Thursday, February 24, 2011

GENERAL BUHARI YA KADDAMAR DA SHAFIN YANAR GIZO NA KAMFEN DINSA

General Muhammad Buhari dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar CPC ya kaddamar da shafin yanar gizo na yakin neman zabensa, wanda ta wannan shafi ne za'ake samun labarai kai tsaye da dumi duminsu game da yakin neman zabe da za'ayi a jihohi, da sauran labarai game da duk abin da ya shafi wannan takara.

General Buhari ya kuma nemi shawarar masoya wadanda tuntuni suka bude irin wannan shafuka don san kai da su rufe su zo su bada da gudunmawa a wannan da aka bude don a gudu tare a tsira tare. Shafin shine (http://www.buhari4change.com).

Wannan shafi yana samu kullawa wasu kwararrun masana fasahar yanar gizo, domin irin yadda aka nuna ganinta wajen gina shafin zai tabbatar da hakan. Shafin an hada shi da wasu shafuka da suka danganci yakin neman zaben wato shafin Facebook, Twitter da kuma Youtube. Dadin dadawa kai tsaye idan ka shiga shafin zaka iya sanar da yan uwa da abokan arzikinka manufar General Muhammad Buhari, wato ta hanyar sakon wayar hannu. Kai wasu abin burgewar ma dai sai ka ziyarci shafin.

WAYAR SALULA (HANDSET) NA DA MATSALA GA KWAKWALWAR BIL'ADAMA

Wani bincike da cibiyar lafiyar ta Amurka ta
gudanar ta gano cewa wayoyin salula na da illa
ga kwakwalwar bil'adama.
An dai gano cewa ana samun karin yawan
sukari a kwakwalwa bayan minti hamsin da
gama amfani da wayar salula.
Binciken wanda aka wallafa a wata kasidar
kungiyar likitocin Amurka ta ce ba'a tantance
iya illar da wayar ke yi ba.
Amma wasu masana a Burtaniya sun musanta
binciken a yayinda su ka ce, babu kanshi
gaskiya game da batun, saboda a cewar su
wayar salula bata barazana ga rayuwar
al'umma.
Yawaitar amfani da salula
A 'yan shekarun nan da aka samu karuwar
amfani da wayar salula, ba'a samu rahoto
game da illar amfani da wayar ba ga dan
adam.
Wani binciken da aka dauka a kan
masu amfani da masu wayar
wajen 420,000 a kasar Denmark,
bai nuna ko amfani da wayar
salulu na haddasa ciwon daji ba.
Amma wani gwaji da aka gudanar
akan mutane 47, an lurra cewa
akwai wani sinadari da ba'a gani
da ido da wayar ke amayar da shi.
Wannan sinadari dai na illa ga kwakwalwa,
amma ba'a gano takamaimai abun da illar zai
haddasa ba.
Gwaji
A gwajin da aka gudanar an sanya wayoyin
salula biyu an kunnuwa biyu na kowani
mutum. An kashe waya guda a cikin daya
kuma aka kashe muryar, saboda kada wanda
ake gwajin a kansa ya san wanne ne a cikinsu
ke kunne.
An dai gwada kwakwalwansu inda aka gano
cewa akwai karin sinadarin glucose da kashi
bakwai a bangaren kunnen da ke kusa da
wayar da take kunne.
Binciken dai ya yi la'akari da yadda wayar
salula ka shafar yadda kwakwalwa ke aiki.
"Har ila yau sakamakon binciken
bai nuna mahimmacin wannan abu
ko kuma akasin haka ba."
Farfesa Patrick Haggard, wani
masani a harkar kwakwalwa da ke
jami'ar kimiyar kwakwalwa da ke
Landon ya ce; "Binciken na da
mahimmacin domin a yanzu haka
mun sa cewa wayar salula na iya
illa ga kwakwalwa."
"Mun dai lurra cewa illar na rage zurfin tunani."
"Har wa yau, idan mun kara bincike mun ga
cewa wayar salula ba ta da wata mumunar illar
ga kwakwalwa, dolene mu kara wani bincike
muga ko tana da illa ga rayuwar dan adam".
Farfesa Malcolm Sperrin, Direkta a asibitin Royal
Berkshire cewa ya yi; "Binciken na da matukar
mahimmacin musamman yadda ya nuna inda
wayar ke sanya karuwar wasu sinadarai a
kwakwalwa."
"Dolene mu kara aikin wajen gudanarda
binciken da zai duba alakar illar da wayar ta ke
ma kwakwalwa da kuma lafiyar jama'a."
"Kuma na yi matukar farin cikin yadda aka
gudanar da wannan bincike ba tare da rayuwar
wasu ya shiga cikin wani hatsari ba"

Sunday, February 6, 2011

NAZARI NA MUSAMMAN KAN FINA-FINAN HAUSA

Kwaikwayon al’adu da fina-finan wasu:
Fina-finan Hausa sun ciri tuta wajen
kwaikwayon al’adu da kuma fina-finan
wasu kasashe da kuma kabilu, kamar su
Indiya (Bollywood), Amurka (Hollywood) da
sauransu. Hasali ma tarihi ya nuna fina-
finan Hausa na farko-farko an wanko su ne
daga fina-finan kasar Indiya, misali,
Soyayya kunar Rai (1995), wanda aka
kwaikwayi fim din Indiya mai suna Mujhe
Insaaf Chahiye (1983), Soyayya Rayuwa
(1996), wanda aka kwaikwayi Aadmi Chalte
Chalte (1982), Farin Gani (1997) wanda aka
kwaikwayi Raghubeer, Ikon Allah (1997) an
kwaikwayi Pet Pyaar Aur Paap (1984).
Bincike ya kuma nuna fim din Dijengala
(1999) an kwaikwayi fim din Return To
Eden, wanda shi kansa Return To Eden din
aka wanko shi daga fim din Khoon Baremag
(1992).
Hakazalika, idan muka koma fina-finan
Hausa na shekarun bayan kadan, misalan
fina-fiani irin su Dafa’i (Mis Production), an
kwaikwayi Ghayal, Nasara an kwaikwayi
Jeet, Gasa an kwaikwayi Mujse Shaadi
Karogi. Fina-finan FKD Production, irin su
Mujadala, an kwaikwayi Dillaghi, Khusufi, an
kwaikwayi Taal, Zo Mu Zauna an kwaikwayi
Khabi Khushi Khabi Gam, So, an kwaikwayi
Mohabbatein. Idan muka koma ga fina-finan
Hausa da suka koyi fina-finan kudancin
Najeriya, akwai fina-finan Hujja (Mai Shunku
Mobie) an kwaikwayi Disguise, Amaliya
(Al’umma Production), an kwaikwayi
Married to the Enemy. Sai Na Dawo (2-
Effect), an kwaikwayi The King is Mine. Duk
da cewar Yakubu Muhammad ya shaida
cewa sun dauko wata al’ada ce ta mutanen
kasar Ghana. Abin tambayar shi ne, ko an
taba samun inda masu shirya fina-finai na
wata kasa ko kabila sun kwaikwayi fina-
finan Hausa? Shin wannan al’adar da
Yakubu ya kwaikwayo tana da wata
muhimmanci ga al’ummar Hausa? Idan
babu, me ya sa mu muke dauko na wasu?
Fina-finan Indiya sun taka rawa wajen
sanya sunayen fina-finan Hausa da kuma
rubuta sunayen taurarin shirin fim. A wata
hira da na taba karantawa da mujallar fim
mai suna Tauraruwa, ta yi da Hafizu Bello,
ya shaida cewa an kirkiro fina-finan Hausa
don zamo wata garkuwa ta hana kallon
fina-finan Indiya da sauran fina-finai. Bisa
wani nazari da bincike ne da na yi na gane,
tun kafin a fara shirya fina-finan Hausa,
al’ummar Hausawa sun fi raja’a wajen kallon
fina-finan Indiya. To ganin haka ne, sai
masu shirya fina-finan Hausa suka dauki
zubi-da-tsarin fina-finan Indiya, don su ma
fim din su ya samu karbuwa. Wanda a
cewar su, tun da Hausawa suna kallon fina-
finan Indiya, idan suka yi fim irin na su, to
fim din su zai samu karbuwa.
Tasirin fina-finan Indiya a kan fina-finan
Hausa sun hada da: Sanya sunan fim irin
yadda Indiyawa suke rubuta sunayen fina-
finansu, da rubuta sunayen taurarin fim
kamar yadda Indiyawa suke rubutawa da
rawa da waka kamar yadda Indiyawa suke
yi a fina-finansu. Misalan sanya sunan fim
irin na Indiyawa: Baade de Heeral, Sitapurki
Geeta, Amir Aadmi Gareeb, Mere Jeeban
Saathi, Aadm Desh Pramee, Haseena Maan
Jaayegi, Khushi, Chori Chupke Chupke,
sakamakon amfani da Indiyawa suke da
kalmomi irin su ee da ch da kuma gh, sai
Hausawa suke rubuta sunayen fim din su
irin yadda Indiyawa suke. Misali: Huznee (H.
B. Production), Najjee (Multi Purpose
Concept), Jaheed (2-Effect), Zughi (AIDIM
International Company), Inganchi (Man
Entertainment), Khushu’i (Hali Dubu Mobies),
Khusufi (FKD Production) da fina-finai irin su
Chanji, Chanchanta da dai sauransu.
Rubuta sunayen taurarin fim kamar yadda
Indiyawa suke rubutawa: Mansoor Sadeek,
Abbas Sadeek, Ahmad Sani Sadeek, Sadeek
Ahmad, Kabeer Mai Kaba,
Sadeeya Gyale, Suleiman Sa’eed, Tijjani
Ibraheem da dai sauransu da aka rubuta a
fina-finai da yawa.
Waka da rawa: Kowa ya sani idan aka ce za
a kirgo ko lissafo wakokin Indiya da
mawakan fina-finan Hausa suka juya, to za
a dade ba a gama ba. Idan ka dauke
mawaka irin su Sani Yusuf Ayagi da
Mudassir Kassim da Misbahu Ahmad da suka
tsaya kai-da-fata wajen ganin sun rera
wakokinsu cikin siga da kamala da salo da
kuma karin waka irin ta Hausawa, sauran
mawaka irin su Yakub Muhammad, Adamu Hassan Nagudu,
Abubakar Sani, Mahmud Nagudu, Umar M.
Shariff, Sani Tudun Murtala, Auwal Adam,
Auwal Ishak, Nazifi Asnanic da sauransu, duk yawanci suna
rera wakokinsu bisa siga ta kwaikwayon
Indiyawa ko Sudan. Kai har da wakokin
Nasara, masu lakabin Hip-Hop, RnB, Blues da
sauransu, kamar yadda aka yi Kallabi (FKD
Production), Bakace (HB Production) da Tsumagiya (Sarari Ventures) inda Sani Danja
yake rawa irin ta Micheal Jackson, har
gawarwaki suna fitowa, da dai sauran
misalai. A cikin mawakan, gwanda-gwanda
Yakubu Muhammad yana kokari wajen rera
wakokinsa cikin salo, zubi-da-tsari da kuma
karin waka irin na wakokin Hausawa.
Hakazalika, idan aka ce za a lissafa raye-
rayen Indiyawa da aka kwaikwaya, nan ma
ba za a iya lissafawa ba. Dalilin faruwar
hakan kuwa yana da nasaba ne da rawar da
za a yi a waka tana tafiya da karin waka ne,
kuma yawancin karin wakar fina-finan
Hausa, sun samu tushensu ne daga wakokin
Indiyawa.
Idan muka koma al’adun Nasara ma, haka
kawai muka rika kwaikwayon su. Misali, a
fina-finan Hausa za ka ga taurarin da shiga
irin ta Nasara kuma wani abu za ka samu,
ba wai fim din ya kunshi da sai an yi irin
shigar ba ne. Inda za ka ga mutum ba
ma’aikacin banki ko wata ma’aikata ba,
amma za ka gan shi sanye da kwat. Wani
abu kuma, hakazalika a fina-finai da yawa,
sai ka ga jarumai maza, sanye da kaya Body
Hug, ko Yankees da dai sauransu. Haka abin
yake ga fannin mata. Akwai fim din da na
kalla, inda wata mata ta fito a Ustaziya,
amma da aka zo waka sai na gan ta sanye
da matsattsun kaya tana tikar rawa.
Har ila yau, haka kawai mawakanmu na
fina-finan Hausa, suka tsiro waka mai zubi-
da-tsari irin na Makosa, inda a cikin wakokin
nasa mawakin har wani lakabi yake wa
kansa da mai Makosar Hausawa. Ko a ina
Hausa ta samo Makosa kuma?
A karshe, ina kira ga masu shirya fina-finan
Hausa da su sani cewa, lokaci ya yi da ya
kamata su rungumi al’adu da addininmu
hannu biyu-biyu, su kuma zama masu kishi
da kare dukkan al’adun Hausa. Mu lura
yanzu, su kansu Amurkawa (Hollywood) sun
fi mayar da hankalin ga fina-finan al’adu,
kamar su Spartacus, Merlin, Legend Of The
Seeker da sauransu. A karshen–karshe, Allah
Ya sa wannan makalar ta zam mai
amfanarwa.
Bashir Musa, Marubuci, Manazarci da sharhi
kan al’amuran yau-da-kullum ne
08052585817, 08032493020

Saturday, February 5, 2011

DALILAN DA YASA GENERAL MUHAMMAD BUHARI YA DAUKI PASTOR BAKARE A MATSAYIN MATAIMAKINSA

A farkon makon nan ne dan takarar
shugaban kasa a jam ’iyyar CPC, Janar
Muhammadu Buhari ya zabi Fasto Tunde Bakare ya zama mataimakinsa.
Don jin yadda aka yi, Aminiya ta tattauna da
shi, ta kuma ji ra ’ayin wasu na kusa da shi
kamar haka:
Aminiya: Me ya sanya ka nace sai Fasto
Tunde Bakare ya zama mataimakinka a
takara da kake yi ta shugabancin kasar nan?
Buhari: A tsarin jam’iyyarmu hakkin dan
takarar shugaban kasa ne ya zabi wanda
yake so ya zama mataimakinsa, shi ya
sanya na bukaci Tunde Bakare ya cika fom
Aminiya: Ana ta yada sakonnin waya da ke
nuna cewa zaben Buhari zaben Musulunci
ne, me za ka ce game da haka?
Buhari: Ban yarda cewa ’yan jam’iyyarmu
ne suke yada wannan sakonni ba. Ina ganin
daga abokan hamayya ne, kuma mun dauki
matakin magance matsalar, domin ba shi
yiwuwa ka iya neman goyon bayan
kowane bangare na kasar nan ta hanyar
amfani da addini, idan kana bukatar zama
shugaban kasar nan amma ka yi amfani da
addini ba za ka yi nasara ba, domin tsarin
mulikin kasar nan bai ce ga wani addini da
gwamnati za ta rike ba. A Najeriya
Musulunci da kiristanci ne manyan addinai,
amma akwai wadanda suka rude suka ce ba
su yarda da wani addini ba kuma su ma
kana bukatar kuri’arsu, yaya za ka yi da
irinsu?
Aminiya: So suke su ce kai mai tsananin
ra’ayin addinin Musulunci ne?
Buhari: Sun ma riga sun fadi haka, tun a
shekarar 2003 na ziyarci bishop-bishop da
ke kasar nan.
Aminiya: Saboda an dangantaka da addinin
Musulunci ne ya sanya ka jawo Fasto Tunde
Bakare ya zama mataimakinka?
Buhari: A’a, ba don haka ba ne, Fasto
Bakare ya zo har nan ofishin tare da
mutanensa ya zauna a inda kake zaune ya
ce ya yarda cewa nine na fi dacewa daga
cikin ’yan takarar da suka fito suna son su
shugabanci kasar nan. Kuma ya fada wa
mutanen cocinsa a ciki da wajen kasar nan
cewa ni ne dan takaran da ya fi dacewa.
Wannan ba maganar addini ba ce, magana
ce ta wanda yake da mutane kuma ya
amince da tsare-tsarenmu, kuma ya fito ya
bayyana haka ba tare da an roke shi ba. Tun
watanni takwas da suka gabata Bakare bai
zauna ba yana ta kaiwa da kamowa wajen
tuntubar mabiyansa tare da jawo
hankalinsu game da mu.
Aminiya: A shekarar 2003 an ce ka bukaci
kiristoci su zabi kirista, musulmi su zabi
Musulmi, haka ne?
Buhari: Wannan ya faru ne a shekarar 2002,
abin da ya faru shi ne, wani malamin
addinin musulunci ne ya rubuta littafi a kan
shari’a ya bukace ni in shugabanci
kaddamar da littafin, shekarun malamin sun
kai 70, na ce masa zan halarci wurin . Daga
cikin manyan bakin da suka halarta akwai
marigayi Sarkin musulmi Maccido Abubakar,
ina jin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari
ma yana wurin. Idan ka tuna a shekara
2002 ba na cikin harkar siyasa, saboda haka
bayan an kaddamar da littafin sai aka ce in
yi jawabi a matsayina na shugaban taro, na
dubi littafin na ga ni ban san komi ba game
da shi da zan sharhi a kai ba, marubucin
littafin ya zauna a kasar Saudiyya shekara
11 yana nazarin shari’ar musulunci da
musulunci, babu yadda zan yi sharhi a kan
littafin domin ban karata ba. Saboda haka
na ce, mutanen Sakkwato kun san
mutanenku, kwanan nan za a fara harkar
siyasa, don haka ku zabi mutanen da za su
yi muku aiki kuma su yi wa kasa aiki da
gaskiya. Ga alama dan jaridan da ya rubuta
labarin a jaridar Thisday ba musulmi ba ne
kuma Bayarabe ne, bai jin Hausa, sannan ba
a Sakkwato yake zaune ba, ta yaya ya sami
labarin?
Aminiya: Da hausa ka yi magana a wurin ko
da turanci?
Buhari: Da hausa na yi magana, domin da
hausa aka gudanar da taron, to, a ina ya
samo wannan? Wani ne kawai ya tsara
labarin, kuma wannan na daya daga cikin
matsalolin da muke fuskanta kasar nan.
Aminiya: Ta yaya za ka samar da fahimtar
juna a tsakanin mabiya addinai?
Buhari: Samun fahimtar juna a tsakanin
mabiya addinai yana da sauki, muhimmin
abu shi ne ilimi. Idan muka ilmantar da
mutanenmu za su iya kula da kawunansu
kuma ba za su saurari wani shirme daga
kowa ba. Amma idan aka bari hakar ilimi ta
gurgunce, aka kawo maganar bambancin
addini da kabilanci, hakan zai cutar da kasa
ne. Saboda haka amsar da zan ba ka ita ce
mayar da hankali a kan ilimi, kada
shugabanni su ji tsoron ilimantar da
mutanensu domin suna jin tsoron idan suka
samu ilimi za su yi musu bore. Ta yaya za ka
iya gina kasa ba tare da ilimantar da
mutanenta ba?