Wednesday, February 29, 2012

Shin Za a Bukaci Kafafen Yada Labarai Anan Gaba?


Babu shakka shafukan sada zumunta kamar
Facebook, Twitter da You Tube sun sauya
yadda muke samun labarai.

Shafukan sada zumunta sun yi matukar
sauya yadda kafafen yada labarai na
duniya ke gudanar da ayyukansu.

A lokacin wani taro da BBC ta shirya bara
kan shafukan sada zumunta, manajan
editan jaridar Washington Post ya yi wani
jawabi mai daukar hankali inda ya ce "Mai
zai sa na dauki dan jaridar da bashi da
adreshin Facebook ko Twitter?"

Tuni aka fara tattaunawa kan ko nan gaba
za a bukaci kafafen yada labarai kamar
rediyo da talabijin.

Amsar ita ce kamata ya yi a koma a duba
tarihin yadda fasaha ke habbaka.

ALAKAR LAMARIN DA TARIHI

Idan muka duba tarihin gidajen buga
takardu a shekarun 1400, amfani da allunan
buga takardu a 1700, da tarho a 1800, da
kuma rediyo a 1800 zuwa farkon 1900, sun
ci karo da mulkin mallaka da kuma yakin
duniya.

Lokacin da aka kirkiro kowanne daga cikin
wadannan, mutane sun yi hasashen cewa
mafi sabunta daga cikin zai maye gurbin
sauran.

Lokacin da aka fara amfani da tauraran
dan'adam a 1980, an nuna damuwa kan
cewa zai kawo karshen jaridu.

Duk da cewa tauraron dan'adam ya sauya
yadda jaridu suke aiki, amma har yanzu
suna aiki duk da cewa suna fuskantar wani
yanayi mai tsauri.

AL'UMMA A DUNIYAR GIZO MAI CIBIYA A KAN NA'URA MAI KWAKWALWA

Idan aka yi la'akari da shafukan sada
zumunta kamar Twitter da Facebook, wani
sauyi ne aka samu ta fannin fasaha wanda
kamar rediyo da talabijin sun karo da wasu
abubuwan na zamani.

Mafi muhimmanci shi ne boren kasashen
Larabawa wanda ya kai ga kifar da
gwamnatocin kasashen Tunisia da Masar da
kuma Libya. Ya kuma yi tasiri a Wall Street a
Amurka da Turai da ma Afrika.

Wannan tasiri ya kuma sauya fagen siyasan
duniya inda jama'ar da ke amfani da
facebook suka suka ninka adadin yawan
jama'ar Amurka.

Wannan shi ne abinda zan kira kasashen da
suka yi nisa wurin amfani da kafofin
sadarwa na zamani.

Suna cike da matasa wadanda koda yaushe
suna tare da na'urorin kwamfiyuta da kuma
wayoyin na salula masu komai-da-ruwanka.

Sun riga sun saba da amfani da irin
wadannan kayayyakin fasaha na zamani;
don haka kalubalen da ke gaban kafafen
yada labarai na zamani shi ne su shiga a
dama da su a wannan fagen.

Nan da shekaru masu zuwa, wadannan
matasan ne za su zamo masu fada aji, haka
kuma masu shiryawa da kuma sauraran
labarai.

Ban amince da batun da ake na cewa
shafukan sada zumunta ko kuma internet,
za su maye gurbin talabijin da rediyo
kwata-kwata ba. Abinda zai faru shi ne za
su sauya yadda ake gudanar da harkokin
watsa labarai.

Tuni mun fara ganin gidajen talabijin a
Amurka kamar PJTV duk da kayan aikin da
suke da su irin na zamani, amma suna
watsa shirye-shiryen na su kawai a internet.

Nan gaba za a samu karin kafafen yada labarai da za su bi sahun PJTV, amma ba
ruwansu da kalubalen da ainahin gidajen
yada labarai za su fuskanta ba.

KARFAFA DANGANTA

Sai dai akwai abubuwa masu kayatarwa da
talabijin ke samarwa musamman a tsakanin
masu matsakaicin hali. Tana kyautata
dangantaka tsakanin iyalai, kuma wannan
shi ne abinda shafukan sada zumunta ba sa
samarwa cikin sauki.

An fi amfani da su ta wayoyin salula domin
debe kewa a gida ko makarantu ko kuma
wuraren aiki.

Sai dai a wuraren jama'a da dama a kasashe
masu tasowa, rediyo na gudanar da
makamancin wannan a yankunan karkara.

Za a dauki tsawon lokaci kafin shafukan
sada zumunta su maye gurbin tasirin rediyo
musamman a inda rediyon ta kasance
hanya daya tilo ta samun bayanai.

Wani abu da ya fito fili shi ne lokacin da
manyan kafafen yada labarai ke da iko a
kan labarai ta wuce, amma hanyar gudanar
da cikakken tsarin aikin jarida na nan har
gobe.

Kuma wannan shi ne muhimmin abu da ya
rage ga 'yan jarida, kuma wata rana masu
amfani da hanyoyin sadarwa na zamani za
su so su shiga wannan fagen.

Koma dai yaya ta kaya, a yanzu muna
karnin shafukan sada zumunta!

Muhammad Jameel Yusha'u
Malami ne a jami'ar Nothurmbria a
Burtaniya
.

Daga shafi BBCHausa.com

Tuesday, February 28, 2012

Har Yanzu Ba'a Bawa Iyalen Al - Mustapha Shaidar Hukuncin Da Aka Yanke Masa Ba - Shin Kotu Za Tayi Masa Adalci Kuwa?

"Shin anya za'a yi wa Major Hamza Al - Mustapha adalci kuwa?" Wannan tambayar ita nayi ta maimaitawa a cikin zuciya tun jiya, bayan da naji dan uwan Al - Mustapha, mai suna Haruna Al - Mustapha ya bayyanawa gidan radio Wazobia FM dake Kano, halin da suke ciki tun bayan yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata kotu da yanke masa a jihar Lagos. Amma abin mamaki har yanzu ban samu amsar tambayar da nake tayi wa kannawa ba, duk da daman ban yi tsammanin samun amsar tambayar cikin sauki ba, ko ma nace bazan taba samun amsar tambayar tawa ba, kawai dai zuciyata ce take son yaudara ta, da wahalar da ni akan tunanin nemo amsar tambayar da ba mai iya amsa ta sai 'yan tsurarun mutanen da zuciyata ke yin tambayar akansu.

Dalilin daya sa nayi wa kan nawa wannan tambaya shi ne halin da naji iyalen Al - Mustaphan sun bayyana suna ciki, ta bakin Haruna Al - Mustapha, kamar yadda na bayyana tun da farko. A jiya da misalin 8:30 na dare, ina sauraren wani shiri mai suna KASUWAR BUKATA wanda Muhammad Suleiman Gama ke gabatarwa a gidan radio Wazobia FM, a cikin shirin dan uwan na Al - Mustapha ya bayyana cewa suna cikin halin tsoro da damuwa tun bayan hukuncin kisa da kotu a jihar Lagos, karkashin Jagorancin mai shari'a Justice Dada ta yankewa dan uwan nasa.

Haruna Al - Mustapha ya bayyana cewa, tun bayan yanke hukuncin da aka yi suke ta kokarin daukaka kara a kotun gaba, amma har yanzu abin ya ci tura, ba don komai ba sai don rashin samun takarda a rubuce ta shaidar hukuncin da aka yankewa Al - Mustaphan, daga kotun da ta yanke hukuncin. Wanda kuma daukaka kara ba zai taba yiwuwa ba har sai da kwafin takardar shaidar yanke hukunci daga kotun baya.

Dan uwan na Al - Mustapha ya kara da cewa a kundin tsarin mulkin Nijeriya, sati daya ne mafi nisa ga duk wanda kotu ta yankewa wani hukunci kowane iri ne ta bashi a rubuce, amma sai gashi wata daya da yanke hukuncin, suna ta fafutukar samun rubutacciyar shaidar amma basu samu ba. Sannan yace a kundin tsarin mulkin na kasar nan, duk wanda aka yankewa hukunci bai daukaka kara ba tsawon wata biyu, to lailai ya gamsu da hukuncin da aka yanke masa kenan, hakan yana nufin idan bamu samu wannan rubutacciyar takarda ba har wata biyu ta cika za'a rataye mana dan uwa, ba tare da aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.

Sanin kowane bayan yanke wannan hukunci daya daga cikin manya - manyan shaidun da suka bada shaidar cewa Al - Mustapha ne ya sa su, suka kashe Hajiya Kudirat Abiola, mai suna Abdul Katako ya fito ya bayyanawa duniya cewa shaidar karya aka tursashi yayi a gaban kotu, domin za'a bashi wasu makudan kudade da gidan zama duk inda yake son zama a fadin kasar nan.

A karshe Haruna Al - Mustapha ya bayyana cewa a tsakanin yau da gobe zasu dauki matakin shari'a, za su kai karar kotun da ta yanke wannan hukunci, a gaban hukumar shari'a ta kasa, saboda rashin basu takardar shaidar hukuncin da aka yankewa Major Hamza Al - Mustapha akan lokaci.

Ya Allah ga bawanka, Ka fitar da shi daga wannan hali da yake ciki, Ya Allah kar kabawa azzalumai damar yin zalunci akan wannan bawa naka.

Monday, February 20, 2012

Daman Haka Muke Tsammani - Wamako Ya Sake Komawa Kujerar Gwamnan Jihar Sokoto


Gwamna Alh. Aliyu Magatakarda Wamako ya sake komawa kujerarsa ta gwamnan jihar Sokoto a karo na biyu. Wamako na daya daga cikin gwamnoni biyar da kotu ta sauke daga mukaminsu a baya bayan nan.

Jami'un adawa sun bayyana rashin amincewa da zaben tun kafin a bayyana sakamakon zabe a jiya, jami'un na adawa sun bayyana cewa an sace musu wakilansu, wasu kuma an tirsasa su wurin sa hannu a takardar sakamakon zaben.

Gwamna Wamako, ya ce duk wanda bai yarda da sakamakon zaben ba to ya garzaya kotu.

Kai lallai PDP power!!!

Saturday, February 18, 2012

Gen. Muhammad Buhari Zai Dawo Kaduna Da Zama Daga Abuja Saboda Ba Zai Iya Biyan Miliyan 20 Kudin Haya

General Muhammad Buhari, tsohon janar din soja, tsohon gwamnan jihar Arewa maso gabas, tsohon ministan man fetur, tsohon shugaban tarayyar Nigeria, tsohon shugaban hukumar tattara rarar man fetur (PTF), dan takarar shugabancin kasa karo uku, zai tattara iyalansa daga birnin tarayya Abuja daga gidan da yake haya zuwa gidansa na jihar Kaduna.

Hakan ya biyo baya sakamakon iya biyan kudin hayar gidan da yake zaune a birnin tarayyar. General Buhari na zaune a gidan na tsawon shekara guda wanda wani abokinsa General Danjuma ya biya masa kudin hayar gidan Naira miliyan sha biyar N15,000,000 a shekarar da ta gabata saboda Buharin ya samu sakin zirga - zirgar da yake yawan yi tsakanin Kaduna da Abuja, a lokacin yakin neman zabensa.

'Yan kwanaki kadan ya rage lokacin hayar gidan ya cika, masu gidan suka aiko da takardar sabunta kudin hayar, inda suka sanar da cewa sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kayayyaki ya samu kudin hayar gida ya karu da kaso daya bisa uku na kudin hayar gidan a bara, wato kudin hayar gidan yanzu ya kama naira miliyan ashirin N20,000,000.

General Buhari, bai yi kasa a gwiwa ba ya nuna ba zai iya biyan wannan kudi ba, kuma ba zai je wurin wani don neman taimakon a biya masa kudin hayar gidan ba, saboda haka ya tabbatar da komawa gidansa na Jihar Kaduna.

Gaskiya wannan ba karamin al'ajabi ba ne, a ce mutum kamar Buhari da ya rike irin wadannan mukamai amma bai mallaki unguwanni, kamfanunuwa, filaye a kowace jiha a kasar nan ba, sanin kowane ba wani mutum da ya taba rike mukami daya daga cikin mukaman da Buhari ya rike amma bai mallaki gidaje a birnin na tarayya ba, kai wasu ma har kasashen waje suke zuwa suna mallakar manya - manyan gidaje.

Hakan ya kara tabbatar min da dalilin da talakawan Nigeria suka dage sai ya sake dawowa sun zabe shi a matsayin shugaban kasa. Mafi yawa daga talakawan Nigeria sun baya Buhari kuri'arsu din din din, wato idan zai fito sun dubu ba tare da yayi nasara ba ko nace ba tare da an bashi ba, to za su zabe shi sau dubu, wasu daga cikin talakawan ma alkawari suka dauka idan ba Buhari ba to ko rijistar zabe ba zasu yi ba balle ma sau zabi wani. Kuma hakan ya kara tabbatar min da dalilin da yasa talakawan suke kiran Buhari da sunan Mai Gaskiya.

Thursday, February 16, 2012

Kotu Ta Yankewa Umar Farouk Mutallab Hukunci


Wata kotu a Amurka za ta yanke wa dan Najeriyar nan hukunci wanda ya so ya tayar da bam da yasa cikin dan kamfansa a Jirgin saman Trans-Atlantika na Amurka.

Shari'ar za ta kawo karshen gurfanar da wanda ake zargi da aikata ta'addanci a kotun farar hula a Amurka. Umar Farouk Abdulmutallab ya amsa laifukan da aka tuhume shi da aikatawa guda takwas a watan Octoban shekarar da ta gabata.

Masu sharhi akan al'amuran shari'ah dai na ganin cewar za a iya yi masa sassauci musamman idan akai la'akari da shekarun sa.

A ranar 25 ga watan Disambar shekara ta 2009 ne dai Umar Farouk Abdulmutallab yai yunkurin tayar da bam a jirgin saman na Amurka.

Daga shafin BBC Hausa

Thursday, February 9, 2012

Gaskiya Ta Fara Bayyana - Katako Ya Bayyana Shaidar Karya Yayi akan Hukuncin Al-Mustapha


Muhammad Abdul, wanda aka fi sani da Katako, daya daga cikin sahun gaba wuri bada sheda game da kisan da aka yi wa Hajiya Kudirat. Katako a karon farko ya bada shedar cewa Major Hamza Al-Mustapha ne tsohon dogarin Sani Abacha ya bada umarnin harbe Kudirat Abiola, wanda wannan dalili ya sa wata kotu a jihar Lagos ta yankewa Al-Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Katako a jiya ya bayyana cewa wannan sheda daya bada shedar zur ce, gwamnati ta ba shi cin hanci ne yayi wannan sheda. Kuma ya bayyana cewa Al-Mustapha ba mai lefi ba ne.

Ya bayyana hakan ne a gidan radiyon Hausa na France (RFI) Katako yace "Eh, shedar zur nayi, amma daga baya da nayi tunani na ga akwai ranar lahira, duk wani abu da na samu anan duniya akan karya ranar lahira gaskiya za ta bayyana, wannan ya sa na koma kotu na tabbatar da cewa karya nayi".

Da aka tambaye shi mai ya sa ya bada shedar karyar sai ya bada amsa da cewa "An yi min alkawari abubuwa masu tarun yawa, da farko an tsare ni akan maganar Muhammad Sani Abacha, sun tabbatar min cewa sun gano wasu kudi masu dumbin yawa a wurinsa, idan na bada shedar karya aka karbo wadannan kudade za'a ba ni kaso 10 a ciki ko nawa ne, kuma za su hada min da gida a ko ina nake son yin rayuwa. A karshe kuma sai suka kawo min maganar Al-Mustapha suka karanta min duk irin zargin da suke yi masa, da kuma irin abin da zan fada idan an je kotu".

Ya kara da cewa "Mun zauna da manyan lauyoyi da dama, har nake tambayarsu shin ba abinda zai same ni? Suka tabbatar min da ba abinda zai faru da ni, suka ce kar na damu wannan magana ce ta gwamnati kuma ni sheda ne na gwamnati".

Katako yace yanzu yana nadamar wannan karya da yayi, saboda a matsayinsa na Musulmi an hore shi da zamu mutumin kirki, kar ya cuci kowa ko yayi sanadin mutuwar wani, sannan ya kara da cewa "Duk da ya koma kotu tun da wuri ya sanar da cewa shedar zur ya bada, amma kotun ta ki amincewa da cewa karya nayi, da maganata ta farko za suyi amfani. Saboda haka yanzu nake son kowa da kowa yasan cewa shedar zur na bada a kotu, kuma Al-Mustapha ba shi da laifi"

Da aka tambaye shi ko an cika masa alkawuran da aka yi masa? Sai yace "Alkawari daya aka cika min an bani gida a Jos, kudi na bayyana cewa karya nake yi ba don ba'a cika min alkawuran da aka daukar min ba. Na yi hakan ne saboda sanin idan har aka kashe shi ta hanyar rataya ransa yana kai na, kuma duk dadewar da zanyi anan duniya dole zan mutu, don haka ina so duniya ta san cewa ba Al-Mustapha ne yayi sanadiyar mutuwar Kudirat Abiola ba, kuma shi ba mai laifi ba ne".

Ya Allah ka kara bayyana gaskiya, kuma ka baiwa gaskiya nasara akan karya, ka kubutar da bawanka Al-Mustapha daga hannun azzalumai.

Source: Nairaland.com via People Daily Newspaper.

Real Madrid Ce Kungiyar Kwallon Kafa Da Ta fi Kowacce Kudi a Duniya


Kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain wato Real Madrid itace kungiyar da ta fi kowacce kungiya kudi a fadin duniya.

Kudaden shigar kungiyar Real
Madrid ya kai euro miliyan dari hudu
da tamanin, hakan ya bawa kungiyar damar zama a matakin farko a kudi a
duniya, in ji kamfanin Deloitte mai
hada hadar harkar wasanni.

Bayanan da kamfanin Deloitte ya
fitar ya maida hankali ne a kan kakar
wasanni shekara ta 2010/2011.
Real Madrid dai ce ta ke rike da wannan kambu na kungiyar da ta fi kudi a duniya na tsawon
shekaru bakwai a jere, kamar yadda kamdanin mai hada hadar harkokin wasanni ya fitar.

Abokiyar hammayar Real Madrid din, wato
Barcelona ce ta biyu a yayinda kuma
Manchester United ta zama ta uku.
Bayern Munich ce ta hudu sannan
Arsenal tana ta biyar, Chelsea dai ce
ta shida a teburin.

Ga jerin Kungiyoyi kwallon kafa guda 10 da su ka
fi kudi a duniya
:-

1. Real Madrid - 479.5m euros
2.
Barcelona - 450.7m euros
3. Man Utd - 367m euros
4. Bayern Munich - 321.4m euros
5. Arsenal - 251.1m
euros
6. Chelsea - 249.8m euros
7. AC
Milan - 235.1m euros
8.
Internationale - 211.4m euros
9.
Liverpool - 203.3m euros
10. Schalke - 202.4m euros.

Monday, February 6, 2012

Sarauniyar Ingila Ta Cika Shekaru 60 a Gadon Sarauta

A yau ranar Litinin ne ake bikin cika shekaru sitti (60) da hawan sarauniya Elizabeth II ta Ingila gadon sarauta.

Sarauniya Elizabath II mai shekaru 85 a duniya, A wani sako da ta aika, ta bayyana godiyarta ga wadanda suka bata goyon baya da kuma karfafa mata gwiwa a shekaru sittin din da ta shafe akan gadon sarauta.

An dai shirya wasu taruka a wannan rana don gudanar da jawabai game da sarauniyar Ingilar.

Sarauniya Elizabeth II ta soma mulki ne bayan da mahaifinta Sarki George na shida ya rasu a ranar shida ga watan Fabrairu ta shekarar 1952.

Wannan wata rana ce ta murna ga sarauniyar da kuma sauran magoya bayanta musamman turawan yankin Birtaniya.

Daga Shafin BBC Hausa