Tuesday, March 29, 2011

ZUWAN BUHARI KANO YA BATAWA WASU RAI AMMA BANDA NI

A yau ne General Muhammad Buhari dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam'iyar CPC ya kawo ziyarar yakin neman zabensa a jihar Kano (Cibiyar Masoyansa) tabbas taro ya kai taro, har kuwa ya fice kiyastawa, idan kuwa za'a kiyasta to za'a iya cewa a kalla mutanen da suka halarci taron zasu kai kimanin Mutum million daya da rabi ko million biyu (1.5 million or 2 million). Mata da maza, yara da manya, tsofaffi da dattijai duk sun halarci wannan gangami. A zahiri tunda nake a rayuwata ban taba halartar taro mai yawan jama'a kamar na yau ba, saboda kuwa ban taba zuwa Aikin Hajj ba, duk da kuwa a jiya da daddare aka sanar da taron a gidajen radio amma mutane sun fita taryar limamin Canji.
Baba Buharin Kanawa.

Da misalin karfe 3:30 na yamma jirgin Gen. Buhari ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda mutane sama da miliyan daya suke jiran zuwansa tunda sanyin safiya, bayan da ya sauka kai tsaye aka nufi gidan Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero don gaisuwar ban girma. Saboda cunkoson mutane da gosulon motoci ba'a samu damar zuwa gidan sarki ba, sai waje 5:30 na yamma. Daga gidan sarki kuma tawagar limamin canjin ta nufi filin sukuwa ne (Polo) inda aka tanada don yin taron, nan ma saboda yawan mutane da motoci, babura da kekuna ba'a halarci wurin taron ba sai wajen 7:00 na yammaci.

To anan abin ya batawa jama'a da dama rai, wasu kuma saboda soyayya basu nuna ransu ya baci ba, amma dai sun damu sosai, dalili kuwa jama'a masoya General Buhari tun shekarar 2003 wasu basu kara ganinshi ba, domin baizo yakin neman zaben 2007. Wasu kuwa daman ma basu taba ganinshi ba, hakan tasa jama'a suka yi cincirindo don ganin Baba, wasu sun bar suna'o'insu, wasu sun bar karatunsu, sunzo tun safe don ganin wanda suke so kuma shima yake sonsu. Akwai wadanda naji suna cewa sunzo filin nan tunda 9:00 na safe. To ko ni ma dai naje wurin ne tun wajen 10:30 na rana, baci ba sha, Sallan Azhar dai na samu nayi amma La'asar, Magrib da Isha'i duk sai bayan na dawo gida nayi su, ba don komai ba kuwa sai rashin haryan fita saboda jama'ar da suka zo don ganin Buhari. A zahiri nasha wahalar da ban taba shan irin ta ba, na sha taku wurin jama'a an mammatse ni, an bubbuge ni, an tutture ni. Amma saboda nazo ne domin Babu Buhari ko kadan ban damu ba, kuma ban nuna gajiyawa ko kosawa ba.

Duk da irin wannan wahalhalu da nasha ni da sauran jama'a abin haushi bamu samu damar biyan bukatarmu ba, domin kuwa abinda muka je don gani yayi mana nisa, a takaice General Muhammad Buhari bai samu halartar zuwa wurin taron ba, saboda wasu dalilai, wasu sunce yazo wurin taro a mota amma bai fito ba, wasu kuma sunce daga gidan Sarki ya nufi wani wurin, mu dai da muke cikin wurin taro sai labari cewa yazo muka ji amma ko rigarsa bamu gani ba.

Babban abin haushin ma aka rasa wanda zai sanar da mutane da dalilin rashin zuwansa, kuma a baiwa jama'a hakurin jiran gawon shannu da suka yi. Wannan tasa jama'a da dama suka bar wurin taro suna yan surutai marassa dadi. Wai suna cewa don kar ya daga hannun Muhammad Sani Abacha dan takarar gwamnan a jihar Kano shi yasa yaki zuwa, wasu kuma sun ce jami'an tsaro suka hanashi fitowa, saboda gari ya fara duhu.

A gaskiya dai idan akan karya daga hannun Abacha yasa yaki zuwa wurin taron to tabbas wanda ya bashi shawarar yayi hakan ya zalunci mutane, domin nasan General Buhari ko yaushe mai son ganin bai batawa jama'a ba yake, sai gashi yau ko waye ya bada shawarar yasa jama'a da dama ransa ya baci saboda Buhari abinda mukam masoya bamu so ba.

Ni dai kam tabbas nima banji dadi ba, amma dai ranna bai baci ba, saboda son da nake masa yafi karfin ya bata min rai, sai ma hakuri da na rinka bawa jama'a ina nuna musu ba laifin Buhari ba ne. Wasu sun fahimci hakan wasu kuma sunki tsaiwa ma su saurare ni akan ko suna ganin ni yaro ne ko kuma ransu ne ya baci sosai oho.

A karshe ina kira da masoya Baba Buhari da mu sake juriya da jajircewa domin wannan abu muna yin sane badan kanmu ba, sai don cigaban Nijeriya da yan Nijeriyar baki daya. Allah ya amsa adu'o'inmu ya wannan lokaci ya albarkance mu da shugabanni nagari dun daga sama har kasa a kasarmu NIGERIA ameeen.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
2348032493020

No comments:

Post a Comment