Thursday, November 24, 2011

HALIN BABBAN YARO (ABBA MUHAMMAD SAVIOLA)

Abba Muhammad Saviola, abokina ne kuma aminina ne. Allah ya hore masa iya sarrafa zance gami da mai dashi yayi dadi, wannan tasa yake jan hankalin 'yan mata da zarar ya samu damar magana dasu, wannan dalili yasa yake yiwa kansa kirari/lakabi da cewa ABBAN MAI RABO, wato duk macen da ta same shi a matsayin mijinta to itace mai rabon.

Abba babban yaro ne, wadda kalmar babban yaro a yaren samari da 'yan mata na nufin wani dan saurari kyakkyawa da yake da fafa da ji da kansa, ta bangaren iya mu'amala da ta shafi zamantakewa a tsakanin samari da 'yan mata.

Wata rana Saviola ya tashi da sanyin safiya aljihunsa babu ko kobo gashi a matsayinsa na babban yaro shi kansa ya tabbatarwa kansa ba girmansa bane ya fito yana fadin bashi da kudi. Babban tunaninsa a lokacin yadda zai samu kudin da zaiyi transpot daga hostel zuwa school, domin kuwa wannan yafi damuwa dashi ba ciki ba.

Can yana cikin wannan hali sai yaji karar shigowar sakon text a wayarsa dake cikin aljihu, yana duba sakon sai yaga sako ne daga banki ana sanar dashi an aiko masa da kudi a account dinshi. Nan take yayi wani bushasshen murmushi tare da tashi tsaye, anan ya fara tunanin yadda za'ayi aje bankin don dauko kudin, domin kuwa babu kudin da za'aje bankin dasu. A karshe ya yanke shawarar tafiya a kafa.

Isar sa bankin ke da wuya sai ga wata tsaleliyar budurwa son kowa kin Bashir Ahmad, tunda kuwa ya rasa, ta fito daga bankin. Abba komai girman budurwa bata bashi tsoron yi mata magana, kuma da zarar ta bashi dama to kuwa ya gama da ita. Kamar yadda na fada a baya. Hakan tasa bai nuna tsoro ko shakka ba, ya tunkari wannan budurwa tare da yi mata tambaya "Gimbiya don Allah nan ne Zenith Bank?" tayi murmushi ta amsa masa "eh nan ne" saboda kuwa tasan ba wannan magana ce a zuciyarshi ba, kawai dai yayi tambayan nan don ya samu daman magana da ita.

Da bashi amsa bata tsaya karin bayani ba sai tayi gaba, shi kuwa Abba maimakon ya shiga bankin tunda ya samu amsar tambayarsa, sai shi ma kawai yabi bayanta, da ta fuskanci ya biyo bayanta sai ta tsaya tace "Malam ko akwai wata tambayan ne"

Na takaice muku bayani dai, tuni Abba ya sanar da ita abin dake zuciyarshi, har ma yana kokarin karban phone number ta, sai anan ya tuna saboda farin cikin turo masa kudi da akayi a lokacin da yake bukatansu, ya bar phone din nashi a hostel. Aka kuma nemi takardar da za'a rubuta number ba'a samu ba, kawai sai yarinyar ta bude jakarta (Hand Bag) ta dauko sabuwar N1000, ta rubuta masa number a gefe.

Karka manta da cewa Abba babban yaro ne, mai son nuna isa da fafa. Sannan kuma ka tuna tashin da yayi a ranan ba tare da ko sisi ba. Da karbar wannan sabuwar one thousand maimakon ya jefa ta a aljihu sai kawai ya yage gefen da aka rubuta number, sauran kuma ya rinka yayyagawa yana wasa da su lokacin da suke tafiya da yarinyar zai rakata wurin da tayi packing din motarta.

Lalle Abba ya cika babban yaro, wannan abu da Abban yayi ba karamin kara burge tsaleliyar budurwar yayi ba, gami da kara sace sauran zuciyarta gaba daya. Bayan ta shiga mota sukayi sallama da alkawarin zai kirata da zarar ya koma hostel.

To fa, a karshe da Saviola ya shiga banki don amsar kudin da aka turo masa sai jami'an bankin suka tabbatar masa da cewa ai an samu matsala ne ba account dinsa akayi niyyar turo kudin ba, saboda haka ma tuni wanda ya turo kudin ya debe abinsa. Da farko har Abba ya bata rai, sai kuma ya tuno irin barazanar da yayi wa kyakkyawar budurwan nan kawai sai yaji farin ciki ya mamaye shi, har ma ya samu damar komawa hostel cikin kwarin gwiwa.

Kaji kadan daga cikin halayen manyan yaro.

A karshe ina jinjina ga babban yaro, Abban mai rabo kuma madugu uban tafiyar shafin DAUSAYIN MASOYA a shafin sada zumunta na Facebook.

NB: It is not true life story, it is just for joke.


Bashir Ahmad
bashirahmad29@yahoo,com
08032493020, 08050600160

2 comments:

  1. *** YADDA ZAKA SA MATA KAUNAR KA TUN DAGA NESA **
    Ci gaba ....
    Bari kaji yadda abin yake ;A matakin farko kana bukatar ka san abinda yake burge 'yan mata da kuma abinda suke so tukunna. Ah' ah ha ! Kwantar da hankalin ka kaji mana ! Kaa ga! duk ba maganar kokarin ka a makaranta bane ,ko sai Mahaifin ka ya zama wani sannan a soka. Wohoho ! Dadina da kai gajen hakuri ! Nace maka ba sai kayi quru ka sayi Mashin ko Mota ba.To waima bari in tambaye ka. Gayu nawa kasha gani basu da ko sisi amma 'yan mata sun makale musu? Ah toh! Ka ganima ko! Ai na fada maka babu mummuna a Maza !!! Bari kaji sirrin ...
    Abinda zakayi tashin farko da ka hangeta shine ...
    Amma kafin ka tunkare ta ya kamata kasan wadannan sharuddan kamar haka
    -Mace bata son matsoraci ko wanda ya cika fariya ko mai girman kai
    -Mata basa son namiji mai yanga duk sai yabi ya gundure ta , ah ' eh mana ,kana yanga tana yanga me kenan akayi?
    - mace tafi son wanda baya jin kunyar fada mata duk wani motsin sonta dake zuciyar sa
    - kuma mata basa son hauragiya da harigido ,saboda haka ka natsu ka fuskance ta
    - mace tana son namijin da yasan darajar mata ,kaga kenan kar ka kuskura ka bata labarin cewa wai mata dayawa suna sonka amma ka wulakanta su saboda ita da zarar taji haka to kashin ka ya bushe koda ta amsa tana sonka,
    -Sannan kar kaje kai tsaye kace 'Ina sonki' ai sai ka firgitata, ana buqatar abinnan da turawa suke kira 'Introduction' kaga zaka tanaji yan bayanai masu ma'ana kenan wanda suka dace da ita domin ba sakin baki zakayi ka rinka zuba kamar kanyar da ba dadi ba
    - kuma ka nuna mata kasan darajar kanka ,don haka kar ka kuskura ka roqe ta ta soka sai ta raina maka wayau ko kuma ta ja maka aji sosai kafin idan kaci sa'a ta amince ,idan kuma ba'ayi sa'a ba to kuma ....abin dai ba'a cewa komai
    Alhamdulillahi kaga 'yar halak gata can kamar tasan muna nan . Maza tashi ka sameta kaga yadda zata amsa maka.... Ah! ah! me nake gani haka ? Haka zaka tafi da fuskar shanu kamar an maka mutuwa? Dawo! Dawo! Zo in koya maka yadda ake murmushi da irin salon tafiyar da ake yi idan za'a tun kari Budurwa , kwantar da hankalin ka ai ba wahala, yanzu duk zaka iya kafin ta kara so ... Ko baka kalle ni ba zaka iya insha Allahu !yadda ake murmushi shine .....

    ReplyDelete