin kakanmu na ganin za'a koyawa 'yayansu (Iyayenmu) addinin Kiristanci, wannan matsala har yanzu tana addabar ilimi a wannan yanki namu.
Wata babbar matsalar dake kara zama nakasu ga ilimin itace, shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma shan magunguna ba tare da ka'ida ba, irin wannan shaye shaye na lalata hanta, hunhu, koda da kwakwalwa, wanda a sakamakon haka matasa ke rasa hankalinsu. Abin haushin kuma wannan shaye shaye daga maza har mata ba'a bar kowa a baya ba. Sannan wannan matsala ita ce jijiyar duk wata fitina a wannan yanki, gami da munanan dabi'u da halaye irinsu, Fashi da makami, fadan kabilanci, gaba tsakanin matasa, da sauran abubuwa mararsa dadi.
Sai kuma matsalar satar jarrabawa, ita ma wannan matsala ce dake addabar ilimi, satar jarrabawa wani bangare ne na cin hanci, da mafiya yawan daliban da basu mai da hankalinsu akan karatu ba ke yi a wannan zamani. Hakan tasa matasa da dama basa samun aikin yi bayan gama karatu, daga nan kuma sai su shiga sahun masu shan miyagun kwayoyi.
A karshe mafita ga wadannan matsaloli sune: Gwamnati take bada gudunmawa mai tsoka ga bangaren ilimin, kamar yadda kasashen da suka cigaba ke ware kaso mafi tsoka ga bangaren ilimi daga cikin arzikin kasashen. Sannan ake tantance malamai wurin daukarsu domin koyarwa a makarantu.
Wayar da iyayenmu musamman na karkara da suke barin 'yayansu suna tafiya manyan makarantu don samun ilimi mai zurfi, a bangaren kimiya da fasaha, tattali, ilimin noma, na'ura mai kwakwalwa da sauransu.
Attajirai suke taimakawa yara masu basira, wadanda iyayensu basu da halin daukar nauyin karatunsu zuwa makarantun gaba da sakandare ko wurin siyen litattafan kimiya masu tsada.
Koyar da wani darasi koda daga makarantun firamare ne zuwa karamar sakandare game da kishin kasa, da bada labarun wasu jarumai da irin gwagwarmaya da wahalhalun da suka sha wurin nemawa kasashensu 'yanci da ci gaba.
Bude wasu santoti domin koyawa masu rubuta jarrabawar karshe ta NECO da WAEC yadda tsarukan jarrabawar yake da yadda ake amsa tambayoyi, hakan zai kawo raguwar faduwa jarrabawar da ake yi a wannan yanki namu na Arewa.
Allah ya kara daukaka wannan yanki, ya kawo masa zaman lafiya a lungun da sakon yanki dama kasarmu Nigeria baki daya.
Bashir Ahmad
Sakataren Kungiyar Tsangayar Alheri
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160
No comments:
Post a Comment