Wednesday, March 24, 2010

KASAR NIGERIA

Kasar Nigeria kasa ce dake yammacin nahiyar Africa, Nigeria ta samo sunanta ne da daga Kogin Niger (Niger Area), a shekarar 1898, kasar Nigeria tafi kowace kasa dake nahiyar Africa yawan mutane tana da mutane sama da 130 million. Sannan Allah ya arbarkaci Nigeria da arziki kala kala, masu tarun yawa. Nigeria na da kabilu da yawa wadda tana cikin kasashen da suka yawan kabilu a duniya.
Nigeria na da kabilu sama da 250, manya daga cikinsu sune: Hausa, Fulani, Yoruba, Igbo, Kanuri, Nupe da Ijew.
Addinin Musulunci shine yafi kowane addini rinjaye a kasar, sannan Addinin Christians. Da kuma sauran addinai kala kala.
Kasar Nigeria na da jihohi guda 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, sannan da kananan hukumomi guda 773.
A shekarar 1914 turawan Britain suka hada arewancin Nigeria da kudanci ya zama kasa daya, sannan kuma suka mamaye kasar a matsayin mulkin mallaka. Lokacin da Nigeria ke karkashin mulkin Britain, turawa ne ke mulkin kasar har zuwa ranar 1 October 1960 lokacin da Nigeria ta samu yancin kanta daga turawan mulkin mallakar kasar England.

Bayan samun yancin kai ne Dr. Nmandi Azikiwe ya zama dan kasa na farko wanda ya shugabanci Nigeria. Sannan Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama Prime Minister.
Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), kuma ya zama Prime Minister Jihar Arewa. Wadannan shugabanni sunyi aiki tukuru wajen ganin kasa ta cigaba, amma a 1966 akayi musu juyin mulki kuma a wannan juyin mulki ne aka kashe Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto).

General Aguiyi Ironsi ya hau mulkin kasar bayan wannan juyin mulki a January 1966 amma shima bai dade ba akayi Juyin Mulki. General Yakubu Gowon ya karbi mulki a July 1966.
A 1975 sojoji suka sake yin juyin mulki General Murtala Ramat Muhammad ya hau mulkin kasa. Amma shi wata takwas yayi yana mulki a kayi juyin mulki kuma aka kashe shi.
Sannan General Olusegun Obasanjo ya karbi mulki yayi shekaru uku sannan ya mika mulki a hannun farar hula. Inda Alhaji Shehu Shagari yayi nasarar hawa mulki a 1979 a matsayin zababbe.
Mulki bai dade a hannun farar hula ba sojoji suka sake yin juyin mulki, General Muhammad Buhari ya hau kujerar mulki, a 1983 shima bai dade ba aka sake yin juyin mulki amma ba'a zubar da jini ba.
Sakamakon wannan juyin mulki General Ibrahim Badamasi Babangida ya dare kujerar mulki
a 1985 har zuwa 1993 sannan shima akayi masa juyin mulki. Chief Ernest Shonekan ya hau mulki na yan watanni sannan General Sani Abacha ya karbi mulki a 1993.
Ranar 8 Auguest 1998 Allah yayiwa Gen. Sani Abacha rasuwa. Kuma shine shugaban Nigeria na farko da ya mutu yana kan mulki.

Bayan rasuwar General Sani Abacha. General Abdussalam Abubakar ya hau mulki na rukon kwarya. Tun daga wannan lokaci mulki ya dawo hannu farar hula har zuwa yau. Ranar 29 may 1999 General Olusegun Obasanjo ya hau mulkin Nigeria a matsayin damukradiya (Democratic) Chief Obasanjo yayi mulki har na tsawon shekara takwas bayan sake lashe zabe da yayi a 2003.
Ranar 29 may 2007 Alhaji Umaru Musa Yar'adua yayi nasarar hawa mulkin kasar Nigeria kuma har zuwa yau shi ke mulkin kasar. Sannan zabe gaba za'ayi shi a 2011.

Kamar sauran kasashe Nigeria na da alamomin kasa (National Symbols) masu yawa wanda suke da muhimmanci a wurin kowane dan asalin kasar Nigeria.

TUTAR KASA (National Flag) Taiwo Akinkami dan kasar Nigeria shine ya tsarata a 1959 amma a lokacin ba'a amfani da ita. Tun 1914 Nigeria ke amfani da tutar British Union har zuwa tsakiyar daren ranar 30 September 1960 washe garin samun yancin kai, sannan Nigeria ta fara amfani da ita.
Tutar Nigeria na da kala biyu da aka raba gida uku (Kore, Fari, Kore). Koriyar kala na nuni da kyakkyawar kasar noma. Sannan Fara kana na nuni da zaman lafiya da hadin kan kasar.

TAMBARIN KASA (Coat and Arm). An samar da tambarin a 1960. Tambarin na dauke da bangarori kamar haka:
MIKIYA wadda ke nuni akan karfin Nigeria.
DAWAKAI guda biyu na nuni akan martabar Nigeria.
Y na nuni akan manyan ruwan kasar guda biyu. Kogin Niger da Kogin Benue.
FILAWA na nuni akan arzikin noma da kasar ke dashi. Sannan a karshe an rubuta "HADIN KAI DA IMANI, ZAMAN LAFIYA DA CIGABA" wanda ke nuni akan shine manufar Nigeria.

TAKEN KASA (National Anthem). Taken Nigeria na nuni akan bukatar kowane dan kasa yayi biyayya tare da yin aiki tukuru domin samu zaman lafiya da hadin kan kasa baki daya.

RANTSUWA (National Pledge). Wani alkawari ne da rantsuwa da dan kasa ke dauka domin yiwa kasa aiki bisa aminci.

A karshe wannan shine kadan daga cikin abubuwan da suka shafi kasarmu Nigeria musamman yadda akayi mulki tunda daga samun yancin kai. A ranar 1 ga October 1960, ranar da duk dan Nigeria ke alfahari da ita.
Allah (SWA) ya kara daukaka kasar Nigeria ya bamu shugabanni nagari.

3 comments:

  1. Muna faranciki kwarai da gaske. Stey bless

    ReplyDelete
  2. Malam Bashir wannan na yaba da wannan himma taka, kuma Allah ya kara maka karfin gwiwa.

    ReplyDelete