Monday, March 23, 2015

Na Sake Tabbatarwa Muhammadu Buhari Ne Sabon Shugaban Nijeriya

Tun bayan samun nasarar kafa jam'iyyar APC shekaru 2 da suka gabata, na ji a jikina cewa idan Allah ya nufi Janar Muhammadu Buhari zai sake mulkar kasarmu Nijeriya to lokaci yayi. Saboda tun a lokacin na hango shi a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben 2015. 

Na kara samun karfin guiwa bayan da Buhari ya samu nasarar lashe zaben cikin gida na jam'iyya, inda ya fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa, gwamnoni da kuma maigidana. Ba komai ya sa na samu karfin guiwar ba, sai don sanin cewa wakilan da suka zabi Buhari sun zabe shi ne ba don kudinsa ba, domin duk cikin 'yan takarar ba wanda bai fi shi tarun dukiya ba.

Bayan haka karfin guiwa ya kara zuwa min a ranar da Buhari ya bude yakin neman zabensa a jihar Rivers, wanda na halarta, nan na ga mutanen yakin su Jonathan sun fito suna ihun 'Sai Buhari' wannan lokacin canji suke so. Daga nan kullum nake ta samun karfin guiwa musamman yadda muka kammala zagayen jihohin Neja-Delta lafiya, kuma ko ina mutane sun fito sun karbe cikin aminci da soyayya, kar ku manta Janar Buhari a 2011 bai yi yakin neman zabe a yankin ba, saboda rashin wadanda suke son na gaskiya a yankin, wasu jihohin ma ko ofishin yakin neman zabe bai da shi balle a samu fastocinsa, har ya samu magoya bayan da za su zabe shi, su kasa, su tsare kamar yadda yake kiran magoya bayansa su yi a kodayaushe.

Soyayyar da na ga Yarabawa sun nunawa Janar Muhammadu Buhari, a duk inda ya shiga ta sake sauya min tunani kan cewa PDP za su iya yin magudi, koda Buharin ya lashe zabe, bana tunanin akwai jiha daya a yankin Yarabawa da idan PDP ba ta ci ba za ta iya murda zaben, saboda 'yan ganin kashe-nin magoya bayan da Buhari da APC suke da su a yankin a yanzu.

A yankin Arewa, kusan duk jihar dana shiga yayin yakin neman zaben sai da na zubar da hawaye, saboda ganin mutanen Arewa har yanzu suna ba su canja soyayyar da suke yi wa Buhari ba tun daga lokacin da ya fara fitowa zabe a 2011 har yanzu, sai na ga cewa yanzu ne  ma suka yanke shawarar sadaukar da komai don nasarar Buhari, saboda sanin cewa idan wannan damar ta wuce ba za ta sake dawowa ba har abada.

A yau kuma na kammala samun nutsuwa a zuciyata cewa Janar Buhari ne shugaban Nijeriya na nan gaba, idan har Allah ya nufi zai sake mulkar mu a karo na biyu. Yau Buhari ya gudanar da taron yakin neman zabensa a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan, wato yankin Inyamurai, wadanda a baya ake gani su suka fi kowace kabila nunawa Buharin kiyayya saboda shi Bahaushe ne.

Dalilin da ya sa na samu nutsuwa bayan yakin neman zaben yau shi ne, bayan daga zabe da sati 6 da hukumar INEC ta yi, PDP ba abinda suka fi maida hankali shi ne yada farfagandar karya kan Buhari a kafafen yada labarai, wanda a tunanina wannan farfagandar za ta yi aiki a wurin Inyamuran, sai na ga ashe ba haka abin yake ba, su ma sun kammala yake sharawar su kamar Hausawa da Yarabawa. Dubban jama'a sun fito maza da mata, manya da yara a birnin Owerri na jihar Imo, tun daga gidan gwamnatin jihar har zuwa filin taro mutane ne jere suna rawa da waka, da farin cikin ganin Buhari, kai wallahi abin sai wanda ya gani, bayani na ba zai gamsar daku yadda ya kamata ba, amma dai ina tabbatar muku da cewa Inyamurai ma suna son Janar Buhari, kuma sun gaji da mulkin Jonathan marar manufa, marar alkibla.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda taron yakin neman zaben ya kasance, watakila idan kun gani da idonku, zaku fi fahimtar abinda nake so na bayyana.

A karshe zan kara maimaita abin da na fada tun da farko "Janar Muhammadu Buhari ne sabon shugaban Nijeriya, idan Allah ya nufi zai sake mulkarmu a karo na biyu".

Bashir Ahmad
Memba a kwamitin yada labarai
Na yakin neman zaben Janar Muhammadu Buhari 



Sunday, March 22, 2015

HOTUNA: Taron Da Buhari Ya Gudanar Da Miskinai A Nasarawa

Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa a APC, a jiya ya gudanar da taro da miskinai, wato guragu, makafi, bebaye da sauran su, a garin Lafia jihar Nasarawa.




Friday, March 6, 2015

TAYA MURNA: Mansur Ahmad Ya Cika Shekaru 24

Hausawa masu hikima suka ce 'shekara kwana' amma fa ga masu lafiya...


Ina taya dan uwana kuma yayana a yanzu (lolz), Mansur Ahmed murnar cikarsa shekaru 24 a duniya (wow lalle Mansur ka girma). Allah ya kara nisan kwana cikin koshin lafiya, arziki da kwanciyar hankali.


Mansur abokina ne na kud-da-kud, duk da muna da bambanci akida a siyasance amma muna girmama juna, kuma muna mutunta ra'ayoyinmu.


Mansur dan jam'iyyar PDP, ni kuma zan iya kiran kaina dan APC. 


Mansur, Sule Lamido ne mai gidansa a siyasance, yayin da ni kuma Gen. Muhammadu Buhari da Sam Nda-Isaiah su ne masu gidana a siyasance, amma duk da haka ba mu taba samun sabani ba.


A madadin babban bawana Aliyu Danlabaran Zaria ina kara taya ka murnar zagayowa wannan rana, Allah ya nuna mana ranar aurenka.: Hausawa masu hikima suka ce 'shekara kwana' amma fa ga masu lafiya...


Ina taya dan uwana kuma yayana a yanzu (lolz), Mansur Ahmed murnar cikarsa shekaru 24 a duniya (wow lalle Mansur ka girma). Allah ya kara nisan kwana cikin koshin lafiya, arziki da kwanciyar hankali.


Mansur abokina ne na kud-da-kud, duk da muna da bambanci akida a siyasance amma muna girmama juna, kuma muna mutunta ra'ayoyinmu.


Mansur dan jam'iyyar PDP, ni kuma zan iya kiran kaina dan APC. 


Mansur, Sule Lamido ne mai gidansa a siyasance, yayin da ni kuma Gen. Muhammadu Buhari da Sam Nda-Isaiah su ne masu gidana a siyasance, amma duk da haka ba mu taba samun sabani ba.


A madadin babban bawana Aliyu Danlabaran Zaria ina kara taya ka murnar zagayowa wannan rana, Allah ya nuna mana ranar aurenka.

Thursday, March 5, 2015

RAHOTO: Hasashen Yadda Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Zai Kasance

Daga Ahmad Abubakar, Abuja

Cikin wannan rahoton da editan #HAUSA24 na harkokin siyasa ya hada mana, ya yi duba kan yadda ake tsammanin sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Maris zai kasance, idan an gudanar da zaben ba tare da aringizon kuri'u ko magudi ba.

Adadin Masu Rijistar Zabe Ta Dindindin A Yankunan Kasar Nan

Kudu Maso Yamma - 13,731,090

Kudu Maso Gabas - 7,665,859

Kudu Maso Kudu - 10,059,347

Arewa Maso Yamma - 17,620,436

Arewa Maso Gabas - 9,107,861

Arewa Ta Tsakiya - 9,767,411

FCT Abuja - 903,613

Hasashen Yadda Sakamakon Zai Kasance

Kudu Maso Yamma - GMB 65%, GEJ 35%

Kudu Maso Gabas - GMB 20%, GEJ 80%

Kudu Maso Kudu - GMB 20%, GEJ 80%

Arewa Maso Yamma - GMB 90%, GEJ 10%

Arewa Ta Tsakiya - GMB 60%, GEJ 40%

Arewa Maso Gabas - GMB 70%, GEJ 30%

FCT - GMB 40%, GEJ 60%

A karshe lissafin zai nuna Buhari zai samu kaso 365%, yayin da Jonathan zai samu kaso 335%.

A LURA: lissafin ba yana nufin na adadin yawan kuri'un da Buhari ko Jonathan za su samu ba ne, lissafin na nufin kason da ake hasashen kowanne su zai samu a yankunan kasar nan guda shida da birnin tarayya Abuja.