Wednesday, December 28, 2011

GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!!

Bayan sallama irin wadda addinin Musulunci ya koya mana "Assalamu Alaikum" da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai, nake gayyatar 'yan uwana maza da mata, yara da manya, dattijai da tsofaffi kai har ma samari da 'yan mata, taron kungiyar TSANGAYAR ALHERI na kasa baki daya, karo na II mai taken "KANO AGAIN 2012"

Za'a gabatar da laccoci guda a wurin wannan taro, wadda ta farko mai taken "Mahangar Musulunci game da sada zumunta a shafukan Yanar Gizo" Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shugaban hukumar rundunar Hizbah na jihar Kano zai gabatar. Sai lacca ta biyu mai taken "Cigaba da kalubalen da Yanar Gizo ta kawowa matasan Nijeriya" wadda Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq) mashahurin masanin Fasahar zamani, marubuci a shafin Kimiyya da Fasaha na jaridar Aminiya kuma malamin makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa dake shafin Yanar Gizo, zai gabatar. Sai sharhin wadannan laccoci daga bakin Malama Sadiya Adamu, shugabar kungiyar mata Musulmi reshen jihar Kano da kuma babban marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino.

Bayan wadannan laccoci akwai lambobin yabo da kungiyar zata raba ga wasu mutane, saboda irin jajircewarsu a bisa aikin alheri ga al'umma da kasa baki daya, sannan za'a bada irin wadannan lambobin yabo ga mashawartan kungiyar da kuma wasu daga cikin 'yayan kungiyar da suka yiwa kungiyar hidima ba dare ba rana domin ganin ci gaban kungiyar ta kowane bangare.

Za'a gudanar nan da wannan gagarumin taro a ranar Lahadi daya ga watan sabuwar shekarar miladiya (1st January 2012) a babban dakin taro na Sheikh Bashir El-Rayyah dake makarantar koyon harshen larabci (School for Arabic Studies [SAS]) Dake kan titin zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr. Ado Bayero. Da misalin karfe 11:00 Na safe. Uban taro Mai Girma Galadiman Kano, Alh. Tijjani Hashim.

A washe garin taron kafin komawar bakin da suka zo Kanon Dabo daga wasu jihohin a sassan kasar nan, za'a kai ziyara babban gidan Yari (Prison) na Kano sannan kuma za'a kaiwa Mai Girma Dan Masanin Kano Alh. Dr. Yusuf Maitama Sule ziyara girmamawa. Daga nan kuma sai a sallami baki kowa ya koma garinsu sai kuma wata shekarar idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.

Bashir Ahmad
Sakataren Riko na Kasa baki daya.

No comments:

Post a Comment