Thursday, January 5, 2012

NEMAN 'YANCI BANA RAGO BANE

HAUSAWA wata kabila ce ta daban, wadda Allah ya bata kaifin basira da hasken nesa, ba komai yasa na fadi haka ba, sai tuno wata magana da Hausawan suka dade suna fada wato "NEMAN 'YANCI BANA RAGO BANE" zahiri wannan magana haka take, kuma na tabbatar da hakan da kaina.

Sanin kowane tun ranar da mahukuntan kasar nan suka sanar da kudirinsu na janye tallafin man fetur, al'ummar kasar suka daura haramin zanga - zangar nuna kin jin wannan kudiri, saboda kuwa talaka ne zai kara kuntata da shan wahala bayan wadda yake sha. Hakan ce tasa matasan Kanon dabo musamman daliban manyan makarantu su ma suka fito don nuna rashin goyan baya.

To saboda irin kishin kasa da kishin talaka da yake kunshe cikin zuciyata, yasa banyi kasa a gwiwa ba na shiga cikin wadannan matasa da suka yi dandazo a filin Silver Jubilee Square wannan matasan suka canzawa suna zuwa Liberation Square wato Dandalin 'yanci, wanda yake bai fi nisan kilo mita daya ba zuwa fadar gwamnatin jihar Kano daga gabas daga yamma kuma zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Mun fara wannan zanga - zangar 'yancin ne tun da sayin safiyar ranar Laraba 04/1/2012 wanda muka shafe yinin ranar har zuwa dare ba tare da mun bar motoci suna zirga - zirga ba, a dai - dai wurin da muka mamaye, su kuwa jami'an tsaro sun zuba mana na mujiya gami da kange duk wata hanya da zata sada mu da fadar gwamnatin jihar. Wani abin sha'awa a wannan rana idan lokacin sallah yayi kowa zaiyi alwala sannan a samu liman ya ja sahu mu gabatar da sallah, su kuma wadanda ba mabiya addinin Musulunci ba, suna tsaye suna jiranmu har sai mun idar da sallah.

A haka har dare yayi dare can da misalin 1:45 zuwa 2:00 lokacin babu kowa daga mu sai jami'an tsaro, kawai ba zato ba tsammani sai muka ji ruwan barkonon zuwa (Tear Gas) ganin haka yasa muka ga ya kamata mu maida martani tunda kuwa muna yin wannan zanga - zanga ne ta lumana ba tare da tashin hankali ba. Nan muka fara jifan jami'an tsaron da duwatsu da kuma Pure Water, ganin haka sai suka fara danno mu suna kara har ba mana barkonon tsohuwa, ana haka ana haka, muka samu nasarar fasa musu gilas din motarsu. To fa daga nan sai suka fara harbe - harbe sama, wannan harbe - harbe shi yasa muka karaya muka fara gudun ceton rai, saboda sanin jami'an Nijeriya basu san darajar dan Adam ba.

A karshe dai jami'an tsaron sun samu nasara akanmu, inda suka tarwatsa mu, kowa ya nemi wurin da zai fake don gudun rasa ransa. Wasu daga cikinmu sunji munanan raunuka, wasu kuma sun kwana a tsaye ba tare da kwanciya ko yin bacci ba. Ni dai nayi sa'ar samun mafaka a gidansu wani abokina a Unguwar Kabara.

Ina fatan wannan ba zai sa zuciyoyinmu su karaya ba, zahiri NEMAN 'YANCI BANA RAGO BANE.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

No comments:

Post a Comment