Mutuwa ita ce karshen duk wani abu da Allah (SWA) Ya halitta, mutum, aljan, dabbobi da sauran halittu na ciki ruwa, na doron kasa har ma dana sararin samaniya. Mutuwa na dauke mutum ba dare da saninsa ba, ma'ana ko ya shirya ko bai shirya ba. Kuma bata son kai, wato ta dauki talaka tabar mai kudi, don tarun dukiyarsa, ko tadauki mai kudi tabar talaka don jin tausayinsa. Bata barin yaro bare babba, bata barin mace bare namiji. Ita ke raba 'yayan da iyayensu, ba tare da tayin la'akari da halin da zasu shi ba. Ita ke raba ango da amarya duk kuwa da irin soyayyar dake tsakaninsu. Saboda kuwa bata sabawa umarnin mahaliccinta kuma mahaliccinmu Allah daya.
Wasu mutanen na ganin mutuwa bata da tausayi ko kuma itace babbar makiya a gare mu, musamman a wurin mutanen da ta dauke musu iyaye tabarsu cikin watangaririya, halin kuncin rayuwa, da rashin kulawa ta musamman.
Gaskiya ni a tunanina, mutuwa bata da laifi ko kadan, idan ka hada ta da LOKACI, domin kuwa shi ke tura mutum koyaushe kusa da mutuwa har ta dauki shi. Da zarar an haifi mutum duk wani dakika (second) daya da yayi, to lokaci yana kara kusan tashi da mutuwa ne. Mutuwa bata zuwa ta dauki wani har sai lokaci ya dauke shi ya kaita wurinta, wato sai wa'adinsa (lokacinsa) yayi. Ga shi lokacin kullum kara gudu yake, Shekara ta zama kamar wata, wata ya zama kamar sati, sati kuma kamar kwana. Kuma babu yadda zamuyi mu tsayar da gudun lokacin ko murage shi. Lalle karshen duniya ya zo.
Ta hanya daya zamu ci ribar wannan lokaci tun kafin ya kaimu ga mutuwarmu, wannan hanya itace mutattara rayuwarmu gaba daya mu koma kan Al-Kur'ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Muyi kokarin ganin kar dakika daya ta wuce ba tare da munyi amfani da ita ta hanya mai kyau ba. Koyaushe ya zamana ace bamu da lokacin daya fi na bautar Allah ko neman ilimin yadda za'a bauta masa. Idan mukayi haka to munci ribar lokaci.
A karshe karmu manta duk dakika daya da tawuce bazata sake dawowa ba har abada. Mu daina cinye lokacinmu, wurin kalle kalle marar amfani. Yi amfani da lokacin da kake cinyewa a shafukan Internet ta hanya mai amfani. Yawaita ziyartar shafukai fatawoyin addinin Musulunci dan karu da abinda baka sani ba. Maimakon karanta tarihin manya manyan kafirai makiya Allah, makiyanmu mu Musulmai binciko tarihin manya manyan malamai da suka bada muhimman gudunmawa a addinin Musulunci.
Allah yayi mana jagora a dukkan al'amuranmu na yau da kullum. Ya bamu ikon yin amfani da lokacin daya bamu ta hanyar bauta masa bata hanyar saba masa ba.
Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020
Allah ya saka da alkhairi
ReplyDelete