Tuesday, August 23, 2011

Abin mamaki ko abin dariya? Sa'insa tsakanin Obasanjo da Babangida

Chief Olusegun Obasanjo, da General Ibrahim Badamasi Babangida tsofaffin shugabannin kasar nan ne, kuma suna daga cikin dattawan kasar nan da ake ganin girmansu saboda irin mukaman da suka rike da kuma gwagwarmayar da suka sha game da yakunkunan basasar kasar nan, da kuma kokarinsu na ganin kasar ta zauna a matsayin tarayya guda mai cikakken iko.

Abin mamaki ko nace abin dariya duk da dattijantaka irin ta wannan bayin Allah wadanda duk sun haura shekaru 60 a duniya, amma bai hana barkewar zazzafar sa'insa a tsakaninsu ba, ko sun manta da cewa 'yayansu dasu zasuyi koyi oho.

Obasanjo ya bayyana Babangida a matsayin wawa a shekaru 70, kuma bai amfanarwa kasar nan komai ba a shekaru 8 da yayi na mulkin soja. Dalilinsa kuwa, yace yayi amfani da izu na 26 aya ta 4 da ta 5 na cikin littafin Karin Magana (Proverbs).

Shi ma Babangida ya bayyana mulkin da Obasanjo yayi tsakanin 1999 zuwa 2007 ba za'a kira da komai ba sai bata lokaci domin kuwa bai tsinanawa kasar nan komai ba sai ci baya. Ya kuma bayyana Obasanjon a matsayin mai karancin tunani da hangen nesa.

Nan shi ma Obasanjon ya cigaba da cewa IBB yana da damar gina tashoshin wutar lantarki, lokacin da yake kan mulki, saboda irin kudin da kasar ke dasu a lokacin, kamar yadda shi ya gina Jebba dam, da Shiroro dam kuma ya fara shirin gina Egbin wanda Shehu Shagari ya gina a lokacin mulkinsa.

Obasanjo yace "Na gina dam guda biyu saboda muhimmancinsa, kowa yasan wutar lantarki ita ce kashin bayan ci gaban duk wata kasa mai tasowa. Tun lokacin da aka gina tashar Egbin har na dawo mulki a 1999 babu wata tasha wutar lantarkin da aka sake ginawa, kusan shekaru 20 kuma Babangida yayi shekaru 8 a lokacin yana mulki, wannan ba karamin rashin cigaba bane.

Bayyana mulkina na 1999 da 2009 da IBB yayi a matsayin bata lokaci da koma baya, ya kamata ya nemi afuwar fadin hakan. Na karanta inda yake cewa a lokacin mulkinsa ya bada ribar demokradiya, duk da ya nuna nadamarsa, to amma masu iya magana na cewa wawa a shekaru 40, wawa ne har abada. Ni kuma nace nadama a shekaru 70, makararriyar nadama ce, kuma nadama ce ta kabari".

A martanin da Babangida yayi ta bakin mai magana da yawunsa, Prince Kassim Afegbua yace "wannan ba dabi'ar Babangida bace ya shiga irin wannan sa'insa marar ma'ana. Tarihin Obasanjo a bude yake, lokacin da ya roki IBB ya bashi damar kara wa'adin mulkinsa, IBB ba wawa bane sannan. Lokacin da aka sake shi daga kurkuku, aka yi masa wanka aka bashi kayan alfarma ya saka a karshe ya zama shugaban kasa, IBB ba wawa bane sannan, sai yanzu da yakai kololuwar tunaninsa, zai cirewa IBB zani a kasuwa, ya kira shi da wawa"

Anan dai ya kamata talakawan Nigeria wadanda suka ga mulkin wannan dattijai guda biyu suyi alkalancin wanene wawa, Babangida ko shi kansa Obasanjon?

A matsayina na wanda naga mulkin Obasanjo na 1999 zuwa 2007, idan nine alkali zan kira Obasanjo ne wawan ba IBB ba, idan nayi duba da irin mulkin kama karyar da ya shinfida a kasar nan. Yayi ikirarin ya gina tashoshin bada wutar lantarki guda biyu a mulkinsa na soja, amma kuma ya zo ya lalata wutar kasar nan a mulkinsa na farar hula, shin wannan ba wawanci bane? Ya zo ya samu man fetur a kasa da naira 30 lita daya, ya maida shi sama da naira 60, shin wannan ba wawanci bane? Ya zo ya samu kasar nan da tsaron da kasashen waje ma na tsoronsa, amma ya kori manyan sojoji, ya lalata tsaron, idan su al'ummar kasar ma ke masa barazana, wannan ba wawanci bane?

Amma kuma kai tsaye ba zance Obasanjo wawa ba, saboda ko kadan bansan yadda shi IBB ya gudanar da nasa kalar mulkin ba ko nace nasa kalar wawancin. A wannan sa'insa aikinmu kadai kallo, inda akayi abin dariya, muyi dariya. Inda akayi abin mamaki, muyi mamaki. Inda akayi abin haushi muyi Allah wadai.

A karshe, fatanmu Allah ya kawowa kasarmu dauki. Ya fatattaki duk wasu azzalumai, Ya canja mana adalai a madadinsu.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

No comments:

Post a Comment