Saturday, July 23, 2011

Kamfanin Google yayi wa shafin Facebook kishiya

Kamfanin Google ya gabatar da sabon shafin sada zumunta mai suna Google Plus (Google+) wannan shafi zai bawa masu amfani dashi damar karba da aika sakonni, zuwa ko ina a fadin duniya, wato shafin yayi kamanceceniya da shafukan Facebook da Twitter da kuma mySpace, duk da shugaban kamfanin na Google Larry Page ya musanta cewar shafin an kwaikwaiyi wani shafi ne na daban.

Bayan fitowar wannan shafi mutane da dama a fadin duniya sun tofa albarkacin bakinsu game da shafin, inda wasu ke ganin shafin ya fi dukkan shafukan da muke amfani dasu a halin yanzu a duniyar yanar gizo, inda wasu kuma ke ganin ina ai shafin Google yayi nisan da ba wani shafin sadarwa da zaizo ya kamo shi nan da kusa, inda shafin ke da masu amfani dashi sama da 720 miliyan.

A halin yanzu shafin na amfani akan kumfutoti da kuma manyan wayoyi irin su iPad, Apple da sauransu. Ga mai sha'awar yin rijista a wannan shafi zai ziyarci (plus.google.com) don ganin wainar da ake toyawa.

Shafin Google Plus cikin dan lokaci kalilan har tara masu amfani dashi sama da 20 miliyan, ciki har da mai kamfanin Facebook Mark Zuckberg. A nazarin da jaridar New York Daily ta kasar Amurka da gabatar tabbatar da cewa babu wani shafin sadarwa da ya samu irin wannan daukaka cikin dan kankanin lokaci, hakan tasa ake ganin lalle shafin zai zamewa shafin Facebook babban kalubale, duk da wasu masana harkar sadarwa sun nuna cewa wannan tagomashi da shafin ya samu ya same shine da taimakon shafin Facebook da Twitter, domin tun lokacin da kamfanin na Google ya sanar da aniyarsa ta yin Google+ din, masu amfani da shafukan suka rinka sanarwa abokanansu na sassan daban daban na duniya. Tabbas nima zan iya yadda da hakan domin nima na samu labarin wannan shafi ne daga wuri wani abokina dan kasar India.

To koma dai menene dai, fatanmu Allah ya bawa jama'armu basirar yin amfani da wannan shafuka da hanyar da baza sabawa addininmu na Musulunci ba, Allah ya bamu ikon yin amfani da wannan shafuka na sadarwa wajen yada addinin Musulunci.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

No comments:

Post a Comment