Tuesday, March 16, 2010

LABARIN MALAM BUBA

Assalamu Alaikum. Malam Buba mutum ne mai son abin dariya a koda yaushe, yana zaune a kauye shida iyalansa kuma yana da garken dabbobi masu yawa.
Wata rana Malam Buba yana son cin dariya, sai ya fara tunanin yadda zaiyi don cin dariya, can sai dabara tazo masa, kawai sai ya shiga cikin kauyen da yake zaune a guje yana ihu-ihu a taimake ni Zaki ya shigo cikin garken dabbobi na zai cinye su. Yayi wannan dabarar ne kawai don yaga ya mutanen garin nan zasuyi wane irin mataki zasu dauka. Mutanen garin kuwa da jin ihun Malam Buba sai kowa ya fara fitowa daga cikin gidansa, kowa dauke da makamai wasu ko riga babu a jikinsu, suka nufi gidan Malam Buba don taimakonsa. Da zuwansu sai suka tarar da Malam Buba yana ta dariya har da faduwa kasa, kuma ga dabbobinsa na cin abinci cikin kwanciyar hankali. Wannan abin ya batawa mutanen kauyen rai, sukace da Malam Buba ina Zakin da ya shigo zai cinye ma dabbobin, sai kawai yace dasu "nayi haka ne kawai don naci dariya" mutanen kauyen kowa ya koma gidansa cin fushi da jin haushi.
Wata uku da yin wannan abu sai ga Zaki ya baiyana a gaskiyan ce a garken Malam Buba ya fara gaggatsa dabbobin Malam Buba suna mutuwa, nan take Malam Buba ya shiga cikin kauyen yana ihu yana kiran azo a taimake shi. Sabida yaudarar da Malam Buba yayiwa mutaten kauyen a baya yasa ba wanda ya fito don taimakonsa. A karshe Zakin ya kashe duk dabbobin Malam Buba.
Malam Buba ya zama talaka, sannan ya koyi babban darasi.

A karshe wannan labari yana nuna mana muhimmanci fadar gaskiya a kowanne hali. Domin da Malam Buba bai yaudari mutanen kauyensa ba da baiyi hasarar dabbobinsa ya koma talaka ba.

1 comment:

  1. masu fadar gaskiya sunyi karanci musamma a wannan zamani. Allah kabamu ikon fadarta ako wane hali

    ReplyDelete