Malam Salihu Sagir Takai, babu tantama kan
cewa shi ne dan takarar Gwamna a karkashin
Jam ’iyyar ANPP. Gwamna Malam Ibrahim
Shekarau ke son ya zama magajinsa a zaben
shekara mai zuwa, hakan na nuni da cewa
Shekarau ya fi natsuwa da ganin cancantar
Takai kan sauran mabiyansa. Kamar
Mataimakin Gwamna Abdullahi T. M. Gwarzo da
Garba Yusuf da Sani Lawan kofar-Mata da
Injiniya Sarki Labaran da Musa Iliyasu
Kwankwaso da Malam Ibrahim Khalil.
Kafin zancen ya fito fili kan goyon bayan
Takai rahotannin sun nuna cewa mabiya
Malam Shekarau a jam ’iyyance sun ba shi
dama ya zabi duk wanda yake ganin ya fi
cancanta su yi masa biyayya. Amma da ya
buga gangar zuwa ga Takai, sai masu
sha ’awar takarar Gwamna da ’yan siyasa suka
yi tsaye, don rawar ba za ta yi daidai da kidan
ba, inda suka fara koke-koke da kokarin nusar
da Gwamna ya yi adalci wajen fitar dan
takara. A takaice suna kira da a yi zaben fitar
da gwani a jam ’iyyar don su zabi wanda suke
ganin ya fi dacewa ya gaji Gwamna Shekarau.
Takai ya taba zama Kwamishinan kananan
Hukumomi a gwamnatin Shekarau, Gwamnan
ya zabe shi ne bisa wasu dalilai na kashin
kansa, har yanzu bai fito ya bayyana wa
al ’ummar Jihar Kano dalilansa na fifita Takai a
kan sauran masu neman takarar Gwamna ba.
Shekarau ya yi amfani da wannan damar ce
ya tsayar da dan takara, don ya san cewa a
tsari na dimokuradiyya da wuya Gwamna ya
tsayar da dan takara, jam ’iyyarsa ba ta tsayar
da nata ba.
Jam ’iyyar ANPP a Jihar Kano ta yi farin jini,
masu son tsayawa takarar Gwamna a cikinta,
suna da yawa kwarai kuma jiga-jigai a
jamiyyar, irin su Mataimakin Gwamna
Abdullahi Tijjani Gwarzo da Sanata Kabiru Gaya
da Sani Lawan kofar-Mata da Malam Ibrahim
Khalil da Habibu Sale Minjibir da sauransu suna
nan.
A bisa tsarin jam’iyyu, a kan ba ’yan takara
damar yin sulhu a tsakaninsu, in hakan ta
gagara sai a sake ba su wata dama ta shiga
zaben fitar da gwani, a nan ne ake gwada
farin-jini da kwanji don samun wanda ya yi
nasara a tsakaninsu. Kukan da ’yan takara a
Jam’iyyar ANPP a Kano ke yi, don hanyar da
aka dauka ga dukkan alamu suna zargin ba za
a yi masu adalci ba ne.
Tuni mafi yawan ’yan takarar sun fito karara
sun bayyana rashin amincewa, da take-taken
Gwamna Shekarau na kin ba su dama ta
hanyar cusa nasa dan takarar. Sanata
Mohammed Bello ya fito ya bayyana wa
duniya cewa in har ba a ba shi damarsa ba, zai
fice daga jam ’iyyar da hakarsa ba ta cimma
ruwa ba, ya cika alkawari ya tafi Jam’iyyar
PDP. Haka kuma sauran ’yan takarar duk sun yi
magana da murya guda wajen kin yarda da
tsaida Takai da kuma mara masa baya.
Mene ne ya sa Gwamna Shekarau ya kafe a
kan Takai ne dan takara? Ko kuwa yana ganin
cewa shi ne zai ci gaba da manufofin
gwamnatinsa? Shin shi ne zai kawar da kai ga
masu bukatar a tono abin da ya binne bayan
ya bar mulki? Ko kuma yana ganin a tunani da
hangen nesa irin nasa Takai ya fi sauran masu
neman Gwamnan Jihar Kano cancanta ce?
Sauran ’yan takarar suna ganin sun cancanta,
sun kuma taimaka wa Shekarau a zaben
shekarar 2003 da 2007. Don haka, suna ganin
suna da goyon baya da masoya da magoya
baya da za su iya kai su gaci a zabe mai zuwa.
Wannan ya sa suka yi gangami, inda
kowanensu ya nuna wa duniya karfinsa a
siyasance.
Tsayar da Takai na fuskantar tirjiya, ba daga
’ yan takarar Gwamna kawai ba, har da sauran
’yan takara na kananan hukumomi da jami’an
gwamnati da masu fada-a-ji a Jam’iyyar ANPP.
Saboda wasu dabi’u da ake zargin Takai yana
da su, kamar rowa da rashin iya hulda da
jama ’a.
Shawara ga Malam Ibrahim Shekarau, idan har
yana son Jam ’iyyar ANPP ta taka rawar gani a
zabe mai zuwa, ya kamata a matsayinsa na
uba kuma jagora, ya hada kan ’ya’yan
jam’iyyar. Ya kuma zama mai yin biyayya ga
tsarin dimokuradiyya, ta hanyar ba kowa
damarsa, ta bari a yi zaben fitar gwani a
jam ’iyyar ba tare da fitowa karara yana mara
wa wani dan takara baya ba.
Gwamna Shekarau ya sani cewa idan ya matsa
sai Takai, hakika wadansu daga cikin
aminansa da abokan tafiyarsa a siyasa za su
iya yin tsalle su ma fice daga jami ’iyyar, da ma
ba ta gama farfadowa daga halin da ta shiga
ba sakamakon ficewar Janar Muhammadu
Buhari daga jam ’iyyar, sannan wadansu za su
iya kin ficewa daga jam’iyyar su kuma yi mata
zagon kasa.
Ya kamata Gwamna Shekarau ya tambayi
kansa, shin yana da tabbas in Takai ya zama
Gwamna ya samu biyan bukatunsa? Ba ya
kallon yadda ake kwashewa tsakanin
gwamnonin da suka sauka da wandanda suka
gaje su?
Shekarau kada ya manta akwai jan aiki a
gabansa, ko da ’yan jam’iyya kansu a hade
yake, kafin su iya lashe zaben shekarar 2011.
A kullum Jam ’iyyar PDP a Jihar Kano sai kara
karfi take yi ga kuma sabuwar Jam’iyyar CPC
da Janar Buhari ke ciki, in har sun tsaida dan
takaran Gwamna mai nagarta su ma za su iya
lashe zaben Gwamna a Kano a shekarar 2011.
Tsakanin Gwamna Shekarau da Takai da masu
adawa ba a san maci tuwo ba, sai miya ta
kare. Ko Takai zai taki sa ’a ya zama magajin
Shekarau? Lokaci ne kadai zai bayyana mana.
Shehu Mustapha Chaji
No comments:
Post a Comment