Monday, April 28, 2014

HIRA TSAKANIN BABAN DA MAMAN FAISAL KAN JARUMAN FINAFINAN HAUSA


Hira tsakanin miji (Baban Faisal) da maidakinsa (Maman Faisal) akan jaruman finafinan Hausa da suke goyon baya.

"Kai Safiya gaskiya fa duk 'yan fim din Hausa babu mai birge ni kamar Zainab Indome"

"Lallai maigida na ga kana yawan sayo fina finan da ta ke ciki"

"A she dai kin lura?"

"Haba Baban Faisal ai na dade da lura da haka"

"Wato Dear ko bata min rai kika yi idan na kalli idanuwan Indome sai na ji na huce"

"Ok shi ya sa na ga daga mun sami matsala ko ba wuta sai ka tayar da inji ka sanya fim din ta.?"

"Kwarai ma kuwa, ba ma kamar a ce fim din da ta ke dan rausayawa, kin san ta iya rawa"

"Gaskiya kam Zainab Indomee ta yi"

"Ga ta duk kayan da ta sanya sai ki ga ya yi daram a jikin ta.

"Gaskiya Baban Faisal ka gama yarda da alamarin Zainab Indome"

"A zakin murya kuma idan kika sami Nafisa sai wata rana an gama,"

"Kai maigida Nafisa har wani dadin murya ne da ita?"

"Kwarai ma kuwa idan ta na magana kamar ta na rera waka"

"Hm Baban Faisal ba ka da dama"

"Kin san kuma wa ta fi kira da diri?

" Sai ka fada maigida"

"Na ba ki gari sahibata Safiya"

" Maigida ai ni a duniya babu mai birge ni kamar Ali Nuhu, ban taba ganin namijin da a duniya ya iya sanya kaya kamar Ali nuhu ba. Babu ma kamar idan ya sanya kananan kaya, wani fim da ya sanya wani wando iya gwiwa har tsayar da wajen na yi dan kawai na sha kallo........."

" Ke Safiya ki na da hankali kuwa?"

" Haba Baban Faisal da hankalina mana, rawa kuma da iya girgiza ban taba gajiya da kallon Adam Zango ba, A jikin sa kuma kasumbar da ya ke bari ita ta fi daukar min hankali"

"Safiya dakata ya isa haka, wace irin magana ce wannan ta rashin hankali?"

" Baban Faisal yadda ka dire dole nima sai na dire, ba rashin hankali a ciki. Murmushin Maishunku kuma shi ke sanya ni nutsuwa a duk lokacin da ya yi"

" Idan kika sake magana sai na shake ki 'yar iskar banza kawai"

" Baban Faisal sahibi ko kashe ni za ka yi wallahi sai na kai karshe yadda yadda ka dire na ka. Abinda ya sa kuma ka ji ban rabuwa da wakar Alan Waka ko da a bandaki na ke kuma ko muna tare muryar sa na sumar da ni gaba daya, wani lokacin sai na ji kamar na yi mutuwar tsaye"

" Gaskiya Maman Faisal kin yi gamo da bakaken aljanu, wannan rashin hankali har ina, wadannan maganganu na ki kare ba zai ci ba, sai ka ce arniya"

" Kar ka hada ni da arniya, kafi kowa sanin ni musulma ce kamar kai"

" To lallai ki na bukatar a yi miki rukiyya ko kuma aje wajen malamai su rubuta miki Innahu Ala Rajaihi lakadir kafa bakwai bakwai na kwana bakwai"

" Lafiya ta ras"

" To kuwa ba karamar 'yar rainin wayau ba ce ke kuma dole manyan ki su san wannan maganar gaskiya ba zan lamunce ba wallahi, haba sai ka ce a garin gaba gaba, ki na matar aure ki na fadin wai ki na sha'awar mazan waje dan iskanci, daga yau ma ba za a sake kallon fim a gidan nan ba"

...Shin tsakanin Baban Faisal da Maman Faisal wane ne ya fi gaskiya?    

GAYYATA!!!

INTEGRITY ICONS INTERNATIONAL na farin cikin gayyatar daukakin jama'a zuwa laccar shekara-shekara karo na biyu ta SAM NDA-ISAIAH, mai taken "Adalci Da Kyautatuwar Shugabanci Shi Ke Kai Kasa Ga Gaci".

•Babban mai masaukin baki, Mai Girma Gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamakko, (Sarkin Yakin Sokoto).

•Karkashin jagorancin shugabancin Kakakin Majalisar Tarayya, Hon. Aminu Waziri Tambuwal, (Matawallen Sokoto).

•Uban Taron, Mai Alfarma, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III.

•Uwar Taron, Dr. Baraka Sani, tsohuwar kwamishiniyar noma ta jihar Kano.

•Bako mai jawabi, Dr. Tukur Muhammad Baba, na Jami'ar Usmanu Danfodio.

•Manyan Baki na Musamman, Alhaji Shehu Usman Shagari (Turakin Sokoto), tsohon shugaban kasa, Bishop Mathew Hassan Kukah.

>Rana: 1 ga Mayu, 2014
>Lokaci: 11:00 na rana
>Wuri: Sultan Maccido Institute for Qur'anic & General Studies, Sokoto.

Don Karin Bayani Tuntubi:
-Muhammad Saidu Etsu - 08069789087
-Bashir Ahmad - 08032493020
-Abdulmumin S. Balogun - 08069727798
-Sadauki Abubakar Gawu - 08057009909