Thursday, September 27, 2012

Nigeria: Zan Cika Shekaru 52 Bayan Samun 'Yancin Kai Na

Kwanaki uku ya rage na cika shekaru 52 bayan samun 'yancin kai na daga hannun turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya. Zan yi murnar zagayowar ranar ne kawai saboda ta cancanci hakan, amma ba don ina da 'yancin kan nawa ba, domin kuwa a tarihin rayuwa ta ban taba shan wahala, da rayuwa marar 'yanci ba kamar bayan samun 'yancin kan nawa da ake ikirarin wai na samu. Hmmm ta bangare na dai ba wani 'yanci da zan iya cewa na samu, sai dai samuwar rayuwar bauta da na sake samun kai na a ciki. To ku kuma 'yayana, mai za ku ce da wannan rana ta 1st October? Na san kalilan daga cikin ku suna murna da ranar har bukukuwa suke yi sakamakon zagayowarta. Amma dai bari na ji amsa daga gare ku. Shin kuna farin ciki da zagayowar ranar? Ku ziyarci Dandali Domin ba da amsoshinku.

Tuesday, September 18, 2012

Mu Kauracewa Amfani Shafin YouTube


Yan uwa ya kamata mu kauracewa amfani da shafin YouTube da rage mu'amala a shafin matambayi baya bata na Google, sakamakon kin cire video wasan kwaikwayon da aka yi isgilanci ga Fiyayyen Halitta Annabin Muhammad (SAW).

Tun bayan fitowar wannan wasan kwaikwayo a shafin na YouTube gwamnatin kasar Amurka ta umarci kamfanin Google da ya mallaki shafin na YouTube da su cire video daga shafinsu, saboda kyale shi cin zarafin mabiya addinin Musulunci ne.

Amma kamfani na Google ya kekasa kasa da cewar yin hakan ya saba dokar kare hakkin loda video na masu amfani da shafin.

Wannan dalilin ya sa wasu kasashen Musulmai suka yanke shawarar kauracewa amfani da YouTube a ranakun 20, 21 da 22 na watan Satumba da muke ciki, don nuna fushin su ga kin cire video da shafin yayi. Wanda kuma akalla Musulmai sama da miliyan 100 suna amfani da shafin a kowace rana.

To ya kamata mu ma mu shiga sahun 'yan uwanmu Musulman duniya, na kauracewa amfani da shafin a wadannan rana ku, koda kuwa akwai muhimmin aiki da za muyi a cikin sa, yin hakan ba karamin asara zai haifarwa kamfanin ba, idan kuma hakan ma suka ki yarda da bukatarmu na cire video, to sai mu dauki matakin daina amfani da shafin na dindindin, wato na har abada.

Aikawa, sauran 'yan uwa wannan sako.

Friday, September 14, 2012

Na Yi Nadamar Yin Zanga - Zangar Janye Tallafin Man Fetur


Ban taba tunanin zan yi nadamar kasancewa daya daga cikin miliyoyin jama'ar kasar nan da suka gudanar da zanga - zangar nuna rashin amincewa da kudirin gwamnatin tarayya na janye tallafin albarkatun man fetur ba, hasalima a kullum na tuna lokacin sai naji nishadi ya baibaye dukkan zuciyata koda kuwa ina cikin yanayin bakin ciki ne, kai har alfahari nake da lokacin musamman ranar da ni da wasu jajirtattun matasa muka fita shatale-talen Silver Jubilee dake tsakanin fadar masarautar Kano da fadar gwamnatin Kano da daddare da niyyar kwana a filin duk don mu nunawa duniya cewar bama goyon bayan kudirin na gwamnati, duk da bamu yi nasarar kwana a wurin ba kamar yadda muka shirya yi sakamakon jami'an tsaro da suka tarwatsa mu cikin talatainin dare da harbin harsashi da barkonon tsohowa.

Ba komai yake sani alfahari da ranar ba, sai don a tarihin Nijeriya mu kadai ne muka taba yunkurin yin hakan duk kuwa da bamu yi nasarar kwana a wurin ba. Amma duk da irin jami'an tsaron da aka jibge a Silver Jubilee a lokacin sai da washe gari jama'a suka sake fitowa nuna rashin goyon bayansu duk saboda a tunaninmu idan gwamnati ta janye tallafin man fetur din nan zamu shigo wani sabon kangi na wahalhalun rayuwa, to a karshe dai gwamnatin ba ta fasa aiwatar da kudirin na ta ba, sai dai 'yar kwaskwarima kadan da tayi masa, wadda wasu ke alakanta hakan da zanga - zangar da muka yi a sassa daban - daban na kasar nan.

Kamar yadda na fada a baya bana tunanin zan taba yin nadamar yin hakan a sauran rayuwata da ta rage, wanda nasan kuma ba za ku ga laifina ba, saboda kuwa na nuna kishin kasata da kokarin kwatowa talakawa 'yanci, wadanda wahalhalun da muke tunanin za a shiga za ta fi shafa, sai ga shi lokaci daya nadamar yin hakan ta wanzu cikin zuciyata ta hanani sukuni da jin dadin rayuwata.

Tun a ranar da tsinannun kafiran Amurka suka fito da wani yanki daga cikin wasan kwaikwayon da suka shirya mai taken Innocence of Muslims wanda suka shirya isgilanci da batancin da ba'a taba yin irin sa a tarihin duniya ba akan Annabi Muhammad (SAW) na shiga wannan nadama tawa, ba don komai ba sai a duk lokacin da na kamo gidajen television da suke nuna labaran da suka shafi duniya sai naga ba labarin da suke nunawa sai zanga - zangar da ake kan gudanarwa a kasashen larabawa sakamakon shirya wannan wasan kwaikayo, sai naga cewa shin mu menene dalilin daya sa bamu fita zanga - zangar ba domin nuna rashin amincewarmu akan fim din, saboda fita wannan zanga - zangar itace mai asali da kuma tushe ba wadda muka yi a baya ba.

Kowace kasa aka nuno za ka ga manyan malamai da attajirai sune a sahun gaba, ana kona tutar Amurka da yin tofin alatsine a gare su, a kasar Libya kuwa tun da sanyin safiya suka dauki matakin kashe jakadan Amurka dake kasar, wanda kuma shi ne karo na farko da aka taba yiwa Amurka haka, a kasar Sudan manyan jami'an gwamnatin kasar ne suka shirya zanga - zangar, haka kasar Egypt, Tunisia, Pakistan, Iran, India, Morocco, Syria da sauran kasashe masu kishin addinin Islama.

To a Nijeriya fa???

Ina malamanmu suke? Menene dalilansu nayin shiru akan wannan maganar, shin ko sun manta da cewa wannan maganar ta fi karfi a yi shiru a barta a fatar baki? Menene dalilin da zai sa su zauna a gida ba zasu fito su jagorance mu ba, mu shiga sahun miliyoyin Musulmai duniya wurin yin Allah wadai ga Amurka?

Ya Allah ka gaggauta daukar mataki mummuna akan dukkan wanda yake da hannu a cikin shirya fim din.

Tuesday, September 11, 2012

Hukuncin Wanda Yayi Kisan Kai Bisa Gangaci: Sheikh Ja'afar Mahmud Adam


Ya yan uwa musulmi, yana daga cikin manufofin shari'ar musulunci tsare rayukan bil'adama tsare jinin su, don haka ne nassoshi suka zo acikin alkurani mai girma da abin da ya inganta na hadisan manzon Allah salallahu alaihi wasallam, wadan da suke nuna haramcin jinin bil'adama mu samman dan adam musulmi.

Ubangiji ta'ala ya yi wannan bayani ta hanyar salon zance da ban da ban, ta hanyar nau'ikan magana da ban da ban, Salon zan ce na farko. Ubangiji ta'ala ya wajabta kisasi (ramuwar gayya) ga dukkan wanda ya kashe musulmi da ganganci, hukuncin sa shi ne a kashe shi, dukkan wani mutum da ya kashe musulmi da ganganci ya yi amfani da wani abu wanda ya iya zare rai, ya nufi dan uwan sa musulmi ya aiwatar da wannan makamin akan sa har ya kashe shi, to shi ma akamashi a kashe shi ko shi kadai ne, ko su da yawa ne, sai dai fa idan dangin wanda aka kashe musu dan uwan su suka ce sun yafe, zasu karbi diyya, to sai a basu diyya.

To amma idan ba hakaba hukuncin su da Ubangiji Ta'ala ya nassanta shi ne kisasi, ko da mutum daya ne, ko biyu, ko uku, ko sama da haka, sukayi taron dangi suka kashe mutum daya, kuma hakan ya tabbata, ta hanyara tabbatar da laifi a addinance, a musulunce, hukuncin su shi ne akamasu a kashe su gaba dayan su; Kamar yadda aikin Umar bin Khaddab ya nuna lokacin da wani adadi na wasu mutane suka yi taron dangi suka kashe wani mutum daya su kadai, Umar ya ce a kashesu su duka, wadansu suka yi masa inkari da cewa ya ya za a yi ace a kashe rayuka da dama bayan rai daya suka kashe, Umar ya ce wallahi inda mutanan birnin san'a za su hadu su kashe rai daya to wallahi da na kashe su gaba daya.

Hikimar hakan cikin shari'ar musulunci, shi ne in da ace ana yin kisasi ne kadai idan mutum ya kashe mutum daya za'a kashe shi, sai wanda zai yi kisan ya raba goran gayyata ga abokansa, ko yan uwansa, su je, su kashe wane, don sun san insunyi baza a kashe suba, gobe kai ma idan kana jin hashin wani sai karaba goran gayyata ga wadan da zasu taya ka fada domin kuje ku kashe wane. Wannan sai ya bayu zuwa ga hasarar rayuka, amma idan mutum biyu ko uku ko sama da haka sukayi haka aka kashe su,wannan zai sa dukkan wani da da wani ya rabawa goron gayyata cewa zaka rakani in kashe wane to bazai je ba saboda yasan idan ya aikata hakan to zai bayu zuwaga akashe shi, don haka sai rayukan mutane su zauna cikin aminci. Allah ta'ala yana cewa "lallai kuna da tabbatacciyar rayuwa a cikin kisasi matukar an tabbatar da kisasi a bankasa, wanda duk ya kashe wani da ganganci da kowanne irin dalili cikin dalilai to shi ma za'a kama shi a kashe shi" to wannan sai ya bayu zuwa ga tsare rayukan mutane, kisa ba zai yaduba a bankasa da kowanne irin dalili cikin dalilai. wannan salon magan na farko kenan.

Salon magana na biyu, Ubangiji Ta'ala ya saukar da narkon azaba da firgitarwa da rudarwa da kidimarwa ga dukkan mutumin da ya kashe mumini da ganganci yana ji yana gani sakamakon sa wutar jahannama, zai dawwama a cikin ta ubangiji ta'ala ya yi fushi da shi, ya tsine mashi, sannan yayi masa tanadin azaba maigirma. kaji irin wannan firgici, ka ji irin wannan razani, ka ji irin wannan tsawa, da ya sauka cikin suratul Nisa'i domin aja hankalinka aja hankalina kada kayi dukkan wani yunkuri na zubar da jinin dan uwanka musulmi bisa ganganci.

Salon magana na uku, Ubangiji Ta'ala ya nuna cewa duk wanda ya kashe mumini da ganganci, to baya cikin siffofin muminai nagari, wadan da ubangiji ta'ala ya jero siffofin su a cikin suratul furqan a inda Allah ta'ala yace "sune wadan da basa kiran wani tare da Allah, suna kiran Allah ne kadai dan jawo amfani ko dan ko dan dauke musu wata cuta, sannan ba sa kashe wata rai da Allah ya haramta kisan ta sai ta hanyar gaskiya da adalci”. Sannan kuma cewa mumini baya kisan kai, wannan dalili ne da yake nuna cewa idan kuna son kalmar adalci ta tabbata a kanku to kuyi iyakar kokarinku na tsare jinin yan uwan ku musulmi.

Sannan salon magana na gaba, Ubangiji ta'ala ya danka amana ko ya bayara da iko a hannu wadan da aka kashe wa dan uwa da ganganci, dangin duk wanda aka kashe bisa ganganci. Haka ya ce ya basu iko duk wanda aka kashe bisa ganganci ya bada dama ga yan uwan sa, a hannun dangin sa ko makusantan sa, wannan iko kodai su nemi a basu diyya, ko su nemi a kashe wanda da ya kashe musu dan uwansu, Allah ya basu kowacce daya daga cikin biyun nan a matsayin zabi in suka zabi na farko ya yi in suka zabi na biyu ya yi.

Bayan haka ubangiji subahanahu wata'ala, ya nuna tsare jinin mumini, tsare jinin musulmi, kare jinin dan uwanka musulmi, wannan daya ne daga cikin wasiyyoyi guda goma da Allah ya kebanci al-ummar manzon Allah dasu, wadan da suka zo a jere cikin "suratul An'am" Ya ‘yan uwa musulmi! Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam, ya labarta mana cewa dukkan wani mutum da ya kashe dan uwansa da ganganci, to za a zo dasu, ranar alkiyama sai wanda aka kashe ya rike wanda ya kashe shi, hannun sa yana kan zankonsa ya ja shi sutafi gaban Ubangiji Ta'ala ya ce ya ubangiji tambayi wane, me nayi ya kasheni? Alokacin da zai fadi haka jijiyoyin wuyan sa suna furzar da jini domin a halartowa da makshin munin hotan abin da ya akata a gidan duniya, yace tambayi wane me nayi ya kashe ni akan wanne dalili? banbancin siyasa, ko addini, ko manufa, zai ce ya ubnagiji tambayi shi me nayi ya kashe ni. Haka hadisi ya tabbata acikin Sinanu Nisa'i wanda ya ke hadisi ne sahihi.

Ya yan uwa musulmi, addinin musulunci a lokacin da yake haramta kisan kai, ba wai yana haramta zubar da jinin muminai ba kadai! a a hatta daga cikin kafirai wanda shariar musulunci ta kare masu jinin su da dukiyoyinsu, to in ya zamto dokokin Allah da ya saukar ta haramta zubar da jinin wanda bai furta kalmar shahada ba, jinin wanda ya ce Allah uku ne, wanda ya ce Uzairu Binullah! To ya ya kima da daraja da tsada ga jinin wanda ya ce ya shaida babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzan Allah ne.

Haka kuma, kafiri wanda kuka yi yarjejeniyar zaman lafiya tsahon wasu shekaru kan cewa ba za ku yaki juna ba a iya wannan sheakarun na yarjejeniya, to haramunne ka kashe daya daga cikin su ko ka kwace dukiyar sa, sai wadan da kuka yi yarjejeniyar basu rushe ko wanne irin sharadi ba na yarjejeniyar, kuma baku tallafawa wasu ko wani akan ya yake su ba. To, irin wannan, ku tsare masu alkawarin su na tsahon lokacin da kuka yi alkawarin da su, alokacin inda zaku kashe wani kafiri to wanda yayi kisan, Manzan Allah ya ce tsakanin sa da Al-jannah tshon tafiyar shekara dari biyar, haka ya bayyana acikin hadisi sahihi, ga shi kuma arne ka kashe ba musulmi ba, to ina ga dan uwanka musulmi! Ka dauki bindiga da kowanne irin dalili cikin dalilai ka rabashi da rayuwar sa, to kai kuma kayi me a bankasa? kuma mu duba muga "Al-mu'utamalun" wadan da yaki tsakanin ku da kasar su wanda akace inda daya da ga cikin su ya nemi izinin zuwa kasar ku, kuma ku ka bashi dama ya zo yayi iya ka kwanakin da zai yi, to wajibine ku tsare masa jinin sa da dukiyar sa har ya gama iyakar kwanakin da zaiyi, kuma ku yi masa rakiya har sai kunje inda zai ji ya amintu daga gare ku. Wannan ya na nuna kulawar shari’ar musulunci da dokokin Allah dangane da tsadar rayuwar biladama, ko da ya ki da aka shar’anta mana ba wai an halarta mana shi ne kawai don malalar da jinin kafirai ba, manufar shar’anta yaki ne idan kafirai suka furta kalmar shahada bisa ga zabin su sai a kyale musu jinin su, wannan tasa idan kafirai sukaki su furta kalmar shahada amma zasu shiga cikin "amman dinku" wato karkashin gwamnatinku, ku kyale su akan addinin su, baza ku kashe su ba. Ashe da manufar itace kisa to da idan amfito sai an kashe mutum koda ya yi kalmar shahada, sai ace ai anriga anfito lokaci ya kure me yasa yaki yi kafin a fito, da manufar itace kisa to da babu yadda za'a ce an samu wasu kafiran amana wadan da zasu zauna karkashin daular musulunci, kuma a tsare musu jinin su da dukiyar su ba tare da anribace su ba.

To wannan ya nuna cewa addainin musulunci addini ne da yake kare rayuwa, ba na salwantar da rayuwa bane, duk wanda dokokin addini suka ce a salwantar da rayuwarsa, to idan ka duba zaka ga babu abin da yafi dacewa sama da a salwantar da ratuwar sa, shi yasa kafirai duk kafircin su duk barnar da sukayi a bankasa, Allah ya ce idan sun tuba ta hanyar furta kalmar shahada sun bayar da zakkah, kar a kashe masu rayukansu kar a ribace su, to ina ga dan uwanka musulmi wanda ba tuba ya yi ba, dama can shi musulmi ne, bawai tuba yayi ba, yana sallah, yana zakkah, yana karatun al-qurani, da salati da istigfari gwargwadon iko, yana yi, tare da haka kace zaka rabashi da rayuwar sa da wanne dalili cikin dalilai.

Ya yan uwa dalilan da suke sanya mutane kisan kai suna da yawa, amma ga misali, yan fashi da makami wanda zasu kashe mutum don su kwace dukiyar sa sawa'un a cikin gidan sa ko akan hanya lokacin da yake tafiya a kashe shi don a kwaci dukiyar sa, to wadannan Allah ya fadi sakamakon su acikin Al-qurani hukuncin su shi ne akashe su ko a tsire su ko a yan ke musu kafar dama da hannun hagu ko kuma akore su daga kasar musulmi.

Haka kuma, ‘yan ta’adda wadan da su ba dukiyarka suke da bukata ba, rayuwarka kawai suke son dauka, saboda kawai wata manufa ta duniya da suke fatan samu, sannan da tunanin watakila kana iya zamar musu barazana wajen samun abinda suke son samu.

Wannan dai Khudba ce da Marigayi Shiekh Jafar Adam ya gabatar a masallacin Juma’a na Dorayi a lokacin da yake raye. Muna addu’ar Allah ya kai rahama gareshi, ya kyauta makwancinsa.

Shin Menene Madubi???


Madubi dai kusan duk wanda ka tambaya me ye Madubi? Zai ce maka wani abu ne da ake duba sura da shi wato zati, madubi dai kana duba shi ne yana baka zahirin zatin ka, wato yana kara tabbatar maka da cewar wannan shi ne wane. Kai tsaye zamu iya fassara ma’anar haruffan madubi kamar haka, wato MA tana nufin “Ma’auni” haruffan DUBI kuma suna nufin “Rayuwa” wannan fassara ce bisa abinda muka fahimta.

Menene Madubi? Madubi dai zamu iya cewa wani irin sinadari ne wanda ake sarrafa shi ta hanyar wasu abubuwa da ake samu misali akwai mudubin da ake kira Plane glass wanda bai da zane wato mai ruwan Garau Garau, sannan akwai madubi wanda ake kira Curves glass wato mai zane ko wanda aka yabe bayansa da wani abu, madubi an samoshi sama da shekaru miliyan daya da dari biyar da suka gabata.

Madubi dai yana baka hoton rayuwarka ne ta zahiri wadda kake acikinta. Lallai idan ka tsaya ka nutsu zaka samu cewa madubi yana baka hoton irin yadda rayuwarka ta ke, kuma madubi yana gaya maka waye kai, misali Baki, fari, gajere, dogo, kyakykyawa, mummuna da sauransu wannan shi ne kai tsaye abinda madubi yake gaya maka game da kanka.

Madubi yana tarkato Dukkan abinda yake iya kaiwa gareshi. Wato a fakaice yana gaya maka waye kai? Ina zaka? Me zaka yi? Hakika Madubi yana yin isharori da yawa izuwa gareka, amma mai hankali da lura ne kadai yake ganewa. Idan ka dauki misali madubin gefen mota, yana yi maka ishara ne da abinda yake wajen wato ina zaka je, ka kusa zuwa ko ka wuce, ko zaka fada wani wajen da bai kamata ba. Ka dauki kuma madubin mota da yake a gaba wato saman kurar mai tuka mota, yana dauko hoton abinda yake baya ne yake isar da shi zuwa ga matukin motar nan. To shakka babu haka madubi yake a cikin rayuwa, ba wai kawai yana nuna maka cewa kai wane ka yi kyau ko baka yi kyau ba a’a yana baka labarin rayuwar da ta gabata a gareka da kuma wadda zata zo nan gaba, domin idan ka tsaya tsaf ka kalli kanka sai kaga da fa ba haka nake ba, amma yanzu gashi nayi kaza da kaza.

Idan ka yi sa’a kai kadai ne a cikin daki, kuma ka dauki madubi ka duba fuskarka me ne yake fara zuwa ranka? Wani ya yi murmushi, wani ya yi sigina wa kansa, wani watakila har gwalo yake yiwa kansa, duk saboda ya samu damar ganin aininhin zatinsa a zahiri. A lokacin da ka kalli Madubi ka tambayi kanka da babu madubi duk wannan abubuwan da ke jikinka da madubi kan sada su da idanuwanka baza ka samu damar ganinsu ba. Madubi wani jakada ne a gareka da yake baka sakon izna zuwa gareka cewa lallai fa ka shiryawa mai aukuwa a gareka, domin kai matafiyi ne ba mazauni ba, kamar yadda wata mawakiya ta ke cewa “rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba’a yiba” shakka babu wannan haka yake, domin da za’a dauki Madubi a haska sai a hango ga wane can ya tafi, haka nan za’a yi ta wucewa kamar ba’a rayu a wannan duniyar ba.

Lallai mu tsaya tsaf mu lura da irin abinda madubi yake nusar da mu izuwa gareshi. Lallai ka duba rayuwarka ta baya ka ga me ye abinda ka aikata na kuskure ka gyara sannan kuma, ka duba abinda ya kamata ka yi a gaba. Kukan kurciya . . .

Wannan bayani ne wanda dan uwana Auwalu Adamu Tahir Sabon Gida ya taba gabatarwa, ni kuma naga dacewar na yi masa ta’alika na kawo muku.

Daga Mallam Yasir Ramadan Gwale

Tuesday, September 4, 2012

Mallam Nasiru el-Rufai: Dangajere Kusar Yaki!


Kamar yadda tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya taba fada a wata hira da ya yi da Jaridar This Day, cewar tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya buka ce shi da ya zabo masa mutum mai jini a jika kuma wanda ba shi da tsoro, wanda idan ma ta kama zai iya yin akuya ga mahaifiyar obasanjon don ya bashi mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja saboda ya dai-daitawa mutane sahu daga karkacewar da ya yi. Atiku ya shaidawa Obsanjo cewar Nasan wasu mutane guda biyu abokai da Allah bai sanya sun taba hada hanya da tsoron wani mahaluki ba a fadin tarayyar kasar nan, daya daga cikinsu kuwa shi ne Nasiru el-Rufai, wanda a lokacin shine shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnati ta kasa (Director General Bureau of Public Enterprises (BPE) and the Secretary of the National Council of Privatisation).

Tabbas Mallam Nasiru el-Rufai ya nuna cewar shi ba matsoraci bane, lokacin da majalisa ta zo tantance shi a matsayin mutumin da za’a nada minister. Domin idan zamu iya tunawa anyi dauki babu dadi da el-Rufai kafin a nada shi minister, inda aka nemi ya bayar da cin-hanci shi kuma ya yi kememe ya ki bayarwa, wanda wannan ta sanya wasu da yawa daga cikin shugabannin majalisa a wancan lokacin jin kunya ciki kuwa harda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Nasir Ibrahim Mantu, inda el-Rufai ya bayyana a majalisa dauke da al-qur’ani a hannunsa ya yi rantsuwa cewar an nemi hanci daga wajensa, kuma shi Mantu ya karyata, inda el-Rufai ya bukaci Mantu shima da ya rantse da Al-qur’ani amma hakan ta gagara inda ya ce shifa bashi da tsarki duk kuwa da cewar akwai makewayi a majalisar, kusan zamu iya cewa tun a wannan lokacin el-Rufai ya nuna jarumtaka da tabbatarwa da duniya cewar shifa ba mutumin banza bane. Wannan namijin kokari da bajinta da el-Rufai ya nuna, shi ya sa jihar Georgia da ke kasar Amerika ta bashi izinin zama dan wannan jihar, wanda yanzu haka el-Rufai yana daga cikin ‘yan Najeriya da suke zuwa kasar Amerika ba tare da anyi musu binciken kwakwaf ba.

Lokacin da Mallam Nasiru el-Rufai ya zama babban ministan babban birnin tarayya ya nuna babu sani babu sabo. Domin ya kau-da duk wasu gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba, ciki kuwa harda gidan matar shugaban kasa marigayiya Stella Obasanjo da gidan shugaban PDP na wannan lokacin Sanata Amadu Ali da wasu manya manyan kusoshin gwamnati a wancan lokacin. Haka dai el-Rufai ya ringa sanya gireda yana ma-ke duk wani gini da aka gina shi ba bisa kai’da ba a Habuja. Mallam Nasiru el-Rufai kusan shine ministan Abuja mafi dadewa a tarihin wannan birni tun daga 1999 har zuwa 2007, kuma ya yi aiki dai-dai nasa.

Tun da Marigayi Mallam Umaru Yar’Adua ya zama shugaban kasa el-Rufai ya tsallake yabar kasar nan inda ya tafi kasar Amerika ya koma makaranta, ya halarci kwasa kwasai da dama a fannoni daban daban, ciki kuwa harda katafariyar Jami’arnan ta Harvard, kadan daga Makarantun da el-Rufai ya halarta sun hada da Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria, Najeryia, Jami’ar London ko University of London a Burtaniya da Harvard Business School, Arthur D. Little School of Management a birnin Massachusetts da Georgetown University da School of Foreign Services a birnin Washington dukkaninisu a kasar Amerika da kuma D.C. da John F. Kennedy School of Government da Harvard University duk dai a can Amerika. Sannan el-Rufai yana da babbar Lambar yabo ta kasa wadda ake kira OFR (Officer of the Order of the Federal Republic of Nigeria) wadda aka bashi tun yana BFE, haka kuma a shekarar 2005 jami’ar Abuja ko University of Abuja ta bashi Babban digirin girmamawa da ake kira Doctorate Degree D.Sc (honoris causa).

Bayan da el-Rufai ya dawo gida Najeriya, ya fada Jam’iyyar adawa ta CPC inda ya mara baya ga takarar tsohon shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari duk kuwa da ana kallon zai goya baya ne ga takarar babban abokinsa wato Mallam Nuhu Ribadu. A halin yanzu dai Mallam Nasiru el-Rufai shi ne babban bakaniken jam’iyyar ta CPC wadda Buharin ya dora masa wannan nauyi na dai-daita sahun jam’iyyar kamar yadda a yiwa birnin tarayya Abuja, saboda fama da matsaloli da jam’iyyar ta ke yi a kusan daukacin jihohin kasarnan.

Bayan haka kuma, el-Rufai shi ne kusan mutum daya tilo wanda tauraruwarsa ke haskawa wajen adawa da gwamnati mai ci ta Goodluck Jonathan da kuma Jam’iyyar PDP. Mallam Nasir el-Rufai ya dauki lokaci yana sharhi akan kasafin kudi na wannan shekarar ta 2012 inda ya yi kaca-kaca da wannan gwamnatin ya nuna ma basu san me suke yi ba. Hakan ta sanya el-Rufai ya dinga daukan hankalin jama’a a ciki da wajen kasarnan wajen yadda yake fashin baki a harkar tafiyar da wannan gwamnatin musamman a harkar da ta shafi tattalin arziki, wannan ta sanya jami’an SSS suka ringa sanya masa tarko suna kamashi a kusan duk lokacin da zai yi wata tafiya zuwa kasashen waje, haka nan yake tsallake irin wannan turaku da ake sanya masa.

Bahaushe ya ce al-kalami ya fi Takobi, lallai wannan magana haka ta ke, domin shakka babu wannan gwamnati mai ci babu wani alkalami da ta ke jin tsoro a kullum kamar na el-Rufai, domin sun san cewar mai ilimin gaske ne kuma masani ta fannoni da daman gaske. Mallam Nasiru el-Rufai dai idan ka ganshi irin mutanan nan ne da zaka gansu ‘yan tsirit wato ba shi da wani cika ido, wannan ce ma ta sanya abokansa suke masa lakabi da sunan GIANT wato wani babban mutum kamar dai yadda Bahaushe yake ce wa gajere malam dogo. Lallai kam ya zuwa yanzu babu wani daga cikin ‘yan Adawa wanda tauraruwarsa take haskawa kamar el-Rufai ba, kuma duk wannan ya faru ne ta sanadiyar al-kalaminsa da yake caccakar wannan gwamnati da shi. Tabbas maganar Bahaushe gaskiya ce da ya ce Alkamai ya fi takobi, domin idan da fada za’a iya da takobi watakila da farat daya za’a gama da el-Rufai amma da yake fadan na alkalami ne, babu yadda aka iya da shi sai dai a kayar da shi da hujja idan ana da ita.

Lallai Najeriya tana bukatar mutane masu gaskiya wadan da zasu iya yakar cin-hanci da rashawa da gaskiya kuma hazikai irinsu Mallam Nasiru el-Rufai.

Daga marubuci Mallam Yasir Ramadan Gwale.

Monday, September 3, 2012

Babbar Magana: Tsakanin Shugaba Goodluck Da Fastor Tunde Bakare


Bari mu waiwayi tarihi na baya-bayan nan. La’alla a matsayinsa na fasto, dan siyasa, mai wa’azi, mutumin Allah, lauya ko mai kwato hakkin ’yan kasa – wanda dukkansu shi ne – Fasto Tunde Bakare a koyaushe ya kasance mai akida kuma maras wargi...

A matsayinsa na lauya ya yi aiki a karkashin Gani Fawehinmi. A 1999, a lokacin da kusan kowa ke zumudin takarar Olusegun Obasanjo, Bakare ya fito gaba-gadi ya ayyana cewa ba a dauko mai ceton al’umma ba. Ya yi ikirarin cewa, a hakikani ma dai Obasanjo zai sake yamutsa matsalolin Nijeriya ne. Tuni a ka tabbatar da gaskiyar batunsa a aikace. Ba ma haka kadai ba, Obasanjo ya zama annoba ta yadda ya dasa harsashin gurbataccen shugabancin da duk ya biyo bayansa.

A lokacin da Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya gaza saboda jinya, kwakwalwarsa ta daskare kuma ’yan ma’abban gwamnatinsa su ke amfani da rashin lafiyar wajen hana mataimakin shugaban kasa na lokacin, Goodluck Jonathan, ya gaje shi, Fasto Bakare ya jagoranci kungiyar Save Nigeria Group (SNG) wacce ta tilastawa ’yan siyasar aikata abinda ya dace. A yanzu Shugaba Jonathan ya shaku da sabbin abokansa har ya mance da kokarin Fasto Bakare a mawuyacin lokaci. Dukkanmu, har shi Tunde Bakare, mun dage a kan sai an aiwatar da sashe na 144 na kundin tsarin mulkin kasa ne, wanda zai bai wa mataimakin shugaban kasa Jonathan darewa karagar mulki kai tsaye ba wai a matsayin mai rikon kwarya ba, saboda hakan ne daidai. Ni na ga wautar majalisar dattawa ma da su ka yi amfani da wani abu wai shi ‘matakin tilashi’ su ka ayyana mataimakin shugaban a matsayin shugaba na rikon kwarya alhali sashe na 144 a fayyace ya ke kan abinda ya dace kasar ta aikata a irin wancan hali.

Fasto Bakare ya kausasa harshe ga masu rike da madafun iko kamar yadda littafin Bible ya wa’azantar. Ba wai kawai rashin tsoro ne da faston ba, ya na ma da kwakwalwar yin kyakkyawan hasashe.

’Yan kwanaki kadan da su ka gabata, jami’an tsaro na farin kaya, SSS, su ka gayyaci faston bisa lafazansa. Akwai shakkun cewa idan SSS za su iya gayyatar Bakare ba tare da izinin shugaban kasar ba. Wannan cin zarafi ne ga ’yancin fadar albarkacin baki kuma hakan bai dace da dimukradiyya ba a ko’ina cikin duniya. Irin wadannan ne abubuwan da su ke faruwa a Nijeriya lokaci zuwa lokaci wadanda ke nuni da cewa babu dimukradiyya a Nijeriya sabanin abinda a ke ikirari. An gayyaci Fasto Bakare ne saboda ya ce makomar Jonathan ita ce talauta Nijeriya bisa la’akari da irin almundahanar da a ke tafkawa a kasar tun ma kafin 2015. Abinda Bakare ya fadi kenan. Har yanzu babu wanda ya shaida mi ni cewa an gano bindigu ko bama-bamai a gidansa ko mujami’arsa da za a iya yin kokwanton cewa ya na shirin kifar da gwamnatin Jonathan ne ko kuma a matsayin wata shaida da ke nuna cewa shi dan ta’adda ne.

To, amma mene ne laifin kalaman na Fasto Bakare, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar CPC a zaben 2011? Idan don ya ce makomar Jonathan ita ce talauta Nijeriya, to me ye laifi a wannan? Shin ba abinda Jonathan ke aikatawa din ba kenan? Idan har Jonathan zai iya barnata Naira tiriliyan 2.6 ga masu kawo mai na karya, alhali sauran shugabannin kasar na baya su na kashe kasa da biliyan 300, ta yaya ma wani zai ga laifin lafazan Bakare? Ko kuwa shugaban ya na so ya mari ’yan Nijeriya ne ya kuma hana su kuka? Gaskiyar magana ita ce, idan har shugaban kasa zai kashe tiriliyan 2.6 a shekarar zabe maimakon biliyan 245 na tallafin mai, shin ba zai zama abu mai sauki ga dan kasa ya ce Jonathan ya na neman tsiyata kasarsa ba? Kai Bakare ma ya yi sassauci da yawa ga shugaban kasar. Lamarin ya fi haka la’acewa. Idan da a ce dimukradiyya na aikinta yadda ya dace, ai da tuni an tsige shi bisa aikata wannan danyen aiki na barnata tiriliyan 2.6 ba bisa ka’ida ba.

Faston ya kuma nusar da cewa, a matakin da cin hanci ya ke a kasar da Jonathan ke jagoranta, babu fa’ida a yi magana ma kan 2015. Fasto Bakare ya furta abinda kowa ke furtawa ne. Ya yiwa shugaban alfarma ne ma da ya sanar da shi abinda kowa ya fadi – ciki kuwa har da wadanda ke ikirarin su na tare da shi – amma su ke fadi a bayan idanunsa. Ni Ina mamakin yadda babu wanda ya taba bude baki ya gaya ma sa gaba da gaba. Tiriliyan din Nairori da a ka sace a karkashin kulawar Jonathan za su iya sanyawa kasar ta durkushe idan ba a hana ba.

Sace kudin tallafin mai, fashin kudin ’yan fansho, wawure gangar mai akalla 400,000 kullum ba bisa ka’ida ba, cefanar da rijiyoyin mai 245 da sauransu da sauransu ba abubuwa ne da sa mu su idanu ba. Eh, Nijeriya ta yi suna wajen tafka almundahana a idanun duniya, amma ba irin wannan rashin hankalin da mu ke gani a gwamnatin Jonathan ba. Wannan ne hakikanin abinda ya hana komai aiki a kasar. Lokacin da Jonathan ya yi alkawarin kawo sauyi, ba mu san irin sauyin da ya ke magana a kai ba. Hatta Naira biliyan 300 da Yar’Adua ya saki kafin ya kwanta jinya don gyara yankin Neja Delta, har yau ba a san inda su ka kwana ba. Rabin kudin PTF ta kashe a kasar bakidaya a ka ga bambanci.

Kuma ma don karin abin haushi shi ne Shugaba Jonathan ya umarci matsiyancin gwamnan can Henry Seriake Dickson na jihar Bayelsa ya nada matarsa mukamin babbar sakatare. Hakan ya biyo bayan bai wa bokansa, Tompolo, kwangilar tsaron tashar sauke kayan da a ka yi jigalar su a jirgi ne fa. Watarana lokaci zai zo wanda a bainar jama’a za a shaidawa ’yan Nijeriya hakikanin dangantakar Jonathan, babban kwamandan askarawan Nijeriya, da dan bindiga (tsoho ko mai yi), wanda ayyukansa su ka halaka sojoji da dama a kasar. ’Yan Nijeriya da dama har ma da ’yan kasashen waje sun shiga rudani kan ainihin dangantakarsu. Hakika lamari ne mai cike da dimuwa.

Ya kamata Shugaba Jonathan ya san cewa, ’yancin fadar albarkacin baki ya na daya daga cikin alfarmar dimukradiyya. Kamar yadda ’yancin wallafawa da yin abota su ke, haka nan fadin albarkacin baki ba za a turbude shi a dimukradiyya ba. Tauye hakkin fadin albarkacin baki ya zama al’ada a gwamnatin Jonathan. Shugaban ya na so ne ya rika aikata duk abinda ya ga dama ba tare da a na sanya ma sa shingaye ba. Ya na son kashe Naira tiriliyan 2.6 a shekarar zabe duk da majalisar dokoki ta kasafta Naira biliyan 245 ne kacal, amma ba ya so Fasto Bakare ya ce kanzil! A bara an tsare Nasir el-Rufai, daya daga cikin ’yan adawa na siyasa, a filin saukar jiragen sama, saboda rubutun da ya yi a kan shugaban kasar, kuma a 2011, gabanin zabe, jami’an SSS sun gayyaci Bola Tinubu saboda ya ce, ’yan Nijeriya su daina sauraron bugaggen mai kamun kifi, wato ya na nufin Jonathan. Martani ne fa ga Jonathan din bisa kiran ’yan jam’iyyar ACN da ya yi da ‘’yan iska’ a lokacin da ya ce “Kudu maso Yamma ta wuce a bar wa ’yan iska ita”. Tabbas al’ummar yankin Kudu maso Yamma sun mayar da martani ta hanyar kin zaben jam’iyyar Jonathan da Obasanjo a bakidayan yankinsu, kuma a nan an gane su wa su ka mayar ’yan iskan.

Abu ne mai wahala ga duk wanda ke kaunar Nijeriya ya iya tsuke baki ya na kallon yadda a ke tafiyar da kasar a halin yanzu. Fasto Bakare ya taimakawa shugaban kasar ne kawai don ya fahimci yadda ’yan Nijeriya ke ji a ransu game da shi. Fasto Bakare ya kuma ce, juyin-juya hali lallai zai afku a Nijeriya, saboda salon yadda a ke tafiyar kasar, musamman kan irin yadda a ke barnatar da arzikin kasar.
Shugaban ya nuna cewa, hakan fa ko a jikinsa. Shugaba Jonathan ya kamata ya sani cewa, ya na rubutawa kansa tarihi ne ta hanyar sigar da ta tafiyar da Nijeriya. Don haka tilas ya sauya salonsa ya kuma fara nuna halin-ko-in-kula.

Daga Jaridar Leadership Hausa

Saturday, September 1, 2012

Buhari Ya Ziyarci Kwankwaso


Tsohon Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa a zaben bara a karkashin Jam’iyyar CPC Janar Muhammadu Buhari ya kai ziyarar jaje ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso dangane da tashe-tashen hankula da jihar ke fama da su,

inda ya nemi Gwamnatin Tarayya ta yi duk abin da za ta iya don kawo karshen rashin tsaro da ke dada tura mutane cikin ‘bakin talauci’ a Arewa.
Janar Buhari wanda ya ziyarci Gwamna Kwankwaso a shekaranjiya Laraba ya bayyana rashin tsaro a Jihar Kano da wasu jihohin Arewa a matsayin “Babban abin bakin ciki,” inda ya ce ya yi matukar kawo nakasu ga kasuwanci da sauran harkokin tattalin arziki.
Janar Buhari ya ce: “Na zo ne domin in gaida Mai martaba Sarkin Kano kuma in yi muku jaje kai da shi kana bin bakin cikin da ke faruwa na tashin bama-bamai da kuma tsauraran matakan tsaron da ake dauka da suke takura wa jama’armu.”
Janar Buhari, wanda ya je jihar don bude sakatariyar Jam’iyyar CPC ya ce, Kano wadda a baya ta yi suna a duniya wajen harkar kasuwanci a yanzu tana neman komawa kufai. “Wannan babban abin bakin ciki ne, kuma ina fata za ku kawo karshen hakan cikin gaggawa,” inji shi.

A cewar Buhari, duk da macewar kamfanoni da matakan tsaron da ake dauka a Kano, ba kowa ne daga farko ya fahimci tabarbarewar al’amuran tattalin arziki a kasar nan ba, “said a matsalar Borno da Yobe ta yi kamari,” inji shi.
“Kasancewar na yi Gwamna a yankin, na san a kullum akalla motoci 200 ke barin nan zuwa Maiduguri wasu kuma su yiwo nan. Kuma a Maiduguri za ka iske ’yan kasuwa daga kasashen Kamaru da Chadi da Nijar. Wanna yanzu ya zama tarihi. Ku tsaya ku yi nazari dimbin ’yan Najeriya musamman na wannan yanki da a yanzu aka jefa su a cikin mummunan talauci. Don haka ina fata gwamnatin tsakiya za ta yi duk abin da za ta iya wajen an magance matsalar cikin gaggawa,” inji shi.

Daga nan sai Janar Buhari ya ce Jam’iyyar CPC za ta bude sakatariyarta a Kano ne, domin ta kintsa tare da taka rawar ’yar adawa ganin an riga an kawo karshen rikicin cikin gida da ke damunta.

A nasa jawabin Gwamna Rabi’u Kwankwanso ya ce, gwamnatinsa tana aiki da hukumomin tsaro don janye shigayen duba ababen hawa, domin ba jama’ar damar walawa da shiga da faitar da kaya daga jihar.

Gwamna Kwankwaso ya yaba wa Janar Buhari kan samun lokaci ya kai masa ziyarar girmamawa duk da bambancin jam’iyya da suke da shi. “Abin da Janar ya yi shi ne abin da ya kamata dukkan ’yan siyasa su rika yi, saboda bambancin siyasa ba yana nufin zama abokan gaba ba ne.”

A yayin da yake gabatar da jawabi a harabar sakatariyar jam’iyyar, shugaban rikon Alhaji Muhammad Ahmad ya bayyana farin ciki da ziyarar ta Janar Muhammadu Buhari, a inda ya ce “ziyarar tana da muhimmanci wajen tabbatar da kawo gyara a cikin jam’iyyar, tare da tabbatar da hadin kai a tsakanin mabiyanta a jihar.”
Sai dai Janar Buhari wanda ya isa wajen taron a cikin bakar mota kirar Jeep, bai samu sukunin fitowa daga cikin motar ba, sai dai ya fito da kansa ta tagar rufin motar, inda ya rika karbar gaisuwa, tare da daga hannunsa ga cincirindon jama’ar da suka taru, sannan ya bar wurin.

Daga cikin wadanda suka yi masa rakiya akwai Shugaban Jam’iyyar CPC na kasa Yarima Tony Momoh da dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar a zaben bara Janar Lawal Ja’afaru Isah da tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Aminu Bello Masari da Alhaji Faruk Adamu Aliyu da Alhaji Sule Yahaya Hamma da Alhaji Buba Galadima da Alhaji Nasiru Baballe Ila da Abdulmajid dan Bilki Kwamanda da Kantoman Jam’iyyar CPC na Jihar Kano Dokta Mohammed Ahmed da sauran jami’an jam’iyyar na jihar da na kasa.

Daga Jaridar Aminiya