Monday, January 23, 2012

Wasikar Boko Haram Zuwa Ga Mahukuntan Jihar Kano

Tun bayan harin bama - baman da yayi asarar daruruwan bayin Allah a yammacin Juma'ar da ta gabata a sassan birnin Kano, nake ta mamakin da wata wasika dana rinka cin karo da ita a shafukan gidajen yanar gizo daban - daban, kamar su Nairaland, Sahara Reporters, All Africa, Facebook, Nigeria Information da sauran su. Wannan wasika budaddiyar wasika ce zuwa ga gwamnatin jihar Kano da kuma wasu mutum uku daga cikin manyan mutane a jihar, wadanda ake ganin kimarsu da girmarsu a fadin jihar dama fadin Nigeria baki daya.

Wannan wasika ta nuna yadda kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram ta aikawa gwamnati da wadannan manyan mutane, sakon gargadi akan aka daina kama musu mutane, kuma a saki wadanda suke hannun hukuma, sannan a cikin wasikar sun bayyana cewa idan har ba'a yi musu wannan abu da suka bukata ba to garin Kano zai gamu da munanan hare - hare marassa iyakaci sama wanda yake faru Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Sun bayyana cewa jihar Borno ma, wadda ada ake yi wa kirari da cibiyar zaman lafiya, sun aika irin wannan gargadi kafin garin ya zama yadda yake a yanzu, amma sai hukumomi suka dauki maganar tasu a matsayin wasa. Wanda a cikin wannan wasika suka rantse da girman Allah mahaliccin samai da kasai, wadda ya aiko annabawa da manzanni tun daga kan Annabi Adamu (A.S) har zuwa Annabi Muhammad (S.A.W), akan cewa ba wasa suke ba.

Sun ce sun dade suna yungurin kawo hare - hare jihar ta Kano domin daukar fansar mutanensu da aka kashe a shekaru biyu da suka gabata a garin Wudil, amma saboda darajar manyan malaman da suke cikin garin na Kano shi yasa suka daga kafa, sanadiyyar hakan ne ma yasa suka dauki matakin aiko da wannan wasika, domin mahukunta su dauki mataki.

Wani abin mamaki da daurewar kai, shi ne wannan wasika ta Boko Haram sun aika ta ne tun a wata takwas (August) na shekarar da ta gabata 2011. Amma gwamnati da sauran wadanda aka aikawa wannan wasika basu dauki matakin biyawa wannan jama'a bukatun nasu ba, kuma basu dauki matakin kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu ba.

Tambaya anan itace: Shin gwamnatin jihar Kano da wadanda aka aikawa wannan wasika su ma sun dauki wasikar ne a matsayin wasan yara kamar yadda hukumomin jihar Borno suka yi? Ko kuma wasikar ce ba tazo hannunsu ba, bare su san matakin da zasu dauka? Zahirin gaskiya idan wannan wasika da Boko Haram ke ikarin sun aiko musu tazo hannunsu amma basu dauki matakin komai ba, to su ma sun bada muhimmiyar gudunmawa wurin je fa al'ummar Kano a wannan mummunan hali na tashin hankali da muka tsinci kanmu ciki da kuma asarar daruruwan rayukan bayin Allah wadanda basu ji ba kuma basu gani ba.

Ya Allah ka kawowa jiharmu Kano da kasarmu Nigeria zaman lafiya. Ya Allah ka taimaki shugabanninmu Ka nuna musu hanyar gaskiya Ka kuma basu ikon binta, Ka basu ikon yi mana adalci. Mu kuma mabiya Ka bamu ikon binsu da yi musu biyayya.

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

1 comment:

  1. Allah ya bamu lafiya da zama lafiya a jiharmu da kasarmu Nigeria.

    ReplyDelete