Sunday, October 9, 2011

Muhimman Shafukan Gidajen Yanar Gizo domin karuwar Musulmai

Yanar gizo (Internet) a wannan zamani ta zama abokiyar rayuwa, wanda masu amfani da ita ba zasu iya koda kwana daya ba tare da sun kai ziyara ba, sai dai da wani kwakkwaran dalili, kamar rashin lafiya ko rashin service. A wani bincike da masana suka gabatar a wannan zamani jama'a sunfi cinye lokacinsu a wurin amfani da Yanar Gizo sama da komai. Wasu na cinye lokacin nasu a bincike bincike da kalle kalle marar amfani, wasu kuma basu da aiki sai neman abokan hira daga sassan duniya daban - daban, wasu kuma Allah ya taimake su, suna cinye lokacin nasu ne akan karin neman ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci.

Ga duk masu sha'awar amfanar lokacin a duniyar yanar gizo ga shafuka masu muhimmanci domin Musulunci da Musulmai:-

Islami City (http://www.islamicity.com) - shafi ne daya kunshi abubuwa masu yawan gaske kamarsu bayani game da Shika-shikan Musulunci, Lokutan sallah, litattafai da sauransu.

Qur'an Complex (http://www.qurancomplex.org) - shafi ne da tsohon sarkin kasar Saudi Arabia King Fahaq bin Abdallah ya samar dashi game da Al Qur'an Mai girma.

Fatwa Islam (http://www.fatwaislam.com) - shafi ne dake cike da fatawoyin manya manyan Malam na da dana yanzu. Sannan kuma mutum zai iya tura fatawarsa a dawo masa da amsa nan take.

Islam Online (http://www.islamonline.com) - wannan shafi ne daya danganci bangaren labarun abubuwan dake faruwa a duniyar Musulunci. Sai kuma hira ta keke da keke (Video Chat) tsakanin Musulmai dake sassan duniya daban - daban.

Islam Question & Answer (http://islamqa.com) - shafi ne dake kunshe da tambayoyi da amsoshinsu dangane da abubuwan da suka shigewa Musulmai duhu.

Ja'afa Mahmud Adam (http://www.jaafarmahmudadam.org) - wannan shafin na kunshe da wa'azin Marigayi Malam Ja'afar Mahmud Adam da kuma fatawoyinsa.

Haruna Yahya (http://www.harunyahya.com) - Shafin haziki kuma fasihi Harun Yahya wannan yake bayani game da kimiya da fahasa, a mahangar Musulunci.

Idan kuma mutum yana neman wani abu bai samu ba, a cikin wadannan shafuka dake sama zai iya ziyarta shafin bincike na Google don bincikowa. Allah ya kara taimakon addinin Musulunci da Musulmai baki daya.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

2 comments:

  1. babu shakka ko tantama akan duk abubuwan da ka fada... Wanda kuma karancin mutane irinku ne ya haifar da wannan matsalar... Toh nidai babu abinda xan iyacewa sai godiya ga Allah da kma mutane irinku... Da fatan Allah ya kara basira...

    ReplyDelete
  2. Bashir kasan zuciyar dan'adam kamar tsirrai yabanya ne yana bukatar ruwan , in har ba ruwa sai yayi yaushi har ya bushe. Saboda haka muna bukatan nasiha

    ReplyDelete