Wednesday, May 4, 2011

INA MAFITA MATASAN AREWA?

Matasan Arewa gaisuwa gareku, ya
zabukan da suka gabata? Matasan
Arewa, mafi yawancinmu Hausawa ne
kuma mabiya addini daya wato
Musulunci sannan masu akida daya
wato akidar son ganin Nigeria ta
cigaba, ana gogayya da ita cikin
manya manyan kasashen duniya
masu tattalin arziki, kamarsu America,
England, Germany da sauransu.
Shin yaushe wannan buri namu da
muke ta mafarki da muradi zai cika?
Shin kuma wace irin gudunmawa
zamu bayar wajen ganin wannan buri
ya cika? A tunani bamu da wata
gudunmawa illa ta zaben shugabanni
nagari, tabbas munyi hakan har karo
uku amma Allah bai cika mana
wannan buri ba (wato shugaban da
muke ganin shine nagari Allah bai
bashi nasara ba karo ukun) kuma
gashi ahalin yanzu ya sanar da ajiye
muradinsa nason zama shugaban
namu ba don ya karaya ba sai don
yawan shekaru.
To yanzu wane mataki kuma ya dace
mu dauka nan gaba, kowa yana sane
da yadda wannan kabila tamu ke
zama koma baya a ko yaushe a kasar
nan, alhali mune mafiya rinjaye,
Hausawa ya kamata mu farka baccin
ya isa haka kafin lokacin da za'a zo a
tashe mu ace mu ba yan kasar bane,
Eh mana tabbas idan zamu tafi a haka
to nan gaba za'a ce Hausawa ba yan
Nigeria bane.
A tunani na mafita itace mu shiga
wayar da kan yan uwanmu matasan
Arewa, game da halin da wannan
kabila ke ciki, kowa yana sane da
cewa ba wata kabila a kasan nan da
bata da iyaye sai kabilarmu ta Hausa,
wadanda suke ikirarin sune iyayen to
dasu akewa kabilar zagon kasa, kuma
kowa yasan haka. A duk cikin
Hausawa babu wani mutum guda
daya da yake kare wannan kabila da
kuma kwato mata hakkinta.
Hakan tasa mu matasa ya zame mana
dole mu tashi mu karbi jagorancin
wannan kabila mu kwace ta daga
hannun makiyanta, idan kuwa ba
haka ba, wata ran za'a wayi gari
zaman Nigeria yayiwa Bahaushe
wuya. Mu tashi muyi gwagwarmaya
dan kwato hakkinmu a wurin masu
siyar mana dashi.
"Mu tashi mu farka yan Arewa mu bar
bacci aikin kawai ne" Mamma Shata.
Allah ubangiji ya bawa Arewa
jagorori nagari, masu kishinmu,
al'adarmu da addininmu. Amin.

1 comment:

  1. Bashir Yahuza MalumfashiMay 5, 2011 at 4:47 AM

    Allah Ya taimake mu baki daya, amin. Hakika ya dace mu tashi tsaye, mu yi ayyukan kwarai da gabobinmu, sannan kuma mu tabbatar da cewa mun ci gaba da ilimantarwa da fadakarwa ga al'ummarmu, domin mu gane inda kanmu ke mana ciwo.

    Allah Ya yi mana jagora, amin.

    ReplyDelete