Tuesday, January 15, 2013

Dariya: Tafiya Daga Kano Zuwa Lagos


Wata tsohuwa ce a garin Kano ta je tashar mota ta hau zuwa jihar Lagos, an fara tafiya kenan sai tsohuwar nan da tuni ta samu kujera ta zauna cikin fasinjoji tace Mallam Direba idan an je Kaduna ka sanar dani, direba dake tuki yace to Baba. An jima kadan Tsohuwa ta sake cewa Direba idan an zo Kaduna ka fada min fa, Direba ya hasala yace Gyatuma ai naji kuma ban manta ba, aka ci gaba da tafiya, can a wajen Kura tsohuwa ta sake nanata zancenta, yanzu kam sauran fasinjoji ma sai da suka ji haushinta, aka ce haba gyatuma ai ko Direba ya manta zamu tuna masa Amma kin dake sai kace wanda za'a sace ki.. Wasu daga ciki suka ce ayi ha}uri gigin tsufa ne ! Allah cikin ikon sa tsohuwa ta kwanta barci, Direba kuma Allah ya mantar dashi, haka ma sauran mutanen dake motar duk suka manta, tsohuwa bata farka daga barcinta ba sai da tafiya tayi nisa, tsakaninsu da Ikko bai fi 50km, sai tsohuwa ta farka, tayi mika tayi hamma tace ]a na har yanzu ba'a zo Kadunan bane? Nan take kowa hankalinsa ya tashi, aka fa]a wa tsohuwa halin da ake ciki, nan take ta rusa kuka.. Da jama'a suka ga haka sai aka yi shawara akan cewar dole direba yayi hakuri a koma Kaduna tunda matar nan ta tsufa da yawa, kuma bata da laifi tunda tayi ta nanatawa.. Aka yi karo-karo aka karawa direba kudin mai aka juyo Kaduna, can wajen Magriba aka iso, aka ce Baba gashi anzo Kaduna... Tsohuwa tayi mika ta juya tace mun zo? Akace kwarai kuwa, tace to Alhamdulillahi, tasa hannu ta bu]e jakarta ta hannu! Ta lalima ta dauko PANADOL ]an gwangwani guda biyu, ta jefa a baki ta bishi da ruwa, tace dama Jikata ce ta bani guda hudu tace lallai lallai na sha 2 a Kaduna maganin gajiya ne, in mun isa Ikko na karasa 2, to tun da yanzu na sha na Kaduna sai kuma munje Ikko sai na sha sauran biyun.