Tuesday, December 14, 2010

MU CIGABA DA SON MATANMU BAYAN AURE

Akwai wani mutum mai suna Balarabe, yana
neman wata budurwa mai suna Ladidi da aure. Kullum
yana zuwa hira gidansu da yamma budurwar
tana kawo masa ruwan sha a duk lokacin
da ya zo gidansu hira.
Wata rana da yazo
sai kakar Ladidi ta ce mata: “Ga kunu mai
dumi ki kai wa Balarabe ko zai sha.” Ladidi ta ce to. Sai
ta zo ta tambayi saurayin cewa zai sha
kunu? Bayan ya yi dan murmushi ya ce "eh zan
sha", sai Ladidi ta koma cikin gida ta dauko
kunun da nufin ta kawo masa. Tana zuwa
kusa da shi sai santsi ya dauke ta ta zame ta
yi tangal-tangal ta fadi, kwanon kunun nan
ya kife a jikin sabon dinkin shadda da
wannan saurayi ya ci ado da ita. Hankalin
wannan budurwa ya tashi, ta rude ta rasa
me za ta ce masa. Amma shi gogan naka bai
damu da jika shi da kunu da ta yi ba,
hankalinsa yana kanta ne, yana cewa: “Ladi
di sannu, ina fatan dai ba ki ji ciwo ba?” Yana ta
kokarin daga ta da lallashinta, ita kuma da ta
tashi abin da ya fi damun ta shi ne yadda ta
bata masa ado da ruwan kunu. Nan take ta
je ta debo ruwa a buta tana zuba masa yana
wanke jikinsa, tana ta ba shi hakuri. Shi
kuma yana murmushi yana ce mata, ai ba
komai. Da ya ga Ladidi tana ta nuna
damuwarta kan abin da ya faru, sai ya nuna
mata alamun cewa za ta bata masa rai, ya za
a yi ta rinka damuwa kan abin da baitaka-
kara-ya karya ba! A haka dai abin ya wuce.
Bayan wani lokaci sai aka daura auren Balarabe
da Ladidi, Allah Ya azurta su da ’ya’ya guda
biyu. Wata rana da yamma Balarabe ya dawo gida
don yin wanka, sai Ladidi ta kawo masa
abinci. Bayan ta ajiye, sai ta je debo masa
ruwa a kofi da nufin idan ya gama cin abincin
ya sha ruwa. Bisa hadari sai ga babbar
rigar da Balarabe ya tube ta sarkafe Ladidi ta fadi
kasa, ruwan da ke kofin ya zube a jikin
Balarabe, ai sai ya mike tsaye ya rinka
bambami, kai ka ce wuta ta zuba masa. “Ke
dai wallahi ban san ranar da za ki yi hankali
ba! Sam ba ki da lissafi da natsuwa! Idan ban
da hauka da rashin hankali, me ya jawo
haka? Ke dai kam Allah wadaran ki........!”
Karshe dai wannan dalilin sai da ya janyo
Balarabe ya saki Ladidi.

Mu yi nazarin wannan abin da idon basira,
lokacin da Balarabe ke neman matarsa da aure,
ta yi masa barin kunu mai zafi a jikin sabbin
tufafinsa, amma bai nuna bacin ransa ba,
hasali ma yana nuna wannan abin ba komai
bane illa hatsari. Amma yau barin ruwan
sanyi ya zama tamkar ruwa narkakkiyar dalma! Mu duba
yadda ya damu da ita a wancan lokacin,
amma yau ba damuwarsa ne ta ji ciwo ko
ba ta ji ba, shi dai kawai laifin da ta yi masa
yake kallo.

Ya kamata Maza murin ka tuna baya lokacin da matayen mu suka saba mana ba kawai mu yanke hukunci a lokacin ba.

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020

No comments:

Post a Comment