Thursday, March 18, 2010

TAKAITACCEN TARIHIN REAL MADRID

Real Madrid Club de Futbol ko Los Blancos. (The White) Kwararriyar kungiyar kwallon kafa ce dake birnin Madrid na kasar Spain.
Itace kungiyar da FIFA ta zaba a matsayin kungiyar da tafi samun nasara a karni na 20, domin ta lashe kofin rukuni-rukuni na kasar Spain (La-liga) sau 31, Spanish Cup sau 17 da kofin zakarun nahiyar turai sau 9 da kuma kofin UEFA sau biyu.
An kafa kungiyar Real Madrid a shekarar 1902 (6 March 1902). A shekarar 1900 aka kafa kungiyar Club Espanol de Madrid. A 1902 kungiyar ta rabu biyu hakan ya kawo kafuwar Madrid Fooball Club.
A shekarar 1905 Madrid FC ta fara yin nasarar daukar kofi, bayan ta doke Athletic Bilbao a kofin Spanish Cup.
Madrid FC na daya daga cikin wakilan hukumar FIFA na farko kuma wakiliyar rushasshiyar kungiyar G-14 na manyan kungiyoyin da ake ji dasu a nahiyar turai.
A 1920 ne aka canja sunan kungiyar zuwa Real Madrid bayan da sarki Alfonso ya amince a yi amfani da lakabi Real da ake nufin Royal ga kungiyar.
A shekarar 1929 ne aka fara gasar La-liga inda Real Madrid ta jagoranci gasar har zuwa wasan karshe inda tayi rashin sa'a a hannun Athletic Bilbao. Ta zama ta biyu bayan Barcelona. Real Madrid ta fara lashe gasar La-liga ne a 1931/1932, sannan shekarar gaba ma ta sake lashewa.
A 1940 Santiago Bernabeu Yeste ya zama shugaban kungiyar, kuma a mulkinsa ne Real Madrid ta sake gina filayen wasanninta na Santiago Bernabeu da Ciudad Deportiva, bayan yakin basasar kasar Spain.
Santiago Bernabeu a shekarar 1953 ne ya fara dakko kwararrun yan wasa daga kasashen waje. Fitacce daga cikinsu shine Alfredo di Stefano, wannan ya bashi damar kafa tarihin kungiyar da ta fara tattara yan wasa daga sassan duniya a tarihin kwallon kafa. A karkashin Bernabeu ne Real Madrid ta zama gagabadau a fagen kwallon kafa a kasashen turai.
Real Madrid ta lashe kofin kasashen turai (Uefa Champions League) sau biyar a lokaci daga a tsakanin 1956 zuwa 1961 wanda ya hada da ci 7-3 da tayiwa kungiyar Eintracht Frankfurt a filin wasa na Hampden Park a wasan karshe a 1960. Cin kofin sau biyar a jere yasa kungiyar ta samu mallakin kofin na ainihi tare da bata damar sanya tambarin girmamawa na UEFA.
Real Madrid ta lashe Uefa Champion League karo na shida a 1966 bayan ta doke FK Partizan da ci 2-1 a wasan karshe.
Ranar 2 July 1978 shugaban Real Madrid Santiago Bernabeu ya rasu. A shekarar 1996 shugaban Real Madrid na lokacin Lorenzo Sanz ya kulla yarjejeniyar daukar Fabio Capello a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar na tsayon shekara daya.
A 1998 Real Madrid ta sake yin nasarar daukar kofin Uefa Champions League karo na bakwai bayan ta samu nasara akan Juventus da ci 1-0 a wasan karshe.
A watan bakwai na shekarar 2000 aka zabi Florentino Perez a matsayin shugaban kungiyar, a mulkinsa ya samu nasarar kawo shahararrun yan wasa kungiyar, wanda suka hada da Zinedine Zidane, Ronaldo, Luis Figo, Roberto Carlos, Raul da David Beckham. A shekarar ne kungiyar ta sake cin kofin Uefa Champions League karo na takwas. Sannan kuma ta samu nasarar daukar na tara a shekarar 2002 da kuma kofin La-liga a 2003 duk a lokacin mulkin Perez.
Ramon Calderon ya zama shugaban Real Madrid ranar 02 July 2006 da zuwansa ya sake dakko Fabio Capello a karo na biyu a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar, da kuma tsohon dan wasan kungiyar Predrag Mijatovic a matsayin manajan kungiyar.
Real Madrid tayi nasarar cin kofin La-liga karo na 30 a shekarar 2007. Sannan ta sake cinye kofin a 2008. Ranar 01 June 2009 Florentino Perez aka sake zabarsa shugaban kungiyar karo na biyu. Da zuwansa ya sayo shahararren dan wasan AC Milan da Kasar Brazil wato Ricardo Kaka akan kudi £60m. Sannan kuma sai dan wasan duniya na lokacin Cristiano Ronaldo daga kungiyar Manchester United ta kasar England, akan kudi £80m. Wannan sayayyar itace tafi kowacce tsada a tarihin kwallon kafa bayan dan wasar kasar France Zinedine Zidane.
Duk da Real Madrid tafi kusa da kungiyar Athletic Madrid. Amma babbar abokiyar adawarta itace kungiyar Barcelona.
Real Madrid itace kungiyar kwallon kafa da tafi kowacce kungiya samun nasarar daukar kofuna. Ga jerin wasu kofuna da kungiyar ta dauka:
9 Uefa Champions League.
31 Spanish La-liga.
19 Spanish Cup.
18 Regional Cup.
3 Intercontenatal Cup.
8 Spanish Super Cup.
5 Community Cup.
2 Uefa Cup.
2 Spanish League Cup.
2 Latin Cup.
2 Little Cup.
1 European Super Cup.

No comments:

Post a Comment