Thursday, December 20, 2012

Budadden Sako Zuwa Ga Sabon Gwamnan Jihar Kaduna

Zuwa ga Mai Girma, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, Gwamnan Jihar Kaduna. Assalamu – Alaikum! Da farko ina yin mana jaje na rashin Gwamnanmu da mukayi Mr. Patrick Ibrahim Yakawo, a sanadiyar hadarin jirgin sama, muna fatan Allah Yasa ya taradda da yan’uwansa acan, mu kuma Allah Ya kyautata namu bayan nasu Yasa mu cika dakyau da Imani, ba yanda za ayi domin dukkan mai rai mai mutuwa ne. Bayan haka, inaso in yi anfani da wannan dama domin inyi maka nasiha da kuma bada shawara, kasancewar bani da wata hanya da zanzo in sameka ni dakai sai ta wannan hanyar wanda na tabbata, in baka gani ba, wadanda suke kusa dakai zasu gani kuma zasu sanar dakai. 1. Da farko ina tunatar dakai da kara sanya jin tsoron Allah a cikin al’amuranka duka na yau da kullun, domin shi ne zai zame maka jagora akan dukkan abin da ka fuskanta. 2. Ka godewa Allah a bisa wannan ni’ima da ya yi maka. Ta yaya zaka gode maSa? Shi ne ta hanyar aikata abin da duk Ya umurce ka dasu gwargwadon ikonka, ka kuma nisanci duka abubuwan da Ya hanaka, idan ka siffantu da haka, to, shi zaisa Ya yi maka kari a bisa wannan ni’iman da Yayi maka yanzu. 3. Ka zamo mai adalci a bisa wadanda Allah Ya daura maka alhakinsu a kanka. Duk mai hakki ka bashi hakkinsa gwargwadon yanda doka ta tsara. 4. Ka zamo mai gaskiya da rikon amana da kuma daukan alkawarin abubuwan da kasan bisa ikon Allah bai fi karfinka ba. 5. Ka guji yin duka wani abu da zai zamo nau’in yin zalunci ne ga wadanda kake shugabanta, domin babu shamaki tsakanin addua’an wanda aka zalunta da Mahaliccinsa, kamar yanda Manzon Allah Sallallahu Alayhi Wasallam ya sanar damu haka, ya kuma ja kunnen mu akai. 6. Ni a tawa shawaran, ina ganin akwai wasu abubuwan guda biyu da suke neman sufi karfin talaka gabaki daya, wato sune harkan ilmi da abin da ya shafi harkan lafiya, ka sanya ido kai tare da bada dukkan gudummuwan da zaka iya badawa. 7. Ka sakamma kananan hukumomi mara domin suma su sami daman yin ma nasu al’ummomin ayyukan morewa. Ka kuma sanya ido akan yanda suke gudanar da harkokinsu gudun kada su wuce gona da iri. 8. Kula da harkan tsaro shima yana da matukar muhimmanci, domin sai da zaman lafiya ake samun daman gabatar da duk wasu ayyuka. Daga karke, ina rokon Allah da Yayi maka jagora, Ya sanya maka hannu a bisa wannan nauyi da ya daura maka, Ya kasance tare dakai a duk inda kake, Ya baka ikon sauke dukkan nauyin da Ya daura maka, Ya kuma sanya maka katangar karfe tsakaninka da dukkan makiya mutun ko aljan. Muma Allah Ya biya mana dukkan bukatummu. Wassalamu Alaykum, ABDULKARIM MUH’D TANKO