Friday, July 29, 2011

TSARABAR WATAN AZUMI

Azumi a addinin Musulunci na nufin kauracewa cin abinci, shan ruwa, fadin munanan maganganu, shan taba, saduwa tsakanin ma'aurata da kuma dukkan wani aiki da ya sabawa koyarwa addinin Musulunci tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana da nufi bautawa Allah madaukakin sarki.

Azumi na daya daga cikin shika-shigan Musulunci guda biyar, haka tasa ya zama wajibi ga dukkan Musulmin da ya balaga, a duk watan tara (Ramadan) na shekarar Musulunci kamar yadda Allah ya bayyana a cikin Al Kur'ani mai girma inda yake cewa "Ya ku wadanda suka yi imani, mun wajabta azumi a gare ku kamar yadda muka wajabtawa wadanda suka gabace ku, domin ku kara tunawa da Allah" Q2:V183

A watan Ramadan Allah ya saukar da Al Kur'ani mai tsarki ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Watan azumi wata ne na rahma, alfarma, gafara da karbar addu'a. Wata ne da dukkan wani Musulmi ke kara zage dantse wurin ibada da kyautatawa yan uwa Musulmai don samun rahmar Allah.

Amma abin mamaki wasu daga cikin Musulmai na yin amfani da wannan wata mai albarka wajen kara tsauwalawa yan uwa Musulmai, misali wasu daga cikin yan kasuwa da zarar watan azumin ya kusanto sai su fara tashin farashin kayan masarufi kamar shinkafa, nama, lemo, kayan miya da sauran kayan masarufi saboda ganin ya zama wajibi ayi amfani dasu, saboda duk wanda ya sha ruwa zaiso yadan karya da abinci mai dan dadi.

Haba bayin Allah, shin mai zai sa ba zamu rinka rage farashi ba idan watan azumin yazo sai akasinsa, shin bama ganin yadda yan kasuwa mabiya addinin Kirista ke yi ne idan lokacin Kirismeti yazo zasu rinka rage farashin kayayyaki, bai kamata a ce su suke wannan aikin kyautatawa ba mu ba.

Wasu ma daga cikin yan kasuwan namu suna siyan kayan ne suna boyewa kafin watan azumin don idan watan yazo su sami riba mai yawa. Haba yan uwa, mu tuna fa komai yawan wannan riba da zamu samu Allah bazai taba sa mata albarka ba. Shin ina ta shekarar da ta gabata? Shin wane amfani tayi mana nasan wadannan tambayoyi zasuyi wahalar amsawa.

Sai dai ko yaushe na Allah basa karewa, wasu bayin Allah daga cikin yan kasuwan su kuma suna yin iya kokarinsu kanin sun kyautata a wannan wata mai albarka, suna rage farashin kayansu ko da kuwa zasu tashi babu ribar komai, amma sai kaga saboda Allah yasa albarka sunfi yan uwan nasu walwala da jin dadi, ga kuma lada mai tarun yawa da yake can yake jiransu ranar alkiyama.

A karshe a matsayinka na dan kasuwa yi kokari ka rage farashin kayanka koda kuwa kana ganin ba zaka samu riba da yawa ba, idan Allah ya sawa abinda zaka samu komai kankantarsa albarka yafi wanda zaka samu komai yawansa marar albarka. Sannan ya kamata mu yi kokarin ciyar da junanmu koda da kwayar dabino guda daya ne.

Allah ya karbi ibadunmu a wannan wata mai albarka, Allah yasa muna cikin wadanda za'a yanta a yi musu gafara, Allah ya taimaki yankinmu na AREWA ya kara daukaka shi tare da kasarmu Nigeria baki daya.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

2 comments:

  1. Allah sakamaka da alherinsa. Mun godeAllah sakamaka da alherinsa. Mun gode

    ReplyDelete
  2. Halima Tijjani NasidiAugust 7, 2011 at 3:56 PM

    Bashir, fatan wadanda kayi tsokacin dominsu zasu duba da idon basira. Tabbas rayuwa ta lalace yan kasuwa basu da lokaci gallazawa yan uwa Musulmai sai lokacin azumi. Allah ya kyauta.

    ReplyDelete