Wednesday, July 13, 2011

Takaitaccen Tarihin Dr. Abubakar Imam

An haifi Alhaji Dr. Abubakar
Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.)
N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin
garin kagara sa’an nan tana cikin
lardin Kwantagora, yanzu kuwa
Jihar Neja. Ya Yi makaranta a
Katsina Training College kuma ya
kama aikin malanta a Makarantar
Midil to Katsina a shekarar 1932.

Yana da shekara 22 ya rubuta
`Ruwan Bagaja’. Ganin kwazonsa
wajen Raga labari mai ma’ana ya
sa Dr. R.M. East shugaban
Offishin Talifi na Zariya ya roki a
ba da shi aro daga Katsina ya yi
aikin rubuce rubuce a Zariya.
Bayan ya koma Katsina aka bi shi
da rokon ya kara rubuta wasu,
littattafan. A can ya rubuta
‘Karamin Sani kukumi’ cikin 1937.

A cikin shekara 1938 sai
Gwamnan Kaduna ya roka a
dawo da Imam Zariya a koya
mashi aikin edita ya zama editan
jaridar farko to Arewa. Shi ne ma
ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi
Kwabo’ aka fara bugawa a
watan Janairu na shekara 1939.
Ya yi shekara 12 yana wannan
aiki na edita har ma ya rubuta
wani littafi a lokacin `Yakin
Duniya Na Biyu’ watau `Yakin
Hitila’ da ya ba suna `Tafiya
Mabudin Ilmi’. Wannan littafi ya
ba da Iabarin tafiyarsa tare da
wasu editoci na jaridun Africa to
Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa
a shekara 1943.

Wani mashahurin littafi kuma da
ya rubuta shi ne ‘Tarihin Annabi
da na Halifofi’ wanda aka fara
buga shi a shekara 1957 lokacin
nan yang shugaban Hukumar
Daukar Ma’aikata to Nijeriya to
Arewa.
Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka
fara nadawa Kwamishinan Jin
Kararakin Jama’a a shekara 1974
a Jihar Kaduna, lokacin ana
kiranta Arewa to Tsakiya. Ya rasu
yana da shekara 70 a duniya
ranar Juma’a 19 ga watan Yuni,
1981.

Alhaji Abubakar Imam ya rike
cewa wannan aiki da ya yi, na
talifin ‘Magana Jari e’ ya yi masa
amfani ainun. Ya kan ce wannan
aiki shi ne ya ba shi damar zama
tare da mashahurin Baturen nan
na talifin Hausa, Dr. R.M. East,
O.B.E. Ya ce daga gare shi ne ya
koyi duk dan abin da ya koya na
game da talifi.

Abin mamaki, shi kuma wannan
Bature, Dr. East O.B.E., a wajen
`Mukaddamar’ da ya yi da
Turanci tun farkon buga ‘Magana
Jarice, ga. abin da ya ce : ‘Muna
godiya ga En’e ta Katsina, saboda
da taimakonsu, da hangen nesa da
suka yi, har suka yarda,suka bamu Malam Abubakar Imam.
Suka yarda, ya bar aikinsa, na
koyar da Turanci a Midil to
Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi
wata shida domin ya taimake
mu, mu sami wadannan
littattafai a cikin harshensa.

`Iyakar abin da mu ma`aikatan
wannan ofis muka yi, na game
da talifin wadannan littattafai,
shi ne aiki irin na ofis, na shirya
al’amuran, yadda suka kai har
aka buga su. Ban da wannan sai
su kuma taimakonsa da muka yi
na tattara masa littattafai iri iri,
don ko zai kwaikwayi wani
samfur. Sai fa kuma wajen
shiryawa bayan da ya rubuta.
‘Kai, in dai har muna da wani
abin da za mu yi kirari mun yi,
game da talifin wadannan
littattafai, to, babban abin
kirarimmu kawai, shi ne yadda
muka yi har muka binciko
wannan malamin talifi’.

7 comments:

  1. Na Gode Malam Bashir Ahmad!!! Allah Ya saka maka da Alkhairi mai yawa. Mu Hausawa babu abin da za mu yiwa Malam Abubakar Imam sai addu'a Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, amin. Domin ya fito da harshen Hausa. Allah ya gafarta masa, ameen.

    ReplyDelete
  2. Salam. malam don Allah ina son mu tattauna da kai kan wannna batu. Ko za ka bani lambar waya ko email? Nagode.

    ReplyDelete
  3. Ok zaka iya samu na kan wannan layin 08032493020 ko bashahmad29@yahoo.com

    ReplyDelete
  4. An gaisheka da wannan aiki. Keep it up.

    ReplyDelete