Tuesday, January 31, 2012

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Matasan Arewa


Aminci a gare ku ya ku matasan yankin Arewa!

A matsayina na daya daga cikinku zanyi amfani da wannan dama na tunatar damu wasu muhimman abubuwa da suke hakki ne a gare mu amma muke yin sakaki da su. Sanin kowa ne cewa matasa sune kashin bayan kowace al'umma, domin kuwa sune iyaye kuma shugabannin gobe. Haka ne ma yasa masana masu hangen nesa suka ce duk al'ummar da matasanta suka hada kansu suka zama tsintsiya mai madauri guda, to wannan al'umma nan gaba za ta zama ja gaba a kowane irin fanni na rayuwa, ta kuma yi wa sauran al'ummomin zamanin fin-cin-kau.

Ya ku matasa Arewa! Wai shin ina muka dosa ne? Shin bama ganin yadda wannan yanki namu ke cikin wani hali na rashin kulawa ne? Shin wane irin mataki muka dauka ko muke shirin dauka akan wannan hali?

Matasan Arewa bai kamata mu koma gefe muna ganin laifin shugabanni, sarakuna, malamai da manyan Arewa kadai ba, duk wani abu na rashin dadi daya faru sai mu dora musu laifi muna fadin ba sa kishin Arewa. Zahirin gaskiya wannan ba daidai bane, kuma ban yarda wadannan jagororin Arewa sune ke da laifi kadai ba, idan har suna da laifi to muma muna da namu laifin. Saboda kuwa idan manya sun kasa mai zai sa mu kuma muyi shiru mu kasa cewa komai?

Misali a matsayinmu na shugabannin gobe wane irin shiri mukayi don daukar wannan nauyi? Shin mun san tun lokacin da Sardauna, Tafawa Balewa da Aminu Kano suka fara gwagwarmaya? Idan muka koma tarihi zamu ga sun fara gwagwarmaya akan Arewa tun suna da karancin shekarun da basu fi 20 zuwa 30 ba. To mu fa yaushe zamu fara? A matsayinmu na masu ikirarin kishin na Arewa.

Zan dan yi wasu tambayoyi ga 'yan uwana matasan Arewa, wadandan tambayoyi sun dade suna zirga zirga da kai kawo a cikin zuciyata, amma kuma har yanzu na kasa samun koda amsar tambaya daya daga cikin tambayoyin. Fatan daga yau zan samu dukkan amsoshin wannan tambayoyi.

TAMBAYOYIN SUNE

Shin a matsayinmu na matasa masu so da kishin Arewa wace irin gudunmawa muka bada wurin ganin burin marigayi tsohon shugaban Kano Umar Musa Yar'adua ya cika na zuwan teku Arewa?

Shin a lokacin babban zaben daya gabata wace irin rawa muka taka wurin fitar da dan takara guda daya kwakkwara daga yankin Arewa?

Shin wane irin kokari muke yi ganin dawo da zaman lafiya a Arewa kamar yadda muke a shekarun baya?

Shin an ya kuwa akwai wani shiri da muke yi na ganin samun hadin kai da soyayyar juna a tsakanin kabilu da addinan wannan yanki na Arewa a matsayinmu na jagororin kishin Arewa?

Akwai tambayoyi makamantan wannan masu dumbun yawa dake kunshe a zuciyata wadda na tabbar ku ma ba za'a rasa irinsu a zuciyoyinku ba. Fatanmu mu hada hannu mu samarwa kanmu amsoshin wadannan tambayoyi.

Sai tambayata ta karshe, shin tawa ne hali zamu kawowa kanmu mafita? Amma saboda saukin wannan tambaya zanyi kirinkin bada amsarta. Amsar tambayar itace mu matasa mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinmu daya, bayan haka kuma mu zama masu kishi da soyayyar yankinmu. Sannan mu zama masu magana da harshe guda, wato idan matashin jihar Adamawa yace eh, to idan aka samu na jihar Kwara ma yace eh. Hakan kuwa zaiyi wahala har sai munyi wata kungiya da zata tattaro dukkan matasan Arewa ta dunkule mu wuri guda. Yin hakan ne kadai muryarmu zata ke isa inda muke so da bukatar taje, sannan hakan ne zai sa asan muhimmancimu, ta haka ne kadai zamu samu damar kare 'yancinmu da mutuncimu.

A karshe nayi amfani da wannan dama ne don na isar da wannan sako ga duk wani matashi wannan wasika, saboda sanin wannan ce hanya kadai da zan aika sakon nawa kuma ya isa zuwa wurin wadanda na aika dominsu. Fatan duk wanda ya karanta wannan wasika zai aikawa sauran abokansa ta haka ne zata samu isa zuwa ga duk wani matashi mai kishin Arewa.

Sannan zanyi kokarin ganin an buga wannan wasika a jaridu da mujallu musamman masu amfani da harshenmu na Hausa.

Allah ya daukaka Arewa, Allah ya daukaka kasarmu Nigeria!

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Monday, January 30, 2012

Shin Kotu Ta Yiwa Hamza Al-Mustapha Hukuncin Adalci?


Kotu ta yankewa Major Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan shafe sama da shekaru 13 a gidan yari. Alkaliyar Kotun Mrs Dada ta bayyana cewa an yankewa Al-Mustapha hukuncin ne saboda da sa hannunsa aka kashe Hajiya Kudirat Abiola matar MKO Abiola. Al-Mustapha yaje kotun ne sanye da fararen kaya wanda bayan yake hukuncin ya fito yana murmushi gami da dagawa mutane hannu. Wannan dalili yasa wasu daga cikin magoya bayansa kuka, wasu kuma na Kabbara.

Major Al-Mustapha ya bayyanawa manema labarai cewa a matsayin na Musulmi bayyi mamakin hakan ba, kuma dukkan wani munafiki karshensa bazai yi kyau. Lauyan da yake kare Al-Mustaphan ya bayyana cewa zasu daukaka kara kuma suna sa ran samun hukuncin adalci a kotun gaba.

TAMBAYOYI: Shin wannan hukunci da kotu ta yakewa Al-Mustapha akwai adalci a ciki? Shin duk shekarun daya shafe a gidan yari basu isa hukunci ba? Shin duk mutanen da Ojukwu ya kasha mai yasa ba'a yanke masa hukuncin kisa ba? Shin ina labarin mutanen da Al-Mustaphan ya lissafo a kwanakin baya wanda da sa hannunsu aka kashe MKO Abiola? Shin wane mataki manyan Arewa suka dauka don ganin ba'a yiwa dansu hukuncin zalinci ba?

Ya ALLAH ga bawanka Hamza Al-Mustapha kar ka bari ayi masa hukunci na zalinci.

An Yankewa Al-Mustapha Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

A Najeriya wata kotun daukaka
kara a jihar Legas ta yanke wa
tsohon dogarin marigayi Janar
Sani Abacha, Hamza Al-
Mustapha hukucin kisa ta
hanyar ratayewa sakamakon
kisan uwargidan marigayi MKO
Abiola.

Mai shari'a Mojisola Dada ta ce ya
kamata a rataye Manjo Hamza Al-
Mustapha, sakamakon samunsa
da hannu a shirya kisan
uwargidan shahararren dan
kasuwa kuma dan siyasa
marigayi Moshood Abiola.

Al-Mustapha, shi ne na hannun
damar tsohon shugaban mulkin
soji Janar Sani Abacha, ya shafe
shekaru 13 yana zama a gidan
yari, tun bayan da aka zarge shi
da shirya kisan.

Wannan shari'a ta ja hankalin
jama'a sosai a kasar, musamman
ganin lokacin da aka shafe ana
gudanar da ita - da ma
abubuwan da suka rinka faruwa
a lokacin shari'ar.

Anta samun shaidu masu cin
koro da juna a lokacin shari'ar,
yayin da kungiyoyi daban-
daban suka nuna damuwa kan
yadda aka dade ana gudanar da
ita.

A shekarar 1996 ne aka kashe
Kudirat Abiola sakamakon wani
harbi da wasu mutane suka yi
mata.

Marigayi Moshood Abiola ne ake
kyautata zaton ya lashe zaben
shugabancin kasar da aka
gudanar a shekara ta 1993,
wanda daga bisani gwamnatin
mulkin soji ta Janar Ibrahim
Babangida ta soke.

Kuma babu wani abu da yake
tunawa 'yan kasar wancan zabe
kamar wannan shari'ar.
Sai dai babu tabbas ko wannan
hukunci zai kawo karshen
sa'insar da shari'ar ta haifar.

Wannan hukuncin ya zo a daidai
lokacin da Najeriya ke cikin
mawuyacin hali ta fuskar tsaro
da kuma siyasa, abinda masu
lura da al'amura ke ganin ka iya
kara cakuda al'amura a kasar.

Daga shafin BBC Hausa

Thursday, January 26, 2012

Ba Zan Sake Tsayawa Takarar Kowane Irin Mukami Ba - IBB

Tsohon Shugaban kasar Nijeriya, kuma daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, wanda ya janye daga takarar a zaben shekarar da ta gabata ta 2011, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shaida cewa ya yi bankwana da siyasa kuma ba zai kara neman wani mukamin a gwamnatance ba.

IBB ya yi wannan magana ne a wani taron shekara da kamfanin Trust Media LTD ya shirya wanda aka gabatar a Transcorp Hilton Hotel dake birnin tarayya Abuja, wanda yayi magana a matsayin shugaban taron.

Babangida ya ce "Ina da labari ga duk kafafen yada labarai na kasar nan baki daya, duk da zan ci gaba da zama mai bada shawarwari ga 'yan siyasa masu zuwa anan gaba, amma ba zan kara tsayawa takara don a zabe ni a kowane irin mukami ba anan gabata. Ya ce Babangida ba zai sake tsayawa kowane dan takara don samun nasarar wani mukami ba".

Tsohon shugaban kasar ya yi amfani da irin kalaman da tsohon shugaban kasar Amurka Richard Nixon ya yi a lokacin da shi ma yake bankwana da siyasa.

Shugaba Goodluck ya Bukaci Tattaunawa da 'Yan Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kalubalanci kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram da su fito su bayyana kansu su kuma bayyana bukatunsu a matsayin matakin farko na fara tattaunawa da su.

Shugaban ya kuma amince cewa amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen tashe-tashen hankulan ba. Sai dai Jonathan ya kara da cewa, sabanin tsagerun Naija Delta, matsalar 'yan Boko Haram ita ce ba a san shugabanninta ba balle a tattauna da su.

Sai dai shugaban Kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya ce ba za su tattauna da gwamnatin Najeriyar ba. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Jonathan ya ce babu tantama kungiyar boko Haram tana da alaka da sauran kungiyoyi masu jihadi a ketaren Najeriya.

Akalla mutane 186 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da kungiyar ta kai a Kano ranar Juma'ar da ta gabata. "Idan suka bayyana kansu, suka kuma ce ga dalilin da ya sa muke gwagwarmaya, ga dalilin da ya sa muke fito na fito da gwamnati, ga dalilin da ya sa muke lalata dukiyoyin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, to daga nan za a samu ginshiki na fara tattauna wa, in ji shugaba Jonathan.

Shugaban na Najeriya ya kuma kara da cewa, "Za mu tattauna da ku, ku sanar da mu matsalolinku, za mu warware muku su, amma idan ba su bayyana kansu ba, da wa za ka tattauna?" Sai dai shugaban na Najeriya ya bayyana cewa akwai bukatar a kawo ayyukan ci gaba a yankunan arewacin kasar inda ake da dimbin matasa marasa aikin yi, abinda yake baiwa kungiyoyi masu tada kayar baya damar samun magoya baya cikin sauki.

"Amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen hare-haren ta'addancin ba," in ji shi, "ana kuma bukatar a samar da yanayin da zai baiwa matasa damar samun ayyukan yi".

Daga shafin BBC Hausa
www.bbchausa.com

Wednesday, January 25, 2012

MD Abubakar ne Sabon Sifeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da nadin Mohammad D. Abubakar a matsayin Sipeto Janar na 'yan sanda na riko.

Sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara ta fannin yada labarai Mista Ruben Abati ya fitar, ta ce sabon sipeto janar din na riko ya maye gurbin Hafiz Ringim wanda zai soma hutu daga ranar Laraba.

Sannan kuma shugaban Jonathan din ya amince da ritayar duka masu rike da mukamin mukadashin sipeto janar din wato DIG's ba tare da bata lokaci ba.

Nadin sabon shugaban rundunar 'yan sandan ta Najeriya ya zo ne kwana daya bayan wani hari da ake zargin 'yan kungiyar nan ta jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fisani da Boko Haram da kai wa a kan wani ofishin 'yan sanda a unguwar Sheka da ke Kano.

A ranar Juma'ar da ta wuce, kungiyar Boko Haram ta kai hari a Kanon, inda akalla mutane dari da tamanin da biyar suka hallaka.

Kuma an rika kira ga shugaban 'yan sandan, Hafiz Ringim, da yayi murabus, bayan da wani da ake jin shi ne ya tsara harin da aka kaiwa wani coci a Abuja, kabiru Sokoto ya sullube wa 'yan sanda.

Shugaba Jonathan ya daura wa sabon Sifeto Janar din aikin yin garambawul ga rundunar 'yan sandan kasar domin ta iya shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Jonathan ya kuma nada wani kwamiti da zai sanya ido wajen ganin an kawo sauye-sauye a rundunar da kuma dalilan da suka janyo jama'a suka fidda kauna da rundunar 'yan sandan Nijeriyar.

Masu sharhi a kan al'amura na ganin 'yan sandan Najeriyar sun gaza shawo kan hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wa a sassa dabam- daban na kasar.

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch ta ce kungiyar Boko Haram ta kashe kimanin mutane 935 tun da ta fara kai hare-hare a shekarar 2009.

Daga shafin BBC Hausa
www.bbc.co.uk/hausa

Boko Haram Na Kashe Jami'an Tsaro - Jami'an Tsaro Na Kashe Farar Hula

A daren ranar Talata al'ummar unguwar Tsamiyar Boka dake yankin Hotoro a cikin birnin Kano suka samu kansu cikin wani mawuyacin hali wanda jami'an tsaro suka rinka harbe - harbe a kokarinsu na farautar 'yan Boko Haram, wanda jami'an tsaron ke zargin unguwar a matsayin mafakar 'yan Boko Haram din.

A wannan zargi da jami'an tsaro ke yi wa mutanen unguwar yasa suka je gidan wani bawan Allah mai suna Uzairu Abdullahi suka bude masa wuta suka kashe shi tare da matarshi 'yar shekara 18 mai dauke da juna biyu. Wata majiyar ma ta bayyana cewa har da mahaifiyarsa marigayin a cikin gidan lokacin da jami'an tsaro suka budewa gidan wuta, kuma ita ma nan take Allah ya yi mata rasu.

Uzairu Abdullahi matashi ne dan kasuwa, wanda yake sai da shaddodi da atamfofi a kasuwar Kwari cikin birnin Kano, kuma al'ummar unguwar da yake zaune sunyi masa shaida akan mutumin kirki ne, kuma suka tabbatar da cewa ba dan kungiyar Boko Haram ba ne, sannan yana zaune a unguwar sama da shekara bakwai. Wasu daga cikin mazauna unguwar ta Tsamiyar Boka sun bayyana cewa jami'an tsaron sun harbe Uzairu da iyalansa ne akan zargin dan Boko Haram ne saboda kawai yana da dogon gemu kuma yana dage wandonsa.

SANAYYA TA DA UZAIRU ABDULLAHI

Na san Uzairu tun ina karamin yaro sama da shekaru goma da suka gabata, na san gidansu na san mahaifansa da sauran 'yan uwansa, a yadda na fahimci dabi'o'insa ko kadan ba suyi kama da na 'yan kungiyar Boko Haram ba. Kai ko ma dai ace shi din dan Boko Haram ne, ai kamata yayi a ce lokacin da jami'an tsaro suke zargin dan Boko Haram ne, kama shi ya kamata suyi su gudanar da bincike akansa domin tabbatar da zargin da suke yi masa, idan sun tabbatar da hakan sai su mika shi kotu don yi masa hukuncin daya dace dashi. Saboda hakan ne kadai zai kawo mana karshen wannan bala'i da muke ciki.

Ya Allah ka kawo mana dauki, ka sanya mana garkuwa a tsakaninmu da makiyanmu, Ka kawo mana zaman lafiya a jiharmu da kasarmu baki daya.

Ko Za a Samu Bore Irin Na Kasashen Larabawa a Afrika?

A daidai lokacin da ake bukukuwan tunawa da boren da aka yi a kasashen Tunisia da Masar wanda ya kifar da gwamnatocin kasar, sannan ya haifar da bore a wasu kasashen Larabawa: Tambayar ita ce ko za a sami makamancin wannan boren a kasashen Afrika?

An kifar da gwamnatoci, masu mulkin kama-karya sun sha kasa, an watsa boren a gidajen talabijin ta hanyar da ba a taba tsammani ba watanni 12 da suka gabata.

Nahiyar Afrika na daga cikin sassan duniya da ke da shugabannin da suka dade suna mulkin kama-karya - kuma wannan shi ne abinda mazauna kasashen Larabawan ke adawa da shi.

Sai dai bore makamancin wannan a nahiyar Afrika zai mayar da nahiyar baya ne - maimakon ciyar da ita gaba.

A takaice ma zai kawo cikas ne kan nasarorin da wasu kasashen suka samu a shekarun 1980 da kuma farkon 1990 - lokacin da suka kawar da masu mulkin kama-karya domin gudanar da zabuka na jam'iyyu da dama.

'Azzaluman shugabanni'

Sai dai, kada kuri'a kadai ba zai wadatar ba - kuma demokuradiyya bata kare a kada kuri'a ba kawai, kamar yadda kasashen Tunisia da Masar suke kokarin lalubo mafita bayan juyin-juya halin da aka yi.

Babu wata kasar Larabawa da ke da ikon gudanar da zanga-zanga ko kalubalantar gwamnatocinsu kafin boren da aka yi a Tunisia a ranar 14 ga watan Janairun 2011.

Zanga-zangar da aka gudanar a watan Yulin shekara ta 2011 a kasar Malawi, ba an shirya ta bane domin kifar da gwamnati ko neman shugaba Bingu wa Mutharika ya yi murabus ba.

Ana korafi ne game da tabarbarewar tsarin demokuradiyya wanda ya baiwa gwamnati mai ci damar yin mulki ba tare da wani kalubale ba.

Haka lamarin yake a Najeriya - baya ga rikicin kungiyar Boko Haram. 'Yan kasar na zanga-zanga ne kan matakin gwamnati na cire tallafin man fetur - suna kira ga gwamnati da ta sake tunani amma ba wai kokarin kifar da ita suke yi ba.

A kasar Uganda, an gudanar da zanga-zanga kan farashin albarkatun man fetur - ba wai don neman kifar da gwamnati ko kawar da shugaban kasa ba.

Irin wadannan bukatun za a iya shawo kansu ne kawai ta hanyar samar da hukumomi - ba wai kawar da shugabanni ko kifar da gwamnatocinsu ba.

Kuma wannan shin ne mataki na gaba da ya kamata a dauka a fagen demokuradiyya a nahiyar Afrika - ba wai bore makamancin na kasashen Larabawa ba.

Fassarar sharhi Jimmy Kainja - Malamin Jami'a a kasar Malawi, daga BBC Hausa

Monday, January 23, 2012

Wasikar Boko Haram Zuwa Ga Mahukuntan Jihar Kano

Tun bayan harin bama - baman da yayi asarar daruruwan bayin Allah a yammacin Juma'ar da ta gabata a sassan birnin Kano, nake ta mamakin da wata wasika dana rinka cin karo da ita a shafukan gidajen yanar gizo daban - daban, kamar su Nairaland, Sahara Reporters, All Africa, Facebook, Nigeria Information da sauran su. Wannan wasika budaddiyar wasika ce zuwa ga gwamnatin jihar Kano da kuma wasu mutum uku daga cikin manyan mutane a jihar, wadanda ake ganin kimarsu da girmarsu a fadin jihar dama fadin Nigeria baki daya.

Wannan wasika ta nuna yadda kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram ta aikawa gwamnati da wadannan manyan mutane, sakon gargadi akan aka daina kama musu mutane, kuma a saki wadanda suke hannun hukuma, sannan a cikin wasikar sun bayyana cewa idan har ba'a yi musu wannan abu da suka bukata ba to garin Kano zai gamu da munanan hare - hare marassa iyakaci sama wanda yake faru Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Sun bayyana cewa jihar Borno ma, wadda ada ake yi wa kirari da cibiyar zaman lafiya, sun aika irin wannan gargadi kafin garin ya zama yadda yake a yanzu, amma sai hukumomi suka dauki maganar tasu a matsayin wasa. Wanda a cikin wannan wasika suka rantse da girman Allah mahaliccin samai da kasai, wadda ya aiko annabawa da manzanni tun daga kan Annabi Adamu (A.S) har zuwa Annabi Muhammad (S.A.W), akan cewa ba wasa suke ba.

Sun ce sun dade suna yungurin kawo hare - hare jihar ta Kano domin daukar fansar mutanensu da aka kashe a shekaru biyu da suka gabata a garin Wudil, amma saboda darajar manyan malaman da suke cikin garin na Kano shi yasa suka daga kafa, sanadiyyar hakan ne ma yasa suka dauki matakin aiko da wannan wasika, domin mahukunta su dauki mataki.

Wani abin mamaki da daurewar kai, shi ne wannan wasika ta Boko Haram sun aika ta ne tun a wata takwas (August) na shekarar da ta gabata 2011. Amma gwamnati da sauran wadanda aka aikawa wannan wasika basu dauki matakin biyawa wannan jama'a bukatun nasu ba, kuma basu dauki matakin kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu ba.

Tambaya anan itace: Shin gwamnatin jihar Kano da wadanda aka aikawa wannan wasika su ma sun dauki wasikar ne a matsayin wasan yara kamar yadda hukumomin jihar Borno suka yi? Ko kuma wasikar ce ba tazo hannunsu ba, bare su san matakin da zasu dauka? Zahirin gaskiya idan wannan wasika da Boko Haram ke ikarin sun aiko musu tazo hannunsu amma basu dauki matakin komai ba, to su ma sun bada muhimmiyar gudunmawa wurin je fa al'ummar Kano a wannan mummunan hali na tashin hankali da muka tsinci kanmu ciki da kuma asarar daruruwan rayukan bayin Allah wadanda basu ji ba kuma basu gani ba.

Ya Allah ka kawowa jiharmu Kano da kasarmu Nigeria zaman lafiya. Ya Allah ka taimaki shugabanninmu Ka nuna musu hanyar gaskiya Ka kuma basu ikon binta, Ka basu ikon yi mana adalci. Mu kuma mabiya Ka bamu ikon binsu da yi musu biyayya.

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Sunday, January 22, 2012

Ba Zamu Janye Yajin Aiki Ba - Shugaban ASUU

Shugaban Kungiyar gamayyar malaman jami'o'in kasar nan ASUU Prof. Ukachuchwu Awuzie ya bayyana cewa ba zasu koma aiki ba daga yajin aikin da suka tafi har sai gwamnati ta biya musu bukatun da suka nema a wurinta. Ba kamar yadda ministan ilimi Prof. Ruqayya Ahmad Rufai ta bayyana ba, cewa malaman zasu janye yajin aikin a koma karatu ranar Litinin, ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da manema labarai bayan fitowa daga wata tattauwa da tayi da wasu daga cikin mataimakan shugabanin jami'o'i a birnin tarayya Abuja.

Amma shugaban na ASUU Prof. Awuzie ya bayyanawa jaridar Leadership a daren jiya cewa kungiyar malamai ba kungiyar mataimakan jami'o'i ba ce, saboda haka basu san maganar janye yajin aiki ba, har sai bukatunsu sun biya.

Prof. Awuzie yace ASUU zasu zauna su tattauna da shugaba Goodluck Jonathan ranar Litinin, kuma da zarar an biya mana bukatunmu to zamu janye yajin aiki su koma aiki.

Saturday, January 21, 2012

Mutane Sama Da 100 Sun Rasu Sakamakon Tashin Bama - Bamai a Kano

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga Allah muka zo kuma gare zamu koma baki daya. Ya Allah ka jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon tashin bama - bamai a yammacin jiya a ofisoshin jami'an tsaro daban - daban a birnin Kano.

A wata sanarwa da wani gidan radio mai zaman kansa na Freedom Radio ya bayyana cewa wakilansu sun ganewa idon su gawarwakin mutane sama da mutum dari a asibitoti daban - daban, wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon wannan tashin hankali.

Sai dai kawowa yanzu hukumar tsaro ko kuma gwamnatin jihar ta Kano basu bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba. A labaran safe da gidan radiyon jihar Kano mallakar gwamnatin jihar ya bayyana cewa an samu asabar rayukan mutum bakwai, wanda biyu daga ciki jami'an tsaro ne sauran kuma fararen hula ciki har da wani wakilin gidan talabijin na Channel TV daga jihar Lagos.

Ya Allah ya kawo mana zaman lafiya a jiharmu da kasarmu Nigeria baki daya.

Friday, January 20, 2012

Al'ummar Kano Na Neman Addu'arku

Zahiri mu jama'ar Kano muna neman addu'arku, sanin kowa ne Kano gari ne mai dumbin al'umma sama da mutum miliyan hudu ne ke cunkushe a cikin kwaryar birnin na Kano, wanda kuma kaso 98% dukkanmu Musulmai ne kuma Hausawa.

A yammacin wannan rana ne, wani abu ya faru wanda mu jama'ar Kano zamu iya cewa bamu saba ba, ko ma muce bamu taba ganin irin hakan ba. Ba komai ne ya faru a Kanon ba sai tashin wasu bama - bama a wasu sassan hukumomin tsaro a cikin birnin na Kano, wanda ya kawo asarar rayukan da har yanzu ba'a tabbatar da adadinsu ba.

Wannan tashin bama - bamai ba karamin je fa mu cikin tashin hankali yayi ba, musamman bayan da bama - baman suka tashi, sai kuma harbe - harbe da ihun jiniyoyin jami'an tsaro, abin kamar a filin yaki. Wannan harbe - harbe shi yafi komai tayar mana da hankali.

Jama'ar Nigeria da sauran na sassan duniya baki daya muna rokon addu'arku ne saboda tashin bom a birnin Kano ba karamin asarar rayuka da dokiyoyi zai haifar ba, saboda yawan al'ummar birnin kuma a cunkushe wuri guda kamar yadda na fada a baya.

Ya Allah ka kawowa jiharmu Kano daukin gaggawa, da sauran jihohin da irin wannan abubuwa ke faruwa. Ya Allah ka bamu zaman lafiya a jiharmu da kasarmu Nigeria baki daya.

An Saka Dokar Hana Zirga - Zirga Na Tsawon Awa 24 A Birnin Kano

Hukumar 'yan sanda tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano sun bada sanarwar hana zirga - zirga (Curfew) a cikin birnin na Kano na tsawon awanni ashirin da hudu 24, sanarwar ta fito daga bakin kwamishinan yada labarai na gwamnatin jihar Hon. Umar Jibrin.

Wannan sanarwa ta biyo baya sakamakon tashin wasu bama - bamai a sassa daban - daban na jihar, ciki har da babban ofishin 'yan sanda na jihar shiya ta daya, da kuma ofishin jami'an shiga da fice (Immigration) da kuma wasu kananan ofishoshin 'yan sandan. Wanda kungiyar nan dake ikirarin kishin Islama ta Boko Haram ta bayyana cewa ita take da alhakin tashin bama - baman.

A wata sanarwa daga hukumar 'yan sandan ta bayyana jin kadan bayan tashin bama - baman, ta bayyana cewa 'yan sada guda biyu sun rasu, sai kuma wasu sama da mutum 29 da suka samu raunuka wanda suke karbar magani a asibitoti daban - daban.

Thursday, January 19, 2012

Jami'an Tsaro Sun Sake Kama Dan Boko Haram Bayan Kubucewa Da Yayi Daga Hannunsu

Kai amma wannan wasan kwaikwayo yayi kyau ga jan hankali gami ban dariya har ma da ban haushi. Ba sai na ja ku da nisa ba, na takaice muku labari dai a yau ne hukumar jami'an tsaro ta kasa ta bada sanarwar sake kama Kabiru Sokoto aka bayyana cewa dan kungiyar Boko Haram ne, kuma ake zarginsa da shirya harin ranar Kirismeti a garin Madalla, dake jihar Niger.

An sake kama Kabiru Sokoto ne a lokacin da yake kokarin tsallake kasar nan a tsakanin iyakar kasar nan da kasar Chadi a jihar Borno, bayan kubucewar da yayi daga hannun jami'an tsaro a ranar Lahadin da ta gabata.

Babban abinda ya fi bada mamaki ko nace abin haushi shi ne bayan kubucewar wannan bawan Allah daga hannun jami'an tsaron shugaban kasa Jonathan Goodluck ya bawa jami'an tsaron umurnin cewa su fito da Kabir Sokoto duk inda yake a fadin kasar nan, cikin kasa da awa ashirin da hudu ko kuma ya dauki tsatstsauran mataki.

Jami'an da suka bada umarnin wannan wasan kwaikwayo sun nuna kwarewa a aikin nasu wanda saura 'yan awanni kalilan umarnin na mai girma Shugaban Kasa ya cika, sai ga sanarwar sake kama Kabiru Sokoto.

"Ba komai yasa na kira wannan labari da wasan kwaikwayo ba sai saboda wasu dalilai nawa wanda kuma nasan kuma idan kuka dubi dalilan nawa da idon basira zaku gane cewa wannan labari shiryayyen wasan kwaikwayo ne da ake son wasa da kwakwalwar jama'ar kasar nan"

Idan mukayi duba da yadda hankalin gwamnati ya tashi akan 'yan kungiyar Boko Haram ba yadda za'ayi ace an kama daya daga cikin 'yayan kungiyar amma jami'an tsaro suyi sakaki har ya kubuce daga hannunsu ba tare da anyi musayar wutar da zatayi sanadiyar asarar rayuka ba.

Baya ga haka idan har ba so ake ayi wasa da hankalinmu ba, babu yadda za'ayi ace shugaban kasa ya bawa jami'an tsaro umarnin kamo wani mai lefi a kayyadadden wani lokaci a kasar nan kuma kafin lokacin ya cika, jami'an tsaron suka cika aikinsu da kyakkyawan sakamako.

Tambaya anan itace idan har muna da irin wadannan jami'an tsaro da za'a basu umarnin kamo mai laifi cikin kasa da kwana daya kuma suka kamo shi, to mai yasa Shugaba Goodluck bai bada umarni a kamo wadanda suka kai harin ranar cikar shekaru 50 da samu 'yancin kan Nigeria ba, duk da kuwa shugaban yayi ikirarin yasa wadanda suka kai harin.

A baya bayan nan an hare hare ciki har da babban ofishin jami'an tsaro na kasa da kuma ofishin majalisar dinkin duniya dake birnin tarayya Abuja. Ga kuma hare - haren kwanan nan irin nasu Maiduguri, Yobe, Adamawa da sauransu, amma duk shugaban bai bada umarnin kamo wadanda suke kai hare - haren ba, duk kuwa da irin wadannan jami'an tsaro masu kamo masu laifi cikin kankanin lokaci da yake da su.

"Na san da wannan 'yan dalilai nawa idan ku ma kuka zurfafa tunani akan hakan za ku gano cewa kawai wasan kwaikwayo aka shiryawa 'yan Nigeria"

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com

Wednesday, January 18, 2012

BANKIN MUSULUNCI YA FARA AIKI A NIGERIA

Sakamakon Hargowar da aka
shiga satin da ya gabata, wato kowa na cikin gwagwarmayar neman 'yanci sakamakon tallafin man fetur da gwamnati ta cire, hankalin
da yawa daga cikinmu bai kai kan wannan ci
gaba da Musulunci da Musulman Nigeria su ka
samu ba.

Bankin Musulunci karkashin Ja'iz International Bank ya fara aiki a wannan kasa tamu, bayan suka da bankin ya rinka sha ta hannun mabiya addinin Kirista. Bankin dai ya fara aiki ne ran
ar 10/01/2012 Ya kuma bude
Ofisoshi biyu a shiyyar Abuja
da kuma Kano.

Kamar yadda tsarin bankin yake kowa da kowa na iya yin ajiya a cikinsa wato ba iya mabiya Addinin Islama ne kadai ke da damar ajiya a ciki. Za'a fara a jiyar farko a bankin da kudi Naira dubu Goma
N10,000:00 zuwa sama. Kuma kamar yadda kowa yadda kowa ya sani banki na tafiya ne kafada da kafada da dokokin Musulunci, saboda haka babu RUWA (Interest) a tsarin ajiyar bankin.

To daga yanzu
dukkan wani Musulmi da yake ajiya a wasu bankunan da suka sabawa dokokin Musulunci kuma yake fakewa da cewa lalura ce to dai yanzu ga karshen lalurar ya zo.

Yan Kasuwa, 'yan siyasa, sarakuna, malamai, dalibai da sauran daidaikun jama'a sai mu tanadi amsar da zamu bawa Allah akan mu'amalantar Riba a sauran
Bankuna.

Kamar yadda bankin yake kukan rashin
yawan masu mu'amala dashi, idan har kaunarmu da Addininmu
da son ci gabansa ba'a iya fatar bakinmu ya tsaya ba, ya kamata masu ajiye
kudadensu ko baso (loan) su
daga bankunan Riba, zuwan
wannan bankin sai muyi kokari mu dakatar da hakan mu koma amfani da namu, saboda hakan ne hanya daya da za
ta daukaka shi da bunkasa shi tare
da saurin yadashi zuwa
bangarorin kasar nan cikin kankanin lokaci.

Malamai da masu fada a ji, Ba sai
ka jira an tuntube ka ba, Lalle mu
hada karfi da Karfe don kara
tallata al'amuran wannan banki da zaburar da
mutane da su bada hadin kai
wajen samarwa bankin abokan
hulda.

Ba zan bari a fara shuka wannan
alkairin ba tare da hannuna ciki ba, da zarar Allah ya hore min abinda zan ajiye
zan fara sanya
ajiyata. To kai/ke fa yaushe zaka/ki fara ajiyar domin daukakuwar wannan banki saboda daukakarsa daukaka ce ta addinin Musulunci.

An rawaito daga Danbuzu Multi-Purpose Medium

Gyarawa da karin bayani
Bashir Ahmad
08032493020, 08050600160

Shafin Wikipedia Ya Tafi Yajin Aiki Don Nuna Rashin Goyon Bayansu Akan Dokar Satar Fasaha

Shahararren shafin samar da bayyanai na Wikipedia bangaren Turanci ya tafi yajin aiki na tsawon awanni 24 a yau Laraba domin nuna adawa da sabuwar dokar hana satar bayanai ta Internet da Amurka ke shirin bullo da ita. Su ma shafukan Reddit da kuma na Boing Boing sun ce za su shiga cikin yajin aikin. Shafukan internet din na adawa ne da dokar hana satar bayanai da kare fasaha wacce yanzu haka ake tattaunawa a kanta a Majalisar Dokokin kasar.

Sai dai shafin sada zumunta na Twitter ya ce ba zai shiga cikin yajin aikin ba. Takwaransa kuma shafin Facebook har yanzu bai ce komai ba a wannan al'amarin. Mutumin da ya kafa shafin na Wikipedia, Jimmy Wales, ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa: “Mutanen da ke goyon bayan dokar sun rikide tsakanin masu adawa ko goyon bayan dokar. “Amma wannan bashi ne zancen ba, lamarin shi ne an fadada dokar da yawa, kuma an rubuta ta ta yadda za ta shafi duk wani abu da ka sani, ba ta da wata alaka da hana satar bayanai.

Amma masu goyon bayan dokar sun ce an shirya ta ne domin hana kudade shiga hannun kamfanonin internet na bogi. Akwai wata dokar makamanciyar wannan da ke kan hanyar zuwa majalisar dattawan kasar ta Amurka. A ranar Asabar fadar White House ta fitar da wata sanarwa inda ta nuna goyon baya ga masu adawa da dokar.

Sanarwar ta ce: “A yayin da muka amince cewa satar bayanai babbar matsala ce, ba za mu goyi bayan dokar da za ta rage ‘yancin fadin albarkacin baki ba, kara rashin tabbas ta fuskar tsaro a Internet, da yin zagon kasa a fagen Internet”.

An rawaito daga shafin: BBCHausa.com

Sunday, January 15, 2012

Sako Zuwa Ga Dakarun Gwagwarmayar Neman 'Yanci

Ya ku 'yan Nigeria! Gwamnati tayi imanin cewa bamu da juriya kuma bamu da kokarin rike yunwa da kishirwa, kwanaki kalilan zamuyi cikin wannan hali na yajin aiki da zanga - zanga zamu gajiya ma'aikata su koma bakin aikinsu, dalibai su koma makarantunsu, 'yan kasuwa su kuma kasuwanni, ba tare da munyi nasara sun dawo da farashin man fetur yadda yake ba. Don Allah kar mu yarda mu bada kai bori ya sau, mu dage mu jajirce har sai munyi nasara. ALUTA CONTINUA!

Al'ummar kasashen Libya, Tunusia, Egypt, Syria da sauran kasashen larabawa, ba gwagwarmayar kwanaki uku kawai sukayi ba suka samu nasara, sai da suka jajirce ba dare ba rana, suka bar gidajensu, 'yayayensu har ma da matayensu. Sun rurrufe kasuwanninsu, dalibai sun hakura da zuwa makarantu, sun manta da kowane irin jin dadi ko yin wasanni, sun bar gadajensu sun koma kwana a fili a cikin tantuna, har sai da duniya taji muryoyinsu, a karshe kuma sukayi nasara. Fatan zamu dauki darasi daga wadannan al'ummomi wanda a zahiri kowa yasan sun fi mu jin dadin rayuwa, sun fi mu samun shugabanni nagari da sauran abubuwan more rayuwa.

Duk wani dan Nigeria daya haura shekaru 35 bai taba jin dadin shugabanni ba, kowane shugaba yazo yana shinfida mulkin kama kara har wa'adinsu ya kare. Lokaci yayi da ya kamata mu tashi domin 'yancinmu, mu tashi tsaye don kawo karshen wannan bakin mulkin na zalinci da ake yi mana. Zamu sha wahala kafin muyi nasara, amma da munyi nasara wahalar ta wuce 'yayanmu da jikokinmu zasu gode mana nan gaba akan jajircewar da mukayi domin kyautatuwar rayuwarsu.

Ba abin alfahari bane a gare mu muyi hijira daga kasarmu ta gado Nigeria zuwa wasu kasashe da suka ci gaba don yi kyakkyawar rayuwa acan har mutuwa tayi ahalinta. Ina kira ga dukkanin mu, karmu gajiya kuma kar muyi tunanin gajiyawa, kar mu karaya kuma kar muyi tunanin karaya, mu ci gaba da goyawa kungiyar 'yan Kwadago baya, tunaninsu a kullum talaka ya samu 'yanci ya fara jin dadin rayuwa da amfanar arzikin kasarsa kamar kowa, ba iya wasu 'yan tsiraru daga su sai 'yayansu ba.

Idan mukayi hakuri muka ci gaba da wannan yajin aiki da zanga - zangar neman 'yanci ba iya mu muke abin yake shafa ba, hatta gwamnatin Nigeria da 'yan kanzaginta abin yana shafarsu. A satin daya gabata Sanusi Lamido Sanusi shugaban bankin kasa na CBN ya bayyana irin biliyoyin kudin da gwamnati take yin asara a kullum tunda aka fara wannan yajin aiki.

Samun goyan bayan hukumar hako man fetur ta PENGASSAN ba karamar nasara bace a wannan gwagwarmaya, sanin kowane babu wani abu da muke fitarwa don samun kudin shiga a kasar nan sama da man fetur, da zarar PENGASSAN sun tafi yajin aiki to aikin gama ya gama, barawo zai rasa inda zaije ya saci kudi. Sun saba da yin baccin har da munshari akan dukiyar kasarmu. A karshe tunanin da suke yi mana na cewa yunwar 'yan kwanaki zata sa mu koma bakin aikinmu da wuraren sana'armu, to reshe zai juye da mujiya. Zasu zo suna rokon kowa ya dawo aikinsa, sun dawo da man fetur din yadda muke so N65. Mu kuma anan zamu sanar da abubuwan da ke cikin zociyoyinmu na irin bakin mulkin zalincin da suke shinfida mana, idan zasu gyara mu dawo bakin aiyukanmu, idan kuma ba zasu gyara ba to su sauka su bamu mulkinmu, muma zamu iya tafiyar da kasarmu yadda muke bukata.

Na bada damar kwafar wannan rubutu don aikawa sauran 'yan uwa jagororin gwagwarmayar neman 'yanci.

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Saturday, January 14, 2012

Yau ma Gwamnati da NLC/TUC basu cimma matsaya guda ba. Yajin Aiki da Zanga Zanga zasu ci gaba Ranar Litinin

Yau ma kamar ranar Alhamis kungiyar Kwadago (NLC) da kungiyar 'Yan kasuwa (TUC) ba su cimma matsaya guda ba a zaman da sukayi da jami'an gwamnatin tarayya akan janye tallafin man fetur da gwamnati tayi da kuma yajin aikin gama gari da kungiyoyin suka kira tun ranar Litinin da ta gabata.

A halin yanzu bamu samu labarin yadda zaman ya kasance ba, amma wani jami'in kungiyar Kwadago ya sanarwa yan jarida cewa yajin aiki da zanga zanga zai ci gaba a ranar Litinin bayan tafiya hutun kwana biyu da akayi domin bada dama ga jama'a su sake shiri. Wannan yana nuna lalle zaman ba'ayi nasara ba.

A yammacin wannan rana ma dai kungiyar PENGASSON mai hakar man fetur ta bada sanarwar tafiya yajin aiki a daren ranar Lahadi idan har gwamnati basu daidai ta da 'yan Kwadagon ba.

Thursday, January 12, 2012

Ba'a samu matsaya guda ba tsakanin Gwamnati da 'Yan Kwadago

Zaman da shugabannin 'yan kwadago (NLC) da shugabannin 'yan kasuwa (TUC) da sukayi jami'an gwamnatin tarayya akan tattauwa game da janye tallafin man fetur, da yajin aikin da ma'aikatan kasar nan suka tafi, ba'a samu wata matsaya guda daya ba.

Zaman anyi shine a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja (Aso Rock) tun da misalin 5:30 na yammacin wannan rana har zuwa misalin 10:00 na dare, wanda ya hada shugabannin majalissun kasar nan ta dattijai da wakilai (Senates and Reps) da kuma ministar kudi Mrs Ngozi Okunjo-Iweala.

Shugaba Goodluck Jonathan da mataimakinsa Muhammad Namadi Sambo sun bar dakin taro jin kadan da isowar shugaban 'yan kwadago Alhaji Abdulwaheed Omar da takwaransa na kungiyar 'yan kasuwa. Amma shugaban da mataimakin nasa sun sake dawowa dakin tattaunawar awa daya kafin tashi daga tattaunawar.

Za'a sake zama wannan tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan kwadagon a ranar Asabar da misalin 10:00 na safe, a fadar mulkin ta gwamnatin tarayya. Bayan fitowa daga tattaunawar shugaban 'yan kwadago Alhaji Abdulwaheed Omar yace yajin aikin da ma'aikata suka tafi zai ci gaba kamar yadda aka tsara.

Tuesday, January 10, 2012

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar yawo na tsawo awa Ashirin da Hudu

Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin gwamna Patrick Ibrahim Yakowa, ta bada dokar hana yawo ga al'ummar birnin jihar da kewaye na tsawon awa 24.

Gwamnatin ta sa wannan doka ne saboda masu zanga - zangar nuna kin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi, suna neman karya doka da oda a cewar Patrick Yakowa.

Shugabannin 'yan kwadago na jihar ta Kaduna wadanda suke jagorantar zanga - zangar, su ma sun sanar da dakatar da zanga - zangar zuwa wani lokaci, amma sun bayyana cewa yajin aiki yana nan daram har sai gwamnatin tarayya sun janye kudirinta na janye tallafin man fetur din.

@thisdaynews

Monday, January 9, 2012

BAN MUTU BA - BASHIR AHMAD

A ranar 9/1/2012 wanda aka yiwa lakabi da ranar 'YANCI, miliyoyin al'ummar Nijeriya, suka fita zanga - zangar lumana, domin neman 'yanci da nunawa gwamnati da sauran al'ummar duniya, kin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnatin tayi a farkon shekarar nan.

Ni ma da sauran al'ummar Kano manya da yara mun fita kwammu da kwarkwatarmu. A wannan fita da mukayi mun tafi rukuni guda daga unguwarmu, inda muka hadu da daliban Jami'ar Bayero dake Kano muka tafi tare dasu, munyi tafiyar sama da 10km a kafafuwanmu zuwa dandalin 'yanci (Liberation Square) wanda aka fi sani da Silver Jubilee.

Allah mai iko! A cikin wannan tawaga tamu jami'an tsaro suka harbi dan uwanmu, kuma Allah ya dauki ranshi jin kadan bayan kai shi asibiti. A daidai lokacin da abin ya faru banyi kasa a gwiwa ba na aikawa 'yan uwana da abokaina na shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter, wanda cikin dan lokaci kalilan jama'a suka fara aiko min da sakonnin ta'aziyya da kuma addu'ar Allah ya kare mu.

Wannan sako dana aika Facebook da Twitter ba karamin rudani ya jefa wasu daga cikin 'yan uwa da abokaina ba, inda wani daga cikin abokina ya yiwa sakon nawa gurguwar fahimta, inda shi ma ya aikawa abokansa cewa "Bashir Ahmad ya rasu a wurin zanga - zanga" wasu daga cikin wadanda suka ga sakon dana aika, sai suka ce "ai ba shi ne ya rasu ba dan uwansa ne" wasu kuma suka ce "ai bayan an kashe dan uwan nasa shi ma an kashe shi" haka dai akai tayin muhawara akan na mutu ko ban mutu ba.

Abinda ya kara tsorata mafi yawancin abokaina sun kira wayata sun samu wayar a kashe, kuma sun kasa samun wanda zai tabbatar musu da cewa ban rasu ba. Dalilin rashin samu na a waya da ba'ayi ba, haka ya faru ne sakamakon chaji daya kare kuma ina cikin gungun masu zanga - zanga don haka ban samu damar sa chaji ba.

Bayan komawa ta gida da misalin 4:45pm ina kunna wayata sai ga kira daga wasu a cikin abokaina suna tambaya "shin Bashir Ahmad ne akan layi?" bayan tabbatar musu da cewa eh ni ne, sai suka sanar dani halin dake faruwa akan jita - jitar da ake yi akan na rasu, kuma suka bukaci dana koma shafin Facebook da Twitter na sanar da cewa ba ni ne na rasu ba.

Ba tare da bata lokaci ba, na shiga wadannan shafuka na sanarwa da 'yan uwa da abokan arziki ina nan da rai na, ban rasu ba. Nan ma dai abokan nawa suka rinka aiko min da sakonni Allah ya kiyaye kuma Allah ya kara nisan kwana.

A karshe ni mika godiyata ga duk wadanda suka nuna kulawa, damuwa da soyayyarsu a gare ni, musamman wadanda suka kira ni waya ko suka aiko min da sakonni. Nagode! Nagode!! Nagode!!!

Sunday, January 8, 2012

KUNGIYOYI ZASU TAFI YAJIN AIKI TARE DA GABATAR DA ZANGA - ZANGAR LUMANA

Kungiyar kwadago ta kasa NLC da kungiyar 'yan kasuwa TUC da kungiyar malam jami'o'i ASUU da kungiyar dalibai SUG da kungiyar lauyoyi NBA da kungiyar Muryar Talakawan Nigeriya da kungiyar gamayyar kungiyar UNG da sauran daruruwan kungiyoyi masu zaman kansu wadanda bana gwamnati ba, sun kira yajin aikin gama gari tare da zanga - zangar lumana mai taken (OccupyNigeria) a fadin kasar nan baki daya, domin nuna kin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnati tayi, wanda aka zartar a ranar sabuwar shekarar nan ta 2012.

Shugabannin wadannan kungiyoyi da zasu jagoranci zanga - zangar da yajin aikin, sun bayyana cewa zasu tafi wannan yajin aiki ne da kuma zanga - zanga saboda kuncin rayuwar da talakawan Nigeria wanda sune kaso 80% na yawan al'ummar kasar, zasu shiga idan har gwamnati bata dawo da tallafin man fetur da take badawa ba.

Za'ayi wannan yajin aiki ne da zanga - zangar a ranar Litinin 9/1/2012 a daukakin fadin tarayyar Nigeria. Sannan jagororin wannan zanga - zanga sun gargadi mutane da tada zaune tsaye, ko kuma jifan jami'an tsaro da yi musu ihu.

A karshe muna addu'ar Allah yasa wannan yajin aiki da zanga - zanga da za'ayi yasa shine silar daidaituwar al'amura a Nigeria.

OccupyNigeria!!!

Friday, January 6, 2012

TASIRIN SHAFUKAN YANAR GIZO A SIYASAR WANNAN DUNIYA

Shafukan Yanar Gizo musamman shafukan sada zumunta da yin abokanta (Social Networks) irinsu Facebook, Twitter, Yahoo Messanger, Gtalk, Live Messanger, MySpace da sauransu, ba karamin sauyi suka kawo ba, a siyasar duniya a wannan karni 21 da muke ciki.

Wadannan shafukan sun kawo sauki ga siyasar da kuma 'yan siyasar, ta irin wadannan shafuka 'yan siyasa ke samun damar aikawa da sakonninsu zuwa ga al'umma domin neman goyan bayan su cikin kankanin lokaci, kuma sakonnin su samu isa inda aka aika su ba tare da jin kiri ko tsaye - tsaye ba.

Haka zalika bayan aika sakonnin neman goyan baya da 'yan siyasa ke yi kai tsaye ga al'umma, suna samun martanin sakonnin da suka aika, na amincewa ko akasin hakan, ta haka ne 'yan siyasa masu dabara ke yiwa abokannan hamayyarsu fin cin kauuu.

Anan zan dauki shafin sada zumunta na Facebook nayi misali dashi saboda kasancewarsa shafin da 'yan siyasar duniya suka fi amfani dashi wurin aika sakonnin nasu. Saboda shafin ne suke ganin ya fi hada mutane daban - daban na sassan duniya da dunkule su wuri daya. Kamar yadda Mark Zuckerberg wanda ya kirkiro shafin ya dauki alwashin tattara al'ummar duniya da dunkule su wuri guda, wanda kuma zamu iya cewa lalle ya dauki hanya, idan mukayi la'akari da yadda mutane daga kowane bangare na duniya ke kulla abota da sada zumunta a shafin, kamar suna tare da juna.

A wannan misali da zan kawo zan dauki wasu manya - manyan 'yan siyasar duniya na bada misalin dasu. Akwai Shugaba Barrack Obama na kasar America, yayi amfani da shafin Facebook wurin tallata kansa da irin manufofinsa ga al'ummar America da sauran al'ummar duniya baki daya, yayi hakan a lokacin yakin neman zabensa don zama shugaban na America, haka saboda ganin alfanun yin hakan, a wannan yakin neman zarcewa da yake muradin yi a wannan shekara 2012, ya dauki shafin na Facebook a matsayin rukukin farko, sahun gaba wurin yakin neman zaben nasa, ta nan yake aikawa magoya bayansa da masu adawa dashi abinda zai yi musu idan suka sake amincewa dashi ya koma kan kujerarsa.

Haka shugaba David Cameron na kasar England, yayi a lokacin nasa yakin neman zaben har yakai ga yin nasara.

Kamar yadda wannan shafi na Facebook yayi silar darewar wasu shugabanni gadajen mulki, ta wani bangare kuma shafin yayi silar tumbuke wasu shugabanni daga kan gadajen mulkinsu, kamar Shugabannin wasu daga cikin kasashen arewacin Africa (Egypt, Tunisia, Libya) wannan shafi ba karamin gudunmawa ya bada ba, wurin saukar da wadannan shugabannin kasashe, saboda kuwa ta shafin ne jagororin da suka jagoranci tumbuke shugabannin suka rinka aikawa da sakonni ga matasan kasashen, da kuma sanar da al'ummar duniya halin da suke ciki da kuma irin nasarorin da suke samu.

To muma nan Nigeria ba'a bar manya - manyan 'yan siyasarmu a baya ba, shi kansa mai gayya mai aikin wato shugaba Jonathan Goodluck yayi amfani da irin wannan dabara, haka babban abokin hamayyarsa General Muhammad Buhari. Da sauran wadanda sukayi takarar zama shugaban kasa a 2011 kamar Nuhu Ribadu da Malam Ibrahim Shekarau.

Kamar yadda bahaushe yace tun sassafe ake kama fara, tun yanzu wasu daga cikin masu muradin mulkar kasar nan a zaben 2015, ko nace magoya bayansu sun fara bayyana aniyarsu a shafin na Facebook. Kadan daga cikin sun hada da Senator Ahmad Sani Yariman Bakura (Yarima Vision 2015), Malam Ibrahim Shekarau (Tsangayar Masoya Sardaunan Kano), Atiku Abubakar (Atiku Abubakar 2015) sai Muhammad Namadi Sambo (Sambo 2015)

Haka ma wasu magoya bayan Gen. Buhari na da nasu shafin (Buhariyya & Gen. Muhammad Buhari Suppoters' Group) da sauran ire - iren wadannan shafuka a dandalin na Facebook.

A karshe ina fatan matasan Nigeria za muyi amfani da wannan dama wurin tantance aya a cikin tsakuwa, wato lokacin zabe mai zuwa mu tattara manufar kowane dan takara mu auna ta a sikelin tunani wanda yayi rinjaye muyi masa ruwan kuri'unmu, sannan Mu kasa, mu tsare, mu raka, mu jiraci sakamako, ba don komai ba sai don ceto kasarmu daga lalurar mutuwa dake kokarin kama ta.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

Thursday, January 5, 2012

NEMAN 'YANCI BANA RAGO BANE

HAUSAWA wata kabila ce ta daban, wadda Allah ya bata kaifin basira da hasken nesa, ba komai yasa na fadi haka ba, sai tuno wata magana da Hausawan suka dade suna fada wato "NEMAN 'YANCI BANA RAGO BANE" zahiri wannan magana haka take, kuma na tabbatar da hakan da kaina.

Sanin kowane tun ranar da mahukuntan kasar nan suka sanar da kudirinsu na janye tallafin man fetur, al'ummar kasar suka daura haramin zanga - zangar nuna kin jin wannan kudiri, saboda kuwa talaka ne zai kara kuntata da shan wahala bayan wadda yake sha. Hakan ce tasa matasan Kanon dabo musamman daliban manyan makarantu su ma suka fito don nuna rashin goyan baya.

To saboda irin kishin kasa da kishin talaka da yake kunshe cikin zuciyata, yasa banyi kasa a gwiwa ba na shiga cikin wadannan matasa da suka yi dandazo a filin Silver Jubilee Square wannan matasan suka canzawa suna zuwa Liberation Square wato Dandalin 'yanci, wanda yake bai fi nisan kilo mita daya ba zuwa fadar gwamnatin jihar Kano daga gabas daga yamma kuma zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Mun fara wannan zanga - zangar 'yancin ne tun da sayin safiyar ranar Laraba 04/1/2012 wanda muka shafe yinin ranar har zuwa dare ba tare da mun bar motoci suna zirga - zirga ba, a dai - dai wurin da muka mamaye, su kuwa jami'an tsaro sun zuba mana na mujiya gami da kange duk wata hanya da zata sada mu da fadar gwamnatin jihar. Wani abin sha'awa a wannan rana idan lokacin sallah yayi kowa zaiyi alwala sannan a samu liman ya ja sahu mu gabatar da sallah, su kuma wadanda ba mabiya addinin Musulunci ba, suna tsaye suna jiranmu har sai mun idar da sallah.

A haka har dare yayi dare can da misalin 1:45 zuwa 2:00 lokacin babu kowa daga mu sai jami'an tsaro, kawai ba zato ba tsammani sai muka ji ruwan barkonon zuwa (Tear Gas) ganin haka yasa muka ga ya kamata mu maida martani tunda kuwa muna yin wannan zanga - zanga ne ta lumana ba tare da tashin hankali ba. Nan muka fara jifan jami'an tsaron da duwatsu da kuma Pure Water, ganin haka sai suka fara danno mu suna kara har ba mana barkonon tsohuwa, ana haka ana haka, muka samu nasarar fasa musu gilas din motarsu. To fa daga nan sai suka fara harbe - harbe sama, wannan harbe - harbe shi yasa muka karaya muka fara gudun ceton rai, saboda sanin jami'an Nijeriya basu san darajar dan Adam ba.

A karshe dai jami'an tsaron sun samu nasara akanmu, inda suka tarwatsa mu, kowa ya nemi wurin da zai fake don gudun rasa ransa. Wasu daga cikinmu sunji munanan raunuka, wasu kuma sun kwana a tsaye ba tare da kwanciya ko yin bacci ba. Ni dai nayi sa'ar samun mafaka a gidansu wani abokina a Unguwar Kabara.

Ina fatan wannan ba zai sa zuciyoyinmu su karaya ba, zahiri NEMAN 'YANCI BANA RAGO BANE.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160