Wednesday, March 31, 2010

BAYAN SAMUN YANCIN KAN NIGERIA


Kadan daga cikin Muhimman abubuwan da suka faru bayan samun yancin kan kasarmu Nigeria.

Ranar 6 July 1967, aka fara yakin basasar Biafra har zuwa ranar 12 January 1970.

Ranar 1 October 1960, Nigeria ta samu yancin kai daga wurin turawan kasar Burtaniya.

Ranar 29 May 1967, Nigeria ta canja kudin kasar zuwa Naira da Kobo.

Ranar 22 May 1973, aka maida tsarin yan bautar kasa wato NYSC kasa da shekaru (24) ashirin da hudu.

Ranar 28 May 1975, aka gina ofishin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS a jihar Lagos.

Ranar 14 February 1976, General Murtala Ramat Muhammad ya dawo da birnin tarayyar Nigeria daga Lagos zuwa Abuja.

Ranar 15 February zuwa 12 March 1977, akayi biki nuna al'adun Afrika karo na biyu a jihar Lagos.

Ranar 13 February 1982, Pope John Paul, ya ziyarci kasar Nigeria a karo na biyu.

Ranar 16 October 1986, Professor Wole Soyinka, ya zama dan kasar Nigeria kuma dan Afrika na farko daya samu nasarar cin gasar Alfred Nobel Prize a Stock Holm dake kasar Sweden.

Ranar 18 February 1988, aka kirkiri Federal Road Safety Commission. Kuma Prof. Wole Soyinka ya zama shugaba na farko.

Ranar 4 April 1988, aka canja kayan yan sadan Nigeria zuwa kalar Baki.

Ranar 11 July 1991, sama da yan Nigeria mutum 250 ne suka rasu a sakamakon hadarin jirgin sama a Jiddah, kasar Saudi Arabia.

Ranar 27 August 1991, shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, ya sanar da karin jihohi da kuma kananan hukumomi guda 47.

Ranar 27 zuwa 29 November 1991, akayi kidayar mutanen kasar Nigeria.

Ranar 2 August 1996, Nigeria ta zama kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta fara lashe gasar Olympic wanda akayi a Atlanta, kasar America.

Ranar 8 August 1998, Allah (SWA) yayi wa General Sani Abacha, rasuwa a Aso Rock, yana da shekaru 54 an binne shi a jiharsa ta haihuwa Kano, a ranar daya rasu kamar yadda tsarin Addinin Musulunci ya tana da.

Ranar 29 May 1999, mulkin kasar Nigeria ya koma hannun farar hula.

Wednesday, March 24, 2010

KASAR NIGERIA

Kasar Nigeria kasa ce dake yammacin nahiyar Africa, Nigeria ta samo sunanta ne da daga Kogin Niger (Niger Area), a shekarar 1898, kasar Nigeria tafi kowace kasa dake nahiyar Africa yawan mutane tana da mutane sama da 130 million. Sannan Allah ya arbarkaci Nigeria da arziki kala kala, masu tarun yawa. Nigeria na da kabilu da yawa wadda tana cikin kasashen da suka yawan kabilu a duniya.
Nigeria na da kabilu sama da 250, manya daga cikinsu sune: Hausa, Fulani, Yoruba, Igbo, Kanuri, Nupe da Ijew.
Addinin Musulunci shine yafi kowane addini rinjaye a kasar, sannan Addinin Christians. Da kuma sauran addinai kala kala.
Kasar Nigeria na da jihohi guda 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, sannan da kananan hukumomi guda 773.
A shekarar 1914 turawan Britain suka hada arewancin Nigeria da kudanci ya zama kasa daya, sannan kuma suka mamaye kasar a matsayin mulkin mallaka. Lokacin da Nigeria ke karkashin mulkin Britain, turawa ne ke mulkin kasar har zuwa ranar 1 October 1960 lokacin da Nigeria ta samu yancin kanta daga turawan mulkin mallakar kasar England.

Bayan samun yancin kai ne Dr. Nmandi Azikiwe ya zama dan kasa na farko wanda ya shugabanci Nigeria. Sannan Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama Prime Minister.
Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), kuma ya zama Prime Minister Jihar Arewa. Wadannan shugabanni sunyi aiki tukuru wajen ganin kasa ta cigaba, amma a 1966 akayi musu juyin mulki kuma a wannan juyin mulki ne aka kashe Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto).

General Aguiyi Ironsi ya hau mulkin kasar bayan wannan juyin mulki a January 1966 amma shima bai dade ba akayi Juyin Mulki. General Yakubu Gowon ya karbi mulki a July 1966.
A 1975 sojoji suka sake yin juyin mulki General Murtala Ramat Muhammad ya hau mulkin kasa. Amma shi wata takwas yayi yana mulki a kayi juyin mulki kuma aka kashe shi.
Sannan General Olusegun Obasanjo ya karbi mulki yayi shekaru uku sannan ya mika mulki a hannun farar hula. Inda Alhaji Shehu Shagari yayi nasarar hawa mulki a 1979 a matsayin zababbe.
Mulki bai dade a hannun farar hula ba sojoji suka sake yin juyin mulki, General Muhammad Buhari ya hau kujerar mulki, a 1983 shima bai dade ba aka sake yin juyin mulki amma ba'a zubar da jini ba.
Sakamakon wannan juyin mulki General Ibrahim Badamasi Babangida ya dare kujerar mulki
a 1985 har zuwa 1993 sannan shima akayi masa juyin mulki. Chief Ernest Shonekan ya hau mulki na yan watanni sannan General Sani Abacha ya karbi mulki a 1993.
Ranar 8 Auguest 1998 Allah yayiwa Gen. Sani Abacha rasuwa. Kuma shine shugaban Nigeria na farko da ya mutu yana kan mulki.

Bayan rasuwar General Sani Abacha. General Abdussalam Abubakar ya hau mulki na rukon kwarya. Tun daga wannan lokaci mulki ya dawo hannu farar hula har zuwa yau. Ranar 29 may 1999 General Olusegun Obasanjo ya hau mulkin Nigeria a matsayin damukradiya (Democratic) Chief Obasanjo yayi mulki har na tsawon shekara takwas bayan sake lashe zabe da yayi a 2003.
Ranar 29 may 2007 Alhaji Umaru Musa Yar'adua yayi nasarar hawa mulkin kasar Nigeria kuma har zuwa yau shi ke mulkin kasar. Sannan zabe gaba za'ayi shi a 2011.

Kamar sauran kasashe Nigeria na da alamomin kasa (National Symbols) masu yawa wanda suke da muhimmanci a wurin kowane dan asalin kasar Nigeria.

TUTAR KASA (National Flag) Taiwo Akinkami dan kasar Nigeria shine ya tsarata a 1959 amma a lokacin ba'a amfani da ita. Tun 1914 Nigeria ke amfani da tutar British Union har zuwa tsakiyar daren ranar 30 September 1960 washe garin samun yancin kai, sannan Nigeria ta fara amfani da ita.
Tutar Nigeria na da kala biyu da aka raba gida uku (Kore, Fari, Kore). Koriyar kala na nuni da kyakkyawar kasar noma. Sannan Fara kana na nuni da zaman lafiya da hadin kan kasar.

TAMBARIN KASA (Coat and Arm). An samar da tambarin a 1960. Tambarin na dauke da bangarori kamar haka:
MIKIYA wadda ke nuni akan karfin Nigeria.
DAWAKAI guda biyu na nuni akan martabar Nigeria.
Y na nuni akan manyan ruwan kasar guda biyu. Kogin Niger da Kogin Benue.
FILAWA na nuni akan arzikin noma da kasar ke dashi. Sannan a karshe an rubuta "HADIN KAI DA IMANI, ZAMAN LAFIYA DA CIGABA" wanda ke nuni akan shine manufar Nigeria.

TAKEN KASA (National Anthem). Taken Nigeria na nuni akan bukatar kowane dan kasa yayi biyayya tare da yin aiki tukuru domin samu zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.

RANTSUWA (National Pledge). Wani alkawari ne da rantsuwa da dan kasa ke dauka domin yiwa kasa aiki bisa aminci.

A karshe wannan shine kadan daga cikin abubuwan da suka shafi kasarmu Nigeria musamman yadda akayi mulki tunda daga samun yancin kai. A ranar 1 ga October 1960, ranar da duk dan Nigeria ke alfahari da ita.
Allah (SWA) ya kara daukaka kasar Nigeria ya bamu shugabanni nagari.

Thursday, March 18, 2010

TAKAITACCEN TARIHIN REAL MADRID

Real Madrid Club de Futbol ko Los Blancos. (The White) Kwararriyar kungiyar kwallon kafa ce dake birnin Madrid na kasar Spain.
Itace kungiyar da FIFA ta zaba a matsayin kungiyar da tafi samun nasara a karni na 20, domin ta lashe kofin rukuni-rukuni na kasar Spain (La-liga) sau 31, Spanish Cup sau 17 da kofin zakarun nahiyar turai sau 9 da kuma kofin UEFA sau biyu.
An kafa kungiyar Real Madrid a shekarar 1902 (6 March 1902). A shekarar 1900 aka kafa kungiyar Club Espanol de Madrid. A 1902 kungiyar ta rabu biyu hakan ya kawo kafuwar Madrid Fooball Club.
A shekarar 1905 Madrid FC ta fara yin nasarar daukar kofi, bayan ta doke Athletic Bilbao a kofin Spanish Cup.
Madrid FC na daya daga cikin wakilan hukumar FIFA na farko kuma wakiliyar rushasshiyar kungiyar G-14 na manyan kungiyoyin da ake ji dasu a nahiyar turai.
A 1920 ne aka canja sunan kungiyar zuwa Real Madrid bayan da sarki Alfonso ya amince a yi amfani da lakabi Real da ake nufin Royal ga kungiyar.
A shekarar 1929 ne aka fara gasar La-liga inda Real Madrid ta jagoranci gasar har zuwa wasan karshe inda tayi rashin sa'a a hannun Athletic Bilbao. Ta zama ta biyu bayan Barcelona. Real Madrid ta fara lashe gasar La-liga ne a 1931/1932, sannan shekarar gaba ma ta sake lashewa.
A 1940 Santiago Bernabeu Yeste ya zama shugaban kungiyar, kuma a mulkinsa ne Real Madrid ta sake gina filayen wasanninta na Santiago Bernabeu da Ciudad Deportiva, bayan yakin basasar kasar Spain.
Santiago Bernabeu a shekarar 1953 ne ya fara dakko kwararrun yan wasa daga kasashen waje. Fitacce daga cikinsu shine Alfredo di Stefano, wannan ya bashi damar kafa tarihin kungiyar da ta fara tattara yan wasa daga sassan duniya a tarihin kwallon kafa. A karkashin Bernabeu ne Real Madrid ta zama gagabadau a fagen kwallon kafa a kasashen turai.
Real Madrid ta lashe kofin kasashen turai (Uefa Champions League) sau biyar a lokaci daga a tsakanin 1956 zuwa 1961 wanda ya hada da ci 7-3 da tayiwa kungiyar Eintracht Frankfurt a filin wasa na Hampden Park a wasan karshe a 1960. Cin kofin sau biyar a jere yasa kungiyar ta samu mallakin kofin na ainihi tare da bata damar sanya tambarin girmamawa na UEFA.
Real Madrid ta lashe Uefa Champion League karo na shida a 1966 bayan ta doke FK Partizan da ci 2-1 a wasan karshe.
Ranar 2 July 1978 shugaban Real Madrid Santiago Bernabeu ya rasu. A shekarar 1996 shugaban Real Madrid na lokacin Lorenzo Sanz ya kulla yarjejeniyar daukar Fabio Capello a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar na tsayon shekara daya.
A 1998 Real Madrid ta sake yin nasarar daukar kofin Uefa Champions League karo na bakwai bayan ta samu nasara akan Juventus da ci 1-0 a wasan karshe.
A watan bakwai na shekarar 2000 aka zabi Florentino Perez a matsayin shugaban kungiyar, a mulkinsa ya samu nasarar kawo shahararrun yan wasa kungiyar, wanda suka hada da Zinedine Zidane, Ronaldo, Luis Figo, Roberto Carlos, Raul da David Beckham. A shekarar ne kungiyar ta sake cin kofin Uefa Champions League karo na takwas. Sannan kuma ta samu nasarar daukar na tara a shekarar 2002 da kuma kofin La-liga a 2003 duk a lokacin mulkin Perez.
Ramon Calderon ya zama shugaban Real Madrid ranar 02 July 2006 da zuwansa ya sake dakko Fabio Capello a karo na biyu a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar, da kuma tsohon dan wasan kungiyar Predrag Mijatovic a matsayin manajan kungiyar.
Real Madrid tayi nasarar cin kofin La-liga karo na 30 a shekarar 2007. Sannan ta sake cinye kofin a 2008. Ranar 01 June 2009 Florentino Perez aka sake zabarsa shugaban kungiyar karo na biyu. Da zuwansa ya sayo shahararren dan wasan AC Milan da Kasar Brazil wato Ricardo Kaka akan kudi £60m. Sannan kuma sai dan wasan duniya na lokacin Cristiano Ronaldo daga kungiyar Manchester United ta kasar England, akan kudi £80m. Wannan sayayyar itace tafi kowacce tsada a tarihin kwallon kafa bayan dan wasar kasar France Zinedine Zidane.
Duk da Real Madrid tafi kusa da kungiyar Athletic Madrid. Amma babbar abokiyar adawarta itace kungiyar Barcelona.
Real Madrid itace kungiyar kwallon kafa da tafi kowacce kungiya samun nasarar daukar kofuna. Ga jerin wasu kofuna da kungiyar ta dauka:
9 Uefa Champions League.
31 Spanish La-liga.
19 Spanish Cup.
18 Regional Cup.
3 Intercontenatal Cup.
8 Spanish Super Cup.
5 Community Cup.
2 Uefa Cup.
2 Spanish League Cup.
2 Latin Cup.
2 Little Cup.
1 European Super Cup.

Tuesday, March 16, 2010

LABARIN MALAM BUBA

Assalamu Alaikum. Malam Buba mutum ne mai son abin dariya a koda yaushe, yana zaune a kauye shida iyalansa kuma yana da garken dabbobi masu yawa.
Wata rana Malam Buba yana son cin dariya, sai ya fara tunanin yadda zaiyi don cin dariya, can sai dabara tazo masa, kawai sai ya shiga cikin kauyen da yake zaune a guje yana ihu-ihu a taimake ni Zaki ya shigo cikin garken dabbobi na zai cinye su. Yayi wannan dabarar ne kawai don yaga ya mutanen garin nan zasuyi wane irin mataki zasu dauka. Mutanen garin kuwa da jin ihun Malam Buba sai kowa ya fara fitowa daga cikin gidansa, kowa dauke da makamai wasu ko riga babu a jikinsu, suka nufi gidan Malam Buba don taimakonsa. Da zuwansu sai suka tarar da Malam Buba yana ta dariya har da faduwa kasa, kuma ga dabbobinsa na cin abinci cikin kwanciyar hankali. Wannan abin ya batawa mutanen kauyen rai, sukace da Malam Buba ina Zakin da ya shigo zai cinye ma dabbobin, sai kawai yace dasu "nayi haka ne kawai don naci dariya" mutanen kauyen kowa ya koma gidansa cin fushi da jin haushi.
Wata uku da yin wannan abu sai ga Zaki ya baiyana a gaskiyan ce a garken Malam Buba ya fara gaggatsa dabbobin Malam Buba suna mutuwa, nan take Malam Buba ya shiga cikin kauyen yana ihu yana kiran azo a taimake shi. Sabida yaudarar da Malam Buba yayiwa mutaten kauyen a baya yasa ba wanda ya fito don taimakonsa. A karshe Zakin ya kashe duk dabbobin Malam Buba.
Malam Buba ya zama talaka, sannan ya koyi babban darasi.

A karshe wannan labari yana nuna mana muhimmanci fadar gaskiya a kowanne hali. Domin da Malam Buba bai yaudari mutanen kauyensa ba da baiyi hasarar dabbobinsa ya koma talaka ba.

Monday, March 15, 2010

HAUSA A WANNAN ZAMANI

Assalamu Alaikum. Ya kamata kafin na fara gabatar da kasidu a wannan dandali na danyi bayani game da cigaban kabilar Hausawa a wannan zamani musamman kan cigaban na'ura mai kwakwalwa. Hausa dai kamar yadda aka sani yare ne kamar ko wanne yara a duniya. Akwai miliyoyin mutate masu amfani da harshen Hausa a Afrika dama duniya baki daya, dukkan wani Bahaushe Allah ya bashi basira sosai. A wannan zamani da cigaban fasahar sadarwa yake da matukar muhimmanci a duniya to ba'a bar Hausawa a baya ba. Domin a halin yanzu Hausawa suma suna kokarin ganin sun zama kwararru akan wannan fanni, duk da cewa Hausa basu da isassun kayan harkar fasahar sadarwa, domin ba kowane yake da damar sayen na'ura mai kwakwalwa ba amma duk da haka zakaga yana son abin a zuciyarsa. Wani zakaga kullum sai yaje yayi sana'a sannan zai samu kudin da zai je Internet Cafe don yin browsing, wani kuma zakaga yana amfani da wayarsa ta hannu don yin browsing da aikawa da sakonni. Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq), mai MAKARANTAR KIMIYA DA FASAHAR SADARWA. ya taimaka sosai wajen tunatar da Hausawa game da cigaban fasahar sadarwa. Domin duk sati yana gabatar da kasida a shafi guda na jaridar Aminiya, game da yadda za'ayi amfani da na'ura mai kwakwalwa, wannan aiki nasa yasa Hausawa sun tashi tsaye wajen neman ilmi game da fasahar sadarwa. Sai kuma gidan rediyon BBC Hausa suma sun bada gudunmawa sosai akan wannan harkar, domin sun bada dama ga masu saurarensu suke yin mahawara a shafinsu na BBC Hausa Facebook, wannan yasa Hausawa sun tashi a tsaye. A karshe kira ga Hausawa shine kara dagewa wajen koyan ilmin sarrafa na'ura mai kwakwalwa, wannan zai rage mana wannan halin rayuwa da muke ciki. Allah ya kara daukaka kabilar Hausa a fadin duniya.

Saturday, March 13, 2010

BARKA DA ZUWA

Assalamu Alaikum. Ina yiwa dukkan wanda ya ziyarci wannan dandali fatan alkhairi. Wannan dandali na gina shine akan kawo jawabai game da abubuwan da suke faruwa a kasarmu Nigeria dama duniya baki daya musamman ma kan harkukin siyasar duniya da ta Afrika. Ina fatan idan mutum ya ga gyara akan wani abu zai sanar dani kuma ina farin ciki da wanda zai ga nayi kuskure ya sanar dani na gyara domin ni dalibi ne wanda har yanzu yake karatu a sakandare bai maje jami'a ba. Allah ya daukaka kasarmu Nigeria ya arzutamu da shugabanni na gari. Naku Muhammad Bashir Ahmad.