Friday, August 27, 2010

MA'ANAR AZUMIN A SHARI'A

AZUMI Shine kamewa daga barin ci da sha, jima'i da kuma maganganun banza, tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin Ibada ga Allah (S.W.T). Saboda fadin Allah cewa "Ku ci ku sha har sai alfijir ya fito daga duhun dare, sannan sai ku cika azuminku zuwa faduwar rana" (Bakara 187).

Hadisin Abu Huraira (R.A) Yace Manzon Allah (S.A.W) Yace "Duk wanda bazai bar kirkire-kirkiren karya ko aikin ashsha ko jahilci (wauta) to lallai Allah baya bukatar ya bar ci da sha don yin azumi (Bukhari da Abu Dauda)

Idan muka yi duba da wannan ayar da hadisin zamu ga cewa lallai idan mutun yana son yayi azumi irin na Shari'a to lallai ne mutum ya bar abubuwan da aka zayyana. Sannan kuma ya kare idonsa da bakin daga abinda Ubangiji ya haramta.

Yana daga abinda yake wajibi akan mai azumi ya nisanta kansa daga kallon fina-finan turawa musamman na batsa. Domin kaucewa kishirwar banza da yunwa wacce ba lada a cikinta.

A karshe muna rokon Allah Ya karemu daga munanan halaye a wannan lokacin na Azumi. Ameen.

Monday, August 16, 2010

MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE

Daga Abdullahi Bin Umar (R.A) Cewa Manzon Allah (S.W.A) yace "Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya bari a cuce shi. Duk wanda ya taimakawa dan uwansa Musulmi wajen bukatartarsa Allah zai biya masa ta sa bukatar. Duk wanda ya yaye bakin cikin dan uwansa Musulmi, Allah za yaye masa bakin ciki daga bakin cikin ranar Alkiyama. Duk wanda ya rufawa dan uwansa Musulmi asiri, Allah zai rufa masa asiri ranar Alkiyama"

Bukhari ne ya rawaito shi.

Monday, August 9, 2010

RAMADAN KAREEM

RAMADAN na daya daga cikin jerin watannin Musulunci guda goma sha biyu. Kuma shine a jeri na tara.
Dukkan Musulmi wajibi ne a gare shi ya azumci wannan wata na RAMADAN Mai Alfarma.

AZUMI na daya daga cikin jerin Shikashikan Musulunci guda biyar. Bayan Shahada da Sallah. Sannan kuma daga shi sai Zakkah da Aikin Hajji ga duk wanda Allah Ubangiji ya nufa da zuwa.

Wannan wata na RAMADAN nada matukar muhimmanci wurin Allah, dan haka sai mu dage wurin neman gafarar Allah a wannan wata mai Alfarma.

Abubuwa da dama sun faru masu muhimmanci a cikin wannan wata, kadan daga ciki sun hada da:
Wahayin Alkur'ani Mai Girma.
Yakin Badar a shekara ta biyu baya hijira.

Allah Madaukakin Sarki na cewa a cikin Alkur'ani Mai Girma " Alkur'ani an saukar da shine a watan Ramadan, sannan kuma Ramadan shiriya ne ga mutane da bayani na shiriya wanda yake banbance tsakanin shiriya da bata. Wanda ya ga wata ko ya ji bayanin ganinsa to ya dau Azumi.
(Baqrat 180).

Allah bamu ikon bauta masa cikin wannan Wata Mai Alfarma kuma ya Gafarta mana dukkan zunubanmu. Ameen.