Tuesday, December 14, 2010

MU CIGABA DA SON MATANMU BAYAN AURE

Akwai wani mutum mai suna Balarabe, yana
neman wata budurwa mai suna Ladidi da aure. Kullum
yana zuwa hira gidansu da yamma budurwar
tana kawo masa ruwan sha a duk lokacin
da ya zo gidansu hira.
Wata rana da yazo
sai kakar Ladidi ta ce mata: “Ga kunu mai
dumi ki kai wa Balarabe ko zai sha.” Ladidi ta ce to. Sai
ta zo ta tambayi saurayin cewa zai sha
kunu? Bayan ya yi dan murmushi ya ce "eh zan
sha", sai Ladidi ta koma cikin gida ta dauko
kunun da nufin ta kawo masa. Tana zuwa
kusa da shi sai santsi ya dauke ta ta zame ta
yi tangal-tangal ta fadi, kwanon kunun nan
ya kife a jikin sabon dinkin shadda da
wannan saurayi ya ci ado da ita. Hankalin
wannan budurwa ya tashi, ta rude ta rasa
me za ta ce masa. Amma shi gogan naka bai
damu da jika shi da kunu da ta yi ba,
hankalinsa yana kanta ne, yana cewa: “Ladi
di sannu, ina fatan dai ba ki ji ciwo ba?” Yana ta
kokarin daga ta da lallashinta, ita kuma da ta
tashi abin da ya fi damun ta shi ne yadda ta
bata masa ado da ruwan kunu. Nan take ta
je ta debo ruwa a buta tana zuba masa yana
wanke jikinsa, tana ta ba shi hakuri. Shi
kuma yana murmushi yana ce mata, ai ba
komai. Da ya ga Ladidi tana ta nuna
damuwarta kan abin da ya faru, sai ya nuna
mata alamun cewa za ta bata masa rai, ya za
a yi ta rinka damuwa kan abin da baitaka-
kara-ya karya ba! A haka dai abin ya wuce.
Bayan wani lokaci sai aka daura auren Balarabe
da Ladidi, Allah Ya azurta su da ’ya’ya guda
biyu. Wata rana da yamma Balarabe ya dawo gida
don yin wanka, sai Ladidi ta kawo masa
abinci. Bayan ta ajiye, sai ta je debo masa
ruwa a kofi da nufin idan ya gama cin abincin
ya sha ruwa. Bisa hadari sai ga babbar
rigar da Balarabe ya tube ta sarkafe Ladidi ta fadi
kasa, ruwan da ke kofin ya zube a jikin
Balarabe, ai sai ya mike tsaye ya rinka
bambami, kai ka ce wuta ta zuba masa. “Ke
dai wallahi ban san ranar da za ki yi hankali
ba! Sam ba ki da lissafi da natsuwa! Idan ban
da hauka da rashin hankali, me ya jawo
haka? Ke dai kam Allah wadaran ki........!”
Karshe dai wannan dalilin sai da ya janyo
Balarabe ya saki Ladidi.

Mu yi nazarin wannan abin da idon basira,
lokacin da Balarabe ke neman matarsa da aure,
ta yi masa barin kunu mai zafi a jikin sabbin
tufafinsa, amma bai nuna bacin ransa ba,
hasali ma yana nuna wannan abin ba komai
bane illa hatsari. Amma yau barin ruwan
sanyi ya zama tamkar ruwa narkakkiyar dalma! Mu duba
yadda ya damu da ita a wancan lokacin,
amma yau ba damuwarsa ne ta ji ciwo ko
ba ta ji ba, shi dai kawai laifin da ta yi masa
yake kallo.

Ya kamata Maza murin ka tuna baya lokacin da matayen mu suka saba mana ba kawai mu yanke hukunci a lokacin ba.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020

Saturday, December 11, 2010

KISHI ASALI YA SAMO

KISHI dai wata damuwa ce da takan sami
zuciyar mutum, ko kuma shi mutum ya sa
kansa a cikin wata damuwa a lokacin da
yake ganin alamar zai rasa wani abu da
yake matukar kauna, wanda idan mutum
ma bai yi hankali ba sai ya shiga cikin wani
irin hali na kaka-nika-yi, har ma ya zo yana
da-na-sani.
Kodayake kishi iri-iri ne, amma wanda muka
fi sani, kuma muke magana a kai, shi ne
kishi na tsakanin matan da ke auren miji
guda. Shi kishi ya samo asali ne tun zamanin
kakanmu Annabi Ibrahim (A.S) A cewar
wasu Malamai, wai tsakanin matansa Saratu
da Hajara. A lokacin da Allah bai ba wa
Saratu haihuwa ba, sai Sarkin Masar ya bai
wa Saratu, Hajarah domin ta rika taya ta
aikace-aikace da wasu hidimomin gida.
Daga bisani ita Saratu ta shawarci mijinta
Annabi Ibrahim (A.S) ya auri Hajarah ko Allah
Zai ba shi haihuwa.
Allah, Mai hikima, cikin ikonSa, bayan an
daura aure da dan lokaci kadan, sai Hajarah
ta sami ciki. Hakan bai yi wa Saratu dadi ba,
ya kuma sosa mata zuciya. Cikin bakin ciki,
ta shawarci mijin nata da ya sa a huda wa
Hajarah kunnuwa da hanci. A cewarta, yin
hakan zai nuna cewar ita kuyanga ce. Bisa
ga ikon Allah sai Hajarah ta kara kyau da
wannan hujin kunne da hanci da aka yi
mata. Har wa yau Saratu ta ce a’a. A daura
wa Hajarah awarwaro, a sa mata ’yan
kunne. Yin haka ya sake kara mata kyau
wanda ma ko wucewa take sai an san
matar Annabi ce ke wucewa.
A karshe duk abin nan da ake yi bai gamsar
da Saratu ba, sai cewa ta yi, ta ga Hajarah
tana kumburi don haka maigida ya fitar da
ita a gidan, kada ta sa musu wata cuta. Allah
mai girma da daukaka Ya umurci Annabi
Ibrahim da ya dauki matarsa wato Hajarah
ya kai can wani gari (Makka) wanda a yau
ya zama tsarkakakken wurin da kowane
Musulmi ke burin ziyarta. Duka shawarwarin
nan da Saratu ta yi ta ba wa Annabi Ibrahim,
ta yi ne a bisa kishi.
To ashe ke nan kishi yana da asali, amma ba
wai ana nufin ya zama halas ba ne don ya
samo asali a wurin Saratu da Hajarah. Kishin
wannan zamani ya sha bamban, nesa ba
kusa ba da irin kishin da Saratu ta nuna. A
yanzu akan nemi a yi kashe–kashe da
asarar dukiya. Matar aure ta kan bi karuwa
gidanta, ta ci mata mutunci, wai don ta ji
labarin mijinta na neman ta. Haka kuma
budurwa ta bi matar aure gida ta ci
zarafinta. Ballantana tsakanin kishiyoyi abin
ba a cewa komai.
Abin tambaya a nan shi ne, shin me ake wa
kishi? To ra’ayin wasu matan dai ya yi nuni
da cewar mazan su ne umul aba’isin da ke
haddasa kishi, a lokacin da suka kasa yin
adalci tsakanin matansu. Alal misali kai ne ke
da mata biyu sai ka nuna fifikon wannan da
‘ya’yanta a kan daya, ka ga dole ne a nan za
'a samu damuwa, wadda ka iya haifar da
kishi tunda dukkansu soyayya ce ta sa ka
tara su, don haka dole ne ka yi adalci, a
tsakaninsu.

Wasu mazan kuwa na ganin wulakancin
matan ne kan ishe su, su shiga aure-aure.
Saboda a lokacin da mace take jin kai, sai ta
yi ta nuna wasu irin halaye daban-daban, a
inda ka yi gargadi ka gaji, dole ne ka nemi
wata wacce za ta kwantar ma da hankali.
Yin hakan kuma shi ke sosa zuciyar mata. A
takaice dai soyayya ake wa kishi.
To, wane lokaci ne ya kamata a nuna kishi?
Alal hakika idan mace ta ga an fita harkarta
kwata-kwata, wato, ba a yi da ita, ta yadda
miji bai kulawa da ita ko ‘ya’yanta, to, a nan
fa dole ne hankalinta ya tashi, saboda ganin
a da shi nata ne ita kadai, a yau kuma ya
koma nasu.
Kashi casa’in bisa dari na maza haka suke,
da zarar sun sami sabuwar amarya ko da ta
’yar tsana ce, sai kwata-kwata su juya wa
uwargida baya, har sai in ruwa ya kare wa
dan kada, sannan a dawo yana tsilla-tsilla a
gefen teku.
Bugu da kari akwai wata babbar matsalar
da ke addabar mata a wannan lokaci ta
yadda maza suke bata wa matansu na aure
suna a wurin abokansu. Misali miji ne ya
sami sabani da matarsa, maimakon ya yi
kokarin yi mata nasiha ko ya gaya wa
iyayenta, a’a, sai dai ka ga ya tafi wata
matattara da ake kira Chamber, yana yi wa
matarsa tonon silili. Wani ma, wallahi, har
yadda yake kwana da matarsa yake fadi.
Yin haka ya kazanta. A nan za a ba wa
namiji shawarar ya je ya kara aure. Auren
da zai yi ba wai don raya sunnar Manzon
Allah (SAW) ba ne, a’a, sai dai don ya ci
zarafin matar gida.
Haka kuma tun daga waje zai zayyana wa
budurwar irin halayen matarsa ta gida, in ta
dauro ma akan yi wa amaryar alkawarin da
zarar ta shigo za a kori ta gidan. A nan idan
ba a iya korarta ba, to, sai a yi ta zaman
kwari, kowa na ji da kanshi, a yi ta zuba
kishi iri-iri. Daga nan in ba a yi hankali ba sai
mazuga su shiga tsakaninsu, su tura su ga
halaka ta hanyar bin gidan bokaye don
neman asirin samun gindin zama a wurin
miji. Uwargida na neman kwatar ’yanci,
amarya na cewa sai ta fita ta bar mata gida.
To, boka na iya yi wa mutum abin da Allah
bai yi niyyar yi masa ba?
Har ila yau akwai wasu mazan da kansu da
kuma hannayensu bibbiyu suke rura wuta a
gidansu, su haddasa fitina, su hana zaman
lafiya, ta yadda namiji yake zana munafiki
tsakanin matansa. Shi wannan namijin, shi
zai ta kai da komowa tsakanin matansa,
wato, in ya je wurin wannan sai ya ce, ai ga
abin da waccan ta ce, ko take yi, sannan
idan ya koma wurin waccan sai ya ce, ai ga
abin da wannan ta yi, ga abin da ta ce. Shi
dai yana jin dadin ya ga kawunansu a
rarrabe, wato a yi ta fada saboda shi.
Jahilan maza har cewa suke in mata suka
hada kansu, namiji ba ya jin dadi. Mu kuma
a wurinmu mata ba abin da hakan ke
haddasawa sai koma baya, ga rashin
kwanciyar hankali, domin ko shi kansa mijin
a cikin fargaba yake a duk lokacin da ya
tunkari gida, sai dai idan ba gida daya ya
hada su ba.
Bari in ba mata misali na wani gida da nake
aminci da su. Kullum na kai ziyara zan iske
matan mutamin su uku tare da maigidansu,
wannan na yi mai, tausa, waccan na
mammatsa masa kafafuwa da sauransu. A
koda yaushe suna cikin farin ciki tsakaninsu
da maigidansu. Da na tambaye shi, ko wane
irin asiri ne ya yi wa matansa?. Sai ya nuna
cewa babu asiri a ciki, illa kawai, dukkan
matan nasa masana ne, kuma shi ba ya
auren mace face sai ya koyar da ita
tarbiyya, na yadda za ta yi zama tare da shi
da kuma kishiyoyi kamar yadda Annabi
(SAW) ya zauna tare da matanSa.
A karshe ina shawartar mata su yi hakuri a
kan maganar kishiya, tunda Allah ne da
kanSa Ya umurci maza da yin aure fiye da
daya. A Alkur’ani Allah Ya ce “Ku auri mata
bibbiyu ko uku, ko hudu, amma in kuna
tsoron ba za ku yi adalci ba, to, ku auri
daya” Suratul Nisa’i. Sannan Manzo Allah
(SAW) Ya ce “Ku yi aure ku hayayyafa,
domin na yi alfahari da ku ranar alkiyama”
Saboda haka aure fiye da mace daya ba
aibu ba ne, in dai an yi don raya sunnar
Manzo ne, tabbas Allah Zai taimaki bawanSa.
Ga mazan kuma ina shawartar ku da ku ji
tsoron Allah! Ku yi hattara! Ku guji
gamuwarku da Allah! Kada ku ga kamar
Allah Ya ba ku ’yanci na aure da saki, ku ce
za ku yi yadda kuke so. Mata amanar Allah
ne gare ku, matukar kuka ci amana, ko
shakka babu za ku tsaya a gaban Allah ku
fuskanci shari’a. Idan muka yi koyi da
yadda Manzon Allah (SAW) ya zauna da
matansa, tabbas za mu samu rayuwa mai
inganci da albarka daga mu har zariyarmu.

Haka nan ina kara shawara jama’a maza da
mata, mu dage mu nemi ilimin Islama,
musamman abin da ya shafi zamantakewar
aure, komai kake yinsa cikin ilimi ya fi dadi,
ya fi sauki. Allah Ya ba mu ikon yi, Ya kuma
sa mu dace da rayuwa mai albarka. Amin.

SIYASAR KANO, A ZABEN 2011

Siyasar Jihar Kano ta dade tana ba ’yan
kasar nan mamaki. Wannan shi ya sa ake yi
mata kirarin “siyasar Kano sai Kano” Wadansu kuma na da ra’ayin cewa “ba'a
mulkin Kano sau biyu” Tabbas kirarinta na
farko yana da muhalli ba a Kano kadai ba
har a Nigeria baki daya. Gwamna Ibrahim
Shekarau ya dakushe ra’ayin “Ba'a mulkin
Kano sau biyu” saboda zarcewar da ya yi,
inda shekara mai zuwa zai cika shekara
takwas a kan mulkin Kano.
A wannan karo za a raba rana ne tsakanin
jam’iyyun siyasa uku watau, Jam’iyyar ANPP
mai mulkin Jihar da Jam’iyyar CPC sai kuma
Jam’iyyar PDP da aka amshe mulki daga
hannunta a zaben 2003. Amma wasu na
ganin cewar tarnakin siyasar na nan
tsakanin Jam’iyyun ANPP da CPC ganin
yadda suke da magoya baya, amma wasu
na ganin cewa duk wanda yake ganin
Jam’iyyar PDP ba barazana ce ga sauran
Jam’iyyun biyu ba, to wata kila baya kasar
Kano lokacin da Jam’iyyar ta yi zagayen
motsa jam’iyya, inda dimbin magoya
bayanta suka tare ta a daukacin kananan
hukumomi 44 da jihar take da su.
Ba nan gizo ke saka ba musamman idan
muka yi la’akari da matsalolin da ke cikin
jam’iyyun uku a kan fitar da ’yan takararsu
a zaben raba gardamar jam’iyyun siyasa da
za a gudanar daga ranar 26 ga watan
Nuwamba zuwa 15 ga watan Janirun badi.
A Jam’iyyar CPC akwai ’yan takara a kalla
biyar da suka hada da: Kanar Lawal Jafaru
Isa, Tsohon gwamnan JiharKaduna da
Injiniya Magaji Abdullahi da Muhammad
Abacha dan marigayin shugaban kasa Janar
Sani Abacha da Dokta Auwal Anwar da kuma
Rufa’i Sani Hanga. Masu nazarin yadda
siyasa ke tafiya sun yi hasashen cewa
Kanar Lawal Jafaru Isa ne ya fi cancantar
jam’iyyar ta tsayar amma bisa dukkan
alamu akwai kishin-kishin cewa Rufa’i Sani
Hanga ne dan-lelen shugabannin jam’iyyar
da Ahmadu danzago ke jagoranta bisa
dalilin da ba su bayyana ba. Har ila yau
wasu na cewa akwai yarjejeniya ta
karkashin kasa tsakanin sauran ’yan takarar
3 ta cewar za su mara wa daya daga cikinsu
baya idan har aka ci gaba da nuna musa
bambanci wanda kuma hasashe jama’a ya
nuna Kanar Lawal Jafaru Isa na iya zama
zabinsu.
A ra’ayoyin mutane da dama suna gani
warware wannan matsala na iya kawo wa
Jam’iyyar nasara a zabe mai zuwa ganin
yadda jama’ar Kano suka yi na’am da
Jam’iyyar CPC , wasu kuma na ganin ko
babu komai farin jinin da Janar Buhari yake
da shi zai iya kawo musu babbar nasara
kamar yadda ya kafa Gwamnatin ANPP a
zaben 2003. Haka nan kuma ita kadai ce
jam’iyyar da ba ta taba mulki ba balle a ce ta
saba wa wani.
Idan muka waiwayi Jam’iyyar ANPP mai
mulkin Jihar Kano za mu ga yadda ’yan
takara da suka hada da: Salihu Sagir Takai Kwamishinan ruwa na jihar da Injiniya
Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo,
Mataimakin Gwamna Ibrahim Shekarau da
Senata Kabiru Gaya da Lawal Sani kofar
mata da Malam Ibrahim Khalil, suka fito da
niyyar karawa da junansu a zaben raba
gardama. Tarnakin da suke fama da shi a
jam’iyyance sun hada da zargin da ake yi na
cewa Malam Ibrahim Shekarau ya fifita
Salihu Sagir Takai a kan sauran ’yan takarar
hudu wanda hakan ke neman kawo cikas a
jam’iyyar da har wasu ke tunani yi wa
jam’iyyar zagon kasa idan har aka yi musu
rashin adalci. Haka nan kuma akwai babban
kalubalen da ke fuskantar gwamnatin Jihar
Kano ta ANPP, shugabannin kananan
hukumominta sun shigar da kara kotu
saboda sauke su da aka yi daga kan mulki.
Akwai tunanin cewa duk wadanda aka yi
wa ba daidai ba zasu iya yi wa jam’iyyar
zagon kasa wanda wasu na ganin
wadannan shugabannin kananan
hukumomi da aka sauke sune ’yan siyasar
kwarai da ya kamata jam’iyyar rike.
Wasu kuma suna hangen cewa maganar da
Alhaji Mahmud Ado Bayero, Hakimin Fagge ya
yi a kan biyan diyya ga wadanda kwayar
maganin Troban ta kamfanin Pfizer ya
nakasa tamkar wani haske ne mai nuni
yiwuwar akwai takun saka tsakanin
masarautar Kano da gwamnatin jihar, kuma
ko da masarauta ba ta cika shiga siyasa kai
tsaye ba, suna da jama’a irin na su
musamman idan aka yi la’akari da irin
martaba da Sarkin Kano yake da ita ga
mutanen jihar.
Wani kalubalen da ake hange kuma shi ne,
idan har aka samu matsala a zaben raba
gardama tsakani Gwaman Shekarau da
mataimakinsa Alhaji Abdullahi Tijjani
Muhammad Gwarzo yana iya haifar wa
jam’iyyar matsalar da Allah kadai ya san
idan za ta tsaya musamman idan
mataimakin na shi ya samu goyon bayan
sauran abokan neman tsayawa takarar
gwamna da suka rasa.
Ita kuwa Jam’iyyar PDP, masu nazarin
siyasar Kano na ganin a aljihun tsohon
gwamnan jihar, Alhaji Rabi’u Musa
Kwankwaso ta ke, saboda har inda yau take
ba za a ce ga takamaiman dan takararta ba
sai dai akwai irinsu Kanar Habibu Shu’aibu
da suka bayyana niyyar tsayawa takararsu
da kuma shi kansa Dokta Rabi’u Musa
Kwankwaso, sai kuma wasu da ke jita-jitar
fitowar Hon. Faruk Lawal. Masu
hasashen siyasa na ganin cewar da wuya
PDP ta yi tasiri musamman idan aka yi
la’akari da dalilan da suka sa Kwankwaso ya
rasa kujerarsa a zaben 2003, watau
matsalar da ya samu da ’yan fansho da
sauran ma’aikata, sai kuma wasu da ke
ganin faduwarsa na da nasaba da rashin
jituwarsa gidan sarautar Kano.
Akwai kuma masu ganin cewa bai kamata a
tsayar da Kwankwaso ba saboda yana da
takardar tunhuma watau white Paper,
saboda haka suna son a fito da sabon dan
takara wanda ba shi da wata matsala da za
ta hana shi cin zabe, sai dai kuma wasu na
ganin wannan ba matsala ce ba tun da a
cewarsu ’yan majalisa sun wanke
Kwankwaso kuma gashi dan lelen Shugaba
Goodluck Jonathan. Duk da haka dai ana
ganin cewa kwankwasiya shugabannin
Jam’iyyar PDP suke yi wa biyyaya, haka nan
kuma ita ke da rinjayen magoya bayan
Jam’iyyar PDP a Kano.
Daga karshe dai masu fashin bakin siyasa
na ganin cewa idan har Jam’iyyar PDP ta
tsayar da Rabi’u Musa kwankwaso a
matsayin dan takararta to zai riga rana
faduwa saboda jama’a ba su san shi,
dalilinsu kuwa shi ne, ya gwada takara ba
sau daya ba yana faduwa kuma ya tsaida
dan takara ya fadi, sa’anan kuma ya kasa
gano inda yake da baraka balle ya dinke ta
ga shi kuma yana goyon bayan Shugaba
Goodluck inda wasu ke cewa sun ce ko
nawa za su kashe sai sun kawo Jihar Kano
A takaice dai guguwar siyasar ta fi kadawa
tsakanin jam’iyyun CPC da ANPP wanda
wasu ke ganin muddin Jam’iyyar CPC ta ba
Kanar Lawal Jafaru Isa takara ganin yadda
mutane ke son shi zai yi tasiri kwarai
wanda har ana yi masa kallon zama
gwamnan jihar, sai dai kuma wasu na ganin
cewar muddin Gwamna Ibrahim Shekarau
ya bari aka yi zaben raba gardama kamar
yadda dokar Jam’iyyar ANPP ta tanadar
akwai kamshin za su iya tabukawa wajen
samar da gwamna a jihar.

(Aminiya)

Thursday, December 9, 2010

FALLASAR WIKILEAKS NA NEMAN TADA HANKALIN HUKUMOMIN NIGERIA


Bayanai na baya-bayan nan da shafin
intanet na Wikileaks mai kwarmata
bayanan sirrin da aka tsegunta masa
ya wallafa, sun bayyana irin rawar da
Amurka ta taka a lokacin da
Goodluck Jonathan yake matsayin
mukaddashin shugaban Nigeria a
yayinda shugaba na wancen lokaci
Umar Yar'adua yake jinya.

Bayanan sun ambato Goodluck
Jonathan da cewar ya na kokarin
shawo kan jama'ar Arewacin Najeriya
wadanda ba su saki jiki da shi ba, ta
hanyar amfani da wasu manyan
mutanen yankin arewan, musamman
tsohon shugaban Nigeria
Abdussalami Abubakar wanda zai
lallashi iyalin 'Yar Adua, su saka shi, ya
yi murabus cikin daraja da mutunci.

Haka kuma zai bi shawarar Amurka ta
nisanta kansa da Olusegun
Obansanjo.
Jakadiyar Amruka a Najeriya a lokacin
Robin Saunders ta gana da
mukaddashin shugaban kasar
Najeriya a lokacin wato shugaban
yanzu Goodluck Jonatahan ranar 26
ga watan Fabrairun bana, jim kadan
bayan da marigayi shugaba 'Yar'adua
ya koma Najeriya daga Saudiyya inda
yayi jinya.

Jonathan ya kuma fada mata cewa a
saninsa jam'iyyar PDP ta zabe shi ne a
matsayin abokin takarar shugaba
'YarAdua a 2007 saboda yana
wakiltar yankin Niger Delta.
Ya ce "ba an dauke ni ba ne na zama
mataimakin shugaban kasa saboda
ina da wata kwarewa ta siyasa. Ba ni
da ita. Da akwai mutane da dama da
suka fi cancanta su zama mataimakin
shugaban kasa, sai dai kuma wannan
ba yana nufin wani zai iya juya ni ba.
Bayanan suka ce Goodluck Jonathan
ya ce yana kokarin shawo kan
jama'ar Arewacin Nigeria wadanda ba
su saki jiki da shi ba, ta hanyar amfani
da wasu manyan mutanen yankin
arewan, musamman tsohon
shugaban Nigeria Abdussalami
Abubakar wanda zai lallashi iyalin 'Yar
'Adua, su saka shi, ya yi murabus cikin
daraja da mutunci.
Hakan in ji Goodluck zai fi sauki a
madanin samun goyon bayan kashi 2
cikin 3 na majalisar ministoci mai
mutum 42. Ya kuma bayyana yadda a
wani zaman majalisar minitocin aka
tashi baram-baram inda aka yi ife-ife.


Goodluck ya dora laifin rudani a kan
mutane hudu
Goodluck ya dora laifin rudanin da
aka shiga a Najeriya a lokacin kan
mutane hudu dake kewaye da 'Yar
'Adua, wato uwargidansa Turai 'Yar
'Adua, da babban mai tsaron lafiyar sa
Yusuf Tilde da dogarin shugaba
'Yar'Adua Mustapha Onoe-dieva da
Tanimu Kurfi mai baiwa marigayin
shawara kan harkokin tattalin arziki.


Haka kuma ya ambaci Abba Ruma
ministan ayyukan noma da Adamu
Aliero ministan birnin Abuja a
matsayin wasu masu hana ruwa
gudu.


Goodluck Jonathan yace ya yarda
wadannan mutane suna da wata
muguwar aniya, tun da yayi imanin
cewa shugaba 'Yar Adua baya cikin
hayyacinsa.

A game da yadda zai tunkari warware
dambarwar siyasar Najeriya kuwa
mukaddashin shugaban kasa
Goodluck Jonathan ya ce zai mai da
hankali kan shirya zabe na fisa-bi-
lillahi.


Kuma baya tsinkayen zai tsaya
takarar shugaban kasa a 2011,
kodayake dai a cewarsa "idan suna so
in tsaya, to wannan wani abu ne da
zan nazarta".

Kuma jakadiyar Amruka ta bayyana
masa cewa wajibi ne ya sallami
shugaban hukumar zabe mai zaman
kanta wato INEC, Prof Maurice Iwu
saboda baya nuna wata alama ta
mutunta tsarin mulki na gari.
Jakadiyar ta yi barazanar cewa
muddin Goodluck bai kori Iwu ba, to
gwamnatin Amurka zata janye duk
wani tallafi na shirin zabuka a Nigeria.

Bayanan na Wikileaks sun ce
jakadiyar Amurka ta kuma baiwa
Mukaddashin shugaba Goodluck
shawarar nisanta kansa da tsohon
shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo,
kuma Goodluck ya ce zai yi hakan.

(BBC HAUSA)
www.bbchausa.com

Monday, December 6, 2010

SHIN "TAKAI" ZAI TAKI SA'A A KANO A 2011 KUWA?

Malam Salihu Sagir Takai, babu tantama kan
cewa shi ne dan takarar Gwamna a karkashin
Jam ’iyyar ANPP. Gwamna Malam Ibrahim
Shekarau ke son ya zama magajinsa a zaben
shekara mai zuwa, hakan na nuni da cewa
Shekarau ya fi natsuwa da ganin cancantar
Takai kan sauran mabiyansa. Kamar
Mataimakin Gwamna Abdullahi T. M. Gwarzo da
Garba Yusuf da Sani Lawan kofar-Mata da
Injiniya Sarki Labaran da Musa Iliyasu
Kwankwaso da Malam Ibrahim Khalil.
Kafin zancen ya fito fili kan goyon bayan
Takai rahotannin sun nuna cewa mabiya
Malam Shekarau a jam ’iyyance sun ba shi
dama ya zabi duk wanda yake ganin ya fi
cancanta su yi masa biyayya. Amma da ya
buga gangar zuwa ga Takai, sai masu
sha ’awar takarar Gwamna da ’yan siyasa suka
yi tsaye, don rawar ba za ta yi daidai da kidan
ba, inda suka fara koke-koke da kokarin nusar
da Gwamna ya yi adalci wajen fitar dan
takara. A takaice suna kira da a yi zaben fitar
da gwani a jam ’iyyar don su zabi wanda suke
ganin ya fi dacewa ya gaji Gwamna Shekarau.
Takai ya taba zama Kwamishinan kananan
Hukumomi a gwamnatin Shekarau, Gwamnan
ya zabe shi ne bisa wasu dalilai na kashin
kansa, har yanzu bai fito ya bayyana wa
al ’ummar Jihar Kano dalilansa na fifita Takai a
kan sauran masu neman takarar Gwamna ba.
Shekarau ya yi amfani da wannan damar ce
ya tsayar da dan takara, don ya san cewa a
tsari na dimokuradiyya da wuya Gwamna ya
tsayar da dan takara, jam ’iyyarsa ba ta tsayar
da nata ba.
Jam ’iyyar ANPP a Jihar Kano ta yi farin jini,
masu son tsayawa takarar Gwamna a cikinta,
suna da yawa kwarai kuma jiga-jigai a
jamiyyar, irin su Mataimakin Gwamna
Abdullahi Tijjani Gwarzo da Sanata Kabiru Gaya
da Sani Lawan kofar-Mata da Malam Ibrahim
Khalil da Habibu Sale Minjibir da sauransu suna
nan.
A bisa tsarin jam’iyyu, a kan ba ’yan takara
damar yin sulhu a tsakaninsu, in hakan ta
gagara sai a sake ba su wata dama ta shiga
zaben fitar da gwani, a nan ne ake gwada
farin-jini da kwanji don samun wanda ya yi
nasara a tsakaninsu. Kukan da ’yan takara a
Jam’iyyar ANPP a Kano ke yi, don hanyar da
aka dauka ga dukkan alamu suna zargin ba za
a yi masu adalci ba ne.
Tuni mafi yawan ’yan takarar sun fito karara
sun bayyana rashin amincewa, da take-taken
Gwamna Shekarau na kin ba su dama ta
hanyar cusa nasa dan takarar. Sanata
Mohammed Bello ya fito ya bayyana wa
duniya cewa in har ba a ba shi damarsa ba, zai
fice daga jam ’iyyar da hakarsa ba ta cimma
ruwa ba, ya cika alkawari ya tafi Jam’iyyar
PDP. Haka kuma sauran ’yan takarar duk sun yi
magana da murya guda wajen kin yarda da
tsaida Takai da kuma mara masa baya.
Mene ne ya sa Gwamna Shekarau ya kafe a
kan Takai ne dan takara? Ko kuwa yana ganin
cewa shi ne zai ci gaba da manufofin
gwamnatinsa? Shin shi ne zai kawar da kai ga
masu bukatar a tono abin da ya binne bayan
ya bar mulki? Ko kuma yana ganin a tunani da
hangen nesa irin nasa Takai ya fi sauran masu
neman Gwamnan Jihar Kano cancanta ce?
Sauran ’yan takarar suna ganin sun cancanta,
sun kuma taimaka wa Shekarau a zaben
shekarar 2003 da 2007. Don haka, suna ganin
suna da goyon baya da masoya da magoya
baya da za su iya kai su gaci a zabe mai zuwa.
Wannan ya sa suka yi gangami, inda
kowanensu ya nuna wa duniya karfinsa a
siyasance.
Tsayar da Takai na fuskantar tirjiya, ba daga
’ yan takarar Gwamna kawai ba, har da sauran
’yan takara na kananan hukumomi da jami’an
gwamnati da masu fada-a-ji a Jam’iyyar ANPP.
Saboda wasu dabi’u da ake zargin Takai yana
da su, kamar rowa da rashin iya hulda da
jama ’a.
Shawara ga Malam Ibrahim Shekarau, idan har
yana son Jam ’iyyar ANPP ta taka rawar gani a
zabe mai zuwa, ya kamata a matsayinsa na
uba kuma jagora, ya hada kan ’ya’yan
jam’iyyar. Ya kuma zama mai yin biyayya ga
tsarin dimokuradiyya, ta hanyar ba kowa
damarsa, ta bari a yi zaben fitar gwani a
jam ’iyyar ba tare da fitowa karara yana mara
wa wani dan takara baya ba.
Gwamna Shekarau ya sani cewa idan ya matsa
sai Takai, hakika wadansu daga cikin
aminansa da abokan tafiyarsa a siyasa za su
iya yin tsalle su ma fice daga jami ’iyyar, da ma
ba ta gama farfadowa daga halin da ta shiga
ba sakamakon ficewar Janar Muhammadu
Buhari daga jam ’iyyar, sannan wadansu za su
iya kin ficewa daga jam’iyyar su kuma yi mata
zagon kasa.
Ya kamata Gwamna Shekarau ya tambayi
kansa, shin yana da tabbas in Takai ya zama
Gwamna ya samu biyan bukatunsa? Ba ya
kallon yadda ake kwashewa tsakanin
gwamnonin da suka sauka da wandanda suka
gaje su?
Shekarau kada ya manta akwai jan aiki a
gabansa, ko da ’yan jam’iyya kansu a hade
yake, kafin su iya lashe zaben shekarar 2011.
A kullum Jam ’iyyar PDP a Jihar Kano sai kara
karfi take yi ga kuma sabuwar Jam’iyyar CPC
da Janar Buhari ke ciki, in har sun tsaida dan
takaran Gwamna mai nagarta su ma za su iya
lashe zaben Gwamna a Kano a shekarar 2011.
Tsakanin Gwamna Shekarau da Takai da masu
adawa ba a san maci tuwo ba, sai miya ta
kare. Ko Takai zai taki sa ’a ya zama magajin
Shekarau? Lokaci ne kadai zai bayyana mana.
Shehu Mustapha Chaji

Friday, December 3, 2010

TAKAITACCEN TARIHIN BABAN SADIQ


Abdullahi Salihu Abubakar wato (Baban Sadiq) an haife shi a anguwar Hausawa, Garki Village dake karamar hukumar Birni (Munincipal) a cikin babban birnin tarayya Abuja, a shekarar 1976 shekaru 34 da suka wuce kenan.

Asalin kakannin Baban Sadiq dama wasu daga cikin mazauna anguwar Hausawa, Garki Village daga Kanon Dabo suka zo, shekaru sama da dari biyu (200) da suka gabata.

Baban Sadiq yayi karatunsa tun daga Firamare, Sakandare har zuwa Jami'a duk a cikin babban birnin tarayyar Nigeria Abuja.

A halin yanzu Baban Sadiq na da shedar digiri akan fannin tsimi da tanadi (Economics) sannan kuma har yanzu yana kan neman Ilimin Al-Qur'ani da sauran fannoni daban daban kan addinin Musulunci.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) mutum ne mai sha'awar rubuce-rubuce da karance-karance da kuma son binciken ilimi kan fanni daban daban musamman Tsimi da tanadi (Economics) da kuma Fasahar Sadarwar Zamani (Information Technology) da sauran fannoni da dama.

Baban Sadiq mutum ne mai son ganin al'ummar Hausawa sun fahimci fasahar zamani, kuma Allah ya hore masa juriyar karatu da rubutu daidai gwargwado.

Saboda yadda yake son ganin Hausawa sun fahimci fasahar zamani suma an tafi dasu kamar kowacce al'umma kar a barsu a baya Baban Sadiq ya rubuta litattafai kan wannan harka mai muhimmanci ga kowacce al'umma. Duk da littatafan bai kammala su ba amma akwai "Fasahar Intanet A Saukake" cikin harshen Hausa wanda ke kan hanyar fitowa ko wane lokaci daga yanzu.

Sannan kuma sai wadanda yake rubutawa sun hada da: Tsarin Mu'amalar Da Fasahar Intanet da kuma Wayar Salula Da Tsarin Amfani Da Ita.

Duk da haka Baban Sadiq bai tsaya nan ba yana gabatar da kasida mai suna "Fasahar Intanet" a jaridar Aminiya duk mako, inda masu karatu ke aiko da tambayoyin abinda basu gane ba yake basu amsa nan take daidai yadda zasu gane.

Bayan haka Baban Sadiq na da makarantar Kimiya da Fasaha a shafin intanet mai suna "Makarantar Kimiyya Da Fasahar Sadarwa" wanda za'a iya samu a (http://fasahar-intanet.blogspot.com) wannan makaranta na da dalibai masu yawa a ciki da wajen Nigeria, kamar su Niger da Cameroon.

A karshe Baban Sadiq na da aure da 'yaya uku Sadiq, Nabilah da kuma Hanan.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
+2348032493020

Wednesday, November 24, 2010

BRIEF HISTORY OF LATE COM. BILYAMINU ABDULLAHI ADANJI

Bilyaminu Abdullahi Adanji was born on 12th July 1983 from the family of Alhaji Abdullahi Adanji.

He attended Umaru Illahu M.P.S. Birnin Kebbi, due to his brilliance, selfishness, dedication and brightness to his educational endeavors, he always took the 1st or 2nd position since his primary one up to primary six. He also became the head boy at the end of his primary education. He then proceeded to Nagari College Birnin Kebbi from 1997 to 2003 for study his secondary school education.

Due to his humble background and zeal to be educated, he was then admitted into Waziri Umaru Federal Polytechnic Birnin Kebbi, where he obtained Ordinary National Diploma. Then he did his compulsory Industrial Training (IT) with Civil Engineering Department at Ministry of Work and Transport Birnin Kebbi in 2006 and higher National Diploma in Civil Engineering. While graduating, he did not disappoints his determination to succeed. So he came out with flying colour result in 2009.

He has keen interest in politics. Always his ambition is to brings change in the system of hatred and impunity to politic of love and ideologies. Bilyaminu gone with many dreams and hope for better Nigeria. He was a good reader and writer. He has attended an uncountable convention of the Association of the Nigerian Authors (ANA) and a lot of others authors association.

He is a member of different associations which include; Nigerian Youth Forum (NYF), Muryar Talaka and Sansani Samari Da Yanmata (Tsangayar Alheri) on Facebook and Dandalin Siyasa, Yan Arewa, Marubuta and Hausa Da Hausawa all in Yahoogroups and many more associations. He also a creator and owner of many groups on website (Social Network).

He was unmention loved to Prophet Muhammad (SAW) and he was very respect and support for Karl Max, Merlin Luther King Jnr, Malcolm X, Barrack Obama, Chinua Achebe, Nuhu Ribadu, Prof. Zainab Alkali and above all he love General Muhammad Buhari (RTD) as his role model.

He is the best son to his family loved by all, cared by all, cherished even by his enemies. Bilyaminu does not believe with a word "enemy" he regarded all as his friends and tries to treat all the best way he can.

Allahu Akbar! Com. Bilyaminu died on 22nd November 2010. As a result of shortest illness.
Bilyaminu is one of the luckiest people on the earth, he died in his mother's hand after she has made some duas for him and then he passed away with KALIMATUL-SHAHADA!

Allah ya jikan Com. Biyaminu Adanji, Allah ya gafarta masa dukkan zunubansa. Ya haskaka kabarinsa. Ya sa Aljannut-Fiddaus ce gidansa na karshe. AMEEN!!!

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
+2348032493020

Tuesday, November 9, 2010

YADDA NA FAHIMCI GENERAL MUHAMMAD BUHARI (RTD)


Yadda na fahimci General Muhammad Buhari a matsayi na na dalibi dan shekara kasa da 20 wanda a lokacin da Buhari yayi mulkinsa ko haifa ta ma ba'ayi ba. Kuma lokacin da ya rike hukumar PTF bani da wayo sosai. Amma duk da hakan tabbas na fahimci General Muhammad Buhari mutum ne mai gaskiya, rikon amana da kaunar talakawa.

Dalili kuwa shine yadda General Muhammad Buhari ya rike manyan manyan mukamai a kasar amma har yanzu talakawa ke sonsa kuma suna muradin ya dawo ya sake mulkarsu a matsayin shugaban kasa,
Na fahimci a kasar nan ko mukamin Chairman mutum ya rike to a karshe magoya bayansa ne zasu dawo suna yakarsa saboda rashin gaskiyarsa da kuma rashin bai tsinana musu abin azo a gani ba.

Amma General Buhari ya rike mukamai kamar haka: Gwamnan jihar Arewa maso gabas (Borno), ya rike shugaban hukumar man fetur ta kasa (NNPC) kuma shine shugaban hukumar karo na farko, sannan ya zama shugaban kasar Nigeria na tsahon shekaru biyu, a karshe kuma ya rike shugaban hukumar PTF a lokacin mulkin General Sani Abacha.
To amma duk wadannan manyan manyan mukaman da General ya rike bai yi amfani da su ba wajen sace kudin talakawa, wannan yasa har yanzu talakawan Nigeria suke Addu'ar Allah (SWA) ya dawo musu da shi.

Buhari yayi takarar shugaban kasa har karo biyu a 2003 da 2007 duk a karkashin jam'iyar ANPP amma saboda rashin yin zaben adalci duk aka ce duk baiyi nasara ba, alhalin kuwa talakawa shi suka fita suka zaba. Duk da hakan General baiyi kasa a gwiwa ba, yanzu ma ya sake tsayawa takara a zaben 2011 amma a karkashin sabuwar jam'iyar da ya kirkira wadda bata fi shekara daya ba, tuni magoya baya suka cika ta makil wato CPC Change, mai dauke da alamar tuta da alkalami a jiki.

A karshe Allah ya karfafawa talakawa gwiwa sama da zabukan da suka wuce baya, su sake fita don kadawa Buhari kuri'a, ba don komai ba sai don shugaban hukumar zaben na yanzu da alama kamar zai kamanta adalci. fitar kuma ita ce hanya mafi sauki da za mu samarwa kanmu mafita a halin da muke ciki a kasar nan. Allah ya taimake mu a wannan zabe na gaba da shugaba adali a kasar mu Nigeria ameeeeeeeeen....!

Thursday, September 30, 2010

SHEKARU 50 DA SAMUN YANCIN KAN NIGERIA SHIN RIBA KO HASARA?

Daga 1th October 1960 zuwa gobe shekaru 50 kenan kuma shekarun da Nigeria suka yi da samun yancin kai daga wurin turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya (England) bayan samun yancin kai Nigeria sunyi shugabanni kala-kala wasu juyin mulki suka yi suka hau wasu kuma zabar su akayi. Su daga nan Arewa wasu kuma daga Kudu.

Shin to a tsawon wannan lokaci riba aka samu ko hasara akayi?

Tuesday, September 21, 2010

BELLO GARBA BELLO (BABA) YA MUSANTA LAIFIN KISAN MAHAIFANSA DA KANNINSA UKU

A sati biyu da suka wuce a cikin birnin Kano aka tashi da wani mummunan tashin hankali mai tsoratarwa da dimautarwa, na kisan gilar wani jami'in tsaron farin kaya wato (SSS) Mai suna Garba Bello da Matarsa da 'Yayansa guda uku Mata biyu Namiji guda daya.

A washe garin wannan rana jami'en tsaron 'yan sanda dana SSS suka gano cewa dansa na cikinsa ne ya kashe Iyayen nasa da sauran kannin nasa. Wanda ake kira Bello Garba Bello (Baba).

Baba ya amsa laifinsa a lokacin da Yan Jaridu ke yi masa tambayoyi. Amma kuma da ake gurfanar dashi a kotu gaban Shari'ah, sai kuma yayi turjiya yace bashi ya kashe Mahaifan nasa da Kannun nasa ba. Yana fada yana zubda hawaye.

A yanzu haka Kotu ta dage sauraren wannan kara zuwa Ranar 7 ga watan October.

Fatan mu dai shine Allah Ubangiji ya bayana mai gaskiya game da wannan sarkakakken al amari mai tada hankalin masu hankali.

A karshe Allah Ubangiji ya samu a tafarkin gaskiya Alfarmar Annabi Muhammad (S.A.W.)

Friday, August 27, 2010

MA'ANAR AZUMIN A SHARI'A

AZUMI Shine kamewa daga barin ci da sha, jima'i da kuma maganganun banza, tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin Ibada ga Allah (S.W.T). Saboda fadin Allah cewa "Ku ci ku sha har sai alfijir ya fito daga duhun dare, sannan sai ku cika azuminku zuwa faduwar rana" (Bakara 187).

Hadisin Abu Huraira (R.A) Yace Manzon Allah (S.A.W) Yace "Duk wanda bazai bar kirkire-kirkiren karya ko aikin ashsha ko jahilci (wauta) to lallai Allah baya bukatar ya bar ci da sha don yin azumi (Bukhari da Abu Dauda)

Idan muka yi duba da wannan ayar da hadisin zamu ga cewa lallai idan mutun yana son yayi azumi irin na Shari'a to lallai ne mutum ya bar abubuwan da aka zayyana. Sannan kuma ya kare idonsa da bakin daga abinda Ubangiji ya haramta.

Yana daga abinda yake wajibi akan mai azumi ya nisanta kansa daga kallon fina-finan turawa musamman na batsa. Domin kaucewa kishirwar banza da yunwa wacce ba lada a cikinta.

A karshe muna rokon Allah Ya karemu daga munanan halaye a wannan lokacin na Azumi. Ameen.

Monday, August 16, 2010

MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE

Daga Abdullahi Bin Umar (R.A) Cewa Manzon Allah (S.W.A) yace "Musulmi dan uwan Musulmi ne, kada ya zalunce shi, kada ya bari a cuce shi. Duk wanda ya taimakawa dan uwansa Musulmi wajen bukatartarsa Allah zai biya masa ta sa bukatar. Duk wanda ya yaye bakin cikin dan uwansa Musulmi, Allah za yaye masa bakin ciki daga bakin cikin ranar Alkiyama. Duk wanda ya rufawa dan uwansa Musulmi asiri, Allah zai rufa masa asiri ranar Alkiyama"

Bukhari ne ya rawaito shi.

Monday, August 9, 2010

RAMADAN KAREEM

RAMADAN na daya daga cikin jerin watannin Musulunci guda goma sha biyu. Kuma shine a jeri na tara.
Dukkan Musulmi wajibi ne a gare shi ya azumci wannan wata na RAMADAN Mai Alfarma.

AZUMI na daya daga cikin jerin Shikashikan Musulunci guda biyar. Bayan Shahada da Sallah. Sannan kuma daga shi sai Zakkah da Aikin Hajji ga duk wanda Allah Ubangiji ya nufa da zuwa.

Wannan wata na RAMADAN nada matukar muhimmanci wurin Allah, dan haka sai mu dage wurin neman gafarar Allah a wannan wata mai Alfarma.

Abubuwa da dama sun faru masu muhimmanci a cikin wannan wata, kadan daga ciki sun hada da:
Wahayin Alkur'ani Mai Girma.
Yakin Badar a shekara ta biyu baya hijira.

Allah Madaukakin Sarki na cewa a cikin Alkur'ani Mai Girma " Alkur'ani an saukar da shine a watan Ramadan, sannan kuma Ramadan shiriya ne ga mutane da bayani na shiriya wanda yake banbance tsakanin shiriya da bata. Wanda ya ga wata ko ya ji bayanin ganinsa to ya dau Azumi.
(Baqrat 180).

Allah bamu ikon bauta masa cikin wannan Wata Mai Alfarma kuma ya Gafarta mana dukkan zunubanmu. Ameen.

Wednesday, June 9, 2010

ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWA TA

Alhamdulillah:
Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki mai kowa mai komai, Ubangijin sammai da kassai da dukkan abinda ke cikinsu.

Tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halitta wanda aka yi duniya, lahira, Aljanna da wuta dominsa, cikamakin Annabawa, Annabi Muhammad (S.A.W.) da Alayensa da Sahabbansa da kuma dukkan wanda suka gastata shi baki daya. Ameeen.

Ranar Litinin 10th June 1991 daidai da 27 Dhul Qidah 1411 wato shekaru 19 kenan yau, ranar ne aka haife ni. Lalle na girma sai Aure!

Godiya Ta musamman kuma mai tarun yawa ga Iyaye na da kuma Kakanni na da suka dauki nauyi na da Allah ya dora musu, kuma suka tarbiyantar dani bisa tarbiyar Addinin Musulunci. Tun ina dan karami suka sani a makarantar Al Qur'ani mai girma, kuma sukai ta dawainiya dani har Allah ya bani haddar Al Qur'ani mai girma (Alhamdulillah) kuma duk da haka suka sakani a makarantar boko a halin yanzu.

Tabbas don haka bani da wata kalma da zan iya furtawa don nuna godiya ta a garesu, game da wannan abinda suka yi min sai dai kawai nace Allah (S.W.T.) ya saka musu da mafificin abinda suka yimin, ameen summa ameen.

Kamar yadda lissafi ya nuna yau Alhamis 10th June 2010 / 26 Jumada Thani 1431. Ina da shekaru 19, watanni 228, makonni 991, ranaku 6,939, sa'o'i 166,551, mintuna 9,993,103 da kuma dakika 599,586,227.

A KARSHE: Ina godiya ga sauran yan uwana da abokai na, maza da mata game da irin shawara da suke bani idan sunga zanyi ko kuma nayi wani abu ba daidai ba. Allah ya saka muku da alkhairi. Ameen.

Friday, May 28, 2010

RIBA KO HASARA

29th May 1999 daga wannan rana zuwa yau shekaru goma sha daya kenan kuma adadin shekarun da kasar Nigeria ta canja tsarin mulkin kasar zuwa tsari democradiya, irin tsarin da kasar America ke amfani dashi.

Cikin wannan shekaru Nigeria tayi shugabanni guda uku biyu daga kudu, daya daga arewa. Biyu daga ciki zaben su muka yi daya kuma ya samu mulkin ne a matsayin na mataimaki bayan shugaban daya ke kai Allah yayi mai rasuwa.

Nigeria kasa ce wadda Allah ya albarkan ce ta da arzukin noma, ma'adanan kasa da kuma man futar, wannan dalili yasa ake ganin duk nahiyar Africa ba wata kasa da takaita arzuki. Ga kuma yawan jama'a da Allah ya hore mata sama da mutum miliyan dari da talatin, 130,000000.

Amma kash duk da irin wannan abubuwa da Allah ya hore mana bamu samu shugabanni nagari ba. Sai dai muna adu'ar Allah ya albarkan ce mu da shugabanni nagari.

Tambaya anan wai shin a wannan tsarin da kasar mu ta zaba na democradiya ta koma. Shin Riba aka ci ko Hasara aka yi.

A karshe ina taya dukkan daukakin al'ummar kasar Nigeria da kuma dukkan masoyanta kasar Murnar zagayowar wannan rana ta demokradiya wato Democracy Day

Thursday, May 13, 2010

BRAZIL BATA GAYYACI MANYAN YAN WASA BA


Brazil ta sanar da sunayen yan wasa 23 wadanda zasu buga mata wasa a gasar cin kofin duniya da za'a buga a kasar South Africa a wata mai zuwa. Abin mamaki shine Brazil bata gayyaci shahararrun yan wasanta ba, kamar su: Ronaldo, Roberto Carlos, Ronaldinho, Adriano, Alexandre Pato da kuma Neymar. Yan wasan da ake gani idan Brazil bata gayyace su ba. Ba abin azo a gani zatayi a gasar ba.

Brazil itace kasar da ta halacci dukkan gasar tunda aka fara, kuma itace wadda tafi kowace samun nasarar daukar kofin har sau biyar.

Brazil na rukunin H ne tare da kasashen Portugal, Ivory Coast da kuma South Korea.

Cikakken jerin yan wasa da aka gayyata:

MASU TSARON GIDA
Julio Cesar (Inter Milan ITA)
Doni (AS Roma ITA)
Gomes (Tottenham Hotspur ENG)

MASU BUGA BAYA
Maicon (Inter Milan ITA)
Daniel Alves (Barcelona ESP)
Michel Bastos (Lyon FRA)
Gilberto (Cruzeiro BRA)
Lucio (Inter Milan ITA)
Juan (AS Roma ITA)
Lusaio (Benfica POR)
Thiago Silva (AC Milan ITA)

MASU BUGA TSAKIYA
Gilberto Silva (Panathinaikos GRE)
Felipe Melo (Juventus ITA)
Ramires (Benfica POR)
Elano (Galatasaray TUR)
Kaka (Real Madrid ESP)
Julio Baptista (AS Roma ITA)
Kleberson (Flamengo BRA)
Josué (VfL Wolfsburg GER)

MASU BUGA GABA
Robinho (Santos BRA)
Luis Fabiano (Sevilla ESP)
Nilmar (Villar Real ESP)
Grafile (VfL Wolfsburg GER)

Sunday, May 9, 2010

GASAR FIFA WORLD CUP 2010


Gasar World Cup 2010 karo na 19th kuma za'a yi shine tsakanin 11 June da 11 July 2010 a kasar South Africa, kuma wannan gasa itace karon farko da za'a yi a nahiyar Africa. Bayan da hukumar FIFA ta maida tsarin gasar nahiya-nahiya.

South Africa ta samu nasarar daukar nauyin gasar ne bayan ta doke abokan takarar ta Morocco, Egypt, Libya da Sudan.

KASASHEN DA ZASU BUGA GASAR

Kasashe 32 ne zasu ta ka leda a wannan gasa daga bangare 6 na duniya, kasashen sune:-

AFC (4)
Australia
Japan
Korea DPR
Korea Republic

CAF (6)
Algeria
Cameroon
Cote d'Ivoire
Ghana
Nigeria
South Africa

CONCACAF (3)
Honduras
Mexico
United States

CONMEBOL (5)
Argentina
Brazil
Chile
Paraguay
Uruguay

OFC (1)
New Zealand

UEFA (13)
Denmark
England
France
Germany
Greece
Italy
Holland
Portugal
Slovenia
Slovakia
Spain
Switzerland

FILAYEN WASA

Za'a yi wannan gasa ne a filayen wasanni guda 12 kuma biyar da cikin su sabbi ne an gina sune domin wannan gasa ta FIFA World Cup 2010, filayen sune:-
Johannesburg (A) 94,700
Durban 70,000
Cape Town 69,070
Johannesburg (B) 62,567
Pretoria 51,760
Nelson Mandela 48,000
Bloemfontein 48,000
Polokwane 46,000
Rustenburg 44,530
Nelspruit 43,589

Kowacce kasa zata zo da yan wasa guda 23 kamar yadda akayi a gasar 2006 a kasar Germany. Kuma dole kowacce kasa ta sanar da sunayen yan wasanta ga hukumar FIFA kafin ranar 1 June 2010.

Thursday, April 29, 2010

KANO STATE LOCAL GOVERNMENT AND THEIR CODES


Kano State Is The Highest Population And Its Has Most Local Government In Nigeria.
The Name Of Kano State Local Government is:

(1) Ajingi AJG
(2) Albasu ABS
(3) Bagwai BGW
(4) Bebeji BBJ
(5) Bichi BCH
(6) Bunkure BNK
(7) Dala DAL
(8) Dambatta DBT
(9) Dawakin Kudu DKD
(10) Dawakin Tofa DTF
(11) Doguwa DGW
(12) Fagge FGE
(13) Gabasawa GSW
(14) Garko GAK
(15) Garun Mallam GRL
(16) Gaya GYA
(17) Gezawa GZW
(18) Gwale GWL
(19) Gwarzo GRZ
(20) Kabo KBK
(21) Kano Munincipal KMC
(22) Karaye KRY
(23) Kiru KKU
(24) Kibiya KBY
(25) Kumbotso KBT
(26) Kunci KNC
(27) Kura KUR
(28) Madobi MBD
(29) Makoda MKD
(30) Minjibir MJB
(31) Nassarawa NSR
(32) Rano RAN
(33) Rimin Gado RMG
(34) Rogo ROG
(35) Shanono SNN
(36) Sumaila SML
(37) Takai TAK
(38) Tarauni TRN
(39) Tofa TFA
(40) Tsanyawa TYW
(41) Tudun Wada TWD
(42) Ungogo UGG
(43) Warawa WRA
(44) Wudil WDL

Thursday, April 22, 2010

SAHABBAI GOMA YAN ALJANNA TUN SUNA DUNIYA


Manzon Allah (S.A.W.) yana da Sahabbai 120,4000. Duk da cewa dukkan wadannan Sahabbai 'yan Aljanna ne to amma akwai wadanda akayi musu bishara da Aljanna tun suna da rai.
Akwai guda goma wannan Manzon Allah (S.A.W.) ya fada a hadisi cewa an yi musu bishara da gidan Aljanna, wato ASHARATUL MUBASHSHIRUN. Wannan Sahabbai sune:-
(1) Abubakar Saddik (R.T.A)
(2) Umar Bin Khaddab (R.T.A)
(3) Usman Bin Affan (R.T.A)
(4) Aliyu Bin Abi Dalib (R.T.A)
(5) Dhalha Ibn Ubaidullah (R.T.A)
(6) Zubair Ibnul Awwam (R.T.A)
(7) Abdurrahman Bin Auf (R.T.A)
(8) Sa'ad Bin Wakkas (R.T.A)
(9) Sa'id Bin Zaid Bin Amr (R.T.A)
(10) Abu Ubaidah Bin Jarrah (R.T.A)

Allah Madaukin Sarki ya bamu albarkacin wadandan bayi nasa.

KALANDAR HIJRAR MUSULUNCI


Abin mamaki a wannan zamanin sai kaga an tambayi mutum yau nawa ga wata sai kawai kaji yace "yau 21 April 2010" da ka ce masa a'a na Musulunci kake nufi sai kaji yace "ban sani ba" wannan gaskiya abin kunya ne ga dukkan Musulmin da za'a tambaye shi kwanan watan turawa ya fadi amma ya kasa fadin na Hijrar Musulunci.

TARIHIN HIJRAR MUSULUNCI

Asalin faruwar Kalandar Hijrar Musulunci, abu ne mai fadi da dogon tarihi, amma dai ta samu asalinta ne lokacin Khalifancin Sayyadina Umar Bin Khaddab (A.S.) a sakamakon wani abu mai muhimmanci daya faru a cikin watan Sha'aban wanda Sahabbai suka yi kokarin tantance wane Sha'aban ne amma abin ya faskara. Wannan dalili ne yasa Sayyadina Umar (A.S.) ya tara Sahabbai inda ya nemi shawarar yadda za'a rika tantance tarihin faruwar al'amura a Musulunci.

Don haka shawara ta tsaya akan fara lissafin kalandar Musulunci daga lokacin da Manzon Allah (S.A.W.) yayi hijra daga Makkah zuwa Madinah, kuma aka sanya watan Muharram ya zama shine watan farko a cikin jerin watannin kalandar Musulunci (Hijrah).

WATANNIN HIJRAR MUSULUNCI

Shekarar Musulunci (Hijrah) tana da watanni goma sha biyu 12 wadannan watanni sune:-
(1) Muharram
(2) Safar
(3) Rabi'ul Awwal
(4) Rabi'ul Thani
(5) Jumada Ula
(6) Jumada Thani
(7) Rajab
(8) Sha'aban
(9) Ramadan
(10) Shawwal
(11) Zhul Qi'idah
(12) Zhul Hajj

WATANNI HUDU MASU ALFARMA

A cikin watanni Hijrar Musulunci guda 12 Allah Madaukakin Sarki ya kebance guda hudu masu Alfarma, sune:-
Muharram wata na (1)
Rajab wata na (7)
Zhul Qi'idah wata na (11)
Zhul Hajj wata na (12)

A KARSHE
Shawara ga dukkan Musulmi ya dage ya ke sa kwanan watan Hijrar Musulunci a dukkan harkokimu na yau da kullum.
Allah ya daukaka Addinin Musulunci da Musulmai, Ya kare mu daga sharrin makiya Manzon Allah (S.A.W) ameen.

Thursday, April 8, 2010

(EL CLĂ€SICO) REAL MADRID VS BARCELONA


El Clásico lakabi ne da ake yiwa wani shahararren wasa a bangaren kwallon kafa, wannan wasa shine wasan da yafi kowanne wasa daukar hankalin masu sha'awar kwallon kafa a duniya.

Wannan wasa shine tsakanin shahararriyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid CF data fito daga Madrid babban birnin kasar Spain. Da kuma babbar kungiyar FC Barcelona data fito daga Barcelona babban birnin Catalonia dake kasar Spain.

Wadannan kungiyoyi guda biyu sune suka fi kowace kungiya samun nasarori a bangaren kwallon kafa a kasar Spain baki daya.

El Clasico shine wasa mafi daukar hakalin mutane a duniya, domin mutane sama da 100 milliyan suna ganin shi daga kasashen daban-daban a fadin duniya, ciki har da kasarmu Nigeria.

El Clásico ya samo asalin sunansa ne a lokacin da Real Madrid ta samu gagarumar nasara akan Barcelona a wasan kusa da karshe na gasar Spanish Cup.
(11-1) a shekarar 1943.

Real Madrid da Barcelona sune suka fi kowace kungiya magoya baya a kasar Spain.
Real Madrid tana da kaso 32.8%. Sannan Barcelona na da kaso 25.7%. Sai ta ukun su Valencia da kaso 5.3%. Game da kidayar da akayi a shekakar 2007.

Tsakanin Real Madrid da Barcelona an hadu sau 160 a gasar La-liga.

Real Madrid ta samu nasara sau 68. Sannan Barcelona ta samu nasara sau 62. Sunyi kunnen doki sau 30 a tsakaninsu.

Real Madrid ta samu nasara sau 50 a gida, sau 18 a waje. Kunnen doki sau 14 a gida sau 16 a waje. Rashin nasara sau 15 a gida, sau 46 a waje.

Barcelona ta samu nasara sau 47 a gida, sau 15 a waje. Kunnen doki sau 16 a gida, sau 14 a waje. Rashin nasara 18 a gida sau 50 a waje.

Yan wasan da suka fi cin kwallaye a El Clásico sune:

REAL MADRID CF
Alfredo di Stefano (14).
RaĂąl (11).
S. Bernabeu (11)
Lazcano (8).
Regueiro (6).
Van Nistelrooy (4).
Alday (4).
Zamarano (3).
Ronaldo (3).
Higuain (2).
S. Ramos (2).

FC BARCELONA
F. Gento (10).
Luis Enrique (6).
Lionel Messi (6).
Rivaldo (5).
Ronaldinho (5).
Escola (5).
Ventolra (4).
Samuel Eto'o (4).
Henry (3).
Kluivert (2).

El Clásico wasan daya wuce a Santiago Bernabeu. Real Madrid 0 - 2 Barcelona, Ranar 10 April 2010.

El Clásico wasan da za'ayi nan gaba a Camp Nou. Barcelona - Real Madrid. Ranar 29 November 2010.

Tuesday, April 6, 2010

ALHAJI (DR) MUHAMMAD ABUBAKAR RIMI


Inna lillahi wa inna illahi raji'un.

A dare ranar Lahadi 4 April 2010 ne, Allah (S.W.A.) yayi wa Alhaji (Dr.) Muhammad Abubakar Rimi tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano (Kano da Jigawa) rasuwa.

Akan hanyar sa daga jihar Bauchi zuwa Jihar Kano, bayan ya dawo daga bikin nadin sarautar gargajiya ya hadu da yan fashi a tsakanin garin Garko da Wudil. Duk da yan fashin basu taba shi ba amma za'a iya cewa sune sanadiyar mutuwar sa.

Bayan yan fashin sun karbe musu kudin su da wayoyin su, sannan suka taho kafin suzo Wudil Muhammad Abubakar Rimi ya gamu da bugun zuciya, nan take aka kai shi asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Wajen karfe 11:40 na dare Allah ya karbi ransa.

Washe garin ranar da ya rasu akayi jana'izar sa, a fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
Jana'izar Muhammad Abubakar Rimi ta samu halartar mutane sama da mutum miliyan daya daga sassa daban-daban na kasar Nigeria baki daya.

TAKAITACCEN TARIHIN ALHAJI MUHAMMAD ABUBAKAR RIMI

An haifi Muhammad Abubakar Rimi a kauyen Rimi na karamar hukumar Sumaila, jihar Kano, Nigeria. A shekarar 1940.
Alhaji Abubakar Rimi na daya daga cikin manya-manyan fiatattun kuma jiga-jigan yan siyasar nahiyar Afrika. Yayi karatun sa na Kos a Zaria, kuma ya samu takardar shedar zuwa jami'ar London, kasar England a 1972. Ya hada diflomar sa a kasar kuma ya samu shedar babban digri.

Rimi yana daga cikin mutanen da suka kirkiri jam'iyyar PRP a shekarar 1978 kuma an zabe shi a matsayin mataimakin jam'iyyar na kasa a taron ta na farko a jihar Lagos.

Abubakar Rimi an zabe shi a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Kano a October 1979 har zuwa May 1983 kuma shine gwamnan farar hula na farko a jihar. A farko 1983 Rimi ya fita daga jam'iyyar PRP ya koma Nigerian People's Party (NPP).

A lokacin mulki Rimi yayi wa jama'ar jihar Kano da Jigawa aikin da wani gwamna bai taba yi ba.
Muhammad Abubakar Rimi shi ya gina gidan jaridar jihar Kano Triumph, ya gina gidan television na CTV Kano, ya gina Kasco da kuma Knarda.

Rimi a lokacin mulkin sa ne ya kirkiro sabbin masarautu na sarakunan yanka. Kamarsu: Kano, Gaya, Rano, Karaye, Auyo da Ringim.

A 1993 Rimi ya zama ministan yada labarai sannan ya zama shugaban NACB da NSPMC. yana cikin mutanen da suka samar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Rimi ya fita daga Jam'iyyar PDP a 2006 ya koma jam'iyyar Action Congress (AC) amma a 2007 Rimi ya sake komawa PDP.

A january 2006 wasu yan ta'adda suka shiga gidansa suka kashe masa matar sa Sa'adat Abubakar Rimi.

Ranar 4 April 2010 ya rasu a asibitin Mallam Aminu Kano. An bunne shi ranar 5 April 2010 kamar yadda Addinin Musulunci ya ta nada.

A karshe Allah ya jikansa, Allah ya kai rahma kabarin sa, Ya saka masa da gidan Aljanna firdausi. Ya baiwa iyalansa hakurin jurewa.

Wednesday, March 31, 2010

BAYAN SAMUN YANCIN KAN NIGERIA


Kadan daga cikin Muhimman abubuwan da suka faru bayan samun yancin kan kasarmu Nigeria.

Ranar 6 July 1967, aka fara yakin basasar Biafra har zuwa ranar 12 January 1970.

Ranar 1 October 1960, Nigeria ta samu yancin kai daga wurin turawan kasar Burtaniya.

Ranar 29 May 1967, Nigeria ta canja kudin kasar zuwa Naira da Kobo.

Ranar 22 May 1973, aka maida tsarin yan bautar kasa wato NYSC kasa da shekaru (24) ashirin da hudu.

Ranar 28 May 1975, aka gina ofishin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS a jihar Lagos.

Ranar 14 February 1976, General Murtala Ramat Muhammad ya dawo da birnin tarayyar Nigeria daga Lagos zuwa Abuja.

Ranar 15 February zuwa 12 March 1977, akayi biki nuna al'adun Afrika karo na biyu a jihar Lagos.

Ranar 13 February 1982, Pope John Paul, ya ziyarci kasar Nigeria a karo na biyu.

Ranar 16 October 1986, Professor Wole Soyinka, ya zama dan kasar Nigeria kuma dan Afrika na farko daya samu nasarar cin gasar Alfred Nobel Prize a Stock Holm dake kasar Sweden.

Ranar 18 February 1988, aka kirkiri Federal Road Safety Commission. Kuma Prof. Wole Soyinka ya zama shugaba na farko.

Ranar 4 April 1988, aka canja kayan yan sadan Nigeria zuwa kalar Baki.

Ranar 11 July 1991, sama da yan Nigeria mutum 250 ne suka rasu a sakamakon hadarin jirgin sama a Jiddah, kasar Saudi Arabia.

Ranar 27 August 1991, shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, ya sanar da karin jihohi da kuma kananan hukumomi guda 47.

Ranar 27 zuwa 29 November 1991, akayi kidayar mutanen kasar Nigeria.

Ranar 2 August 1996, Nigeria ta zama kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta fara lashe gasar Olympic wanda akayi a Atlanta, kasar America.

Ranar 8 August 1998, Allah (SWA) yayi wa General Sani Abacha, rasuwa a Aso Rock, yana da shekaru 54 an binne shi a jiharsa ta haihuwa Kano, a ranar daya rasu kamar yadda tsarin Addinin Musulunci ya tana da.

Ranar 29 May 1999, mulkin kasar Nigeria ya koma hannun farar hula.

Wednesday, March 24, 2010

KASAR NIGERIA

Kasar Nigeria kasa ce dake yammacin nahiyar Africa, Nigeria ta samo sunanta ne da daga Kogin Niger (Niger Area), a shekarar 1898, kasar Nigeria tafi kowace kasa dake nahiyar Africa yawan mutane tana da mutane sama da 130 million. Sannan Allah ya arbarkaci Nigeria da arziki kala kala, masu tarun yawa. Nigeria na da kabilu da yawa wadda tana cikin kasashen da suka yawan kabilu a duniya.
Nigeria na da kabilu sama da 250, manya daga cikinsu sune: Hausa, Fulani, Yoruba, Igbo, Kanuri, Nupe da Ijew.
Addinin Musulunci shine yafi kowane addini rinjaye a kasar, sannan Addinin Christians. Da kuma sauran addinai kala kala.
Kasar Nigeria na da jihohi guda 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, sannan da kananan hukumomi guda 773.
A shekarar 1914 turawan Britain suka hada arewancin Nigeria da kudanci ya zama kasa daya, sannan kuma suka mamaye kasar a matsayin mulkin mallaka. Lokacin da Nigeria ke karkashin mulkin Britain, turawa ne ke mulkin kasar har zuwa ranar 1 October 1960 lokacin da Nigeria ta samu yancin kanta daga turawan mulkin mallakar kasar England.

Bayan samun yancin kai ne Dr. Nmandi Azikiwe ya zama dan kasa na farko wanda ya shugabanci Nigeria. Sannan Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama Prime Minister.
Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), kuma ya zama Prime Minister Jihar Arewa. Wadannan shugabanni sunyi aiki tukuru wajen ganin kasa ta cigaba, amma a 1966 akayi musu juyin mulki kuma a wannan juyin mulki ne aka kashe Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto).

General Aguiyi Ironsi ya hau mulkin kasar bayan wannan juyin mulki a January 1966 amma shima bai dade ba akayi Juyin Mulki. General Yakubu Gowon ya karbi mulki a July 1966.
A 1975 sojoji suka sake yin juyin mulki General Murtala Ramat Muhammad ya hau mulkin kasa. Amma shi wata takwas yayi yana mulki a kayi juyin mulki kuma aka kashe shi.
Sannan General Olusegun Obasanjo ya karbi mulki yayi shekaru uku sannan ya mika mulki a hannun farar hula. Inda Alhaji Shehu Shagari yayi nasarar hawa mulki a 1979 a matsayin zababbe.
Mulki bai dade a hannun farar hula ba sojoji suka sake yin juyin mulki, General Muhammad Buhari ya hau kujerar mulki, a 1983 shima bai dade ba aka sake yin juyin mulki amma ba'a zubar da jini ba.
Sakamakon wannan juyin mulki General Ibrahim Badamasi Babangida ya dare kujerar mulki
a 1985 har zuwa 1993 sannan shima akayi masa juyin mulki. Chief Ernest Shonekan ya hau mulki na yan watanni sannan General Sani Abacha ya karbi mulki a 1993.
Ranar 8 Auguest 1998 Allah yayiwa Gen. Sani Abacha rasuwa. Kuma shine shugaban Nigeria na farko da ya mutu yana kan mulki.

Bayan rasuwar General Sani Abacha. General Abdussalam Abubakar ya hau mulki na rukon kwarya. Tun daga wannan lokaci mulki ya dawo hannu farar hula har zuwa yau. Ranar 29 may 1999 General Olusegun Obasanjo ya hau mulkin Nigeria a matsayin damukradiya (Democratic) Chief Obasanjo yayi mulki har na tsawon shekara takwas bayan sake lashe zabe da yayi a 2003.
Ranar 29 may 2007 Alhaji Umaru Musa Yar'adua yayi nasarar hawa mulkin kasar Nigeria kuma har zuwa yau shi ke mulkin kasar. Sannan zabe gaba za'ayi shi a 2011.

Kamar sauran kasashe Nigeria na da alamomin kasa (National Symbols) masu yawa wanda suke da muhimmanci a wurin kowane dan asalin kasar Nigeria.

TUTAR KASA (National Flag) Taiwo Akinkami dan kasar Nigeria shine ya tsarata a 1959 amma a lokacin ba'a amfani da ita. Tun 1914 Nigeria ke amfani da tutar British Union har zuwa tsakiyar daren ranar 30 September 1960 washe garin samun yancin kai, sannan Nigeria ta fara amfani da ita.
Tutar Nigeria na da kala biyu da aka raba gida uku (Kore, Fari, Kore). Koriyar kala na nuni da kyakkyawar kasar noma. Sannan Fara kana na nuni da zaman lafiya da hadin kan kasar.

TAMBARIN KASA (Coat and Arm). An samar da tambarin a 1960. Tambarin na dauke da bangarori kamar haka:
MIKIYA wadda ke nuni akan karfin Nigeria.
DAWAKAI guda biyu na nuni akan martabar Nigeria.
Y na nuni akan manyan ruwan kasar guda biyu. Kogin Niger da Kogin Benue.
FILAWA na nuni akan arzikin noma da kasar ke dashi. Sannan a karshe an rubuta "HADIN KAI DA IMANI, ZAMAN LAFIYA DA CIGABA" wanda ke nuni akan shine manufar Nigeria.

TAKEN KASA (National Anthem). Taken Nigeria na nuni akan bukatar kowane dan kasa yayi biyayya tare da yin aiki tukuru domin samu zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.

RANTSUWA (National Pledge). Wani alkawari ne da rantsuwa da dan kasa ke dauka domin yiwa kasa aiki bisa aminci.

A karshe wannan shine kadan daga cikin abubuwan da suka shafi kasarmu Nigeria musamman yadda akayi mulki tunda daga samun yancin kai. A ranar 1 ga October 1960, ranar da duk dan Nigeria ke alfahari da ita.
Allah (SWA) ya kara daukaka kasar Nigeria ya bamu shugabanni nagari.

Thursday, March 18, 2010

TAKAITACCEN TARIHIN REAL MADRID

Real Madrid Club de Futbol ko Los Blancos. (The White) Kwararriyar kungiyar kwallon kafa ce dake birnin Madrid na kasar Spain.
Itace kungiyar da FIFA ta zaba a matsayin kungiyar da tafi samun nasara a karni na 20, domin ta lashe kofin rukuni-rukuni na kasar Spain (La-liga) sau 31, Spanish Cup sau 17 da kofin zakarun nahiyar turai sau 9 da kuma kofin UEFA sau biyu.
An kafa kungiyar Real Madrid a shekarar 1902 (6 March 1902). A shekarar 1900 aka kafa kungiyar Club Espanol de Madrid. A 1902 kungiyar ta rabu biyu hakan ya kawo kafuwar Madrid Fooball Club.
A shekarar 1905 Madrid FC ta fara yin nasarar daukar kofi, bayan ta doke Athletic Bilbao a kofin Spanish Cup.
Madrid FC na daya daga cikin wakilan hukumar FIFA na farko kuma wakiliyar rushasshiyar kungiyar G-14 na manyan kungiyoyin da ake ji dasu a nahiyar turai.
A 1920 ne aka canja sunan kungiyar zuwa Real Madrid bayan da sarki Alfonso ya amince a yi amfani da lakabi Real da ake nufin Royal ga kungiyar.
A shekarar 1929 ne aka fara gasar La-liga inda Real Madrid ta jagoranci gasar har zuwa wasan karshe inda tayi rashin sa'a a hannun Athletic Bilbao. Ta zama ta biyu bayan Barcelona. Real Madrid ta fara lashe gasar La-liga ne a 1931/1932, sannan shekarar gaba ma ta sake lashewa.
A 1940 Santiago Bernabeu Yeste ya zama shugaban kungiyar, kuma a mulkinsa ne Real Madrid ta sake gina filayen wasanninta na Santiago Bernabeu da Ciudad Deportiva, bayan yakin basasar kasar Spain.
Santiago Bernabeu a shekarar 1953 ne ya fara dakko kwararrun yan wasa daga kasashen waje. Fitacce daga cikinsu shine Alfredo di Stefano, wannan ya bashi damar kafa tarihin kungiyar da ta fara tattara yan wasa daga sassan duniya a tarihin kwallon kafa. A karkashin Bernabeu ne Real Madrid ta zama gagabadau a fagen kwallon kafa a kasashen turai.
Real Madrid ta lashe kofin kasashen turai (Uefa Champions League) sau biyar a lokaci daga a tsakanin 1956 zuwa 1961 wanda ya hada da ci 7-3 da tayiwa kungiyar Eintracht Frankfurt a filin wasa na Hampden Park a wasan karshe a 1960. Cin kofin sau biyar a jere yasa kungiyar ta samu mallakin kofin na ainihi tare da bata damar sanya tambarin girmamawa na UEFA.
Real Madrid ta lashe Uefa Champion League karo na shida a 1966 bayan ta doke FK Partizan da ci 2-1 a wasan karshe.
Ranar 2 July 1978 shugaban Real Madrid Santiago Bernabeu ya rasu. A shekarar 1996 shugaban Real Madrid na lokacin Lorenzo Sanz ya kulla yarjejeniyar daukar Fabio Capello a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar na tsayon shekara daya.
A 1998 Real Madrid ta sake yin nasarar daukar kofin Uefa Champions League karo na bakwai bayan ta samu nasara akan Juventus da ci 1-0 a wasan karshe.
A watan bakwai na shekarar 2000 aka zabi Florentino Perez a matsayin shugaban kungiyar, a mulkinsa ya samu nasarar kawo shahararrun yan wasa kungiyar, wanda suka hada da Zinedine Zidane, Ronaldo, Luis Figo, Roberto Carlos, Raul da David Beckham. A shekarar ne kungiyar ta sake cin kofin Uefa Champions League karo na takwas. Sannan kuma ta samu nasarar daukar na tara a shekarar 2002 da kuma kofin La-liga a 2003 duk a lokacin mulkin Perez.
Ramon Calderon ya zama shugaban Real Madrid ranar 02 July 2006 da zuwansa ya sake dakko Fabio Capello a karo na biyu a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar, da kuma tsohon dan wasan kungiyar Predrag Mijatovic a matsayin manajan kungiyar.
Real Madrid tayi nasarar cin kofin La-liga karo na 30 a shekarar 2007. Sannan ta sake cinye kofin a 2008. Ranar 01 June 2009 Florentino Perez aka sake zabarsa shugaban kungiyar karo na biyu. Da zuwansa ya sayo shahararren dan wasan AC Milan da Kasar Brazil wato Ricardo Kaka akan kudi £60m. Sannan kuma sai dan wasan duniya na lokacin Cristiano Ronaldo daga kungiyar Manchester United ta kasar England, akan kudi £80m. Wannan sayayyar itace tafi kowacce tsada a tarihin kwallon kafa bayan dan wasar kasar France Zinedine Zidane.
Duk da Real Madrid tafi kusa da kungiyar Athletic Madrid. Amma babbar abokiyar adawarta itace kungiyar Barcelona.
Real Madrid itace kungiyar kwallon kafa da tafi kowacce kungiya samun nasarar daukar kofuna. Ga jerin wasu kofuna da kungiyar ta dauka:
9 Uefa Champions League.
31 Spanish La-liga.
19 Spanish Cup.
18 Regional Cup.
3 Intercontenatal Cup.
8 Spanish Super Cup.
5 Community Cup.
2 Uefa Cup.
2 Spanish League Cup.
2 Latin Cup.
2 Little Cup.
1 European Super Cup.

Tuesday, March 16, 2010

LABARIN MALAM BUBA

Assalamu Alaikum. Malam Buba mutum ne mai son abin dariya a koda yaushe, yana zaune a kauye shida iyalansa kuma yana da garken dabbobi masu yawa.
Wata rana Malam Buba yana son cin dariya, sai ya fara tunanin yadda zaiyi don cin dariya, can sai dabara tazo masa, kawai sai ya shiga cikin kauyen da yake zaune a guje yana ihu-ihu a taimake ni Zaki ya shigo cikin garken dabbobi na zai cinye su. Yayi wannan dabarar ne kawai don yaga ya mutanen garin nan zasuyi wane irin mataki zasu dauka. Mutanen garin kuwa da jin ihun Malam Buba sai kowa ya fara fitowa daga cikin gidansa, kowa dauke da makamai wasu ko riga babu a jikinsu, suka nufi gidan Malam Buba don taimakonsa. Da zuwansu sai suka tarar da Malam Buba yana ta dariya har da faduwa kasa, kuma ga dabbobinsa na cin abinci cikin kwanciyar hankali. Wannan abin ya batawa mutanen kauyen rai, sukace da Malam Buba ina Zakin da ya shigo zai cinye ma dabbobin, sai kawai yace dasu "nayi haka ne kawai don naci dariya" mutanen kauyen kowa ya koma gidansa cin fushi da jin haushi.
Wata uku da yin wannan abu sai ga Zaki ya baiyana a gaskiyan ce a garken Malam Buba ya fara gaggatsa dabbobin Malam Buba suna mutuwa, nan take Malam Buba ya shiga cikin kauyen yana ihu yana kiran azo a taimake shi. Sabida yaudarar da Malam Buba yayiwa mutaten kauyen a baya yasa ba wanda ya fito don taimakonsa. A karshe Zakin ya kashe duk dabbobin Malam Buba.
Malam Buba ya zama talaka, sannan ya koyi babban darasi.

A karshe wannan labari yana nuna mana muhimmanci fadar gaskiya a kowanne hali. Domin da Malam Buba bai yaudari mutanen kauyensa ba da baiyi hasarar dabbobinsa ya koma talaka ba.

Monday, March 15, 2010

HAUSA A WANNAN ZAMANI

Assalamu Alaikum. Ya kamata kafin na fara gabatar da kasidu a wannan dandali na danyi bayani game da cigaban kabilar Hausawa a wannan zamani musamman kan cigaban na'ura mai kwakwalwa. Hausa dai kamar yadda aka sani yare ne kamar ko wanne yara a duniya. Akwai miliyoyin mutate masu amfani da harshen Hausa a Afrika dama duniya baki daya, dukkan wani Bahaushe Allah ya bashi basira sosai. A wannan zamani da cigaban fasahar sadarwa yake da matukar muhimmanci a duniya to ba'a bar Hausawa a baya ba. Domin a halin yanzu Hausawa suma suna kokarin ganin sun zama kwararru akan wannan fanni, duk da cewa Hausa basu da isassun kayan harkar fasahar sadarwa, domin ba kowane yake da damar sayen na'ura mai kwakwalwa ba amma duk da haka zakaga yana son abin a zuciyarsa. Wani zakaga kullum sai yaje yayi sana'a sannan zai samu kudin da zai je Internet Cafe don yin browsing, wani kuma zakaga yana amfani da wayarsa ta hannu don yin browsing da aikawa da sakonni. Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadiq), mai MAKARANTAR KIMIYA DA FASAHAR SADARWA. ya taimaka sosai wajen tunatar da Hausawa game da cigaban fasahar sadarwa. Domin duk sati yana gabatar da kasida a shafi guda na jaridar Aminiya, game da yadda za'ayi amfani da na'ura mai kwakwalwa, wannan aiki nasa yasa Hausawa sun tashi tsaye wajen neman ilmi game da fasahar sadarwa. Sai kuma gidan rediyon BBC Hausa suma sun bada gudunmawa sosai akan wannan harkar, domin sun bada dama ga masu saurarensu suke yin mahawara a shafinsu na BBC Hausa Facebook, wannan yasa Hausawa sun tashi a tsaye. A karshe kira ga Hausawa shine kara dagewa wajen koyan ilmin sarrafa na'ura mai kwakwalwa, wannan zai rage mana wannan halin rayuwa da muke ciki. Allah ya kara daukaka kabilar Hausa a fadin duniya.

Saturday, March 13, 2010

BARKA DA ZUWA

Assalamu Alaikum. Ina yiwa dukkan wanda ya ziyarci wannan dandali fatan alkhairi. Wannan dandali na gina shine akan kawo jawabai game da abubuwan da suke faruwa a kasarmu Nigeria dama duniya baki daya musamman ma kan harkukin siyasar duniya da ta Afrika. Ina fatan idan mutum ya ga gyara akan wani abu zai sanar dani kuma ina farin ciki da wanda zai ga nayi kuskure ya sanar dani na gyara domin ni dalibi ne wanda har yanzu yake karatu a sakandare bai maje jami'a ba. Allah ya daukaka kasarmu Nigeria ya arzutamu da shugabanni na gari. Naku Muhammad Bashir Ahmad.