Thursday, December 9, 2010

FALLASAR WIKILEAKS NA NEMAN TADA HANKALIN HUKUMOMIN NIGERIA


Bayanai na baya-bayan nan da shafin
intanet na Wikileaks mai kwarmata
bayanan sirrin da aka tsegunta masa
ya wallafa, sun bayyana irin rawar da
Amurka ta taka a lokacin da
Goodluck Jonathan yake matsayin
mukaddashin shugaban Nigeria a
yayinda shugaba na wancen lokaci
Umar Yar'adua yake jinya.

Bayanan sun ambato Goodluck
Jonathan da cewar ya na kokarin
shawo kan jama'ar Arewacin Najeriya
wadanda ba su saki jiki da shi ba, ta
hanyar amfani da wasu manyan
mutanen yankin arewan, musamman
tsohon shugaban Nigeria
Abdussalami Abubakar wanda zai
lallashi iyalin 'Yar Adua, su saka shi, ya
yi murabus cikin daraja da mutunci.

Haka kuma zai bi shawarar Amurka ta
nisanta kansa da Olusegun
Obansanjo.
Jakadiyar Amruka a Najeriya a lokacin
Robin Saunders ta gana da
mukaddashin shugaban kasar
Najeriya a lokacin wato shugaban
yanzu Goodluck Jonatahan ranar 26
ga watan Fabrairun bana, jim kadan
bayan da marigayi shugaba 'Yar'adua
ya koma Najeriya daga Saudiyya inda
yayi jinya.

Jonathan ya kuma fada mata cewa a
saninsa jam'iyyar PDP ta zabe shi ne a
matsayin abokin takarar shugaba
'YarAdua a 2007 saboda yana
wakiltar yankin Niger Delta.
Ya ce "ba an dauke ni ba ne na zama
mataimakin shugaban kasa saboda
ina da wata kwarewa ta siyasa. Ba ni
da ita. Da akwai mutane da dama da
suka fi cancanta su zama mataimakin
shugaban kasa, sai dai kuma wannan
ba yana nufin wani zai iya juya ni ba.
Bayanan suka ce Goodluck Jonathan
ya ce yana kokarin shawo kan
jama'ar Arewacin Nigeria wadanda ba
su saki jiki da shi ba, ta hanyar amfani
da wasu manyan mutanen yankin
arewan, musamman tsohon
shugaban Nigeria Abdussalami
Abubakar wanda zai lallashi iyalin 'Yar
'Adua, su saka shi, ya yi murabus cikin
daraja da mutunci.
Hakan in ji Goodluck zai fi sauki a
madanin samun goyon bayan kashi 2
cikin 3 na majalisar ministoci mai
mutum 42. Ya kuma bayyana yadda a
wani zaman majalisar minitocin aka
tashi baram-baram inda aka yi ife-ife.


Goodluck ya dora laifin rudani a kan
mutane hudu
Goodluck ya dora laifin rudanin da
aka shiga a Najeriya a lokacin kan
mutane hudu dake kewaye da 'Yar
'Adua, wato uwargidansa Turai 'Yar
'Adua, da babban mai tsaron lafiyar sa
Yusuf Tilde da dogarin shugaba
'Yar'Adua Mustapha Onoe-dieva da
Tanimu Kurfi mai baiwa marigayin
shawara kan harkokin tattalin arziki.


Haka kuma ya ambaci Abba Ruma
ministan ayyukan noma da Adamu
Aliero ministan birnin Abuja a
matsayin wasu masu hana ruwa
gudu.


Goodluck Jonathan yace ya yarda
wadannan mutane suna da wata
muguwar aniya, tun da yayi imanin
cewa shugaba 'Yar Adua baya cikin
hayyacinsa.

A game da yadda zai tunkari warware
dambarwar siyasar Najeriya kuwa
mukaddashin shugaban kasa
Goodluck Jonathan ya ce zai mai da
hankali kan shirya zabe na fisa-bi-
lillahi.


Kuma baya tsinkayen zai tsaya
takarar shugaban kasa a 2011,
kodayake dai a cewarsa "idan suna so
in tsaya, to wannan wani abu ne da
zan nazarta".

Kuma jakadiyar Amruka ta bayyana
masa cewa wajibi ne ya sallami
shugaban hukumar zabe mai zaman
kanta wato INEC, Prof Maurice Iwu
saboda baya nuna wata alama ta
mutunta tsarin mulki na gari.
Jakadiyar ta yi barazanar cewa
muddin Goodluck bai kori Iwu ba, to
gwamnatin Amurka zata janye duk
wani tallafi na shirin zabuka a Nigeria.

Bayanan na Wikileaks sun ce
jakadiyar Amurka ta kuma baiwa
Mukaddashin shugaba Goodluck
shawarar nisanta kansa da tsohon
shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo,
kuma Goodluck ya ce zai yi hakan.

(BBC HAUSA)
www.bbchausa.com

No comments:

Post a Comment