Tuesday, January 6, 2015

Kungiyar Tsagerun Neja-Delta Sun Bayyana Goyon Bayan Su Ga Buhari

...Jonathan Ya Sake Shiga Tsaka Mai Wuya

Yayin da zaben 2015 ke kara kusantowa, shugaba Goodluck Johnathan dake neman tazarce a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP na kara shiga tsaka mai wuya, yayin da a kullum yunkurin na sa ke kara samun koma baya.

Babban kungiyar 'yan tawayen Neja-Delta, wato MEND a yau ta bayyana cikakken goyon bayanta ga takarar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, wanda ba a taba ganin makamancin irin haka a siyasar kasar nan ba. Haka kuma kungiyar ta MEND ta jaddada cewa ko kadan bai cancanci Jonathan din ya ci gaba da mulkin kasar nan ba, duba da irin yadda Nijeriya take ta samun koma-baya a karkashin jagorancinsa wanda suka kira hakan da abin kunya ne ga yankin na su, inda Jonathan ya fito.

MEND cikin wani dogon jawabi da ta aike kafafen yada labaran kasar nan, mai dauke da sa hannun sakataren ta, ta ce ta yanke shawarar goyon bayan Buhari ne don taimakawa wajen kubutar da kasar nan daga halin da ta samu kanta ciki.

Kafin wannan sanarwa ana tsammanin kungiyar ta MEND za su shiga taya Jonathan fafutuka don ganin mulki ya ci gaba da kasancewa a yankin su.

Kungiyar MEND ita ce ta sanya bom a Abuja, a ranar cikar Nijeriya shekaru 50 da samun 'yancin kai, sai dai a lokacin saboda soyayya, Shugaba Jonathan ya fito ya ce ba su bane duk da sun dauki alhakin kai harin.

Zuwa yanzu dai za a iya cewa Shugaba Jonathan baida wata kwakkwarar makama da zai kama don taimaka masa ya ci gaba da zama a kan karagar mulkin a 2015.