Wednesday, October 26, 2011

JAMILAH TANGAZA: Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram

JAMILAH TANGAZA: Yaya Za'a Warware Matsalar Boko Haram: Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akai. Dalili kuwa shine suna ganin muddin suka yi magana watakila ‘yan Bo...

Sunday, October 23, 2011

Ka Zama Mai Yunwar Ilimi, Ka Zama Mai Budaddiyar Zuciya - Steve Job

"Babu mai son ya mutu. Hatta wadanda ke ganin sun yi aikin kwarai ba su cika son su mutu ba, sai dole. Amma kuma babu
makawa, mutuwa ce masaukin da za ta tattaro mu duka. Babu wanda ya taba guje wa mutuwa
a baya. (Kuma babu wanda zai guje mata a gaba) haka lamarin ya kamata ya zama. Domin mutuwa ce abin da har zuwa yau duniya ba ta taba samar da irinta ba. Ita ce abin da ke kawo canji a rayuwa. Ita ce ke share tsohuwar al’umma don kawo sabuwa. A halin yanzu da nake muku wannan jawabi, ku ne sabuwar al’umma, amma nan ba da dadewa ba, watarana za ku zama tsohuwar al’umma, an share ku don kawo wata sabuwar ta maye gurbinku. Ku yi mini afuwa idan wannan
zance nawa ya firgita ku, amma wannan ita ce hakikanin gaskiya.

Rayuwarku ‘yan kwanaki ne takaitattu, don haka kada ku shagala wajen kwaikwayon rayuwar wani. Kada ku zama
‘yan abi yarima a sha kida. Kada ku yarda surutan wasu su hana ku bin shawarar da za ta fisshe ku a rayuwa. Abu mafi muhimmanci shi ne, ku zama masu juriya wajen bin abin da zai zama maslaha a rayuwarku da fahimtarku. Domin su ne kadai suka fi kowa sanin abin da kuke son ku zama. Duk wani abin da ba wannan ba, to, ya zo a bayanshi".

Wannan wani gutsuren jawabi ne, daga cikin wani dogon jawabi da marigayi Steve Job, shugaban Kamfarin kera kayayyakin sadarwa na Apple Inc., ya gabatar a ranar bikin yaye dalibai na Jami'ar Stanford "STANFORD COMMENCEMENT ADDRESS" a watan June na shekarar 2005.

Inda a karshen jawabin nasa ya kara da cewa "Ka zama mai yunwar ilimi. Ka zama mai budaddiyar zuciya. Kuma a kullum nakan yi wa kaina wannan fata. Don haka na ga dacewar yi muku wannan fata ku ma, a daidai wannan lokaci da kuke kokarin fara wata sabuwar rayuwa bayan barin Jami'a, cewa: "Ku zama masu yunwar ilmi a kullum. Ku zama masu budaddiya zuciya wajen karbar fahimta" Nagode matuka!!!

Saturday, October 22, 2011

Tafiya Mabudin Ilimi (Bashir Ahmad a Sokoto Birnin Shehu)

Gaskiyar Hausawa da suka ce "Tafiya Mabudin Ilimi" duk da na yarda da hakan, amma ban gama tabbatarwa ba, ko nace ban taba jarrabawa ba, sai lokacin da nayi tafiya daga Kano zuwa Sokoto. Taron kungiyar Dandalin Siyasa e-Forum, karo na 3, Tafiyar da ban tabayin mai nisanta ba, a tarihin rayuwata, sai dai kuma nan gaba idan Mai duka ya barmu da rai da kuma lafiya.

Wannan tafiya tawa, mai kunshe da kalubale, alfahari, ilimi gami da abubuwan al'ajabi, nayi tane ranar 14 October zuwa 16 October 2011. Tabbas wannan tafiya ko shakka babu, ta shiga cikin tafiyoyin da bazan taba mantawa dasu ba (Unforgetable Journey).

Da farko a ranar tafiyar na tashi daga bacci tun da sanyi safiya na fara shirye shirye, kamar mai barin kasar kwata kwata. Na fito daga gida misalin 7:56am ba tare dana kammala 'yan shirye shirye na ba, saboda ina tsoron kar mota ta tashi ta barni, kamar yadda aka tabbatar min za'a hadu 7:30am a tashi zuwa birnin Shehu 8:00am.

Na isa kofar shiga tsohuwar Jami'ar Bayero, inda za'a hadu, amma saboda Nigerian Time da wani bawan Allah yayi bamu tafi ba sai 9:00am. Abinka da sabon shiga, fara tafiyar ke da wuya na dakko mujallar MURYAR AREWA na fara karantawa don kar ko gyangyadi ya dauki ni a shige wani wuri ba tare dana kashe kwarkwatar idona ba. Bayan na gaji da karatun jaridar sai na dauki wayata, na shiga shafin sada zumunta na Facebook na rinka sanarwa da yan uwa da abokanan arziki halin da tafiyar tamu ke ciki. Su kuma suna taya mu adduar fatan alheri gami da sauka lafiya.

Can da tafiya tayi tafiya sai wayar ma na hullata a aljihu, nayi zuru na zubawa sarautar Allah ido, wato dai na gaji kenan amma saboda tsegumi irin nawa, ko kadan ban nuna gajiyar ba, balle na kishin gida har bacci ya samu damar kwashe ni.

Nasan masu karatu ku kanku kunsan a wannan tafiya idanuwa na sun sha kallon abubuwan da ba sai na tsaya ina bata bakina wurin lissafa muku su ba, kai zahirin gaskiya ma dai idan nace zan lissafo zan iya yi muku ragi, don haka zan fadi wasu abubuwa guda biyu zuwa uku da suka fi daukar hankalina. Na farko naga shimfida shimfidan tituna amma ba motocin yawatawa akansu a jihar Katsina. Na biyu naga wani rusheshen dutse a jihar Zamfara, wanda idan mutum ya nemi kallo tsayinsa to tabbas hular zata fadi kasa ba tare da ya sani ba. Abu na uku shine karamcin da Sakkwawa sukayi mana, wanda bazan taba mantawa ba.

A takaice dai bamu isa cikin birnin Shehun ba, sai misalin 3:36pm, kai tsaye aka wuce damu, Sokoto Guest Inn, wanda shine masaukinmu. Kai mutane Sokoto akwai iya karbar baki sai kace wadanda suka zo Kano suka dauki darasi, domin kuwa da isarmu ba abinda suka tarye mu dashi sai wani daddadan kilishi hade da sassanyan lemo. Kasan Bakano bai da filako nan take muka tashi da wannan hidima.

Misalin 9:30pm na wannan rana, aka debe mu cikin zungureriyar mota, zuwa wurin wani shakatawa mai suna Daddy's Smart dake cikin birnin na Shehu, domin gabatar da Cultural Night wanda kungiyar ta Dandalin Siyasa ta shiryawa 'yayanta domin debe kewa. A wannan wurin na sha dariyar da tayi kusan sa cikina ciwo, domin kuwa tsohon dan wasan Hausan nan na barkwanci Golobo (Boloko) shine ya cashe tare da jama'arsa.

Washe gari ranar 15 October, ranar da aka ware don yin taron, mun tashi mun shirya, sannan muka nufi wurin da za'a gabatar da taron a dakin taro na makarantar koyon karatun Al Kur'ani da Kimiyya na Muhammad Maccido, amma kafin a fara gabatar da laccocin da za'a gabatar sai da aka kai ziyarar girmama fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III. Bayan an dawo daga fada sai aka koma wurin taron.

An gabatar da laccoci a wurin taro wadanda suka shafi halin da kasarmu Nigeria ke ciki a halin yanzu, kamar irinsu TABARBAREWAR TSARO, ILIMIN BOKO, sai kuma DEMOCRADIYA wanda Prof. S. A. Yakasai na jami'ar Shehu Usman Danfodio da kuma Dr. Usman Muhammad na jami'ar Birnin Tarayya Abuja suka gabatar.

An kammala taro misalin 3:30pm, daga nan bayan an gabatar da sallar La'asar sai kuma aka tafi kai wata ziyarar girmamar gidan Alhaji Abubakar Alhaji (Alhaji Alhaji) Sardaunan Sokoto na yanzu, dattijon arziki, namiji uban masu kudi da 'yan boko. An gabatar masa da kungiya, ya kuma yi farin ciki gami da karfafa gwiwa.

Sai kuma wajen 9:30pm aka tafi wurin dinner a Mr Bigs wanda aka kai har zuwa 11:30pm daga nan kowa ya tafi masaukinsa. Kuma wannan shine abu na karshe da aka shirya gabatarwa a taron.

Washe gari ranar 16 October rana ce da duk wanda yaje birnin na Shehu zai waiwayi inda ya fito, a ranar ne muma da misalin 9:30am muka kama hanyarmu ta dawo gida Kanon Dado mai mata mai mota mai Dala da Goron Dutse.

A karshe ina kara mika godiyata ga dukkan SAKKWATAWA wadanda suka dauki dawainiyarmu tunda muka je har muka dawo gida. Allah yasa da alheri, Allah ya kara hada fuskokinmu da alheri, ameen!

Wednesday, October 12, 2011

Ibada ko Siyasa? Sunan Kwankwasiyya a Gidan Alhazan jihar Kano a birnin Makkah

Hausawa suka ce wai "Sabon salo kidan ganga da lauje" kullum siyasar kasar nan sai zama take yi gara jiya da yau, misali idan yau wannan mai mulki wa'adinsa ya kare wani kuma ya karba, sai kaga talakawa na murnar an samu canji, amma da zarar wanda ya hau an fara ganin rikon ludayinsa sai kaji talakawan sun dawo suna fadin ai gara na jiya dana yau. Ko me ke kawo haka oho. Ko kuma mu duk haka muke Nigeria ba'a zuciyarmu take ba, bama son canji da ci gabanta, mun fiso mu zauna kurar baya kodayaushe, Allahu a'alamu.

Ba komai ne ya sanin fadin hakan ba, sai ganin yadda masu mulki ke wuju - wuju da shafawa talakawa jan baki, ba tare da suna sara suna duban bakin ga tarinsu ba. Anan zanyi misali da siyasarmu ta jihar Kano, wadda masu iya magana ke yiwa lakabi da "Siyasar Kano Sai dan Kano" A lokacin da tsohon gwamna, wadda ya mayarwa da sabon gwamna dake kan karagar mulkin jihar yanzu, bana mantawa duk lokacin daya gudanar da wani sabon abu musamman a bangaren addini, sai kaji ana kiran wai ai fakewa yake da addini yana wawashe kudaden talakawa.

To sai gashi yanzu bayan shudewar tsohuwar gwamnatin, masu shafa jan baki da jar hula suka cigaba da jan ragamar gwamnatin, sai suma suka shigo da sabon salo kala - kala. Wanda duk abin dake faruwa ba wanda ya bani mamaki kamar wannan. Abin mamaki shine kuwa yadda itama sabuwar gwamnatin ke neman aron mayafin tsohuwar gwamnatin ta yafa, wato itama ta fake da addinini ta wawashe kudaden talakawa. Domin kuwa hatta a bangaren aikin Hajjin bana ma sai da gwamnatin tasa siyasa a ciki. Saboda a gidan da alhazan jihar Kano ke yada zango a birnin Makkah sai da aka rubuta KWANKWASIYYA HOUSE da baro - baron rubutu yadda ko makaho ya shafa zai ji alama. Ba a iya nan sabuwar gwamnatin ta cuso harkokin siyasa ba, bangaren aikin Hisbah da kwamitin Shari'a ma duk haka abin yake.

A karshe ba ina kare wani bangare bane, ko goyan baya tsakani wadannan gwamnatotin biyu, kawai ina son na aika wani sakona ne zuwa ga wadanda abin ya shafa don susan tuni mun gane duk wani shiri da suke yi don wawashe dukiyar talakawa.
Fatanmu Allah ya bawa wannan sabuwar gwamnati ta masu jar hula karin gwiwar yi mana aiki da kawowa jiharmu ci gaba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Sunday, October 9, 2011

Muhimman Shafukan Gidajen Yanar Gizo domin karuwar Musulmai

Yanar gizo (Internet) a wannan zamani ta zama abokiyar rayuwa, wanda masu amfani da ita ba zasu iya koda kwana daya ba tare da sun kai ziyara ba, sai dai da wani kwakkwaran dalili, kamar rashin lafiya ko rashin service. A wani bincike da masana suka gabatar a wannan zamani jama'a sunfi cinye lokacinsu a wurin amfani da Yanar Gizo sama da komai. Wasu na cinye lokacin nasu a bincike bincike da kalle kalle marar amfani, wasu kuma basu da aiki sai neman abokan hira daga sassan duniya daban - daban, wasu kuma Allah ya taimake su, suna cinye lokacin nasu ne akan karin neman ilimi, musamman ilimin addinin Musulunci.

Ga duk masu sha'awar amfanar lokacin a duniyar yanar gizo ga shafuka masu muhimmanci domin Musulunci da Musulmai:-

Islami City (http://www.islamicity.com) - shafi ne daya kunshi abubuwa masu yawan gaske kamarsu bayani game da Shika-shikan Musulunci, Lokutan sallah, litattafai da sauransu.

Qur'an Complex (http://www.qurancomplex.org) - shafi ne da tsohon sarkin kasar Saudi Arabia King Fahaq bin Abdallah ya samar dashi game da Al Qur'an Mai girma.

Fatwa Islam (http://www.fatwaislam.com) - shafi ne dake cike da fatawoyin manya manyan Malam na da dana yanzu. Sannan kuma mutum zai iya tura fatawarsa a dawo masa da amsa nan take.

Islam Online (http://www.islamonline.com) - wannan shafi ne daya danganci bangaren labarun abubuwan dake faruwa a duniyar Musulunci. Sai kuma hira ta keke da keke (Video Chat) tsakanin Musulmai dake sassan duniya daban - daban.

Islam Question & Answer (http://islamqa.com) - shafi ne dake kunshe da tambayoyi da amsoshinsu dangane da abubuwan da suka shigewa Musulmai duhu.

Ja'afa Mahmud Adam (http://www.jaafarmahmudadam.org) - wannan shafin na kunshe da wa'azin Marigayi Malam Ja'afar Mahmud Adam da kuma fatawoyinsa.

Haruna Yahya (http://www.harunyahya.com) - Shafin haziki kuma fasihi Harun Yahya wannan yake bayani game da kimiya da fahasa, a mahangar Musulunci.

Idan kuma mutum yana neman wani abu bai samu ba, a cikin wadannan shafuka dake sama zai iya ziyarta shafin bincike na Google don bincikowa. Allah ya kara taimakon addinin Musulunci da Musulmai baki daya.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Friday, October 7, 2011

Lokaci ne babban makiyinmu ba Mutuwa ba

Mutuwa ita ce karshen duk wani abu da Allah (SWA) Ya halitta, mutum, aljan, dabbobi da sauran halittu na ciki ruwa, na doron kasa har ma dana sararin samaniya. Mutuwa na dauke mutum ba dare da saninsa ba, ma'ana ko ya shirya ko bai shirya ba. Kuma bata son kai, wato ta dauki talaka tabar mai kudi, don tarun dukiyarsa, ko tadauki mai kudi tabar talaka don jin tausayinsa. Bata barin yaro bare babba, bata barin mace bare namiji. Ita ke raba 'yayan da iyayensu, ba tare da tayin la'akari da halin da zasu shi ba. Ita ke raba ango da amarya duk kuwa da irin soyayyar dake tsakaninsu. Saboda kuwa bata sabawa umarnin mahaliccinta kuma mahaliccinmu Allah daya.

Wasu mutanen na ganin mutuwa bata da tausayi ko kuma itace babbar makiya a gare mu, musamman a wurin mutanen da ta dauke musu iyaye tabarsu cikin watangaririya, halin kuncin rayuwa, da rashin kulawa ta musamman.

Gaskiya ni a tunanina, mutuwa bata da laifi ko kadan, idan ka hada ta da LOKACI, domin kuwa shi ke tura mutum koyaushe kusa da mutuwa har ta dauki shi. Da zarar an haifi mutum duk wani dakika (second) daya da yayi, to lokaci yana kara kusan tashi da mutuwa ne. Mutuwa bata zuwa ta dauki wani har sai lokaci ya dauke shi ya kaita wurinta, wato sai wa'adinsa (lokacinsa) yayi. Ga shi lokacin kullum kara gudu yake, Shekara ta zama kamar wata, wata ya zama kamar sati, sati kuma kamar kwana. Kuma babu yadda zamuyi mu tsayar da gudun lokacin ko murage shi. Lalle karshen duniya ya zo.

Ta hanya daya zamu ci ribar wannan lokaci tun kafin ya kaimu ga mutuwarmu, wannan hanya itace mutattara rayuwarmu gaba daya mu koma kan Al-Kur'ani da Sunnar Manzon Allah (SAW). Muyi kokarin ganin kar dakika daya ta wuce ba tare da munyi amfani da ita ta hanya mai kyau ba. Koyaushe ya zamana ace bamu da lokacin daya fi na bautar Allah ko neman ilimin yadda za'a bauta masa. Idan mukayi haka to munci ribar lokaci.

A karshe karmu manta duk dakika daya da tawuce bazata sake dawowa ba har abada. Mu daina cinye lokacinmu, wurin kalle kalle marar amfani. Yi amfani da lokacin da kake cinyewa a shafukan Internet ta hanya mai amfani. Yawaita ziyartar shafukai fatawoyin addinin Musulunci dan karu da abinda baka sani ba. Maimakon karanta tarihin manya manyan kafirai makiya Allah, makiyanmu mu Musulmai binciko tarihin manya manyan malamai da suka bada muhimman gudunmawa a addinin Musulunci.

Allah yayi mana jagora a dukkan al'amuranmu na yau da kullum. Ya bamu ikon yin amfani da lokacin daya bamu ta hanyar bauta masa bata hanyar saba masa ba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

Tuesday, October 4, 2011

Labarin Sarki da Babban Amininsa mai taken "Yayi Kyau"

Abu-asid-az-zinayya, sarki ne dake mulkin daular Zinayya a can kudu maso gabashin sahara, wato bangaren tekun Nilu daga bangaren dama.

Abu-asid ya kasance sarki mai adalci ga al'ummar da yake mulka, ga tausayin talakawa da karrama baki, wannan dalili yasa koyaushe baki sai tururuwar zuwa wannan kasa suke yi, wasu na zuwa domin fatauci, wasu kuma na zuwa don yawon bude ido da shakatawa.

Sarki Abu-asid mutum ne mai sha'awar fita farauta tun yana karami, hakan tasa bayan ya hau kujerar sarauta mai bai daina fita wannan farauta ba. Yakan shirya fita yawon farauta lokaci - lokaci don debe kewa da nishadi, koyaushe idan zai tafi farauta suna tafiya ne da abokinsa mai suna Usudul-azman, wanda suka taso tare tun lokacin kuruciya. Saboda saukin kan sarki Abu-asid daya zama sarki ma bashi da abokin zuwa farauta da shawara kamar shi. Usudul-azman yana da wata dabi'a da ta zame masa jiki, wanda shi duk abinda ya faru a gare shi mai kyau ko akasin haka sai yace "YAYI KYAU"

Wata rana sarki da abokinsa sun fita farauta, sai suka ci karo da barewa, a kokarin harbin wannan barewa, sarki bai seta bundigar daidai ba, hakan ta jawo ya harbi hannunsa na hagu, nan take babban dan yatsan sarki ya fadi kasa cikin jini. Duk da irin wannan hali da sarki ya tsinci kansa, budar bakin Usudul-azman abokin sarki, sai yace "YAYI KYAU" Nan take sarki cikin fushi da kunan rai, yana gurnani kamar tsohon zakin da ya shekara baici nama ba yace karya ne baiyi kyau ba.

Saboda wannan magana da Usudul-azman ya fadawa sarki, bayan sun dawo daga farautar, sarki yayi umarnin a kaishi gidan kurkuku a daure shi, kowa yayi mamakin wannan hukunci na sarki, domin kuwa ba'a taba gani ya yiwa wani bawansa irin wannan hukunci ba tare da yin wani laifi ba, bare kuma Usudul-azman babban amininshi. Haka dai kowa ya gama fadin albarkacin bakinshi yayi shiru, domin ba mai iya zuwa yace sarki bakayi daidai ba.

Bayan kusan shekara daya da faruwar wannan al'amari, sarki yana cikin wani kungurmin daji mai nisan gaske yin farauta, wanda duk jarumtaka irin tashi amma hankalinshi bai kwanta da wannan daji ba. Kwatsam! Sai jin ihun arnan daji yayi ta gaba da bayansa, kafin yayi wani kokarin kubuta daga wurinsu tuni sun kamashi, suka daddaure shi hannu da kasa, suka nausa cikin daji dashi, sun ihun samun nasara. Da isarsu gida aka fara shirye - shiryen watanda, daman kuwa sun dade basu ci naman mutum ba sai dabbobi. A lokacin da sarkin wannan arnan daji yazo yanka sarki sai ya gane ashe babban dan yatsansa na hannun hagu ya gutsere. Nan take cikin bakin ciki yayi kururuwa yace ba cikakke bane, wato wani bangare daga jikinsa bai cika ba. Kuma daman a al'adarsu idan suka kama mutane da nakasa a jikinshi basa ci, nan take sarkin nasu ya bada umarni a sake shi ya kama gabansa.

Tun akan hanya sarki Abu-asid ya tabbatar lalle maganar da amininsa, Usudul-azman ya fada lokacin daya harbi hannunsa abune mai kyau, domin kuwa da badon hakan ba da tuni anyi wadanta da namansa yau. Saboda haka yana isa gida yayi umarnin a saki abokin nashi, kuma ace yana son yin magana dashi. Bayan Usudu ya fita sai yazo wurin sarkin don jin mai ya faru. Sarki ya fada masa duk abinda ya faru gare shi, kuma ya roki afuwar abokin nasa saboda sawa da yayi a daure shi.

Budar bakin Usudul-azman sai yace "YAYI KYAU" Nan sarki ya tambaye da mai yake nufi da hakan? Kai da kasha wahala a kurkuku amma kace yayi kyau? Sai Usudu yace "eh mana da badon ina cikin kurkuku ba da tuni ni anyi watandar nama na, saboda da tare da ni za'a kama mu, kuma ni cikakke ne. Nan sarki shima da kansa yace lallai "YAYI KYAU"