Wednesday, October 30, 2013

Hausawa ‘Yan Zamani Ga Dama Ta SamuWakokin Zazzabi da Ala
Ina Hausawa ‘yan kwalisa da suke son tafiya da zamani ga dama ta samu, yanzu za ku iya burge masu kiranku a waya da wakokin Aminu Ala da Sadiq Zazzabi. Kamar sauran wakokin turanci ko na Indiyawa, su ma wadannan mawaka sun shiga jerin takwarinsu na duniya.

Domin samu wakokin a wayoyin na ku aika CODES din wakokin da suka burge ku dake kasa zuwa 4100 a layukanku na MTN.

WAKOKIN AMINU ALA 

033027 Jamia - Aminu Ala
033028 Angara - Aminu Ala 
033029 Jamia lakcara - Aminu Ala 
033031 Daurin gwarmai - Aminu Ala 
033032 Rayuwa aduniya - Aminu Ala 
033033 Hasbunallahu - Aminu Ala 
033034 Gambiza - Aminu Ala
033030 Adali – Aminu Ala

WAKOKIN SADIQ ZAZZABI

033093 Aikin Lawyers - Sadiq Zazzabi
033094 Amina Namadi Sambo - Sadiq Zazzabi
033095 Baka Gane Mai Sonka Sai Babu - Sadiq Zazzabi
033096 Baza SuIyada kaiba - Sadiq Zazzabi
033097 Dalilin Dayasa Nak Son Aure - Sadiq Zazzabi
033098 Iyayene basaso - Sadiq Zazzabi
033099 Jamiar Bayero - Sadiq Zazzabi
033102 Sarkin Gombe - Sadiq Zazzabi
033103 ShaKallo - Sadiq Zazzabi
033104 Sun yi rabo bandani - Sadiq Zazzabi
033105 Talgen Makauniya - Sadiq Zazzabi

Don samun CODES na wadannan wakoki a layukan Etisalat ko Airtel sai a ziyarci BILKYAK CONSULTING

Friday, October 25, 2013

Yadda Biyayya Ta Kai Dingyadi Saman Karagar Babbar Sarauta

Yusuf Dingyadi (Magayakin Garkuwa)
Daga, Sharafaddeen Sidi Umar, Sokoto

Ko tababa babu a duniyar aikin jarida Malam Yusuf Dingyadi ba ya bukatar ko wace irin gabatarwa, kamar kuma yadda ya shige kan gaba a fagen rubutu da marubuta tare da zama fitacce a haujin siyasar yau a hobbasarsa ta ganin an samar da kyakkyawan shugabaci a tarayyar Nijeriya bayan gurbacewar lamurra a tafin hannun shugaba Goodluck Jonathan.

Kwararre ne da ke da kwarewa da gogewa a aikin da ya fi iyawa, wayo da lakanta, hasalima shekaru da dama zuwa yau akwai masu ra'ayin a aikin jarida Dingyadi ya yi wa tsara ratar da sai dai su biyo sahu, domin ko ba komai caran da zakaransa ya yi an jiwo amonsa a ko'ina.

Wadanda suka san shi, da wadanda suka kusance shi da wadanda suka yi hulda da shi sun bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa tare da juriya da naci da sadaukar da kai domin ganin an samu biyan bukatar da ake bukata a lokacin da ake bukata ba tare da rashin biyan bukata ya rinjayi bukatar da ake bukata ba.

Haka ma shekarunsa na rayuwa, shekaru ne da ya rayu rayuwa tagari, rayuwa abin muradi kuma rayuwar Allah-sam barka ta yadda aka shaide shi da biyayya ga magabata da mutunta tsara da kuma zama lafiya da matasa. A daya gefen tare da kasancewa a bisa alkiblar da yake ganin ita ce mafi a'ala kuma mafi dacewa a gareshi da sauran al'umma ba tare da kaucewa alkiblar ba, duk kuwa da bukatar wasu ta son ganin ya kaucewa inda ya dosa.

A haka jama'a da dama ba su yi mamaki ba yayin da Garkuwan Daular Usmaniyya, Dakta Attahiru Dalhatu Usman Bafarawa ya aminta da nadin mashawarcinsa ta fuskar aikin jarida a matsayin Magayakinsa wato Magayakin Garkuwa, wanda zai shige kan gaba wajen kariyar ko wace irin arangama da artabun da aka kai ko ake shirin kaiwa Garkuwa a fagen fama kamar kuma yadda zai zamo Magayakinsa ta fuskar rungumar kowace irin kwaramniyar murhun siyasa a yau da gobe. Kari da karau Magayakinsa a aikin jarida. Yayin da shi kuwa Garkuwa zai ci gaba da aikinsa na kariyar Katafariyar Masarautar Daular Usmaniyya da dukkan karfinsa.

Kamar dai yadda aka sani marigayi Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido (Allah ya lullube shi da bargon Rahama) ne ya nada Attahiru Bafarawa a saman sarautar Garkuwan Daular Usmaniyya a farko-farkon hawansa kan karaga. Shi kuwa daga baya ya nada wasu mutanensa a sarautu daban-daban a matsayin Sarakunan Garkuwa.

Haduwa Da Bafarawa:

A tattaunawar musamman da ya yi da wannan marubucin, Dingyadi ya bayyana cewar duk da cewar duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan ya san da zaman Bafarawa, amma bai samu sa'ar fara hulda da shi ba sai a 1987, a lokacin da Bafarawa ya kara yin fice wajen taimakawa al'umma musamman a kungiyance a lokacin da yake jagorantar "Bafarawa social club". dan jaridar ya ce "Mun shaku da Bafarawa sosai a 1993, hasalima daga lokacin har zuwa lokacin dawowar mulkin siyasa muna tare duk da cewa ba mu taba siyasa tare ba sai a 2007." Ya kara da cewar "Ina matukar farin ciki sosai da a yau Garkuwa ya bani wannan sarautar ta Magayakinsa.

Kima Da Tasirin Bafarawa:

Magayayakin Garkuwa ya bayyana Bafarawa a matsayin nagartaccen basarake kuma dan gwagwarmayar siyasar cigaban al'umma wanda a jiya da yau hidimar al'umma ya sa a gaba. Ya kuma ce Garkuwan Sakkwato "Dattijo ne a magana kuma dattijo ne a kowane irin lamari, domin a bayyane yake bai taba sa kansa a kowane irin lamari na ba daidai ba. A lura Garkuwa bai sa kansa a lamarin sabon Allah, kuma bai sa kansa a wajen cutar jama'a, illa iyaka ya kan sa kansa a duk wata harka da za ta amfani jama'a. Kazalika mutum ne wanda ya san daraja da ciwon wadanda yake tare da su. Baya ga wannan mutum ne mai son aiwatar da gaskiya tare da taimakon marasa gata." Ya bayyana.

Ayyuka Da Tattaki A Cikin Tarihi:

Tattaki a cikin tarihi za a ga Yusuf Abubakar Dingyadi ya zo duniya shekaru 40 da suka gabata a Kwalfa da ke Gundumar Dingyadi a karamar hukumar mulkin Bodinga. Bayan karatun addinin Musulunci a shekarunsa na farko, ya samu kansa a karatun boko domin samun gishirin zaman duniya ta yadda a yau ya ke da muhimman takardun ilimi.

Bisa ga sha'awar da yake da ita ta aikin yada labarai, Dingyadi ya fara aikin jarida a Mujallar Zuma mallakar Umaru Dembo a 1991. Ya kuma yi aiki da mujallar Nasiha a 1992-1993, daga baya kuma ya rika aikawa da labarai a mujallar Sentinel a Kaduna gabanin ya samu matsugunni a Democrat.

Likkafar Dingyadi ta yi gaba a yayin da sashen Hausa na gidan radiyon BBC ya yabawa kwarewa da gogewarsa wadda ta zama silar daukarsa aiki a BBC a shekarar 1994, a matsayin wakilin gidan radiyon da ake aika labarai daga tshohuwar jihar Sakkwato da Kabi da Katsina da kuma wani bangare na Jamhuriyar Nijar.

Bayan barin BBC Hausa, Dingyadi ya zama karamin daraktan yada labarai na yakin neman zaben Obasanjo da Atiku a 1999. Bayan samun nasarar lashe zabe ya zama mataimaki na musamman (P.A) ga Ministan sadarwa, Alhaji Arzika Tambuwal, kamar kuma yadda ya zama mataimaki na musamman ga Jakada Ladan Abdullahi Shuni a matsayin mai kula da kididdigar 'yan Nijeriya da ke shiga birnin Casablanca daga kasar Morocco. Ya kuma yi aiki a matsayin mataimaki na musamman kan aikin jarida ga marigayi Garba Koko Sarkin Yakin Gwandu a lokacin da yake a matsayin shugaban jam'iyyar SDP na jiha da kuma lokacin da yake a matsayin shugaban makarantar horas da ma'aikata (ASCON) da ke Lagas.

Dingyadi wanda a yanzu haka jami'in tuntuba ne kan yada labarai ga hukumar bayar da ilimi bai daya ta jihar Zamfara (ZSUBEB); wasu ayyukan da ya yi a baya su ne; mataimakin daraktan yada labarai na jam'iyyar SDP a bangaren matasa, da daraktan yada labarai na jam'iyyar DPN duka a jihar Sakkwato, da kuma sakataren kwamitin G-15, wadanda suka yi fafatukar ganin Sule Lamido ya zama Gwamnan jihar Jigawa a 2007. Haka kuma ya rike mukamin daraktan yada labarai na yankin Arewa na dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar DPP a 2007.

Daga 2007 zuwa yau Dingyadi shi ne sakataren kungiyar marubuta ta kasa (ANA) reshen jihar Sakkwato, haka ma shi ne mataimakin shugaban kungiyar matasan marubutan Arewa wadda Farfesa Yusuf Adamu na jami'ar Bayero ke jagoranta. Haka ma jami'in tuntuba ne ta fuskar yada labarai ga Majalisar Tarayya ta shida da ta bakwa da ke wakiltar al'ummar kasa a yau, haka kuma yana daga cikin jami'an tuntuba ga kungiyar mataimakan 'yan majalisar tarayya ta kasa reshen jihar Sakkwato.

Hidimar Al'umma:

Haka ma a fili yake cewar Dingyadi wanda yayi takarar kujerar dan majalisar dokokin jihar Sakkwato a tutar ACN domin wakiltar mazabar Bodinga ta Yamma a 2011, za a ga wasu daga cikin kwamitocin da ya yi wa hidima a matsayin manba sun hada da: Kwamitin rubuta manufofi da tsarin mulkin jam'iyyar PDP a 1998, da manba a kwamitin samarwa 'yan asalin jihar Sakkwato aiki a Gwamnatin tarayya daga 2000-2004 da kuma manba a kwamitin gyara tsarin mulkin kungiyar marubuta ta kasa (ANA) a 2008 da kuma manba a kwamitin sake mayar da alkibla da darajar Arewa wanda kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta kafa a 2006 da kuma manba a kwamitin sake daidaitawa da gyara koma]ar sha'anin ilimin furamare a jihar Zamfara (ZSPEAC) da kuma manba a kwamitin shirya taron marubutan Arewa wanda a ka gudanar a Kabi 2013.

Bugu da kari Dingyadi ya samu mabanbantan karramawa da lambobin girmamawa da dama kamar kuma yadda kamfaninsa na Dingyadi Media ya taka rawar gani. Kadan daga ciki su ne; karramawa a matsayin dalibi mafi hazaka wajen karanta labaran safe da kuma gwarzon dalibi wajen samar da ingantaccen tafarki a cikin Hakiman makaranta duka a kwalejin Sarkin Musulmi Abubakar III.

Haka ma ya samu lambar yabon wakilin jarida wanda ya tserewa abokan aiki wajen aika labarai daga Arewa a Mujallar Nasiha. "Ka yi mun gani mun shaida" hakan ce ta tabbata yayin da sadaukar da kai wajen aiki ta kai Dingyadi ga samun lambobin yabo har guda biyu a zamansa a gidan radiyon BBC. Na farko a matsayin wakilin BBC wanda ya fi kowa samun labarai a lokacin da suke faruwa, da kuma dan jarida mafi aika labarai da dumi-duminsu a gidan radiyon BBC. Baya ga wannan Dingyadi ya kuma zama dan jarida mafi kwarewa a kafafen yada labarai na waje daga Arewa maso Yamma a karramawar da aka gudanar a birnin Accra kasar Ghana a 2003.

Kamfaninsa Dingyadi Media na tuntuba kan aikin jarida da yake jagoranta ya samu lambobin yabo a matsayin gwarzon kamfanin yada labarai daga sashen nazarin Hausa a jami'o'in Bayero da ke Kano da kuma Danfodiyo da ke Sakkwato, tare kuma da karramawa daga Mujallar Beacon wadda ake bugawa a jami'ar Bayero. Baya ga wannan manba ne a sama da kungiyoyi 20; daga ciki akwai Dandalin Siyasa na duniyar gizo da majalisar Burin Zuciya da ke cikin LEADERSHIP Hausa.

Littaffai:

Littaffan da alkalamin Dingyadi ya rubuta sun hada da: Halina da Labarina da Ina Muka Kwana? Da Dashen Masoya da Dacewar Yarima a 2003 da Barka Da Zuwa APC da sauransu da dama. Baya ga wannan akwai mukalu da sharhi da rubuce- rubucensa da dama da aka buga a jaridu da mujallun Hausa da Turanci.

Rana Ba Ta Karya:

A yayin da mabanbantan al'ummar kasa suka shirya tsaf domin amsa kiran wannan muhimmiyar sarauta wadda za a gudanar a gobe Asabar a fadar Garkuwan Sakkwato da karfe biyu na rana; abin da zai biyo baya shi ne yadda rayuwar Dingyadi za ta kasance a matsayin Basarake a gidan Sarauta ba ya ga rayuwar da yake a kai ta fitaccen dan jarida, kwararren marubuci kuma karbabben dan siyasar da ke fatar ganin gobe ta yi kyau bayan ganin jiya da yau ta lalace a mulkin mallakar shugaba Jonathan.

- BASHIR AHMAD: Ina taya Mai Girma Magayaki, murnar wannan babban matsayi, Allah ya bada lafiya da nisan kwana. Na gaida Magayakin Garkuwa, Magayakin Matasan Arewa!!!

JAMILAH TANGAZA: Babban Abu Da Ya Sosa Mani Rai

JAMILAH TANGAZA: Babban Abu Da Ya Sosa Mani Rai: Yau shekara biyu da wata uku kenan cif, rabon da na yi rubutu a wannan mattara tawa – Almajira. Na jima ne kuwa ban yi rubutun ba saboda matukar sauye-sauye na halin rayuwa ta yau da kullum.