Saturday, August 13, 2011

Jama'a Ga Mujallar Muryar Arewa

Ina farin cikin gabatar muku da sabuwar mujallar MURYAR AREWA!

Muryar Arewa sabuwar mujalla ce da kamfanin Northern Media Link LTD ke tsarawa da wallafawa wata - wata (monthly) domin samun cikakken labarun da suke faruwa game da yankinmu na Arewa dama kasa baki daya. Babbar manufar Muryar Arewa shine gano matsalolin dake addabar yankin Arewa da kuma kokarin samo hanyoyin magance su, ta hanyar labarai da rahotonni gami da bayar damar fadar ra'ayi, hirarraki da fitattun shugabanni, talakawa, ma'aikata, yan siyasa, malamai, mata da matasa baki daya, duk don samowa Arewa mafita da ci gaba.

Muryar Arewa ta dauki alwashin ganin dukkan jinsunan da ke wannan yanki na Arewa sun hada kansu ba tare da nuna banbanci addini, darika, yare, kabila, sashe ko nuna wani bangaranci ba a tsakaninsu, Muryar Arewa na da burin ganin duk dan Arewa daga kowane bangare ya zauna da kowa lafiya a matsayin uwa daya uba daya.

Ana wallafa Muryar Arewa da harshen Hausa, harshen da kullum yake kara habaka da bunkasa yake a sassan duniya kamar wutar daji.

Kabir Assada shine daraktan gudanarwa kuma babban edita na wannan mujalla, sai kuma kwararrun abokanan aikinsa irinsu: M. K. Muhammad, Ibrahim Basit Ahmad, Sheriff Sidi. Ga kuma wakilai a kusa dukkan jihohin Arewa, sannan kuma ga hazikan marubuta na musamman kamar su Ado Ahmad Gidan Dabino, Yusuf Dingyadi, Binta Spikin, Bashir Ahmad, Nasir Abubakar da sauransu.

Muryar Arewa na da tsari na daban da zai zama abin burgewa da sha'awa ga kowa, inda komai aka tsarashi daki - daki yadda zai kayatar da fahimtar da masu karatu, misali zaka samu rukuni - rukuni a mujallar kamar haka: Labarai, Rahotonni, sharhi, tattaunawa, ra'ayi, taskar al'adu, hirar musamman, tsokaci, kimiya da fasaha, rigar yanci, tsumagiya, nasiha, duniyar finafinan Hausa, adabi, duniyar mata, da sauran shafuka masu ilmintarwa, fadakarwa gami nishadantarwa. Kai abin dai sai wanda ya gani. Sannan kuma akwai shafukan da aka tanada dan talla, don tallar hajar masu karatu.

Kash! Saura kadan na manta da shafin da yafi kowane kayatarwa wato shafin tsakiya, shafin da ya kunshi..... Bari dai na hakura haka, kar na cikaku da surutu, kuma masu iya magana na cewa gani ya kori ji, don haka kayi kokarin mallakar taka don kaima ka samu damar bada labari.

Wannan mujalla an samar da ita don mu Hausawa yan Arewa, saboda haka ya kamata mu bada gudunmawar da zamu iya bayarwa wajen ganin wannan jan aiki da mawallafanta suka dauko an samu gagarumar nasara.

A karshe sako guda daya ko biyu da nake son aikawa ga wannan mujalla shine, ya kamata a samar da filin da masu karatu zasu ke aikowa da gajerun ra'ayoyinsu ta wayar hannu, sannan kuma a samu wani shafi da za'a ke tattaunawa da kungiyoyi don jin manufofinsu da irin ayyukan da suka aiwatar. Hakan zai kara kusanta wannan Mujalla da jama'a na sassa daban - daban. Sannan idan wannan sako nawa ya samu isa cikin nasara, ina fatan wannan mujalla zata bawa kungiyarmu ta TSANGAYAR ALHERI damar bayyana manufofinta ga al'ummar duniya baki daya.

Kafin na ajiye abin rubutun nawa za'a iya samun Muryar Arewa a dukkan wani wurin sai da jaridu da mujallu a kudanci da arewancin kasar nan baki daya, akan kudi kalilan.

Ya Allah ga Mujallar Muryar Arewa don ci gaban Arewa da al'ummar Arewa da ma kasar Nigeria baki daya!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

1 comment:

  1. I am so proud of you.... though I can not write in hausa but I can read and understand very well. God willing I will be visiting your blog. Thank you.

    ReplyDelete