Tuesday, September 6, 2011

Tsangayar Alheri ta kai ziyara da bada taimako ga Gidan Marayu

Kungiyar Tsangayar Alheri ta shafin sada zumunta na Facebook a duniyar yanar gizo, ta kai ziyara Gidan Marayu (Children's House) dake Nassarawa a birnin Kano, ranar 3/9/2011. Bayan makamanciyar ziyarar da kungiyar ta kai Asibitin Kananan Yara na Asiya Bayero a watan daya gabata.

Abdulkadir Sardauna, shugaban kungiyar ta Tsangayar Alheri ya bayyana makasudin shirya wannan ziyara da kungiyar tayi, da cewa ziyara ce domin ganin halin da 'yan uwanmu kuma 'yayanmu ke ciki, da kuma ganin yadda suke kudanar da rayuwarsu ba tare da kulawar iyayensu ba, duk da suna lokacin da suka fi bukatar kulawar iyayen fiye da komai.
Shugaban ya kara ma cewa Tsangayar Alheri ta dauki alwashin bayyanawa duniya halin da wadannan yara marayu ke ciki da kuma irin taimako da suke bukata, ta shafukan kungiyar take Facebook da Yahoo Groups.

Wannan ziyara ta samu rakiyar wasu kungiyoyi masu akida irinta Tsangayar Alheri, kamar kungiyar Gizago Club, karkashin jagorancin Nura Adamu Ahmad. Sai kungiyar Youth Mobilazation via Media karkashin jagorancin Salisu D. Toll. Da kuma Woman Enlightment and Enpowerment Organization, karkashin jagorancin Fatima A. Dala. Kuma wadannan kungiyoyi suma ba'a barsu a baya ba wurin bada taimako ga wadannan Marayu.

A jawabinsa, Shugaban gudanarwar gidan Yaran, ya bayyana cewa a halin yanzu suna da yara tamanin da takwas (88) maza da mata, ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga wurin gwamnati, kamar wurin kula da karatun yaran. A karshe ya mika godiyarsa ga al'ummar da suka kawo wannan ziyara, sannan ya kara mika godiyarsa ga Asibitin Nassarawa da yake bawa duk wani yaro marar lafiya magani kyauta.

Daga karshe shugaba Abdulkadir Sardauna ya mika taimakon da wannan kungiyar ta bayar ga wadannan yara Marayu. Sannan kuma aka hadu aka dauki hotuna kafin kowa ya kama gabansa.

A karshe ina kira da al'umma da su irinka kai irin wadannan ziyara ko ba zasu bada komai ba, hakan zai sa yaran farin ciki, domin ganin ana sane dasu, sannan irin wannan ziyara zata karawa masu imani karfin imani a zuciyoyinmu, da kara godiya ga Allah da ya barmu tare da iyayenmu badon dabararmu ko don mun fi su ba.

Bashir Ahmad
Sakataren kungiyar
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

No comments:

Post a Comment