Saturday, December 11, 2010

SIYASAR KANO, A ZABEN 2011

Siyasar Jihar Kano ta dade tana ba ’yan
kasar nan mamaki. Wannan shi ya sa ake yi
mata kirarin “siyasar Kano sai Kano” Wadansu kuma na da ra’ayin cewa “ba'a
mulkin Kano sau biyu” Tabbas kirarinta na
farko yana da muhalli ba a Kano kadai ba
har a Nigeria baki daya. Gwamna Ibrahim
Shekarau ya dakushe ra’ayin “Ba'a mulkin
Kano sau biyu” saboda zarcewar da ya yi,
inda shekara mai zuwa zai cika shekara
takwas a kan mulkin Kano.
A wannan karo za a raba rana ne tsakanin
jam’iyyun siyasa uku watau, Jam’iyyar ANPP
mai mulkin Jihar da Jam’iyyar CPC sai kuma
Jam’iyyar PDP da aka amshe mulki daga
hannunta a zaben 2003. Amma wasu na
ganin cewar tarnakin siyasar na nan
tsakanin Jam’iyyun ANPP da CPC ganin
yadda suke da magoya baya, amma wasu
na ganin cewa duk wanda yake ganin
Jam’iyyar PDP ba barazana ce ga sauran
Jam’iyyun biyu ba, to wata kila baya kasar
Kano lokacin da Jam’iyyar ta yi zagayen
motsa jam’iyya, inda dimbin magoya
bayanta suka tare ta a daukacin kananan
hukumomi 44 da jihar take da su.
Ba nan gizo ke saka ba musamman idan
muka yi la’akari da matsalolin da ke cikin
jam’iyyun uku a kan fitar da ’yan takararsu
a zaben raba gardamar jam’iyyun siyasa da
za a gudanar daga ranar 26 ga watan
Nuwamba zuwa 15 ga watan Janirun badi.
A Jam’iyyar CPC akwai ’yan takara a kalla
biyar da suka hada da: Kanar Lawal Jafaru
Isa, Tsohon gwamnan JiharKaduna da
Injiniya Magaji Abdullahi da Muhammad
Abacha dan marigayin shugaban kasa Janar
Sani Abacha da Dokta Auwal Anwar da kuma
Rufa’i Sani Hanga. Masu nazarin yadda
siyasa ke tafiya sun yi hasashen cewa
Kanar Lawal Jafaru Isa ne ya fi cancantar
jam’iyyar ta tsayar amma bisa dukkan
alamu akwai kishin-kishin cewa Rufa’i Sani
Hanga ne dan-lelen shugabannin jam’iyyar
da Ahmadu danzago ke jagoranta bisa
dalilin da ba su bayyana ba. Har ila yau
wasu na cewa akwai yarjejeniya ta
karkashin kasa tsakanin sauran ’yan takarar
3 ta cewar za su mara wa daya daga cikinsu
baya idan har aka ci gaba da nuna musa
bambanci wanda kuma hasashe jama’a ya
nuna Kanar Lawal Jafaru Isa na iya zama
zabinsu.
A ra’ayoyin mutane da dama suna gani
warware wannan matsala na iya kawo wa
Jam’iyyar nasara a zabe mai zuwa ganin
yadda jama’ar Kano suka yi na’am da
Jam’iyyar CPC , wasu kuma na ganin ko
babu komai farin jinin da Janar Buhari yake
da shi zai iya kawo musu babbar nasara
kamar yadda ya kafa Gwamnatin ANPP a
zaben 2003. Haka nan kuma ita kadai ce
jam’iyyar da ba ta taba mulki ba balle a ce ta
saba wa wani.
Idan muka waiwayi Jam’iyyar ANPP mai
mulkin Jihar Kano za mu ga yadda ’yan
takara da suka hada da: Salihu Sagir Takai Kwamishinan ruwa na jihar da Injiniya
Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo,
Mataimakin Gwamna Ibrahim Shekarau da
Senata Kabiru Gaya da Lawal Sani kofar
mata da Malam Ibrahim Khalil, suka fito da
niyyar karawa da junansu a zaben raba
gardama. Tarnakin da suke fama da shi a
jam’iyyance sun hada da zargin da ake yi na
cewa Malam Ibrahim Shekarau ya fifita
Salihu Sagir Takai a kan sauran ’yan takarar
hudu wanda hakan ke neman kawo cikas a
jam’iyyar da har wasu ke tunani yi wa
jam’iyyar zagon kasa idan har aka yi musu
rashin adalci. Haka nan kuma akwai babban
kalubalen da ke fuskantar gwamnatin Jihar
Kano ta ANPP, shugabannin kananan
hukumominta sun shigar da kara kotu
saboda sauke su da aka yi daga kan mulki.
Akwai tunanin cewa duk wadanda aka yi
wa ba daidai ba zasu iya yi wa jam’iyyar
zagon kasa wanda wasu na ganin
wadannan shugabannin kananan
hukumomi da aka sauke sune ’yan siyasar
kwarai da ya kamata jam’iyyar rike.
Wasu kuma suna hangen cewa maganar da
Alhaji Mahmud Ado Bayero, Hakimin Fagge ya
yi a kan biyan diyya ga wadanda kwayar
maganin Troban ta kamfanin Pfizer ya
nakasa tamkar wani haske ne mai nuni
yiwuwar akwai takun saka tsakanin
masarautar Kano da gwamnatin jihar, kuma
ko da masarauta ba ta cika shiga siyasa kai
tsaye ba, suna da jama’a irin na su
musamman idan aka yi la’akari da irin
martaba da Sarkin Kano yake da ita ga
mutanen jihar.
Wani kalubalen da ake hange kuma shi ne,
idan har aka samu matsala a zaben raba
gardama tsakani Gwaman Shekarau da
mataimakinsa Alhaji Abdullahi Tijjani
Muhammad Gwarzo yana iya haifar wa
jam’iyyar matsalar da Allah kadai ya san
idan za ta tsaya musamman idan
mataimakin na shi ya samu goyon bayan
sauran abokan neman tsayawa takarar
gwamna da suka rasa.
Ita kuwa Jam’iyyar PDP, masu nazarin
siyasar Kano na ganin a aljihun tsohon
gwamnan jihar, Alhaji Rabi’u Musa
Kwankwaso ta ke, saboda har inda yau take
ba za a ce ga takamaiman dan takararta ba
sai dai akwai irinsu Kanar Habibu Shu’aibu
da suka bayyana niyyar tsayawa takararsu
da kuma shi kansa Dokta Rabi’u Musa
Kwankwaso, sai kuma wasu da ke jita-jitar
fitowar Hon. Faruk Lawal. Masu
hasashen siyasa na ganin cewar da wuya
PDP ta yi tasiri musamman idan aka yi
la’akari da dalilan da suka sa Kwankwaso ya
rasa kujerarsa a zaben 2003, watau
matsalar da ya samu da ’yan fansho da
sauran ma’aikata, sai kuma wasu da ke
ganin faduwarsa na da nasaba da rashin
jituwarsa gidan sarautar Kano.
Akwai kuma masu ganin cewa bai kamata a
tsayar da Kwankwaso ba saboda yana da
takardar tunhuma watau white Paper,
saboda haka suna son a fito da sabon dan
takara wanda ba shi da wata matsala da za
ta hana shi cin zabe, sai dai kuma wasu na
ganin wannan ba matsala ce ba tun da a
cewarsu ’yan majalisa sun wanke
Kwankwaso kuma gashi dan lelen Shugaba
Goodluck Jonathan. Duk da haka dai ana
ganin cewa kwankwasiya shugabannin
Jam’iyyar PDP suke yi wa biyyaya, haka nan
kuma ita ke da rinjayen magoya bayan
Jam’iyyar PDP a Kano.
Daga karshe dai masu fashin bakin siyasa
na ganin cewa idan har Jam’iyyar PDP ta
tsayar da Rabi’u Musa kwankwaso a
matsayin dan takararta to zai riga rana
faduwa saboda jama’a ba su san shi,
dalilinsu kuwa shi ne, ya gwada takara ba
sau daya ba yana faduwa kuma ya tsaida
dan takara ya fadi, sa’anan kuma ya kasa
gano inda yake da baraka balle ya dinke ta
ga shi kuma yana goyon bayan Shugaba
Goodluck inda wasu ke cewa sun ce ko
nawa za su kashe sai sun kawo Jihar Kano
A takaice dai guguwar siyasar ta fi kadawa
tsakanin jam’iyyun CPC da ANPP wanda
wasu ke ganin muddin Jam’iyyar CPC ta ba
Kanar Lawal Jafaru Isa takara ganin yadda
mutane ke son shi zai yi tasiri kwarai
wanda har ana yi masa kallon zama
gwamnan jihar, sai dai kuma wasu na ganin
cewar muddin Gwamna Ibrahim Shekarau
ya bari aka yi zaben raba gardama kamar
yadda dokar Jam’iyyar ANPP ta tanadar
akwai kamshin za su iya tabukawa wajen
samar da gwamna a jihar.

(Aminiya)

No comments:

Post a Comment