Tuesday, June 26, 2012

Tashin Hankali: Tashin Bama - Bamai A Unguwarmu


Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!!

Tashin hankali ba a sa maka rana, yau kam unguwarmu Goron Dutse Dala/Gwale Kano mun shiga tashin hankalin da ba mu taba samun kanmu a ciki ba, abin da muke jin labari a da a kasashen duniya da suke fama da yaki, sai gashi ana tafe ana tafe ya zo kasarmu a yankinmu na Arewa, to sai kuma ga shi a yau ya zo mana har gida, daman masu iya magana na cewa idan gemun dan uwanka ya kama ta wuta sai kayi kokarin sanyawa naka ruwa, tabbas wannan magana haka take a yammacin yau sai da aka shafe sama da awa daya rabi ana rugugin wata da tashin bama - bamai a unguwar tamu, wanda wasu 'yan bindiga suka fara daga bisani kuma sai ga jami'an tsaro da tankokin yaki suma suka fara nasu lugudan wutar, wanda hakan ya sanya hankalinmu ya yi bala'in tashi domin ji muke yi kamar a cikin dakunanmu da tunda aka fara tashin hankalin muka shiga muka kukkule, muna jiran yadda Allah zai yi damu.

Haka za gaji karar tashin bam kamar dakin da kake ciki zai ruguzo a kanka, kafin wani dan lokaci tuni titi da layukan unguwarmu sun zama kamar ba a taba halittar bil'adama ba. Sai dai wani abin haushi da na rasa yadda zan yi sai kawai da dakko radio na kunna domin ko zan ji halin da muke ci, saboda kuwa a lokacin da za a yi min tambayar cewa Bashir a wane hali kake a yanzu? Wallahi amsar da zan bada ita ce Allah a'alamu, saboda kuwa ba zan iya cewa ga halin da nake ba. Amma maimakon na ji gidajen radion dake cikin fadin kwaryar jihar Kano sun sako wani abu daya danganci halin tashin hankalin da muke ciki, sai na ji akasin haka, kowace tasha na murdo sai kawai na ji ana ta shan kida, kamar ma ba su san mai ke faruwa a jihar ba, abin ya bani haushi na kashe radion na dakko wayata na budo shafin Facebook nan na dan ji sanyi a zuciyata, domin kuwa sai naga kowa ba a abinda yake rubutawa sai batun halin da muke ciki, ga kuma 'yan uwa sai addu'a suke ta taya mu, duk da dai na kasa cewa komai a Facebook din amma na dade ina ta kallon abubuwan da jama'a ke bayyanawa game da mu, gami da saurin cewa "amin" idan naga wani ya taya mu da addu'a akan halin da muke ciki.

To dai a halin yanzu komai ya lafa, babu karar harbe - harbe kamar da zu, sai dai dan kadan da za ka dan ji nan da can, sai dai sanarwa da muka samu cewa da zarar munyi sallar Isha'i to kowa ya koma cikin gida ya kwanta, domin kuwa tuni an jibge manyan tankokin yaki da tarun jami'an tsaro a wasu sassa na unguwar tamu. Ni kuwa daman da yake wannan shi ne karon farko da na taba samun kai na a cikin irin wannan hali tun da aka fara abin na shiga gida, sallar Magriba ba a cikin gidan nayi, ba don tsoron mutuwa ba sai don tunanin wahala, saboda kuwa mutuwa dai daya ce kuma na san zan mutu koda ina so ko ba na so, da lokacin ya yi zan koma ga Mahaliccina Allah.

A karshe ba abin da zance sai godiya ga 'yan uwa da suka taya mu da addu'a, musamman wadanda suka yi ta kirana a waya suna tambayar lafiyata, Allah ya saka da alheri, ya kuma bar zumunci.

Ya Allah ka kawo mana karshen wannan tashin hankali a kasarmu. Ka bayyana dukkan masu hannu a ciki, koda kuwa suke rike da madafan ikon kasar nan. Na gode!

Wednesday, June 20, 2012

Addu'a: Hanyar Kawo Karshen Halin Da Muke Ciki A Kasar Nan


Aminci a gare ku ya ku 'yan uwana Musulmai maza da mata, yara da manya, kasarmu Nijeriya na cikin wani mummunan hali, halin da idan ya ci gaba da faruwa to nan gaba komai na iya faruwa.

Wani abin bakin ciki kuma abin da ya fi tayar min da hankali shi ne tun lokacin da wannan mummunan abu ya fara faruwa a shekarar 2009, 'yan uwanmu Musulmai Hausa/Fulani su abin ya fi ritsawa da su, amma kullum kuma mu ake zagi da zargar cewa mu muke haifar da komai, hakan ta sa kullum ake kara tsanarmu, ana zagi da aibanta addininmu.

To mu dai kowa ya sani ba mu da takobi, ba mu AK47 balle kuma jirgin yaki, amma dai duk da haka addininmu ya sanar da mu muna da makaman yakin da ya fi duk wadannan makamai, saboda haka lokaci yayi da zamu maida hankalinmu kan makamanmu, mu dakko shi mu fara amfani da shi, haka ne kadai zai kawo mana daidaituwar wadannan al'amura.

Wannan makami namu ba boyayye ba ne, a wurinmu hasalima, dukkan mu mun iya fafata yaki da shi, kuma mu samu nasara akan abokan gabarmu, ba tare da mun ji rauni ko kwarzane ba, sai dai kawai mantuwa da koyaushe take hana mu fafata yakin da shi.

ADDU'A ita ce makamin namu, wadda kuma ya kamata a tsakaninmu mu dauki wani adadi daga cikin wadanda Al Qur'ani mai girma ya koya mana har sai mun yi nasara, saboda haka mu kudure a cikin zuciyoyinmu daga yanzu kullum muke karanta "HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL" sau miliyan daya (1,000,000.00) da zummar Allah (SWT) ya taimake mu, ya kawo mana karshen wannan hali na rashin tsaron da muke ciki, sannan Allah ya tona asirin duk wanda suke shirya wannan al'amari, koda kuwa Musulmai ne ko kirista Allah ya wargatsa shirin su.

Idan kowanne daga cikin mu zai karanta adadin 1000 a kullum, to tabbas za mu haura yawan adadin miliyan dari ma. 'Yan uwa mu taimaka mu aikawa sauran 'yan uwanmu maza da mata wannan sako, sannan mu sanarwa yara kanana su ta karantawa. Allah ya taimake mu ya amsa addu'o'inmu.

Monday, June 18, 2012

Shin Gaskiya Ne Shahararriyar Jarumar Fim Din Nan Nafisat Abdullahi Ta Rasu?


Tambaya: "Shin gaskiya ne shaharriyar jarumar shirin fina-finan Hausan nan Nafisat Abdullahi ta rasu?" Wannan tambaya ko nace jita - jita, ta dade tana zagayawa a tsakanin al'ummar kasar nan musamman masu sha'awar finafinan Hausa. Hakan kuwa ya samo asali ne tun bayan hadarin da Nafisan daya rutsa da ita da abokin sana'arta Adam A. Zango.

Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayon, ta kawo karshe wannan jita - jita da bakinta a wata tattaunawa da tayi da wakilin jaridar RARIYA, inda take cewa "Ina nan da raina a daina cewa na mutu".

Domin karanta cikakken labarin sai a nemi jaridar RARIYA ta ranar Juma'an nan wadda ke kasuwa a halin yanzu, kuma za a iya samun jaridar a dukkan wuraren saida jaridu dake sassan kasar nan.

Sunday, June 17, 2012

Wa Ke Da Alhakin Tashin Bama - Bamai A Kaduna?


Yau mutanen arewacin Kaduna sun ga tashin hankali, sakamakon tashin wasu bama bamai a wasu majami'u a birnin Zaria da cikin garin Kaduna, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da dokiyoyi masu yawa, dalilin faruwar wannan al'amari ya sa wasu matasan kiristoci sanya shingaye akan titunan da zasu dawo da matafiya Kaduna daga Abuja, da suna daukar fansa, saboda a zargin su Musulmai ne suke da alhakin faruwar al'amarin. Duk kuwa da cewa ba sau daya ko sau biyu ba ana kama kirista da bam na kokarin sanyawa a coci.

Bayan isar wannan mummunan labari cikin kunnuwa na, ba komai zuciyata ta fara tuno min da shi ba, sai wata magana da shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana a kwanakin baya da yake tabbatarwa 'yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta kawo karshe da murkushe kungiyar nan ta Boko Haram, wadda ake zargi da irin wannan aika aika a sassan kasar nan daban daban, a watan June da muke ciki a yanzu.

Ina tunanin ba komai ya sa zuciyata ta yi saurin tuno min da wannan magana ba sai don sanin ba kowa za a zarga da yin wannan aika aika ba sai kungiyar ta Boko Haram, ba don komai ba, sai don kaurin sunan da tayi akan hakan kamar yadda na fada a baya.

To ana cikin haka, sai wani tunanin ya kara kunnuwa cikin zuciyar tawa hade da tambaya. Shin tunda Boko Haram ta zo karshe a wannan wata, kamar yadda shugaba Jonathan ya dau alwashi, kuma kaso mafi rinjaye na al'ummar kasar nan suka gastata maganar tasa, to wa kuma yake da alhakin kai hare - haren bama baman yau din a Kaduna?

Ya Allah ka kawo mana zaman lafiya a kasarmu.

Saturday, June 16, 2012

Ta Tabba Faruk Lawan Ya Karbi Cin Hanci: Wane Hukunci Ya Cancanci A Yanke Masa?


Wannan takaddama tayi daidai da abinda bahaushe ke cewa "Mai Dokar Bacci Ya Buge Da Gyangyadi" ba komai yasa na bude wannan maganar ba, sai game da takaddamar da ke kai kawo a kasar nan ta Hon. Faruk Lawan shugaban kwamitin bankado badakalar tallafin man fetur, wanda ya tsaya tsayin daka, ya kuma jajirce ba tare da jin kunya ko nuna tsoro ba, yayin tafiyar da aikin da aka dora masa a kwamitin nasa, ya gudanar da aikin nasa ba tare da nuna abokan taka ba, duk irin barazanar da shi da sauran 'yan kwamitin nasa suka sha, hakan bai hana su gudanar da ingantaccen bincike ba akan duk wani dake da hannu a cikin badakalar ta tallafin man fetur din ba. Kai na dai takaice jawabina duk wannan kwanci tashin da Faruku da sauran abokanan aikinsa suka sha a karshe sai da suka bayyana sunan duk wani da suka samu da hannun cikin badakalar, ba tare da ware 'yan lele ko abokanai ba. Wannan sakamakon bincike da kwamitin suka bayyana ba karamin burge 'yan Nijeriya suka yi ba, kuma ya karawa jama'ar kasar nan kwarin gwiwa, da jinjina a gare su domin ba wanda ya taba tunanin cewa za a samu gwarzaye marasa tsoron da za su iya jagoranta wannan jan aiki har su kai ga nasara.

Sai dai kuma bayan wasu 'yan satuttuka da bayyanar sakamakon duk kafin a kai ga hukunta wadanda aka gano da laifuka, sai ga reshe na neman juyewa da mujiya, domin kuwa sai ga sanarwar zargin jagoran kwamitin kamo masu laifi ana zarginsa da laifi makamancin irin wanda ya jagoranci bankadowa. A takaice shi ma dai a karshe an bankado ta sa badakalar da ake zarginsa da karbar cin hancin zunzurutun kudi har dalar Amurka $6000,000, da wani kamfanin hada hadar man fetur wanda ba a tantance sunansa ba ya ba shi, kuma a karshe zargin ya tabbata gaskiya sakamakon wasu shaidu da aka gabatar ciki har da faifai hoto mai motsi wato Video, wanda har hakan ya jawo sauke jagoran bankado masu badakala ya bayyana da bakinsa cewa ya karbi na goron, amma domin ya zame masa wukar gindi wurin gurfanar da wadanda suka yi masa tayin na goron a gaban hukumar yaki da cin hanci da yiwa dukiyar kasa zagon kasa wato EFCC. Daga karshe dai wannan tabargaza da jagoran ya tafka ta jawo sauke shi daga dukkan wasu mukamai da yake jagoranta a majalisar ta wakilai.

Baya ga haka, su kuma jami'an hukumar 'yan sanda suka garzayo don gudanar da aikinsu akan Faruku, wato dai tuni suka yi awon gaba da shi don ci gaba da binciken kwakwaf, har su gano gaskiyar lamarin.

To abin tambaya anan shi ne, shin idan masu binciken kwakwaf sun sake gano Faruku da laifi dumu dumu, wane irin hukunci ya cancanci a yanke masa don ya zama darasi ga masu irin halayyarsa?

Na san ni da sauran masu karatu ba za a rasa tarun amsoshin wannan tambaya a cikin kwakwalenmu ba, to amma kafin azo kan amsa tambayar ina labarin baragurbin da kwamitin da Faruku ya jagoranci bankado almundahanar da suka tafka akan tallafin man fetur? Shin su tunda an tabbatar da laifukansu an yanke musu hukuncin da yayi daidai da laifinsu? Idan ba a yanke ba har yanzu, to shin mai ake jira?

A karshe zan bawa hukumomin shari'a da abin ya shafa shawarar ya kamata suyi amfani da maganar da Janar Muhammad Buhari ya fada akan masu hannun a badakalar tallafin man fetur din, inda yake cewa "Da ni ne shugaban kasa, da zan yankewa duk masu hannun a cikin badakalar hukuncin kisa, ko hukuncin dauri a gidan yari" tabbas Janar ya fadi gaskiya kuma bana tunani akwai wani hukunci da za a yanke musu da ya fi hakan dacewa. Kuma da tun farko ana daukar irin hukuncin akan duk wani da aka samu da hannun dumu dumu akan cin hanci da karbar rashawa, da tuni sai an share gumi wurin binciko mutum daya da za a samu da irin makamancin laifi, saboda kuwa duk kasashen da suka yi kaurin suna wurin cin hancin irin hukunci ake amfani da shi ake kawo karshe mummunan aikin.

Thursday, June 14, 2012

Majalisar Wakilai Ta Kira Zaman Gaggawa


Majalisar wakilai ta kasa za ta gudanar da wani zama na ba zata a gobe Juma'a. A wata sanarwa da akawun majalisar, M. A. Sani-Omolori ya rabawa manema labari a daren jiya, ya bukaci daukacin 'yan Majalisar wakilan da su halarci zaman majalisar da za a fara da misalin karfe 10 na safe.

Ana kyautata zato dai zargin badakalar karbar cin hancin da ake zargin Hon. Faruk Lawal ya yi shi ne batun da zai mamaye tattaunawar da wakilan za su yi.

Wani hamshakin dan kasuwa mai safarar mai, Femi Otedola ne yayi zargin cewa, dan majalisar, Faruk Lawan ya karbi cin hanci dangane da binciken kudaden tallafin da majalisar tayi.

Koda a baya dai majalisar dokokin Najeriya ta sha aukawa cikin badakalar cin hanci da rashawa.

Daga BBCHausa.com

Wednesday, June 13, 2012

Sanusi Lamido Sanusi Ya Koma Bakin Aiki Sanye Da Kayan Sarauta


Gwamnan babban bankin kasa CBN Malam Sanusi Lamido Sanusi wanda a ranar Juma'a da ta gabata Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero ya nada shi a matsayin Dan Majen Kano ya koma bakin aiki birnin tarayya Abuja cikin kayan sarauta, wato sanye da babbar riga da alkyabba gami da rawani mai kunnuwa biyu sanye a kansa, ga kuma sandar ban girma rike a hannunsa na dama.

Da shigarsa wurin aikin nasa sauran abokan aikinsa da suke karkashinsa sun zo sun karbi gaisuwa irin yadda ake yiwa sarakuna a yankin kasar Hausa.

Muna kara yiwa Malam Sanusi Lamido Sanusi addu'ar Allah ya taya shi rikon wannan sarauta, Allah kuma ya sa wannan sarauta mataki ce a gare shi.

Darasin Da Nijeriya Za Ta Koya Daga Kasar Brazil Ta Fuskar Bunkasar Noma

Za mu iya daukar darasi daga kasashe irin su Brazil, Indonisiya da Malesiya. Duk da cewa, wadannan kasashe su na samar da mai, arzikin noma ne daya bunkasa su da al’ummarsu bakidaya.

Amurka ta siffanta Brazil a matsayin kasa mafi karfin arzikin noma a duniya. A bangarori da dama Brazil ta na kamanceceniya da Nijeriya. Kowacce ta na da yawan al’umma da fadin kasa. Brazil ta na da yawan mutanen da ya kai miliyan 190, yayin da Nijeriya ke da miliyan 167. Dukkanninsu su na da mai da kuma kasar noma, amma shugabanci ne ya bambanta kasashen biyu.

Llokacin mulkin kama-karya a Brazil an yi sakaci da aikin noma, amma tun lokacin da mulkin dimokuradiyya ya dawo kasar, aikin noma, wanda ya ke bai wa mafi yawa aikin yi sai ya sami bunkasa. Cikakkiyar hikima ita ce dimukradiyya ta bayar da yanayi na sauyi (ban da a Nijeriya), domin komai na dimokurad-iyya ya ta’allaka ne ga mutane. An bai wa noma muhimmanci a Brazil, dalilin da ya sa ya kenan kashi daya bisa uku na masu aikin yi a kasa shi ke ba su aiki.

Sakamakon ba wai ya tsaya ne kawai a kan cewa Brazil ta dogara da kanta ta fuskar ciyar da kai ba ne, a’a, ta na cikin kasashe ne ma mafi fitar da kayan amfanin gona. Brazil ta fi kowacce kasa fitar da rake, kuma ta na daya daga cikin mafi fitar da koko, waken soya da lemo. Kiwo ma ya na da fadi a kasar. Kayan noma su ne kashi 35 cikin 100 na abinda kasar ke fitarwa waje. Brazil ce mafi fitar da jan nama a duniya, rake, kofi, waken soya da kaji.

Arzikin noma na Brazil ya haura na kowacce kasa ne saboda aniyar shugabanninta; sun kafa manyan gidajen gona, yayin da kuma su ka karfafa kananan gonaki, bincike, bude kasuwanci a faifai da kuma amfani da dabarun noma na zamani. Gonakin Brazil su na da girman da ya fi yawancin gonakin Amurka, kuma a na kallon manomansu a mataki na duniya, ba wai cikin kasarsu kadai ba. Babu wani dalili da zai hana yin amfani da salon ’yan Brazil a Nijeriya. Dogaron da a yanzu mu ke yi da kananan manomanmu ba zai kai mu ko’ina ba. Za mu iya aikata abinda ya fi haka. Ba Ina cewa, gwamnatocin jihohi ko ta tarayya su mallaki gidajen mar da gona ba, amma dai su samar da filayen noma domin yin abinda ya ke a can din. Karfin gwiwa ne kadai zai iya samar da hakan. Ya kamata gwamnatoci su sayo iri masu kyau, kuma a samar da matsaya a kasuwannin duniya.

Ya kamata gwamnatin tarayya ta shigo ciki ta hanyar babban bankin Nijeriya, domin samar da rance da kuma noman kansa. Bambancin shi ne, Brazil ta na da filin noma hekta miliyan 76.7, yayin da a ke da fadin kasa na miliyan 170. Don haka ba abin mamaki ba ne don shanun Brazil sun kai miliyan 190, yayin da shanun Nijeriya ba su wuce miliyan 10 zuwa 15 ba. Kai kamar kowane abu ma dai, Nijeriya ba ta da kididdigar yawansu.

Brazil ta na fiye da hekta miliyan 23 da a ke girbe waken soya kadai. Masara ta na da hekta miliyan 12, rake na da miliyan 7, sannan shinkafa na da miliyan 2.5.

Malesiya ma wata abar misali ce. Ta na fiye da hekta miliyan hudu na noman kwakwa. A bara kadai ta sami Dala biliyan biyu a fitar da kwakwa waje. Saboda hazaka da zakakuranci, Indonisiya ta zo ta sha kan Malesiya wajen fitar da kwakwa. Wadannan kasashen fa su na da mai, amma kawai su na da shugabanni na nagri ne fiye da Nijeriya. Akwai lokacin da Nijeriya ce kasa mafi fitar da gyada waje a duniya da manja, roba da koko. Kuma a lokacin mu na cikin kasashen da ke kan gaba wajen fitar da auduga, karo, fata, kashu da sauran kayan amfanin gona.

Ya kamata gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su fara tseren noman a junansu. Ya kamata gwamnatocin jihohi, musamman ma na Arewa tunda sun fi fadin kasar noma, su samar da akalla hekta 500,000 a kowanne yankin mazabar sanata (jihohi da dama za su iya samar da fiye da hakan), sannan su shigar da matasan da ke barazana ga tsaro cikin tsarin aikin yi a gidajen gona. Ya kamata a dawo tsarin wa’adin filaye da hukumar nan ta NALDA (Nigerian Agricultural Land Development Agency), wacce Janar Babangida ya kafa, amma saboda wawanci gwamnatocin da su ka gaji tasa ta rushe.

Ya kamata shugaban kasa ya fara aiki na hakika kan sha’anin noma, ya daina damun mu da batun biredin rogo haka nan.

Tuesday, June 12, 2012

Gidauniyar Rochas Okorocha Za Ta Gina Jami'ar Kyauta A Kasar Nan


Gidauniyar ci gaban ilmi da samar da shi kyauta ga masu karamin karfi ta Rochas Okorocha, ta bayyana kudirinta na gina Jami'ar farko a kasar nan da za ta ke bayar da ilmi kyauta ga masu karamin karfi.

Gidauniyar a halin yanzu na da mallakin makarantun sakandare har guda biyar a fadin kasar nan, wanda duk ake bawa masu karamin karfi ilmi a kyauta a cikin su, makarantun akwai su a bangarorin kasar nan daban daban, akwai a Ogboko jihar Imo, Owerri, Kano, Ibadan da kuma Jos.

Lalle Rochas ya jiri tuta a fadin tarayyar kasar nan, ya kuma zama abin kwatance, da za a samu masu tausayin talakawa kamar sa guda goma a cikin masu mulki da masu arzikin da ke dunkule a kasar nan da ilmi bai gagari 'yan talakawa ba.

Wannan gidauniya ta dade tana tuttula ilmi ga 'yayan da iyayen su ba za su iya daukar dawainiyar biyan kudade karatun 'yayansu ba, kuma wani abin sha'awa tun kafin ya samu mulkin jihar Imo da yake kai a halin yanzu gidauniya ta ke, kuma take yin aikin alkhairai daban daban da suka shafi fannin samar da ilmin zamani.

Sunday, June 10, 2012

Ana Zargin Faruk Lawan Da Hannun Dumu - Dumu Wurin Karbar Cin Hancin $600,000


Ana zargin shugaban kwamitin bincike kan badakalar tallafin man fetur Hon. Faruk Lawan da hannu dumu - dumu wurin karbar cin hancin zunzutun kudi dala mai dukan dala har dalar Amurka $600,000 daga wurin wani kamfanin man fetur da baida suna.

Hon. Faruk an ce da farko ya musanta zargin sai bayan da yaga takardu tsirara dauke da bayanin da ake zarginsa a kai. Tuni majalisar wakilai ta gayyace daya garzaya gabanta domin kare kansa daga wannan zargi.

Rahotonni sun nuna cewa ita ma dai hukumar nan mai yaki da yiwa arzikin kasa zagon kasa wato EEFC ta shirya tsaf domin gayyato Faruku don yi mata bayanin dalla dalla yadda akayi hakan ta faru.

Idan har wannan zargi ya tabbata gaskiya ne Faruk Lawan ya amshi wannan makudan kudade, lalle mu talakawan Nijeriya sai mu fara ja da baya, da rage tunanin cewa nan gaba kasar nan za ta zama daidai, da kuma daina murna da farin ciki duk lokacin da muka samu labarin anyi kokari kawar da wani laifi a kasar nan.

Ba komai ya sani fadin haka ba, sai tunowa da nayi lokacin da Faruk Lawan ya bayyana rahotonsa karo na farko, game da irin yadda kwamitinsa yayi aiki tukuru ba tare ba rana sai aka gano yadda wasu 'yan tsirara suka rinka wadaka da rabebeniya da dukiyar al'ummar kasar nan, da yadda Faruk ya rinka daukar alwashin ba zasu rufawa kowa suka samu da laifi asiri ba. Hakan tasa talakawa suka fara yiwa juna barka da fara tunanin lalle kakarsu ta fara yanke saka, sai kuma gashi kwatsam ana zargin mai dokar bacci da bugewa da gyangyadi. Allah ya kyauta.

Allah Ya Yi Wa Kanin Mataimakin Shugaban Kasa Rasuwa


Allahu Akbar! Allah ya yi wa Alhaji Aliyu Sambo, kanin magirma mataimakin shugaban kasa Arc. Muhammad Namadi Sambo rasu a jiya.

Alhaji Aliyu mai shekaru 40 ya rasu ne sakamakon hadarin mota daya ritsa da shi akan titin Mando yankin Kawo dake cikin garin Kaduna.

Allah ya jikansa da sauran al'ummar Musulmai baki daya.

Alhamdulillah! Yau Na Cika Shekaru 21 A Duniya


Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) Mai kowa mai komai. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SWA). Ina kara godiya ga Allah daya raya ni yau tsawon shekaru ashirin har da daya a wannan duniya mai cike da fadi tashi. Allah ina godiya da ka halicce ni cikin mabiya addinin Musulunci kuma ka zaba min addinin a matsayin addinina, kuma ka dora rayuwata akan tafarkin koyarwar addinin, lalle wannan shi ne babban abin godiya. Ya Allah ina rokonka ka bani ikon karasa rayuwata ba tare da na saba da koyarwa addinin Musulunci ba.

Wannan rana ta 10th June, rana ce mai matukar muhimmanci a gare, kuma rana ce da duk wani masoyina yake taya ni farin cikin zagayowarta. Kamar yadda lissafi ya nuna yau ma Allah ya sake nufarmu da zagayowa wannan rana, saboda haka yau na cika shekaru 21 da haihuwa daidai da watanni 252 ko satuka 1095 ko kwanaki 7671 ko awanni 184104 ko mintuna 11046287 ko sakonni 662777275 hhmm lalle na girma. Ina alfari da wannan rana a matsayin ranar da Allah ya nufi wanzuwata a wannan duniya domin na bauta masa.

A kodayaushe idan wannan rana ta zagayowa abinda yafi tsaya min a raina shi ne yadda iyaye na suka dauki dawainiyata tun daga haihuwata har zuwa yanzu, sun sani makarantu daban daban domin nasan yadda zan bautawa mahaliccina kuma na iya zama da duniya da al'ummar da ke cikin ta lafiya. Zahiri babu wata kalla da zan bayana ta godiya a gare su naji na gamsu sai kawai naci gaba da yi musu addu'ar Allah ya saka musu da mafificin abinda suka yi min na alheri.

'Yan uwa da abokaina ma sun taka muhimmiyar rawa a fannin rayuwata, a koyaushe suna zuwa gare ni idan na bukaci hakan, suna taimako na da bani shawarwari na alkhairi, sukan nuna goyon bayansu a gare ni a dukkan ra'ayi, sukan nuna farin cikin su gare idan abin farin cikin ya same ni, da nuna bakin ciki idan akasin farin ciki ya faru, sukan kasance dani kodayaushe domin kada su bar ni cikin kadai ci. Nagode! Nagode!! Nagode!!!.

Ya Allah ka raya mu, ka bamu ilmi mai amfani da zamu taimaki yan uwanmu da addininmu.

Tuesday, June 5, 2012

Tsakanin Buhari Da PDP Wa Ke So Tarwatsa Nijeriya? IGa duk wanda ya san Janar Muhammadu Buhari zai iya fassara shi a matsayin mutum mai tsattsauran ra’ayi akan abinda ya yarda da shi. Wanda ba ya shakkar bayyana ra’ayinsa ga kowa a kowa ne lokaci, kazalika kuma a ko ina.

Tsayayyen da ya ke fafutukar kawar da mulkin danniya da kama-karya. Kaifin dayan da ba ya fargabar shelantawa duniya manufarsa ta hukunta duk wani barawon shugaban da ya kwashi dukiyar talaka. Wanda a halin yanzu miliyoyin talakawan Nijeriya su ke son sa ba domin giwa ta fadi a sha gara ba, face sai domin kyautata masa zato da su ke yi cewa, shine kwalelen da zai tsallakar da su daga kududdufin karangiyar bakar wahala da su ka tsinci kansu sakamakon rashin nagartaccen shugabanci.

Janar Buhari ya kasance mai alfahari tare da bugun kirjin cewa, ya zama shugaban kasa, ya zama ministan man fetur, ya zama gwamnan tsohuwar Maiduguri kana kuma ya rike shugaban hukumar rarar mai ta kasa, amma kuma bai taba satar ko kwabo ba. Ya kan kuma jaddada cewa, a shirye ya ke ya amsa takardar gayyata daga kowa ne domin kare kansa akan shi ba barawo ba ne. Sau da dama a Nijeriya idan aka samu mutum mai bayyana kansa a matsayin mai gaskiya, sai tafiya ta yi tafiya sai a tsince shi ya hada kai da wadanda a baya ya ke kira a matsayin azzalumai kuma barayi domin karbar nasa kason.

Amma wani abin mamaki da ya kara daukaka kimar Janar Buhari shi ne yadda har yanzu ya ki aminta ya je ya sayar da ‘yancin talakawan da su ke son sa, domin a cika masa asusunsa. Shi ne wanda masu kashi a gindi su ke fargabar ya samu dama domin sun tabbatar ba zai raga musu ba. Janar Buhari ne talakawa ke tsananta son sa ba tare da ya na da kudin da zai kyautar a gare su ba. Sabanin sauran ‘yan siyasa da sun kwashi dukiyar kasa su ke kuma rabar wa ga talaka a yayin da su ka so a sake zabensu.

Janar Muhammadu Buhari ne ake ta kulle-kulle tare da makarkashiyar ko ta wanne hali a samo laifin da za a jingina masa domin a tozarta shi. Ko a yayin da hasalallun talakawa su ka yi tinzurin yi wa PDP korar-kare a wasu jihohin Arewa, sakamakon zargin tafka magudi da aka yi, wanda hakan ya janyo yamutsin da aka yi asarar rayuka da kuma dukiyoyi. An nemi a jingina wannan tarzoma ga Janar Muhammadu Buhari.

Kalamansa na ‘kowa ya kafa ya tsare ya kuma raka kuri’arsa’ a yayin gudanar da zabe, na daya daga cikin abinda ‘yan barandan siyasa da kuma sojojin baka su ka karbo kwangila domin lika masa a matsayin makamashin da ya assasa wutar wancan rikici. Kana kuma an zarge shi da yin amfani da karin maganar ‘jiki magayi’ a matsayin sababin rashin zaman lafiya da ya zama alakakai a wasu jihohin Arewa.

Akwai karashen wannan jawabi a kashi na II a kasa.

Monday, June 4, 2012

Ta'aziya Ga Jama'a Lagos Da 'Yan Nijeriya Baki Daya


Inna illahi wa innaa ilaihi raji'un! Inna illahi wa innaa ilaihi raji'un!! Inna illahi wa innaa ilaihi raji'un!!!

A madadin daukakin makaranta da maziyarta wannan Dandali muna mika sakon ta'aziyarmu ga gwamnatin jihar Lagos karkashin jagorancin Gwamna Babatunde Fashola da sauran jama'ar Lagos dangane da bala'in daya same su a jiya na hadarin jirgin saman fasinja na kamfanin DANA da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane dari da hamsin 150. Sannan muna jajentawa wadanda suka samu munanan raunuka da kuma wadanda suka rasa dukiyoyinsu.

Muna kuma mika makamanciyar irin wannan ta'aziya ga gwamnatin kasar nan karkashin jagorancin shugaba Goodluck Ebele Jonathan da sauran al'ummar kasar nan baki daya, saboda kuwa wannan bala'i ya shafi dukkan daukakin jama'ar Nijeriya.

A karshe muna addu'ar ya Allah ya jikan 'yan uwa Musulman da suka riga mu gidan gaskiya sanadiyar wannan hadari su kuma wadanda ba mabiya addinin Musulunci ba za mu iya cewa RIP.

Ya Allah ya baiwa wadanda suka samu raunuka lafiya, ya maidawa wadanda suka rasa dukiyoyinsu da alkhairi. Ya Allah ya kare mana faruwar irin haka anan gaba.

Sunday, June 3, 2012

Al'ummar Masar Sun Sake Fita Filin Zanga - Zanga Akan Hukuncin Da Aka Yankewa Hosni Mubarak


Dubun dubatar yan kasar Masar ne ke gudanar da zanga-zanga a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira, kan hukuncin da aka yankewa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak da wasu mukarraban sa.

An dai yankewa Mubarak da tsohon Ministan harkokin cikin gidansa Habib al- Adly hukuncin daurin rai da rai sakamakon samun su da aka yi da laifin haddasa kisan daruruwan masu zanga-zanga a rikicin da ya faru cikin shekarar da ta gabata.

Manyan kwamandojin 'yan sanda shida ne kotun ta sallama, yayin da aka wanke Mubarak da dansa daga zargin cin hanci da rashawa. Masu zanga-zangar sun bukaci a yankewa wadanda ake tuhumar ne hukuncin kisa.

Don haka kungiyoyin siyasa suka yi kira ga jama'a su fito kwansu da kwarkwata domin yin Allah wadai da abinda suka ce rashin adalci a shari'ar.

To wai shin a tunaninku mai jama'ar kasar ta Masar ke nufi? Sanin kowa ne jama'ar kasar da goyon bayan su aka kawo karshen mulkin Hosni Mubarak, yau kuma ga shi sun sake dawowa suna nuna goyon bayansu gare shi. Gaskiyar masu iya magana da suke cewa "Duk wanda bai godewa Allah ba, to zai godewa azabarsa".

A karshe ina fatan al'ummar kasata Nijeriya za su dauki darasi daga wannan abu da ya faru kuma yake sake faruwa a kasar ta Masar.

Friday, June 1, 2012

An Kashe Wani Bajamushe a Kano

Rundunar tsaron hadin gwiwa a Kano da ke arewacin Nigeria, ta tabbatar da mutuwar wani dan kasar Jamus da aka sace jihar da kuma wasu mutane biyar a wata musayar wuta da aka yi da safiyar yau a birnin.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar dazu, tace, mutumin ya mutu ne bayan wani samame da ta kai wani wuri da ta ke zargin cewa maboyar wasu jagororin mutanen ne da ke kai hare hare a birnin.

A watan Janairun wannan shekarar ne dai mutanan suka sace Bajamushen wanda injiniya ne dake aiki a kamfanin gine-gine na Dantata and Sawoe, inda tun daga wannan lokaci su ke garkuwa da shi a birnin na Kano.

Yanzu haka dai jami'an tsaron rushe gidan da lamarin ya faru. A wani labarin kuma rundunar 'yan sanda a jihar kwara dake arewacin Najeriya ta ce an sace wani dan kasar Italiya a jihar.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da halin da yake ciki, amma 'yan sanda sunce suna binciken al'amarin.

Haka na zuwa ne 'yan watanni bayan mutuwar wani dan Italiya Franco Lamolinara da wani dan Burtaniya, Chris McManus a Jihar Sokoto wajen cetonsu bayan an sace su a jihar Sokoto.

Mutanen biyu an sace su ne a jihar Kebbi dake arewacin kasar a shekarar 2011.

Rahoto daga BBC Hausa

Gwamnatin Nijeriya Ta Kara Farashin Wutan Lantarki - Amma Ta Ce Karin Ba Zai Shafi Talakawa BaGwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Goodluck Jonathan ta kara maimaitawa 'yan Nijeriya ranar 1 ga January (Ranar da aka janye tallafin mai) saboda kuwa a yau 1 ga June, muka tashi da karin farashin kudin wutar lantarki, kamar yadda gwamnatin ta alkawarta tun a baya. Duk da hukumar da ke kula da wutar lantarkin ta bayyana cewa karin farashin ba zai shafi talakawa ba, sai dai manyan masana'antu. Amma masa fannin tattalin arziki sun bayyana cewa karin farashin ba wanda zai fi sha fa sama da talakawa, saboda idan an yiwa kamfani karin farashin wuta, shi kuma kamfanin akan talakawa za su fanshe.

Shin anya kuwa za'a samu wutar lantarki isashiya a kasar nan? Na yi wannan tambaya ne saboda yadda a cikin satin nan na ci karo da hoton tsohuwar wata jarida a shafukan internet, wannan hoto ya tabbatar min da cewa lalle an dade ana yiwa 'yan kasar alkawarin kawo karshen nai na zama a cikin duhu. Bayanai da suka bayyana a cikin hoton tsohuwar jaridar sun nuna cewa a lokacin shugaba Shehu Shagari ne ke jagorantar kasar nan, kuma gwamnatin nasa ta dau alkawarin daga 1986 ba bu sauran sake zama cikin duhu a kasar nan baki daya.

Amma abin mamaki daga wancan lokacin zuwa yanzu kusan shekaru 30 kenan, amma har yanzu wutar bata samu yadda ake bukata ba, hasalima, kullum lantarkin sai kara tabarbarewa take yi tana ja da baya, kuma kowane shugaba ya zo maganar kenan, ga makudan kudaden talakawa da ake fitarwa lantarkin tana lakusewa.

To mu dai kullum addu'armu Allah ya kawowa kasar nan mafita ta alkhairi, Allah ya bawa kasar nan jagorori na gari.