Gaskiyar Hausawa da suka ce "Tafiya Mabudin Ilimi" duk da na yarda da hakan, amma ban gama tabbatarwa ba, ko nace ban taba jarrabawa ba, sai lokacin da nayi tafiya daga Kano zuwa Sokoto. Taron kungiyar Dandalin Siyasa e-Forum, karo na 3, Tafiyar da ban tabayin mai nisanta ba, a tarihin rayuwata, sai dai kuma nan gaba idan Mai duka ya barmu da rai da kuma lafiya.
Wannan tafiya tawa, mai kunshe da kalubale, alfahari, ilimi gami da abubuwan al'ajabi, nayi tane ranar 14 October zuwa 16 October 2011. Tabbas wannan tafiya ko shakka babu, ta shiga cikin tafiyoyin da bazan taba mantawa dasu ba (Unforgetable Journey).
Da farko a ranar tafiyar na tashi daga bacci tun da sanyi safiya na fara shirye shirye, kamar mai barin kasar kwata kwata. Na fito daga gida misalin 7:56am ba tare dana kammala 'yan shirye shirye na ba, saboda ina tsoron kar mota ta tashi ta barni, kamar yadda aka tabbatar min za'a hadu 7:30am a tashi zuwa birnin Shehu 8:00am.
Na isa kofar shiga tsohuwar Jami'ar Bayero, inda za'a hadu, amma saboda Nigerian Time da wani bawan Allah yayi bamu tafi ba sai 9:00am. Abinka da sabon shiga, fara tafiyar ke da wuya na dakko mujallar MURYAR AREWA na fara karantawa don kar ko gyangyadi ya dauki ni a shige wani wuri ba tare dana kashe kwarkwatar idona ba. Bayan na gaji da karatun jaridar sai na dauki wayata, na shiga shafin sada zumunta na Facebook na rinka sanarwa da yan uwa da abokanan arziki halin da tafiyar tamu ke ciki. Su kuma suna taya mu adduar fatan alheri gami da sauka lafiya.
Can da tafiya tayi tafiya sai wayar ma na hullata a aljihu, nayi zuru na zubawa sarautar Allah ido, wato dai na gaji kenan amma saboda tsegumi irin nawa, ko kadan ban nuna gajiyar ba, balle na kishin gida har bacci ya samu damar kwashe ni.
Nasan masu karatu ku kanku kunsan a wannan tafiya idanuwa na sun sha kallon abubuwan da ba sai na tsaya ina bata bakina wurin lissafa muku su ba, kai zahirin gaskiya ma dai idan nace zan lissafo zan iya yi muku ragi, don haka zan fadi wasu abubuwa guda biyu zuwa uku da suka fi daukar hankalina. Na farko naga shimfida shimfidan tituna amma ba motocin yawatawa akansu a jihar Katsina. Na biyu naga wani rusheshen dutse a jihar Zamfara, wanda idan mutum ya nemi kallo tsayinsa to tabbas hular zata fadi kasa ba tare da ya sani ba. Abu na uku shine karamcin da Sakkwawa sukayi mana, wanda bazan taba mantawa ba.
A takaice dai bamu isa cikin birnin Shehun ba, sai misalin 3:36pm, kai tsaye aka wuce damu, Sokoto Guest Inn, wanda shine masaukinmu. Kai mutane Sokoto akwai iya karbar baki sai kace wadanda suka zo Kano suka dauki darasi, domin kuwa da isarmu ba abinda suka tarye mu dashi sai wani daddadan kilishi hade da sassanyan lemo. Kasan Bakano bai da filako nan take muka tashi da wannan hidima.
Misalin 9:30pm na wannan rana, aka debe mu cikin zungureriyar mota, zuwa wurin wani shakatawa mai suna Daddy's Smart dake cikin birnin na Shehu, domin gabatar da Cultural Night wanda kungiyar ta Dandalin Siyasa ta shiryawa 'yayanta domin debe kewa. A wannan wurin na sha dariyar da tayi kusan sa cikina ciwo, domin kuwa tsohon dan wasan Hausan nan na barkwanci Golobo (Boloko) shine ya cashe tare da jama'arsa.
Washe gari ranar 15 October, ranar da aka ware don yin taron, mun tashi mun shirya, sannan muka nufi wurin da za'a gabatar da taron a dakin taro na makarantar koyon karatun Al Kur'ani da Kimiyya na Muhammad Maccido, amma kafin a fara gabatar da laccocin da za'a gabatar sai da aka kai ziyarar girmama fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III. Bayan an dawo daga fada sai aka koma wurin taron.
An gabatar da laccoci a wurin taro wadanda suka shafi halin da kasarmu Nigeria ke ciki a halin yanzu, kamar irinsu TABARBAREWAR TSARO, ILIMIN BOKO, sai kuma DEMOCRADIYA wanda Prof. S. A. Yakasai na jami'ar Shehu Usman Danfodio da kuma Dr. Usman Muhammad na jami'ar Birnin Tarayya Abuja suka gabatar.
An kammala taro misalin 3:30pm, daga nan bayan an gabatar da sallar La'asar sai kuma aka tafi kai wata ziyarar girmamar gidan Alhaji Abubakar Alhaji (Alhaji Alhaji) Sardaunan Sokoto na yanzu, dattijon arziki, namiji uban masu kudi da 'yan boko. An gabatar masa da kungiya, ya kuma yi farin ciki gami da karfafa gwiwa.
Sai kuma wajen 9:30pm aka tafi wurin dinner a Mr Bigs wanda aka kai har zuwa 11:30pm daga nan kowa ya tafi masaukinsa. Kuma wannan shine abu na karshe da aka shirya gabatarwa a taron.
Washe gari ranar 16 October rana ce da duk wanda yaje birnin na Shehu zai waiwayi inda ya fito, a ranar ne muma da misalin 9:30am muka kama hanyarmu ta dawo gida Kanon Dado mai mata mai mota mai Dala da Goron Dutse.
A karshe ina kara mika godiyata ga dukkan SAKKWATAWA wadanda suka dauki dawainiyarmu tunda muka je har muka dawo gida. Allah yasa da alheri, Allah ya kara hada fuskokinmu da alheri, ameen!
No comments:
Post a Comment