Wednesday, November 20, 2013

Taƙaddama bayan zaɓen gwamna a jihar Anambra

Shugaban Hukumar INEC
Bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Anambra tana shirin barin baya da ƙura tsakanin hukumar INEC da 'yan adawa waɗanda su ka ce ba su yarda da tsarin zaɓen ba. 

An dai share tsawon watanni kusan shida ana shiri ana kuma jibge jami'an tsaron da babu irinsu, to sai dai kuma an ƙare a cikin ruɗani a jihar Anambra inda yanzu haka zaɓen gwamnan jihar ke shirin barin baya da ƙura tun bai nisa ba. 

Duk da cewar dai jam'iyyar APGA da ke mulki a jihar dai ce ke kan gaba da ƙuri'u sama da 174,000, sakamakon zaɓen dai ya gaza kammala a ɓangren hukumar zaɓen da ta ce har yanzu da sauran gyara kuma ke shirin saka wata ranar kammala sassan da ta ke ganin da sauran aiki a cikinsu. 

Ra'ayi dai ya bambanta tsakanin hukumar da ta ce tana shirin sake zaɓen ne a rumfunan da ke fuskantar rikici, da kuma manyan jam'iyyu uku masu adawa da ke cewar sake ɗaukacin zaɓen na zaman mafita na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci a cikinsa.

Zaɓen na Anambra da ake yiwa kallon zakaran gwajin dafi ga ƙoƙarin hukumar zaɓen na shirya zaɓuka masu karɓuwa a shekara ta 2015 dai tuni ya fara jawo ɗar-ɗar a tsakanin 'yan siyasa dama masu kallon baƙin hadari na siyasar rikici a gaba. Ga Tarrayar Najeriyar da ta fuskanci mummunan rikicin da yai barazanar ganin bayanta a shekara ta 2011, sannan kuma ake yiwa kallon dan ba na tashe tashen hankulan da suka mamaye ɗaukacin ƙasar ya zuwa yanzu. 

Tuni dai aka fara kiran karatu na gazawa ga jami'an hukumar zaɓen da suka kai ga kisa na maƙudai na kuɗi ba tare da kai wa ga kwantar da hankula cikin jiha ɗaya tilo ba, abun kuma da a faɗar dr Umar Ardo da ke nazari bisa harkoki na siyasa ke tabbatar da irin halayya ta mutanen da ke jagorantar ayyukan hukumar yanzu haka.

Adalaci a cikin alƙalanci ko kuma son zuciya da cika ɓuri na siyasa dai daga dukkan alamu Tarrayar Najeriya na tsakanin tabbatar da zaɓe mai adalci ko kuma fuskantar ruɗanin da ke iya mummunar illa ga ɗaukacin fagen siaysar ƙasar. Abun kuma da ya kai ga mahukuntan ƙasar a matakai daban-daban jerin alkawuran darma sa'a da nufin bai wa maras'da kunya yayin zaɓukan da tuni suka kama hanyar raba kan yan ƙasar tsakanin addini da ƙabila. To sai dai kuma a faɗar Buba Galadima da ke zaman jigon jam'iyyar APC matsalar ta Anambra na zaman buɗe ido a garesu na sabon shiri da nufin tunkarar sabon ƙalubalen da ƙasar ta Najeriya ke shirin fuskanta a siyasance. 

To sai dai kuma idan ta yi ɗaci ta kuma lalace ga masu adawa a Anambra ga 'yar uwarsu ta APGA da ta kama hanyar sake ɗare mulki a jihar wai duk wani ƙorafi na 'yan adawa bai wuci bakin masu shirin rasa damar mulki ba a faɗar Sani Abdullahi Shinkafi da ke zaman sakataren jam'iyyar na ƙasa .Abun jira a gani dai na zaman mafitar rikicin da ma matakai na gaba a ɓangaren hukumar zaɓen da ke ƙara fuskantar fushi da ba daɗi na 'yan ƙasar a kullu yaumin.

Monday, November 11, 2013

50 ADVICES FROM QUR'AN

Holy Quran
1. Do not mix the truth with falsehood (2:42)

2. Order righteousness to people only after practicing it yourself (2:44)

3. Do not commit abuse on the earth (2:60)

4. Do not prevent people from mosques (2:114)

5. Do not follow anyone blindly (2:170)

6. Do not break the promise (2:177)

7. Do not engage in bribery (2:188)

8. Fight only with those who fight you (2:190)

9. Keep the etiquette of war (2:191)

10. Protect orphans (2:220)

11. Do not have sexual intercourse during menstrual period (2:222)

12. Breast feed your children for two complete years (2:233)

13. Choose rulers by their merit (2:247)

14. No compulsion in religion (2:256)

15. Do not invalidate charity with reminders (2:264)

16. Help those in need by finding them (2:273)

17. Don’t consume interest (2:275)

18. Grant more time to repay if the debtor is in hard time (2:280)

19. Write down the debt (2:282)

20.Keep the trust (2:283)

21.Do not spy and backbite (2:283)

22.Believe in all prophets (2:285)

23. Do not burden a person beyond his scope (2:286)

24. Do not become divided (3:103)

25. Restrain Anger (3:134)

26. Do not be rude in speech (3:159)

27. Think deeply about the wonders and creation of this universe (3:191)

28. Men and Women have equal rewards for their deeds (3:195)

29. Wealth of the dead should be distributed among his family members (4:7)

30. Women also have the right for inheritance (4:7)

31. Do not devour the property of orphans (4:10)

32. Do not marry those in your blood relation (4:23)

33. Do not consume one another’s wealth unjustly (4:29)

34. Family should be lead by men (4:34)

35. Be good to others (4:36)

36. Do not be miserly (4:37)

37. Do not keep envy (4:54)

38. Judge with justice between people (4:58)

39. Do not kill each other (4:92)

40. Do not be an advocate for deceitful (4:105)

41. Standout firmly for justice (4:135)

42. Cooperate in righteousness (5:2)

43. Do not cooperate in sin and aggression (5:2)

44. Dead animals, blood, the flesh of swine are prohibited (5:3)

45. Be just (5:8)

46. Punish for crimes in an exemplary way (5:38)

47. Strive against sinful and unlawful (5:63)

48. Avoid intoxicants and alcohol (5:90)

49. Do not gamble (5:90)

50. Do not insult others’ deities (6:108)

Tuesday, November 5, 2013

YA AKE ZAMA GWANI A HARKAR KWAMFUTA?


Dalibai Na Karantar Kwamfuta
Babu yadda za ayi dalibi ya kware a harkar kwamfuta matukar bai mayar da hankalinsa wurin abin da malamansa suke koya masa ba.

Wani lokaci ba matsalar dalibai ba ce, matsalar abin da zasu yi practice da shi shi ne matsala. Wadansu kuma a lokacin da suke koyan karatun hankalinsu baya wurin malamin.

Idan mutum yana son ya kware kuma ya zama gwani a duk harkar da ya sa a gabansa to ya sani sai ya baiwa wannan abun mahimmanci.

Misali zaka samu dalibai kowa na kokarin ya mallaki kwamfuta amma kuma da zarar ya samu ba shi da abin da zai yi da ita face kallon fina-finai ko kuma yin game ko kuma sauraron wakoki.

Ya ake zama gwani a harkar Kwamfuta? Hanya daya ce, ka daukarwa kanka cewar ina son in zama kwararre a wannan fanni ta hanyar yin kokarin ganin kana aikata ayyukan da aka umarce da su a makaranta.

Wani abu da yake kara goge dalibai shi ne lokacin da dalibi ya dauki ragamar kara fadada bincike da maimaita ayyuka da malamai ba su saka shi ba.

Misali ba yadda za ayi a ce ka san me zaka yi, kawai ka dauko kwamfuta ka bude MS Word, ko Excel, ko Access, ko CorelDraw da makamantansu baka san mene ne dalilin da ya sa na bude su ba.

Misali idan kana koyan aikin Graphics da CorelDraw (Duk da cewar ba a yi shi don Graphics ba) to idan kana son ka zama gwani sai ya kasance kana daukan wadansu takardu da aka yi Graphics din a ciki kana kwatantawa.

Yin haka lallai zai taimaka maka wajen gano mene ne na iya mene ne ban iya ba, a wannan lokaci zaka ga ka kara kwarewa a wani bangare da da iya shi kayi, za kuma ka ga ka fahinci wani abu da da baka ma gane me ake nufi da shi.
 -          Duniyar Computer

Monday, November 4, 2013

JARIDAR RARIYA A FUSKAR FASAHAR ZAMANI


Tambarin Jaridar Rariya

RARIYA jarida ce da take fitowa a duk ranar Juma'a, sai dai bayan haka akwai dama ga masu karatun jaridar da za su ci gaba da kasance wa da ita a kowane lokaci, kamar yadda manyan jaridun duniya ke tafiyar da harkokinsu a shafukan sadarwa na intanet, sakamakon ci gaban zamani, haka RARIYA ma ba a barta a baya ba.

•FACEBOOK: Rariya na da shafi a dandalin sada zumunta na Facebook, wanda cikin kankanin lokacin shafin ya zama kan gaba a tsakanin shafukan jaridun Hausa na Facebook. A halin yanzu sama da mutane dubu saba’in (70,000) ne ke samun labarai kai tsaye ta shafin RARIYA na Facebook. Shiga NAN don kasance da RARIYA a shafin Facebook.

•TWITTER: Ba kowace jarida ke da gurbi a shafin sadarwa na Twitter ba, amma RARIYA tun-tun-tuni ta samu gurbi a shafin, inda jama'ar da suka biye da ita ke samun labarai a koda yaushe ta wannan kafa. Za ku iya biyo RARIYA a Twitter akan @rariyajarida

•YANAR GIZO: A baya RARIYA ta fara kawo wa masu karatu labarai ta shafinta na (www.rariyaonline.com) wanda aka dakatar da shi, sakamakon wani muhimmin aiki da ake yi akan shafin don kara kawata shi, yayi daidai da salo na zamani, wanda nan gaba kadan shafin zai ci gaba da aiki.

•WAYAR SALULA: Sai wani sabon tsari da RARIYA ta fito da shi, wanda shi ne irinsa na farko a tsakanin jaridun Hausawa, tsarin ana kiran shi “RARIYA A WAYAR SALULA” tsarin na bawa masu amfani da shi damar samun labarun RARIYA a kullum a wayoyinsu na salula koda kuwa babu fasahar sadarwa a cikin wayoyin. Za ku iya shiga tsarin ta hanyar aika sakon RARIYA a wurin aika sakon tes a wayoyinku zuwa 700. A halin yanzu tsarin na aiki ne akan layin MTN kadai. Sannan za a caji naira 50 kacal har tsawon kwanaki bawai.

Ku ci gaba da kasancewa da RARIYA a kowane lokaci domin samun ingantattun labarai.