KISHI dai wata damuwa ce da takan sami
zuciyar mutum, ko kuma shi mutum ya sa
kansa a cikin wata damuwa a lokacin da
yake ganin alamar zai rasa wani abu da
yake matukar kauna, wanda idan mutum
ma bai yi hankali ba sai ya shiga cikin wani
irin hali na kaka-nika-yi, har ma ya zo yana
da-na-sani.
Kodayake kishi iri-iri ne, amma wanda muka
fi sani, kuma muke magana a kai, shi ne
kishi na tsakanin matan da ke auren miji
guda. Shi kishi ya samo asali ne tun zamanin
kakanmu Annabi Ibrahim (A.S) A cewar
wasu Malamai, wai tsakanin matansa Saratu
da Hajara. A lokacin da Allah bai ba wa
Saratu haihuwa ba, sai Sarkin Masar ya bai
wa Saratu, Hajarah domin ta rika taya ta
aikace-aikace da wasu hidimomin gida.
Daga bisani ita Saratu ta shawarci mijinta
Annabi Ibrahim (A.S) ya auri Hajarah ko Allah
Zai ba shi haihuwa.
Allah, Mai hikima, cikin ikonSa, bayan an
daura aure da dan lokaci kadan, sai Hajarah
ta sami ciki. Hakan bai yi wa Saratu dadi ba,
ya kuma sosa mata zuciya. Cikin bakin ciki,
ta shawarci mijin nata da ya sa a huda wa
Hajarah kunnuwa da hanci. A cewarta, yin
hakan zai nuna cewar ita kuyanga ce. Bisa
ga ikon Allah sai Hajarah ta kara kyau da
wannan hujin kunne da hanci da aka yi
mata. Har wa yau Saratu ta ce a’a. A daura
wa Hajarah awarwaro, a sa mata ’yan
kunne. Yin haka ya sake kara mata kyau
wanda ma ko wucewa take sai an san
matar Annabi ce ke wucewa.
A karshe duk abin nan da ake yi bai gamsar
da Saratu ba, sai cewa ta yi, ta ga Hajarah
tana kumburi don haka maigida ya fitar da
ita a gidan, kada ta sa musu wata cuta. Allah
mai girma da daukaka Ya umurci Annabi
Ibrahim da ya dauki matarsa wato Hajarah
ya kai can wani gari (Makka) wanda a yau
ya zama tsarkakakken wurin da kowane
Musulmi ke burin ziyarta. Duka shawarwarin
nan da Saratu ta yi ta ba wa Annabi Ibrahim,
ta yi ne a bisa kishi.
To ashe ke nan kishi yana da asali, amma ba
wai ana nufin ya zama halas ba ne don ya
samo asali a wurin Saratu da Hajarah. Kishin
wannan zamani ya sha bamban, nesa ba
kusa ba da irin kishin da Saratu ta nuna. A
yanzu akan nemi a yi kashe–kashe da
asarar dukiya. Matar aure ta kan bi karuwa
gidanta, ta ci mata mutunci, wai don ta ji
labarin mijinta na neman ta. Haka kuma
budurwa ta bi matar aure gida ta ci
zarafinta. Ballantana tsakanin kishiyoyi abin
ba a cewa komai.
Abin tambaya a nan shi ne, shin me ake wa
kishi? To ra’ayin wasu matan dai ya yi nuni
da cewar mazan su ne umul aba’isin da ke
haddasa kishi, a lokacin da suka kasa yin
adalci tsakanin matansu. Alal misali kai ne ke
da mata biyu sai ka nuna fifikon wannan da
‘ya’yanta a kan daya, ka ga dole ne a nan za
'a samu damuwa, wadda ka iya haifar da
kishi tunda dukkansu soyayya ce ta sa ka
tara su, don haka dole ne ka yi adalci, a
tsakaninsu.
Wasu mazan kuwa na ganin wulakancin
matan ne kan ishe su, su shiga aure-aure.
Saboda a lokacin da mace take jin kai, sai ta
yi ta nuna wasu irin halaye daban-daban, a
inda ka yi gargadi ka gaji, dole ne ka nemi
wata wacce za ta kwantar ma da hankali.
Yin hakan kuma shi ke sosa zuciyar mata. A
takaice dai soyayya ake wa kishi.
To, wane lokaci ne ya kamata a nuna kishi?
Alal hakika idan mace ta ga an fita harkarta
kwata-kwata, wato, ba a yi da ita, ta yadda
miji bai kulawa da ita ko ‘ya’yanta, to, a nan
fa dole ne hankalinta ya tashi, saboda ganin
a da shi nata ne ita kadai, a yau kuma ya
koma nasu.
Kashi casa’in bisa dari na maza haka suke,
da zarar sun sami sabuwar amarya ko da ta
’yar tsana ce, sai kwata-kwata su juya wa
uwargida baya, har sai in ruwa ya kare wa
dan kada, sannan a dawo yana tsilla-tsilla a
gefen teku.
Bugu da kari akwai wata babbar matsalar
da ke addabar mata a wannan lokaci ta
yadda maza suke bata wa matansu na aure
suna a wurin abokansu. Misali miji ne ya
sami sabani da matarsa, maimakon ya yi
kokarin yi mata nasiha ko ya gaya wa
iyayenta, a’a, sai dai ka ga ya tafi wata
matattara da ake kira Chamber, yana yi wa
matarsa tonon silili. Wani ma, wallahi, har
yadda yake kwana da matarsa yake fadi.
Yin haka ya kazanta. A nan za a ba wa
namiji shawarar ya je ya kara aure. Auren
da zai yi ba wai don raya sunnar Manzon
Allah (SAW) ba ne, a’a, sai dai don ya ci
zarafin matar gida.
Haka kuma tun daga waje zai zayyana wa
budurwar irin halayen matarsa ta gida, in ta
dauro ma akan yi wa amaryar alkawarin da
zarar ta shigo za a kori ta gidan. A nan idan
ba a iya korarta ba, to, sai a yi ta zaman
kwari, kowa na ji da kanshi, a yi ta zuba
kishi iri-iri. Daga nan in ba a yi hankali ba sai
mazuga su shiga tsakaninsu, su tura su ga
halaka ta hanyar bin gidan bokaye don
neman asirin samun gindin zama a wurin
miji. Uwargida na neman kwatar ’yanci,
amarya na cewa sai ta fita ta bar mata gida.
To, boka na iya yi wa mutum abin da Allah
bai yi niyyar yi masa ba?
Har ila yau akwai wasu mazan da kansu da
kuma hannayensu bibbiyu suke rura wuta a
gidansu, su haddasa fitina, su hana zaman
lafiya, ta yadda namiji yake zana munafiki
tsakanin matansa. Shi wannan namijin, shi
zai ta kai da komowa tsakanin matansa,
wato, in ya je wurin wannan sai ya ce, ai ga
abin da waccan ta ce, ko take yi, sannan
idan ya koma wurin waccan sai ya ce, ai ga
abin da wannan ta yi, ga abin da ta ce. Shi
dai yana jin dadin ya ga kawunansu a
rarrabe, wato a yi ta fada saboda shi.
Jahilan maza har cewa suke in mata suka
hada kansu, namiji ba ya jin dadi. Mu kuma
a wurinmu mata ba abin da hakan ke
haddasawa sai koma baya, ga rashin
kwanciyar hankali, domin ko shi kansa mijin
a cikin fargaba yake a duk lokacin da ya
tunkari gida, sai dai idan ba gida daya ya
hada su ba.
Bari in ba mata misali na wani gida da nake
aminci da su. Kullum na kai ziyara zan iske
matan mutamin su uku tare da maigidansu,
wannan na yi mai, tausa, waccan na
mammatsa masa kafafuwa da sauransu. A
koda yaushe suna cikin farin ciki tsakaninsu
da maigidansu. Da na tambaye shi, ko wane
irin asiri ne ya yi wa matansa?. Sai ya nuna
cewa babu asiri a ciki, illa kawai, dukkan
matan nasa masana ne, kuma shi ba ya
auren mace face sai ya koyar da ita
tarbiyya, na yadda za ta yi zama tare da shi
da kuma kishiyoyi kamar yadda Annabi
(SAW) ya zauna tare da matanSa.
A karshe ina shawartar mata su yi hakuri a
kan maganar kishiya, tunda Allah ne da
kanSa Ya umurci maza da yin aure fiye da
daya. A Alkur’ani Allah Ya ce “Ku auri mata
bibbiyu ko uku, ko hudu, amma in kuna
tsoron ba za ku yi adalci ba, to, ku auri
daya” Suratul Nisa’i. Sannan Manzo Allah
(SAW) Ya ce “Ku yi aure ku hayayyafa,
domin na yi alfahari da ku ranar alkiyama”
Saboda haka aure fiye da mace daya ba
aibu ba ne, in dai an yi don raya sunnar
Manzo ne, tabbas Allah Zai taimaki bawanSa.
Ga mazan kuma ina shawartar ku da ku ji
tsoron Allah! Ku yi hattara! Ku guji
gamuwarku da Allah! Kada ku ga kamar
Allah Ya ba ku ’yanci na aure da saki, ku ce
za ku yi yadda kuke so. Mata amanar Allah
ne gare ku, matukar kuka ci amana, ko
shakka babu za ku tsaya a gaban Allah ku
fuskanci shari’a. Idan muka yi koyi da
yadda Manzon Allah (SAW) ya zauna da
matansa, tabbas za mu samu rayuwa mai
inganci da albarka daga mu har zariyarmu.
Haka nan ina kara shawara jama’a maza da
mata, mu dage mu nemi ilimin Islama,
musamman abin da ya shafi zamantakewar
aure, komai kake yinsa cikin ilimi ya fi dadi,
ya fi sauki. Allah Ya ba mu ikon yi, Ya kuma
sa mu dace da rayuwa mai albarka. Amin.
No comments:
Post a Comment