Wednesday, January 25, 2012

MD Abubakar ne Sabon Sifeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya amince da nadin Mohammad D. Abubakar a matsayin Sipeto Janar na 'yan sanda na riko.

Sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara ta fannin yada labarai Mista Ruben Abati ya fitar, ta ce sabon sipeto janar din na riko ya maye gurbin Hafiz Ringim wanda zai soma hutu daga ranar Laraba.

Sannan kuma shugaban Jonathan din ya amince da ritayar duka masu rike da mukamin mukadashin sipeto janar din wato DIG's ba tare da bata lokaci ba.

Nadin sabon shugaban rundunar 'yan sandan ta Najeriya ya zo ne kwana daya bayan wani hari da ake zargin 'yan kungiyar nan ta jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal jihad da aka fisani da Boko Haram da kai wa a kan wani ofishin 'yan sanda a unguwar Sheka da ke Kano.

A ranar Juma'ar da ta wuce, kungiyar Boko Haram ta kai hari a Kanon, inda akalla mutane dari da tamanin da biyar suka hallaka.

Kuma an rika kira ga shugaban 'yan sandan, Hafiz Ringim, da yayi murabus, bayan da wani da ake jin shi ne ya tsara harin da aka kaiwa wani coci a Abuja, kabiru Sokoto ya sullube wa 'yan sanda.

Shugaba Jonathan ya daura wa sabon Sifeto Janar din aikin yin garambawul ga rundunar 'yan sandan kasar domin ta iya shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Jonathan ya kuma nada wani kwamiti da zai sanya ido wajen ganin an kawo sauye-sauye a rundunar da kuma dalilan da suka janyo jama'a suka fidda kauna da rundunar 'yan sandan Nijeriyar.

Masu sharhi a kan al'amura na ganin 'yan sandan Najeriyar sun gaza shawo kan hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram da kai wa a sassa dabam- daban na kasar.

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch ta ce kungiyar Boko Haram ta kashe kimanin mutane 935 tun da ta fara kai hare-hare a shekarar 2009.

Daga shafin BBC Hausa
www.bbc.co.uk/hausa

No comments:

Post a Comment