Monday, September 29, 2014

Taya Murna Ga Ado Ahmad Gidan Dabino MON

Lambar Girmamawa Ta MON Da Aka Karrama Gidan Dabino Da Ita

Gidan Dabino Yayin Wasu Daga Cikin Tafiye - Tafiyensa A Kasashen Turai

Alhamdulillah! Masha Allah!! A madadin dukkan wani Bahaushe mai son ci gaban harshen da burin ganin daukakarsa, ina taya shugaba na kuma malami na, Ado Ahmad Gidan Dabino MON, murnar babbar lambar girmamawa da kasar mu Nigeria ta ba shi a yau (29/09/2014) a matsayin dan ta, da ya sa ta alfahari a bangaren da ya dauka na rayuwa.

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya mannawa Gidan Dabino lambar mai suna MON.

Ga wanda bai san wane ne Gidan Dabino ba, ko kuma ya san shi yake bukatar karin bayani akansa ga kadan daga cikin tarihin rayuwarsa, wanda na tsakuro a turakar Marubutan Hausa.

An haifi Ado Ahmad Gidan Dabino a Danbagina Karamar Hukumar Dawakin Kudu a shekarar 1964, ya yi karatun allo a Zangon Barebari. Bai samu damar yin karatun boko ba sai da ya kai shekara ashirin, sannan ya fara zuwa makarantar yaki da jahilci ta masallachi, watau makarantar da aka fi sani a Kano da makarantar Baban Ladi,daga nan ya yi karatun Sakandare a GSS Warure inda ya samu SSCE a 1990. Daga nan ya yi kwas na shekara guda akan karatun makafi da koyon aikin kafinta, A shekarar 2005 kuma ya sami diploma akan aikin sadarwa daga jamiár Bayero ta Kano. 

Ado Ahmad na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani kuma littafinsa mai suna In da So da Kauna na daya daga cikin fitattun littattafan Hausa na kowane zamani. 

Ya rike mukamai da dama a Kungiyoyin marubuta, shi ne shugaban Kungiyar Marubuta ta Raina Kama, ya taba zama Mataimakin shugabna ANA reshen Kano, ya zamar mata maáji kafin ya zama shugabanta a 2006. 

Gidan Dabino ya taba zama Edita na FIM magazine kasancewar daya daga cikin wadanda suka kafata a 1999. Kuma shi ne mawallafin Mumtaz. Kazalika shugaba/daraktan gudanawarwa na Gidan Dabino International Nigeria Limited. 

Ya gabatar da makalu a manyan tarrurruka na karawa juna sani a jami'o'i daban daban a gida Nijeriya da wasu daga cikin kasashen turai. 

Za a iya kiransa mashiryin wasan Hausa, dan jarida kuma mawallafi. 

Litattatafansa da suka fito sun hada da:

In Da So da Kauna 1 da 2 (1991)

Hattara Dai Masoya 1 & 2, (1993)

Masoyan Zamani 1& 2, (1993)

Wani Hani Ga Allah 1 & 2, (1995)

Duniya Sai Sannu (1996)

Kaico (1997)

Sarkin Ban Kano (2004) tare da Sani Yusuf Ayagi

Ina kara taya Ado Ahmad Gidan Dabino murna, ina kuma kara yi masa addu'a da fatan alheri, kamar yadda ya karbi wannan kyauta daga Nijeriya, Allah ya nuna mana ranar da zai karba daga Afrika da duniya baki daya. 
Takardar Shedar Girmamawa ta MON da aka bawa Gidan Dabino

Tarihin Galadiman Kano - Alhaji Tijjani Hashim

Marigayi Galadiman Kano
An haifi Galadiman Kano Ahmadu Tijjani dan Turakin Kano Hashimu dan Sarkin Kano Abbas dan Sarkin Kano Abdullahi I dan Sarkin Kano Ibrahimu Dabo a shekarar 1932 a cikin birnin Kano.

Ya fara karatun elementare a garin Bebeji a shekarar 1944. A shekarar 1944 ya shiga makarantar Medil ta Kano inda ya daina a 1951.

A 1952 ya fara aiki a En'e ta Kano da mukamin Malamin Dabbobi, mai duba tsaftar dabbobi da za a yanka a kara ta Kano. A 1956 aka zabe shi dan majalisa mai wakiltar Sumaila a majalisar dokoki ta Arewa.

A zaman sa a wannan majalisa ne ya rike mukamai da dama kamar shugaban hukumar bada kwangila ta Kaduna da shugaban kwamitin tabbatar da jam'iyyar NPC ta lashe zabe a lardin Sardauna. Ministan cikin gida na Jihar Arewa. Kwamishinan lardi mai kula Lardin Kabba wadda akan wannan mukami soja suka yi juyin mulki. Dawowarsa gida ne tasa Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero, ya nada shi sarautar Dan Isan Kano kuma kansila mai kula da ayyukan gayya da taimakon kai da kai.

A 1976 ya sami karin girma zuwa sarautar Turakin Kano da bashi kulawa da gundumar Kumbotso. A 1980, ya sami canji zuwa kansila mara ofis saboda yawan harkokinsa. A 1989, ya sami karin girma zuwa sarautar Dan Iyan Kano da ci gaba rike mukamin kansila mara ofis.

A1992, ya sami karin girma a babbar sarautar Kano a matsayin Galadiman Kano kuma shugaban kwamitin kudi na majalisar Sarki. A 2012 Sarki ya kara masa aikin hakimcin birnin Kano. Kuma a kan wannan aiki ya ke zuwa yau da Allah ya amshi ransa. 

"Galadiman Kano Tijjani mashahurin mutum ne da babu iri nai a wanga zamani wajen taimako, adalci, tausayi da kyautatawa. Shi kadai na sani a wanga zamani mai sarauta attajiri mashahuri Kasaitacce da za ka je wuri nai har ka tadda shi ba mai tambayar ka ina za ka". 

Allah ka dube shi, Ka yi masa rahma ka tausaya masa Ka jikansa, Ka sa Aljanna ce makomarsa.

Friday, September 26, 2014

Game Da Ni (Bashir Ahmad) A Takaice

Cikakken sunana Bashir Ahmad Ishaq, Ni haifaffen jihar Kano ne, mazaunin birnin tarayyar Nigeria, Abuja. 

Ina aiki da kamfanin Leadership Group Limited, masu buga jaridun (Leadership Daily, Leadership Weekend, Leadership Sunday da Leadership Hausa).

Sai dai har yanzu ni dalibi ne mai neman ilmin addini Musulunci (Domin na san yadda zan bautawa Allah, Mahaliccina) Sannan mai neman ilmin zamani (Domin na san yadda zan tafiyar da rayuwata tare da mutanen zamani). 

Ina son jin labarai da tarihin al'ummomin da suka gabata musamman wadanda suka yi nasara a rayuwarsu (Domin daukar darasi daga gare su). 

Ina da burin tafiye - tafiye (Domin tafiya mabudin ilmi ce). 

Ina son haduwa da jama'a daban - daban, masu bambancin ra'ayi (Domin sanin al'adunsu da halayyen su).

Ina sha'awar zama da wadanda suka fi ni ilmi (Saboda koyaushe nayi hakan ina kara daukar sabon ilmi) 

A kodayaushe kuma ina sha'awar zama shahararre kuma sanannen dan jarida (Domin na samu damar bayyanawa duniya ra'ayoyin talakawan Nigeria, daya dade a kunshe cikin zuciyoyinsu ba tare da samun damar bayyanawa ba). 

A yanzu ina son shiga harkokin siyasa (Domin na bada gudunmawa wajen tabbatar da kyakkyawar Nigeria ga kowa).

HANYOYI TUNTUBA

Lamba = +2348032493020 | Email = bashahmad29@yahoo.com | Twitter = @BashirAhmaad | BBM = 2B2B92CB | Instagram = BashirAhmaad
Bashir Ahmad

Babu Tabbas Kan Mutuwar Shekau - Amurka


Gwamnatin Amurka ta ce har yanzu ba ta samu wata shaida da za ta tabbatar da ikirarin gwamnatin Nigeria ba, na mutuwar Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Wani jami'in harkokin wajen Amurka, Rodney D Ford ya ce suna ci gaba da kokarin tabbatar da sahihancin ikirarin gwamnatin Nigeria, da gaskiyar cewa akwai mutanen da ke shigar-burtu da sunan Abubakar Shekau.

A baya dai, rundunar tsaron Nigeria ta ce dakarunta sun kashe wani mutum da ke batar da kama da sunan shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau yayin fafatawa a garin Kunduga.

Mai magana da yawun shalkwatar tsaron Nigeria, Manjo Janar Chris Olukolade ya yi ikirarin cewa Abubakar Shekau ya jima da mutuwa amma wasu ke yin shigar-burtu don ci gaba da yada angizon kungiyar.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da batun mutuwar Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram.

- BBC Hausa

Saturday, September 13, 2014

Ni Da Dan Takarar Gwamna Jihar Jigawa, Pharm. Hashim Ubale Yusuf

Pharm. Hashim Ubale Yusuf, mai neman jam'iyyar APC ta sahale masa takarar gwamnan jihar Jigawa, tare da ni Bashir Ahmad, a gidan gwamnatin jihar Kano, lokacin taron Dandalin Siyasa Online Forum, karo na 5 da aka gudanar a Kano 2014.
Bashir Ahmad da Pharm. Hashim Ubale Yusuf