Friday, December 3, 2010

TAKAITACCEN TARIHIN BABAN SADIQ


Abdullahi Salihu Abubakar wato (Baban Sadiq) an haife shi a anguwar Hausawa, Garki Village dake karamar hukumar Birni (Munincipal) a cikin babban birnin tarayya Abuja, a shekarar 1976 shekaru 34 da suka wuce kenan.

Asalin kakannin Baban Sadiq dama wasu daga cikin mazauna anguwar Hausawa, Garki Village daga Kanon Dabo suka zo, shekaru sama da dari biyu (200) da suka gabata.

Baban Sadiq yayi karatunsa tun daga Firamare, Sakandare har zuwa Jami'a duk a cikin babban birnin tarayyar Nigeria Abuja.

A halin yanzu Baban Sadiq na da shedar digiri akan fannin tsimi da tanadi (Economics) sannan kuma har yanzu yana kan neman Ilimin Al-Qur'ani da sauran fannoni daban daban kan addinin Musulunci.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) mutum ne mai sha'awar rubuce-rubuce da karance-karance da kuma son binciken ilimi kan fanni daban daban musamman Tsimi da tanadi (Economics) da kuma Fasahar Sadarwar Zamani (Information Technology) da sauran fannoni da dama.

Baban Sadiq mutum ne mai son ganin al'ummar Hausawa sun fahimci fasahar zamani, kuma Allah ya hore masa juriyar karatu da rubutu daidai gwargwado.

Saboda yadda yake son ganin Hausawa sun fahimci fasahar zamani suma an tafi dasu kamar kowacce al'umma kar a barsu a baya Baban Sadiq ya rubuta litattafai kan wannan harka mai muhimmanci ga kowacce al'umma. Duk da littatafan bai kammala su ba amma akwai "Fasahar Intanet A Saukake" cikin harshen Hausa wanda ke kan hanyar fitowa ko wane lokaci daga yanzu.

Sannan kuma sai wadanda yake rubutawa sun hada da: Tsarin Mu'amalar Da Fasahar Intanet da kuma Wayar Salula Da Tsarin Amfani Da Ita.

Duk da haka Baban Sadiq bai tsaya nan ba yana gabatar da kasida mai suna "Fasahar Intanet" a jaridar Aminiya duk mako, inda masu karatu ke aiko da tambayoyin abinda basu gane ba yake basu amsa nan take daidai yadda zasu gane.

Bayan haka Baban Sadiq na da makarantar Kimiya da Fasaha a shafin intanet mai suna "Makarantar Kimiyya Da Fasahar Sadarwa" wanda za'a iya samu a (http://fasahar-intanet.blogspot.com) wannan makaranta na da dalibai masu yawa a ciki da wajen Nigeria, kamar su Niger da Cameroon.

A karshe Baban Sadiq na da aure da 'yaya uku Sadiq, Nabilah da kuma Hanan.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
+2348032493020

No comments:

Post a Comment