Monday, July 11, 2011

KANO TA DABO TUMBIN GWIWA

KANO na daya daga cikin manya manyan jihohin Nigeria dama yammacin Afrika baki daya. Kano tsohon gari ne daya haura sama da shekaru 1000+ da kafuwa.

Kano babban gari ne mai dauke da jama'a masu tarun yawa, sama da miliyan tara 9,000,000 kamar yadda hukumar kidaya ta kasa ta tabbatar a kidayar da ta gabata a shekarar 2006. Kuma itace jihar da tafi kowace yawa jama'a a Nigeria da yankin yammacin Afrika.

Wannan yawan jama'a da Kano ke dashi ya samo asali ne sakamakon shahara da garin yayi ta fannoni da dama kamar: Ilmi, tattalin arziki, Kasuwanci, karbar baki, zaman lafiya da sauran dalilai da dama. Tun kafin zuwan turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya Kano tayi kaurin suna wajen wadannan fanni, inda al'umma daga sassan duniya daban daban ke kwararowa don neman ilmi ko kasuwanci.

Kano gari ne daya tara manyan Malam addini, manyan attijirai, manyan sarakai, manyan masu ilmin zamani, manyan komai da komai ciki har da manyan barayi da yan iska. Hakan tasa akewa Kano kirari da "Koda mai kazo an fika" wasu sukewa garin kirari da cewa "Kano ta dabo tumbin giwa, mai mata mai mota, mai Dala da Goron Dutse" ko kuma ace "Jalla babbar Hausa" da sauran kirari dai kala kala na girmamawa.

Mafi yawan mutanen Kano yan kasuwa ne musamman wadanda suke zaune cikin gari, sai kuma manoma da suke zaune a garuruwa kamar Kura, Rogo, Gaya, Dambatta da sauran garuruwa da dama.

Duk wannan martaba da muhimmanci da garin ke dashi amma yanzu a wannan zamanin na siyasa kullum Kano koma baya take samu ba ci gaba ba, garin babu wutar lantarki, babu isasshen ruwan sha, babu kyawawan magudanen ruwa, babu tsari wurin gine gine kullum sai cunkushewa ake yi wuri daya. Babu sana'ar yi a wurin mafi yawan matasa, wanda kuma matasan suka dogara da ita, ko yaushe sai tabarbarewa take yi, amma har yanzu an kasa daukar mataki.

Misalin an bawa yan China dama suna shigo da hajarsu daga kasarsu suna talla, da kuwa mutanen Kano ke zuwa kasashen nasu suna siyowa, suna kuma tafiya musu abinda suke bukata daga nan suna siyarwa a can. Wannan shigowa da yan kasashen waje ke yi da hajarsu zuwa Kano ba karamin nakasu bane ga kasuwancin mutaten Kano, amma har yanzu masu ruwa da tsaki akan abin sunki daukar matakin komai akan wata manufa tasu daban. Haka tasa ake samun karuwar masu zaman kashe wando kullum a Kano.

A shekarun baya kafin wadannan matsalolin su addabi Kano garin yana da kayatarwa, burin duk wanda bai taba zuwa Kano ba yazo ya sha kallo, amma yanzu abin ba haka yake ba. A wancan lokacin ne garuruwa ke daukar salo kala kala a wurinmu, gwamnonin sauran jihohi da sarakuna ke kawo ziyara Kano akai akai ba don komai ba, sai don idan sun zo su ga wani sabon abinda basu san dashi ba, wasu ma daga cikinsu har filaye suka siya suke gina gidaje.

Fatana masu fada aji zasu yi duba irin na basira, su samowa Kano da mutanen ta mafita, Kano ta koma Kanon da aka sani tun tuntuni. Don kuwa Kanon yanzun ba Kano bace kawai suna ne.

A karshe Ya Allah ka daukaka wannan gari na masoya Fiyayyen Halitta bawanKa wanda bai taba saba ma ba, Annabi Muhammad (SAW). Ya Allah ka karawa wannan gari Albarka, zaman lafiya gami da yalwar arziki.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

1 comment:

  1. Bashir Allah ya kawowa jihar Kanonmu mafita. Gaskiya kayi tsokaci mai girman gaske.. Gaskiya kayi tsokaci mai girman gaske.

    ReplyDelete