Saturday, August 17, 2013

Takarar Buhari Da Lissafin Siyasar 2015

Jaridar Daily Trust ta ranar 12 ga watan nan na Agusta ta ruwaito labarin tabbacin da Janar Muhammadu Buhari ya bayar game da sha’anin takararsa. Tsohon shugaban kasar ya ce lalle zai sake tsayawa takara a shekarar 2015. Idan har da gaske Janar ya yi wannan magana, ke nan wannan takarar tasa za ta zama ita ce ta hudu a kirga.

Wannan tabbaci da Buhari ya bayar a jaridar shi ne zai iya kawo karshen shakkun da manazarta suke tayarwa a kan batun takarar tasa, kazalika za a iya cewa, tabbacin zai alkibalantar da siyasar zaben shugaban kasa a 2015 na kasar baki daya zuwa ga fuskar da za ta zama mai sauki da dadi a nazari da bi-biya. Domin ko ba komai dai, sake fitowar Buhari ga takarar shugabancin kasar nan zai sanya jam’iyya mai ci wato PDP ta shiga taitayinta. Saboda adawar da takararsa ke bayarwa, bisa ga al’ada, adawa ce mai gajiyar da duk jam’iyyar da ke ci. Hakan ne kuma, domin tun ba a je ko’ina ba, tuni cikin wasu ’ya’yan PDP ya duri ruwa har ma sun fara daidaita sahunsu, musamman kan rikice-rikicen cikin gida da suka kunno kai cikin jam’iyyar, sun fara yayyafa musu ruwa da kansu. To sai dai kuma yayin da PDP ke kokarin gyatta gininta da ke neman rushewa saboda ganin yadda ginin jam’iyyar APC ke ginuwa cikin hanzari, musamman saboda tabbacin sake takarar nan ta Buhari, akwai wasu tambayoyi da ke tilasta kansu a kan ita dai wannan takara tasa.

Wannan kuma domin kasancewar takarar a kashin kanta tamkar wani tubalin gini ne mai karfi a harsashin ginin da APC ke yi.

Tambaya ta farko ita ce: shin Buhari zai iya cin zabe har ma ya zama shugaban kasa idan aka yi la’akari da nukurar da dattawan kasar nan suke nuna masa, musamman na Arewa wadanda a baya can suka yi ta nuku-nuku a kan sauran takarar da ya yi kafin wannan?

Tambaya ta biyu ita ce: shin wannan hadaka da aka yi da Yarbawa (CPC da ACN), za ta kai Buhari ga tudun mun-tsira game da sha’anin takararsa a 2015 ko kuwa abin nan da wasu Hausawa ke kira da ‘munafuncin’ Yarbawa zai taka rawa a zaben shekarar har Buhari ya gaza kai labari?

Tambaya ta uku ita ce: wane tabbaci Buhari yake da shi game da gaskiyar niyyar jagororin ANPP irin su Ibrahim Shekarau (wanda ake gani bai yi zaman dadi da Buharin a jam’iyyar ANPP ba) da Ali Modu Sharif (wanda ake zargi dan leken asirin jam’iyyar PDP ne a cikin ANPP) da Attahiru Dalhatu Bafarawa (wanda ake gani jin isarsa ya sa yana kallon kansa kamar yana gaba da Buharin a komai) tare da Ahmad Sani Yarima (wanda ake gani iskar son dauwama a mulki za ta iya kada shi zuwa ga wata jam’iyyar a kowane lokaci)? Wane shiri Buhari ya yi idan aka wayi gari wadannan zakakuran ’yan siyasa suka sake juya masa baya kuma suka yake shi daga cikin gida?

Tambaya ta hudu ita ce: Shin da gaske dabi’ar da ake kallon Inyamuri da ita ta sayar da komai nasa don ya samu kudi, ba za ta yi tasiri a tunanin Gwamna Rochas Okorocha ba yayin da wasu ’yan adawan ciki ko na waje suka tunkare shi da rashawa? Idan har hakan ya faru, to wane shiri Buhari ya yi na takara ba tare da la’akari da yankin Kudu maso- gabas ba? Yayin da ire-iren wadannan tambayoyi ke tilasta kansu a sha’anin takarar Buhari a karo na hudu hakazalika su kansu su Buharin, a yadda wannan marubuci yake kyautata zato, ba za su rasa tanadin abin da zukatansu ke raya musu cewa gamsassun amsoshi ba ne ga waxannan tambayoyi. Sai dai kuma abin la’akari a cikin zubin wannan lissafi na siyasa, shi ne sunan Janar TY Danjuma da yake ta karakaina a farfajiyar siyasar Arewa a ’yan kwanakin nan. Wannan karakaina ba zai zama kawai a kan hatsari ba, da walakin…Idan har masoya Buhari ba su yi dace ba, dattawan Arewa za su iya maida karfinsu ga TY Danjuma da bukatar ya fito takara kamar yadda tuni wasu manazarta suka yi ittifaki a nazarin hasashe. Wannan kuma zai yiwu ne idan har Shugaba Jonathan ya tilasta wa ’yan PDP sake tsayawa takara shi ma. Saboda dattawan za su fi samun natsuwa da mutum irin TY Danjuma ya mulke su maimakon a ce Buhari ne ya mulke su. Dalilan hakan kuma ba a bayan labule suke ba, ga su nan a bayyane: Na farko, game da PDP, idan har ya kasance kamar yadda ake zato, jam’iyyar ta ci nasarar magance dukkan kananan matsalolinta na cikin gida a taron kasa da za ta yi nan gaba, to kwadayi zai iya sa ta sanya Jonathan a gaba a takarar 2015. Wannan abu da za ta yi, hasashe na nuna cewa shi ne zai iya kawo karshen mulkinta a Nijeriya. Saboda takarar Jonathan, takara ce da ba za ta yi wa ilahirin dattawan kasar nan dadi a rai ba. Domin za a tauye buqatunsu da dama. Yayin da kuwa suka tabbatar za a iya tauye bukatunsu, to fa sai inda karfinsu ya kare.

Don haka takarar Jonathan a cikin PDP shi ne babban matsalar jam’iyyar. Na biyu, idan kuma har dattawan nan suka juya wa PDP baya saboda takarar Jonathan, to za su iya neman madogara a jam’iyyar APC saboda ita ce tumbatsarta ta tsallaka har ga sauran yankunan kasar kamar PDP, don haka ita ce za ta iya cin zabe.
A sannan ne kuma takarar Buhari za ta ci karo da mushkila mai girman taswira. Saboda dattawan ba za su so su gatanta wanda suke wa zaton zai daddaure su yayin da ya zama shugaban kasa ba. Ko kuma ba za su so su mara wa wanda suke jin yana nuna musu cewa ya fi su tsarki baya ba. A wannan lokaci ne kuma wadancan tambayoyi na baya za su zama ababen la’akari da idon basira a kan tilas. Domin dattawan za su iya sanya wanda ake gani shi ne jagoran Yarbawa a wannan hadaka da Buhari, wato Bola Ahmad Tinubu a gaba da magiya da rokon arzikin kada ya bari Buhari ya ci zaben furamare a APC.

Idan har hakan ta auku, marubucin nan ba ya ganin zuciyar dan siyasa irin Tinubu za ta iya bijire wa magiyar wadannan dattawa wadanda zai yi wuya a farkon tasowarsa (Tinubu) bai yi burin a sanshi tare da su ba. Kazalika a cikin jagororin nan na ANPP da aka ambata a baya, babu wanda shi ma ba zai karkata ga bangaren wancan magiya da rokon arziki na manyan dattawan da ko dai wasun su sun taba zama iyayen gidansu a da, ko kuma suna kallon takarar Buhari da irin wancan ido da dattawan suke kallo ba su ma. Haka lissafin yake ga hatta Gwamna Rochas Okorocha, wanda dama wasu majibintar Buhari na baya, sun taba zarginsa da cefanar da takararsa ta shugaban kasa tare da kokarin tayar da rigima a zaben furamare na jam’iyyar ANPP da aka yi da tsakar dare a dandalin Eagle Square a shekarar 2003. Hanyar kuma da za ta yi saurin karbuwa ga irin wannan juya baya ga Buhari a wannan yanayi, ita ce kutso da Janar TY Danjuma cikin farfajiyar siyasa.

Na farko saboda TY Danjuma yana da darajar zama tsohon janar na soja kamar Buhari. Na biyu saboda shi ma ana ganin yana da kamanta gaskiya kamar Buhari. Na uku saboda shi kirista ne, ana ganin zai fi karbuwa ga kiristocin kasar nan fiye da Buhari wanda har yanzu wasu kiristocin ke yi wa kallon mai tsaurin ra’ayin addini saboda kamfen da aka yi musu. Na hudu, wanda shi ne uwa-uba, saboda dattawan da mabiyansu a siyasa, kai har ma da masu juya al’amuran siyasar duniya da ke ketare, za su fi natsuwa da TY Danjuma wanda suke gani a matsayin nasu na kashin kansu ba bare ba kamar Buhari, wanda ba sa iya hasashen abin da zai yi idan ya zama shugaban kasa.

Kila mai bin wannan marubuci da karatu ya ce, to wai duk me ake nufi da wannan tsattsauran lissafi haka da bai da wata bushara ga talakan da ke son Buhari a karshensa? Wannan shi ne abin da ya kai zancen ga ra’ayin alkiblar nan. A ra’ayin alkiblata, a yanzu ne Janar Muhammadu Buhari yake da damar zama shugaban kasar Nijeriya fiye da kowane lokaci. Amma fa sai idan har shi da kansa ya gane dabarun da zai bi don wannan haka da ya jima yana hakilon yi ta cimma ruwa, in ba haka ba kuwa, takararsa ba za ta iya zama irin ta Abraham Lincoln na Amurka ba.

A bini bashin wadannan dabaru a rubutu mai zuwa idan har Mahaliccinmu (SWA) ya kaimu da rai da lafiya.

Daga jaridar Leadership Hausa

Thursday, August 15, 2013

Labarin Wani Mahaukaci Mai Hikima

Wasu mutane ne ke cikin tafiya a cikin motarsu a tsakiyar daji sai suka ji tayar motar ta gaba tana rawa. Sai suka tsaya suka duba sai suka ga ashe notocin dake daure da taya daya ta gaba notoci uku sun kwance sun fadi saura noti daya kawai ke rike da tayar shi yasa take ta rawa zata fita.

Suna ta shawarwarin abin yi don tsakiyar daji ne ba gari a kusa kuma ababen hawa basa wucewa sannan waya ba zata yi rana a wajen ba don su baki ne masu wucewa. Can sai ga wani mahaukaci zai wuce sai ya kalle su ya kalli tayar data kwance sai ya kwashe da dariya har yana tuntsurawa kasa yana cewa "aradu in nine sai in dauko daya can daya can kuma daya can sai in har hada su in daure shegiya dasu, habawa sai tafiya aradu hahaha... wani aiki sai ni, su kuwa ba za su iya ba" *sai ya kara tuntsurewa da dariya*

Duk basu kula da zancen mahaukacin nan ba sai mutum daya ne daga cikin su ya mayar da hankali yake ta sauraren bankauran mahaukacin nan, sai ya natsu da kyau yaga akwai hikima cikin zancen mahaukacin nan sai shima ya fashe da dariya.

Da sauran abokan suka waigo suga me yasa shi dariya sai yace:
Ai kawai zancen mahaukacin nan zamu bi ma'ana mu kwankwanto notuna daya-daya a sauran tayoyin uku sai mu daurawa na hudun data kwance kawai muyi tafiyarmu lafiya lau ba matsala don rashin noti daya-daya ba zai hana komai ba.

Sai sauran duk suka ce gaskiyarsa amma ya akayi ya tuno wannan dabarar haka su basu tuno ba? Sai ya nuna mahaukacin nan yace kun ga mai hankalin da ya fahimtar damu abin da bamu sani ba.

Duk sai dukkansu kowa ya cika da mamaki.

•Wannan labarin ya nuna cewa Allah ne yake sanya wa mutum ilhama da hikima ba wai hankalinsa ko dabararsa ba, saboda su da suke da hankalin Allah bai nufe su da yin tunanin da mahaukacin yayi ba.

Tsakure Daga Littafin: "KOGIN BARKWANCI" - Bashir Yahuza Malumfashi

Ya ku 'yan uwa da abokan arziki da masoya, ina neman addu'arku, a yayin da nake gabatar maku da kad'an daga gabatarwar sabon littafin da a yanzu haka nake aiki a kansa. Sunan littafin dai: "Kogin Barkwanci!" Yana d'auke da dad'ad'an labaran barkwanci har guda 200, wad'anda suka shafi tsokana tsakanin Kanawa da Zage-Zagi, Katsinawa da Nufawa da Gobirawa da Had'ejawa, tsakanin Bare-Bari da Fulani da sauransu. Kafin in k'ark'are aikinsa, ga tsakure:

Alk’alami Ya Fi Takobi, shi ne taken shirin da marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino yake gabatarwa a Gidan Rediyon Freedom da ke Kano. Kamar yadda ya saba, a sabon shirinsa na wannan makon, ya bijiro da wata gagarumar sanarwa, wacce ke wa masu sauraron shirin nasa albishir mai kima, musamman dangane da ingantaccen shirin da Gidauniyar Bukar Usman ke yi, na gabatar da gasar nishad’antarwa mai taken ‘Kogin Barkwanci.’

“Jama’a masu sauraro, yau kuma d’auke muke da wata tsaraba mai muhimmanci, sabuwa ful daga Gidauniyar Bukar Usman.” Inji Ado, yana magana cikin zazzak’ar murya, tare da jan hankali.

“Ina al’ummar Fulani, abokan wargin Bare-bari? Wannan shiri yana tare da ku. Ku ma Bare-barin, kada ku bari a ba ku labari, shirin naku ne; balle ma d’an uwanku ne ya yanke wa shirin cibi, kasancewarsa d’an k’abilar Bura daga Biu, Jihar Adamawa.” Daidai nan sai muryarsa ta kau, aka zizaro wak’ar Dokta Bukar, wacce ‘Dank’wairon Biu ya rera masa, mai taken: ‘Jarumi.’

Ado ya ci gaba da sanarwarsa: “Ina Katsinawa? Ina Gobirawa? Ina Nufawa? Ku karkad’e kunnuwanku, ga bikin zuwa ya samu; domin kuwa shirin ‘Kogin Barkwanci’ naku ne, tare da ku za a fara kuma tare da ku za a k’ark’are shi.”

Gidan Dabino bai gushe ba, sai da ya cinye tsawon minti talatin na filinsa, yana gabatar da wannan sabon shiri da Gidauniyar Bukar Usman za ta gabatar.

A tak’aice dai Ado ya sanar da al’umma yadda Gidauniyar ta d’auki nauyin farfad’o da nishad’in gargajiya, yadda zai dace da zamani. Gasa ce aka tanada tsakanin k’abilun Najeriya, musamman Katsinawa da Gobirawa da Nufawa da Bare-Bari da Fulani da Kanawa da Zage-zagi.

A gasar, an tanadi alk’alai, wad’anda za su rik’a raba wa masu barkwancin maki, a duk lokacin da suka gabatar da labarinsu. Daga k’arshe za a fitar da wad’anda suka yi nasara, wato wanda ya d’auki na d’aya da na biyu da kuma na uku.

Kamar yadda Ado ya gabatar, alk’alan sun had’a da shahararren malamin nan na Adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Abdallah Uba Adamu da kuma shahararriyar ’yar wasan fim d’in Hausa, Saratu Gid’ad’o (Daso) da Kabir Assada Sakkwato da Mahmoon Baba Ahmad.

Kamar yadda aka tsara, za a gudanar da gasar ne tsawon wata d’aya, a zauren taro na Dandalin Gamji, Kaduna. A kullum da maraice, bayan mutum ya sayi tikiti, zai shiga zauren ya zauna kan ingantattar kujera, sannan ya kalli shirin, tare da kallon wasannin gargajiya na wak’e-wak’e da raye-raye.

A wannan littafi na ‘Kogin Barkwanci,’ za ku karanta yadda wannan gagarumar gasa ta kaya, za ku ga wanda zai yi nasara cikin taurarin da suka fafata. Taurarin kuwa sun kasance gwanayen barkwanci na wannan zamani. Kafin ku ga irin aikinsu, ga jerin sunayensu:

1 - Tantak’washi: Bakatsine, wanda ya k’ware wajen iya barkwanci. Ya haddace labarun barkwanci masu yawa, musamman wad’anda suka shafi Gobirawa da Nufawa da Had’ejawa. Ya samu damar shiga gasar nan ne, bayan ya doke ’yan takara guda biyu a jiharsu ta Katsina. ’Yan takarar da ya doke kuwa, sun fito ne daga shiyyoyin Katsina da Daura. A matsayinsa na mai wakiltar shiyyar da ya fito, wato shiyyar Funtuwa, shi ya yi nasarar zama tauraron Jihar Katsina, wanda kuma zai wakilce ta a babbar gasar barkwanci da Gidauniyar Bukar Usman ta d’auki nauyin gabatarwa.

2 - Tantabara: Ta kasance Banufa, wacce ta gwanance wajen iya tsokanar Katsinawa. Da ita za a fafata a wannan gagarumar gasa ta Kogin Barkwanci, wanda Gidauniyar Bukar usman ta d’auki nauyin gabatarwa. Tantabara, ita ce wakiliyar Jihar Neja, a wannan gagarumar gasa.

3 - Gizago: Gizago ba ka da sabo, masassak’i ka tsare annunka. Wannan bawan Allah Babarbare ne, wanda ya fito daga Maiduguri, amma Allah Ya hore masa iya wasan kwaikwayo. Kafin ya samu nasarar shiga wannan gasa, sai da aka tabbatar ya gwanance wajen sanin sirrin Fulani. Da yake yana auren Bazazzagiya, shi ya sanya wani lokaci yake alak’anta kansa da Zariya. Dalili ke nan ma ya sanya ya tattara labarun barkwanci na tsokanar Kanawa. A wannan gasa ma, ya yi alk’awarin jefo su kad’an-kad’an. Shi ne wakilin Jihar Borno a wannan gasa.

4 - Dangarama: Mace ce ita mai iya raha. Ta kasance Bagobira, wacce ta fito daga Sabon Birni a Jihar Sakkwato. A jiharsu, ta doke ’yan wasan barkwanci da dama, kafin ta tsallake shingen shiga wannan gasa ta ‘Kogin Barkwanci.’

5 - Jauro: Shi ne mutum na biyar da ya samu shiga cikin wannan gasa. Bafulatani ne shi mai kaifin wayau da iya sarrafa magana. A tsawon rayuwarsa, ya-shiga-ya-fita, ya tattara labaran tsokana da barkwanci masu yawa, waxanda suka shafi Bare-Bari. Da yake kuma shi Bakano ne, ya had’a da lak’antar labarun tsokanar Zage-Zagi. Babu shakka za a yi gumu da shi a wannan gasa ta ‘Kogin Barkwanci.’ Ya fafata da abokan karawarsa a matakin jiha, inda ya zama zakara, ya d’auki kambin kare Jihar Kano a wannan gagarumar gasa.

Masu iya magana sun ce, ba a san maci tuwo ba sai miya ta k’are. Mu shiga zauren mu ga yadda za ta kaya, a wannan gagarumar gasa ta ‘Kogin Barkwanci.’

Wednesday, August 14, 2013

APC governors oppose autonomy for Nigeria’s local governments

The governors of the All Progressive Congress, APC, at the end of their meeting on Wednesday rejected autonomy for Nigerian local governments.

The governors, in a communiqué released after their meeting in Lafia, said the National Assembly was right by not including local government autonomy in the ongoing constitutional amendment.

The eight point communiqué released after their five hour meeting in Lafia was read by Governor Kayode Fayemi of Ekiti State.

The governors said autonomy for the local governments would undermine the fundamental principle of federalism and push the country towards a unitary system.

The meeting of the governors, called Progressive Governors Forum (PGF), was attended by nine governors and one deputy governor.

The attendees are the host, Umaru Al-Makura of Nasarawa, Kayode Fayemi of Ekiti, Babatunde Fashola of Lagos, and Abdullazez Yari of Zamfara. Others are Ibikunle Amosun of Ogun, Adams Oshiomhole of Edo, Rauf Aregbesola of Osun, Kashim Shettima of Borno, and Abiola Ajimobi of Oyo. The deputy governor of Imo, Eze Madumere, also attended while Yobe governor was not represented but sent in apology.

“Recognizing the fact that federalism is the basis of our sovereignty, is a matter within the purview of the federating unit and every attempt to legislate by the national assembly on aspect of local government administration will tilt the country towards a unitary state. This will undermine and weaken the fundamental principle of our federalism,” the governors said.

The governors also recommended that the power to amend the revenue allocation formula be removed from the presidency and given to the National Assembly.

“In spite of recommendations made to the presidency, no effect has been given to the extant proposal on the need to give more funds to the states and local governments because that is where the citizens reside. The PGF further recommends that powers to alter the revenue allocation formula currently with the presidency should be vested in the National assembly,” they said.

The communiqué also commended the Independent National Electoral commission (INEC) for registering the APC in the overall interest of the nation. It expressed confidence in the interim leadership of the party in its ongoing efforts to develop a healthy relationship among members.

We have hope once again - so join #APC now.