Friday, January 20, 2012

Al'ummar Kano Na Neman Addu'arku

Zahiri mu jama'ar Kano muna neman addu'arku, sanin kowa ne Kano gari ne mai dumbin al'umma sama da mutum miliyan hudu ne ke cunkushe a cikin kwaryar birnin na Kano, wanda kuma kaso 98% dukkanmu Musulmai ne kuma Hausawa.

A yammacin wannan rana ne, wani abu ya faru wanda mu jama'ar Kano zamu iya cewa bamu saba ba, ko ma muce bamu taba ganin irin hakan ba. Ba komai ne ya faru a Kanon ba sai tashin wasu bama - bama a wasu sassan hukumomin tsaro a cikin birnin na Kano, wanda ya kawo asarar rayukan da har yanzu ba'a tabbatar da adadinsu ba.

Wannan tashin bama - bamai ba karamin je fa mu cikin tashin hankali yayi ba, musamman bayan da bama - baman suka tashi, sai kuma harbe - harbe da ihun jiniyoyin jami'an tsaro, abin kamar a filin yaki. Wannan harbe - harbe shi yafi komai tayar mana da hankali.

Jama'ar Nigeria da sauran na sassan duniya baki daya muna rokon addu'arku ne saboda tashin bom a birnin Kano ba karamin asarar rayuka da dokiyoyi zai haifar ba, saboda yawan al'ummar birnin kuma a cunkushe wuri guda kamar yadda na fada a baya.

Ya Allah ka kawowa jiharmu Kano daukin gaggawa, da sauran jihohin da irin wannan abubuwa ke faruwa. Ya Allah ka bamu zaman lafiya a jiharmu da kasarmu Nigeria baki daya.

No comments:

Post a Comment